Showing 87001 words to 90000 words out of 170049 words
wanda kike so ba damuwa ta nace da hakan da nakai wani loƙaci da na ɗaukar wa kaina zan sake ki ko anaso ko ba'aso yanzu ma akwai dalilin da yasa bazan sakeki ba, loƙaci na cika zan sallame ki kije ki zauna da duk wanda kike so,
Dan haka kidaina damun kanki da wannan haukan da kike dan ke zaki wahalar da kanki abanza kinawa mutane hauka acikin gida ki shiga taitayin ki in bahaka ba kuma zan ɗau ƙwaƙwwaron mataki akan ki, kuma in hanaki kula sa kuma inƙi sakin sai inga yanda zakiyi stupid girl ger out before in karya miki ƙafa anan gurin sannan kuma idan kincika ke mahaukaciya ce kije kigayawa wani duk yanda mukai dake kinga mai zai biyo baya,
Bata kulasa ba duk abun da yake tayi gaba,
Sai yaƙara dakatar da ita tare da cewa come back ki saita nutsuwar ki kifita cikin hankalin ki idan kika saɓa ɗaya daga cikin abubuwan da nagaya miki na lahira sai yafiki jin daɗi kinji ni,
Kai ta ɗaga masa,
"Baki da baki ko ni da kai nayi miki magana, .nanma girgiza masa kai tayi sai kuma tayi saurin cewa eh,
"Hmmm I will teach you lesson very soon get out,
Da sauri tayi gaba ta buɗe ta murɗa muƙullin ta buɗe ƙofar tana buɗewa sai ga Su Maama duk sunyi tsatstsaye agunn wasu sun doka tagumi saboda tun suna kiran sa suna buga ƙofar har suka gaji suka tsaya, suka zubawa sarautar Allah ido suga iya gudun ruwan sa,
Tana buɗewa duk sukayo kanta saidai kuma ganin ta babu alamar duka ko wani abu ajikin ta na alamun dai ba wata cutar wa, akusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya,
Dadda ce ta fara tarar ta ta jawo ta daga bakin ƙofar,sai ta shiga duddu bata tana cewa badai abun da yayi miki koh bai dake kiba, su Maama duk tambayar ta suka shigayi kowa da kalar tasa tambayar,
Itadai Ameesha shiru tayi inbanda kallon su babu abun da take ga kanta dake mata ciwo, Saida taga basu da niyar barin ta, sannan tace "nifa lafiya ta ƙalau babu abun da yayi min ku kwantar da hankalin ku munsasan ta kanmu Allah yabamu zaman lafiya, shikenan dai ko haka kuke sonji koh dan haka dan Allah abar duk wata magana, abarni in huta haka, kowa ma ya huta, tana kaiwa nan ta bar gurin ta tafi ɗakin su,
Oh gaba ɗayan su da ido suka bita dan basu taɓa ganin tayi magana irin haka ba, gashi kuma da yanda ya ɗauke ta ya shiga da ita tana mahaukacin kuka amma yanzu tafito bata kuka kuma tace "babu wata matsala sun amince mai hakan yake nufi saboda da dagaske ne da bazatayi kuka ba, gaskiya da wata a ƙasa,
Maama ce ta kalli su Azeema tace "kuje wajen ta,
Suna tafiya Maama ta kalli Papa tace "ya kake ganin yaran nan zaman su kuwa zaiyiyu baza araba auren nan ba kuwa, dan nasan yarinyar nan hakan bazatayi wannan furucin ba akaran kanta saidai idan shi yayi mata wani abun kuma ya hanata faɗa dan banga alamun yarda ba'attare da itaba ina ginin tusrsata yayi ta faɗi hakan,
Da sauri Fadada ta karɓeta da cewa "A'a bai kamata kiyi wannan batun ba, aure aringa an ɗaura kawai abar su, zasu sasanta wataran, abari muga yana zaman nasu kar wanda yaƙara yi Musa maganar mu basu zuwa wani loƙaci mugani zasu canza ko kuw,
Papa yace "hakane ne maganar ki gaskiya nuna daman bazan taɓa yarda a warware wannan auren, bare ma kuma mahaifinsa bazai taɓa yarda ba, saidai kawai mubi su da addu'a idan zaman su alƙhairi ne Allah ya ɗorar dashi idan kuma ba alkhari bane Allah yayi musu zaɓi nagari,
"Ameen" su Maama suka amsa masa......,
Daga nan dadda ta koma ɗaki wajen Ameesha su kuma su Papa suka koma cikin ɗaki,
Dadda na shiga ɗakin ta tarar da su akan ta tana ta kuka suna bata haƙuri, sai ta ƙarasa gurin tare da cewa duk su fita zatayi magana da ita, basuyi mata musu ba duk suka fita waje Hamra da Amra da kuma sumy suka cewa Azeema bari suje can part ɗin ita kuma ta zauan Rasheeda kuma tun loƙacin da Meera ya fita Khalid yabishi bai same sa, shine ya dawo ya kaɗa kanta yace su tafi zatayi masa gardama saida ya nuna mata ɓacin rai sannan babu yanda ta iya ta tashi suka tafi batare da taji zancen auren ba ta tafi gida.......,
har zuwa dare babu wanda ya ƙara fitowa waje kowa na ɗaki,
Wajajen ƙarfe takwas, wani bafade yaje sashen sarki akayi masa iso da shi, bayan sun gaisa yake sanar dashi sunyi babban baƙo daga masarautar Gombe yazo,
Nan akace a shigo dashi, amma da ya shigo Abu yaga baisan shiba sai yace akaisa gurin Papa,
Can part ɗin aka nufa dashi yana zuwa can aka kira Papa suka fito tare da Maama, Papa na ganin sa, ya ɗan saki fuskar sa, yana cewa a'a ashe babban baƙo mukayi adaren nan daga ina haka, dariya mutumin yayi yace Allah ja da ranka wallahi bansamu fitowa da wuribane shiyasa nayi dare,
Papa yace "to lale marhaban bissmillah mu zauna nan mutumin ya zauna suka shiga gaisawa ya gaida Maama itama tana ƴar fara'arta ta amsa tace kwana da yawa AYUBA rabon dan naganka tun kana sarauyi kodan bana nan shiyasa bana ganin ka,
Papa yayi saurin cewa ai yafi shekara biyar inajin rabonsa da nan yanzun ma dan ankirasane kuma anci sa'a yazo amma da bazaki gansaba,
Haba Papa ai ina ɗan leƙowa idan na shigo garin kawaidai idan nazo yaya SA'ADATU bata haɗa mu sai tace baka nan, amma ina shigowa,
"Dan kaga bata nan shiyasa zaka fake da ita ko, cewar Papa
"A'a wallahi Papa, gaskiya nake faɗa,
"To shikenan yanzu dai muje abaka masauki tunda de yanzu dare yayi gobe sai muyi maganar duk da kasan komai dai amma gobe aƙara yi maka bayanin sannan akaika har gidan sa ɗayan kuma yana nan gidan zuwa da safe zaka gansa, sai ku tafi gidan yayan nasa kusame shi acan sai kuyi maganar ko,
"Eh to shikenan papa Allah ya kaimu goben,
"Ameen, daga nan Papa yasa aka ɗauke sa akace akaisa masauƙi...,
**************************
Rasheeda na gaban mom ɗin ta tana ta bata labarin Meer da yanda taga Ameesha agidan saidai kuma har ta taho batasan alaƙarta da gidan,
Suna zaune suna ta hirar Dady yashigo falon ko sallama babu ya shigo kamar anjefo sa, haka ya faɗi ciki, kana ganin sa kasan babu kwanciyar hankali a tattare da shi,
Mom ce tace "kai kuma lafiya kashigo ko sallama babu,
Rasheeda kuma ganin sa yasa ta tashi da sauri cike da murna tace "Dady yau nagan sa naje har gidan su nagan sa, tayi maganar tana shirin faɗawa jikin ta,
Abun mamaki sai kawai ya daka mata tsawa yace "matsa kiban guri yana kaiwa nan yayi gaba cikin sauri ya fara hawa bene wajen step biyu yake takawa,
Yana hawa ya zaro yaje wajen wata drawer ya buɗe ya zaro waya tare da kunna ta yafara daddanna wa ya lalubo wata number ya kira amma wayar akashe sake gwadawa yayi cikin Sa'a kuwa ta shiga, har kiran ya katse ba aɗaga ba, yana ƙara shirin kira saiga kiran ya shigo, da sauri ya ɗaga ya kara a kunne ba sallama ba hello ana yana ɗagawa yace "burin ki ya cika gashi nan yanzu anzo an ɗauke sa bansan inda yake ba tun farko saida nace miki muka she shi amma kiƙa ji yanzu to mutanen da wancen ɗan iskan yaron ya kwashe su wataƙil an haɗa baki da su anje har can an ɗauke sa,
Shiru yayi yana sauraron abun da ake cewa daga can, tsawon ƴan sakanni sannan yace "aure fa mai yasa kika bari ya aure ta, kuma Ni ina miki wata maganar hankalina duk ya tashi amma ke naga ba alamun hakan, shiru ya ƙara yi sannan yace,
"Ah dole kice haka mana idan anrabu dashi da suka ɗauke sa kinsan dai dole nan zasu kawosa, kuma zai faɗi duk abun da yafaru dashi, kodan kina tunanin bai san fuskar ki ba shiyasa hankalin ki akwance to wallahi kisani muddun asirina ya tonu kema saina tona miki asiri kisan da wannan, dan haka tun wuri ki baza ido kisa agano miki inda suke tunkan ya shiga cikin gidan akawar dashi in ba haka ba kuwa akwai matsala ke kinsani kuma kece a ruwa danni ko yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba,
Shiru ya ƙara yi tsawon loƙaci yana ta sauraron abun da ake cewa kafin daga bisani yace to shikenan Allah yakaimu goben zamu gani idan bakiji ana maganar saba ko kuma kisawa yaron ido ki gano idan da abun da yake shiryawa sai ki sanar dani in ƙara turo wasu mutanen duk motsin sa idan ta fito ana sanar min, ta haka kawai zamu gane sune suka ɗauke sa ko kuma wasune daban ko kuma guduwa yayi, koma dai meye nasa a bincika min cikin garin indai yana cikin garin zai bayya na,
Sannan abu na ƙarshe ki shirya gobe zamu tafi Gombe dan dole sai munje da kanmu.....,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI SAMEER💅
(DA ZAFI ZAFI)
By
❤️Yaya Azeema❤️
*BOOK* 3️⃣
*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*
*_Typing........✍️✍️_*
_Washe gari,
Kamar yanda Papa yayiwa baƙon sa ɗan garin Gombe alƙawarin zuwa da safe zaisa arakasa, hakan ce ta kasan ce,
Safiya nayi Papa ya aika aka kira sa yazo falon, tare sukayi breakfast dashi bayan sun gama ne akaje aka kira Hamza,
Hamza na shigowa ya samu waje ta zauna tare da gaidasu gaba ɗayan su,
Bayan sun gama gaisawa sai Papa ya kalli Hamza yace "malam Hamza wannan bawan Allahn da kake gani nasan baka san shiba, amma ɗan uwan ka ne daga can garin ku yazo shiɗin dangin mahaifin kane, an bashi labarin komai dan haka yanzu zaku ji gidan yayan ka zai gansa, zasuyi magana daga nan sai ku tattara ku je can garin dan magana har ta riga taje can,
Shi wannan shi zaiyi muku jagora saboda duk wani shedu suna hannun mahaifiyar sa kamar yanda SA'ADATU ta faɗa agurin ta zaku karɓi shedun zaku fara yin gaba inyaso daga baya mu sai mubiyo ku sai aga wanda ya dace ya hau kan kujerar sai ku sansan ta a tsakanin ku, kafin zuwa wani satin zamuzo Gomben yanzu ma abun da yasa bazamu tafi tare ba saboda wasu ƴan matsaloli gashi kuma naɗin da akayi jiya jiya bazai yiyu mutafi gaba ɗaya ba amma dai zamuzo, ina fatan ka gane,
Ɗan sunkuyar da kansa Hamza yayi yace "Eh nagane Papa amma Ni dan Allah ina neman wata alfarma abarni anan sude suje amma ni bana jin zan iya zuwa garin nan abarni in cigaba da rayuwata ahaka sai yafi yamin kwanciyar hankali,
"A'a malam Hamza wannan buƙatat taka kuwa bazata karɓu ba dole ka koma can saboda ƙwatowa mahaifin ka ƴanci da dawo da martabar masarautar ku barin ta haka ba daidai bane ka manta da duk wani abun da yafaru ka ɗauke sa matsayin jarrabawa haka Allah ya tsara maka taka rayuwar sai ka watsar da komai ka runguni gaba kuma, kada tunanin abun da mahaifayar ka tayi abun yasa kaƙi amincewa itama duk tayi ne saboda farin cikin ku saboda ta same ku duk dan saboda daku tayi komai yakamata ka kwantar da hankalin komai ya wuce kaji ko ka tashi kuje kar loƙaci ya ƙure muku dan ayau nake son ku tafi,
AYUBA ba ma yace "yaro ai wanna maganar ma bata taso ba zuwa ai yazama dole kai ko ba ace kaje ba ai yakamata kaje kaji komai yake faruwa, kaji ka taimaka kaje ka manta da komai kaji yaro,
Papa da AYUBA suka haɗar masa suna ta nusar da dashi gaskiya da ɗora sa ahanaya,
Cikin sanyin murya batare da yanaso ba ya amsa da to, daga nan dai suka ɗan ƙara tattaunawa sannan sukayi musu sallama suka tafi gidan su Bossay....,
Maama da Papa ne kaɗai suka rage a falon bayan fitar su, sai kuma suka fara tattaunawa akan maganar Meer da Ameesha,
Maama ce tace "ai insan sun wata basu san wata ba badai tace sun sasan ta kansu ba, zasu gani tattara su zanyi su koma wani gidan ko ya kagani ina ganin kamar hakan sai yafi,
Ɗan jimm Papa yayi yana tunani na ƴan daƙiƙu kafin daga bisani ya ɗan numfasa yace "eh to hakan kamar yayi kamar kuma baiyi ba ba kya ganin zai iya cutar da ita idan yagan sa daga ita sai saishi dan gani nake kamar ta faɗa ne bawai hakan gaskiya bane,
"Nima nayi tunanin hakan amma tunda har sukace haka sai arabu dasu muga iya gudun ruwan su wannan yaron inba hakan akayi ba banga ranar da zaiyi aure ba inaji saidai yagama rayuwar sa, ahaka, amma yanzu tuna muka haɗa su sai kiga ansamu sauyi idan Allah ya taimake mu, sai muci gaba da yi musu addu'a Allah ya haɗa zuƙatan su waje guda Allah yasa mu samu abun da muke nema,
"Ameen" papa ya amsa mata dashi tun aloƙacin suka kira Abu suka sanar dashi shawarar da suka yanke shima kuma yabasu goyon baya, amma sun bari sai sun nemo masa gida anan kusa dasu ko kuma agina masa nasa anan cikin masarautar yanda zasu fi saka masa ido da kyau idan yayi ba daidai su nuna masa ɓacin rai, suna ganin hakan shine mafita, da wannan shawarar suka tashi daga falon, Maama ta wuce ɗaki shi kuma Papa ya fita, dan zuwa cikin fada....,
Maama bayan ta shiga ɗakin ta sai kuma ta fito, ɗakin su Ameesha ta dosa, tana ƙarasawa ta tura ƙofar ɗakin ta shiga tare da yin sallama, suna zaune kan gado Ameesha da Dadda Ameesha ta ɗora kanta akan cinyar Dadda, Dadda tana tsefe mata kalbar dake kanta, sunayi suna ɗan hira sama sama, Dadda. nayi mata ƴar nasiha akan auren da akayi musu tana nusar da ita suna cikin haka Maama tashigo hakan ne ya dakatar da ita,
Da fara'ar ta Maama ta shiga ciki tana cewa, yau jikar tawa ko ganin ta banyi ba lafiya har muka gama karyawa banga ƙyeyar ki ba ko fushi ake damu har yanzu ne,
Ɗan yunƙurawa Ameesha tayi ta tashi daga kan ta, ta zauna a gefen Dadda tare da ɗaukan hular ta tasaka akan ta, sai kawai ta sunkuyar da kanta ba tace komai ba, dan wani irin shiru da rashin magana take ji dashi daga jiya zuwa, dan ko da Azeema ta tashi tafiya ko rakata batayi ba kuma bata hana ta tafiya ba, ba kamar da ba, da ace hakannanne bazata barta ta tafi ba ta ringa roƙon ta kar ta tafi amma jiya tana cewa zata tafi tace "to", daga nan kuma bata ƙara cewa komai ba ta juya ta kwanta,
Duk yanda Maama taso ta saki jikin ta amma taƙi saki, da taga haka sai ta kamo hannun ta tace "jikata zo in aike ki kikaiwa mijin ki abinci ke haka ake kula da miji ina kule dashi inajin rabonsa da abinci tun shekaran jiya, ya kamata ki fara kulawa dashi ki taimake shi yaringacin abinci, tundade kun daidai ta kanku,
"Wata iriyar faɗuwar gaba Ameesha taji loƙacin da Maama take waɗannan maganganun, hakan har saida yasa ta ɗago a fusace ta kalle Maama,
Maama kam taga hakan kuma ta karance ta amma sai ta basar kamar bata san tanai ba, tasaki murmushi tace "da kanki jiya kika ce kun sasanta kiga kuwa dole ki bashi kulawa oya taso taso muje tafaɗa tana jawota daga kan gadon,
Dadda de sai dariya take musu tana cewa "shalele na me yasa kike hakane ko duk kin manta nasihar danayi miki ne,
Bata samu amsa ba suka fice daga ɗakin, suna fita itama ta tashi ta shige banɗaki da saƙe saƙe kala kala aranta, wai yau Ameesha ce da aure mai iko abun da bata taɓa kawowa ba, nan kusa, a fili tace Allah yasa kiga mahaifin ki shalele na tana faɗa ta saki murmushi tare da ƙarasa shigewa bayin.......,
Maama suna fitowa bata sake taba har saida suka shiga kitchen sannan ta saketa, da kanta ta ɗauko try ta ɗan harhaɗa abun da tagani saboda sukaɗai sukayi breakfast ɗin basu wani ci mai yawa wasu abubuwan ma ba abuɗe suba, haka ta haɗa masa kala kala, ta bata tace takai,
Ameesha ba musu kuma tunda suka fito bata ce mata komai ba har ta bata ta juya ta nufi ɗakin nasa, duk da gaban ta na dukan uku amma haka ta daure saboda bataso su Maama su gane abun da ta faɗa ƙarya take shiyasa duk take binsu aduk yanda suka bi da ita,
Nocking ɗin ƙofar tayi tana jiran abata umarnin shiga,amma sai taji shiru zata ƙara bugawa kenan Maama dake bayan ta tace "wane irin bugu ne haka kishiga mana kawai wataƙil bacci yake basai ki tashe shi ba,
Nan madai shiru tayi ta tura ƙofar ta shiga kai tsaye, tana saka ƙafar ta maganar sa da yayi mata kashedi ta shiga yi mata yawo akai _tashi kiban waje kuma kar ki ƙara zuwa inda nake ko a hanyar fakon nan banaso muhaɗu kinjini koh_
ji tayi kamar ta juya sai kuma ta tuna idan ta koma kuma ai Maama na nan to yazatayi, yau tana tsaka mai wuya yace kar ta sake zuwa inda yake kuma gashi Maama ta kafa ta tsare ta turo ta, idan ta koma me zata ce mata, komawar ta kamar tonuwar asiri ne,
Damƙe idon ta kawai tayi ta ƙarasa shiga saboda bata