Showing 111001 words to 114000 words out of 170049 words

Chapter 38 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7226

sannan tayi wanka tayo alwala ta fito tana ta faman sassada kai ƙasa, gashi kanta nayi mata wani irin ciwo gefe guda, haka tayi sallar a daddafe sannan ta rarrafa ta koma kan gado ta kwanta, Allah ya isa kam ta jawa Meera ita ba adadi, gaba ɗaya ta gama cika da jin haushin sa, jitayi ta tsanesa ma gaba ɗaya,

Itama wahalallan ba ci ga ɗauke ta,

Duk wani motsin ta Dadda nasane da ita ta rabu da ita kawai, saboda daman suna sane ita da Maama suka tura ta kuma taga alamun kamar, burin su ya ciga, dan ta fahimci wani abun ya faru tsakanin su tunda ta ganta da asuba haka, tasan dai ba babban abun  ya faru ba, tunda ta ganta tana tafiya da kanta ta.......,


Bayan gari ta waye sosai har ankawo musu breakfast gaba ɗayan su har su Abban Ameesha, ko da akazo cin abincin babu Meera babu Ameesha suna can suna bacci, su kuma su Ma'ana dake sun san me suka shirya, sai suka rabu dasu babu wanda ya tashe su, acewar su basu samu bacci ba shi yasa suke baccin wahala,, aka barsu dan kansu sa tashi,

Ameesha nata tashi amma sai ta kasa fitowa tayi zaman ta aɗakin, har ɗaki Dadda ta ta kawo mata abincin ta, harda su lallaɓata, ita abun har mamaki ma yaso yabata gashi basuyi maganar komai b, kuma Dadda nata rawar ƙafa,

Meer kam tun kan ta tashi ma shi ya tashi babu wanda yagansa ya fice daga gidan ma gaba ɗaya, sakamakon kiran da a Khalid ya kirasa, .......,
[15/11, 10:53 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

                         *_🅿️41_*

...........Tun adaren jiya su Dadyn Bossay suka dira a garin kano inda direct suka wuce da Ayuba asibitin su Sam, cikin mawuyacin hali,

Nan danan lokitoci suka rafar masa aka fara basa taimakon gaggawa, dan halin da yake ciki yana daf da rasa ransa,

Koda gari ya waye ma bai farfaɗo ba, sun rasa gane kansa,

Saida Meer ya shiga gurin da aka kwamtar da shi ya shiga yi masa nasa duban, amma har gari yafara haske bai Ayuba, bai farfaɗo ba, amma dai ansamo kan matsalar ƙwaƙwalwar sa ce ta bugu inda ake sa ran koda ya farfaɗo ba lalle bane ya farfaɗo cikin hankalin sa zai iya samun wata matsalar daban......,

Cikin masarauta kam da wajen ta, maganar bayyanar Abban Ameesha ta gama bazuwa wasu na ta zuwa suna ganin sa, ƴan cikin masarautar kam kowa sai kulawa ta musamman ake basa, Ameesha ma, zuwa yanzu ta ɗan saki jikin ta, tana gurin su Amra ma, suna hira tare da Azeema da tunda taji labari ta iso gidan tundan domin taya ƙawar ta murnar bayyanar mahaifin ta, suna zaune harda sumy da har yanzu bata koma gida ba, itama saboda momma ta hanata tafiya,

Fulani kam saboda farin cikin ganin Abban Ameesha, kunsan ta zauna da shi tana matuƙar sonsa, saboda shima, take son Sam har ta dawo dashi part ɗin ta yake zama, saboda ta rasa, Abban Ameesha, dan a loƙacin ma kusan kullum yana gurin ta saboda soyayyar da take nuna masa,

To har yanzu soyayyar tana nan dan haka ta roƙi Allah Annabi ya dawo part ɗin ta, da zama zata basa kulawa marar misaltuwa dan bataso yaƙara nesa da ita, yanda take jin ƙaunar sa aranta, ji take kamar ita ta haife sa,

Ba jayayya kuwa Maama ta kuma aminta da ita akaro na biyu, shima kuma Abban Ameesha, ya yarda saboda yanda yaga tana nuna yanda take son sa sai yaji shima matar ta kwanta masa ya amince zai koma, daman ɗakuna biyu ne aciki, daga na Sam sai extra bayan nata da take dashi a can ciki,

Nan ta ɗau alƙawarin zata sa a canza masa komai na ɗakin ya faɗi kalar da yake so,

Su Dadda da Maama suna cike da farin cikin tarkon da suka haɗawa musu, kuma nan suka sake yanke shawarar nan da sati ɗaya zasu tattara su a ware musu part ɗin su daban, koda gina musu ne, sai ayi, sai kuma Papa ma yace kawai za'a kwashe kayan part ɗin Ammah dai su kuma can, tunda yanzu babu kowa aciki,

Su Maama kam sunji daɗin hakan, tun aranar suka fara shirye shiryen yanda za a fara gyaran part ɗin,

a ranar wunin dai wuni sukayi suna hira, amma ba Meer dan har yanzu bai dawo ba, ita kuma Ameesha tana can part ɗin su Amra,

Amma sauran duk suna tare, Fulani, Dadda, Papa, Maama, ummy, Abuu, sai Abban Ameesha da suka saka a tsakiya, kowa yana kallon sa cike da so da ƙauna......

labarin Ayuba baizo musu ba sai can da yamma Sam ya dawo cikin masarautar yake sanar dasu duk abun dake faruwa da accident ɗin da Ayuba yasamu, dan duk atunanin su accident yayi ba bugesa akayi ba, anan shima yake jin labarin bayyanar Abban Ameesha,  ya nuna farin cikin sa sosai,

Bayan anyi sallar magriba suka tattara gaba ɗaya suka je suka duba sa, har zuwa loƙacin bai farfaɗo ba,

.........Wuni guda da Meer ya fita suna tare da Khalid amma hakan nan sai ya tsinci kansa da kasa basa labarin abun da yafaru tsakanin sa da Ameesha amma loƙaci zuwa loƙaci takan faɗo masa arai da tuna moment ɗin su na daren jiya,

A gidan da suka ajiye mutanen da suka kamo loƙacin da ya tura su Ameesha nan, yaje ya ƙara lugudar su tare da sawa aka tura su can police station ɗin su Khalid,

Tare da Khalid suka tafi shikuma ya tsaya a gidan bai bisu ba,

  Mutane  biyun kuma da ya kamo daga gidan su Rasheeda yaran Dady, su kuma yaja su wani ɗaki suka tattauna game da abun da suka sani akan sa, amma ga mamakin sa sai suka ce masa kawaidai idan ƴarsa tana son wani abun ko kuma wani abun yasamu ƴarsa, ko kuma idan yana son akawo masa wani, to sai suje su ɗauko masa, shikenan aikin da suke masa, amma dai suma kansu sunsan da abun da yake yi marar kyau kuma yana da wasu yaran bayan su, wanda su kuma basu san aikin da suke masa ba,

Nan Meer yace zai basu aiki su koma gidan nasa sannan su saka masa ido akan duk wani shige da ficen sa, sannan duk yanda za suyi yanaso su kawo masa wayar sa, zaiyi bincike a ciki, musamman awaɗan nan ƴan kwanakin yafiso su kula dashi sosai, suga inda zaije da inda yake zuwa,

Nan suma sukayi masa alƙawarin in Allah ya yarda zasu kawo masa, wannan abune mai sauƙi agurin su, sudai burin su kar ya cutar dasu yasa kuma a ƙulle su,

Daga nan Meer ya fito daga tare da su suka wuce can gidan su Rasheeda ɗin shi kuma  ya nufi gida, yana kan hanya, Abuu ya kira sa yana tambayar sa ina yake yace yana kan hanyar dawowa gida,

Yace to yayi sauri ya dawo Uncle ɗin sa yana kiran sa, sai tambayar sa, yake nan yace gashi nan yanzu zai ƙaraso,

Yana cikin tafiya yashigo cikin wata unguwa bayan yasha kwana yana hawa kan titi sai kawai yaga gifatawar wannan tsohon da ya taɓa gani akan mashin shi kuma ya shiga wani lungu,

Da sauri ya taka birki tare da karya kwana yabi inda yaga tsohon yayi, amma abun mamaki sai yaga baigan saba, tafiya yaci gaba da yi amma sai yaga hanyar ta rabe biyu tunanin hanyar da zaibi ya tsaya yi, sai kawai ya yanke shawara yabi wata, sai yaga layin bama ya fita, dawowa yayi yabi ɗayan layin, baiyi nisa ba yaci karo da wani mashin ɗin a fake a gaban wani shago, daga inda yake yayi parking ɗin motar ya fito, ya nufi wajen,

Yana zuwa yayi sallama cikin shagon a tunanin sa ko zaigan sa acikin amma sai yaga wayam,

Mutumin cikin shagon ne yace malam lafiya me za'a baka,

kallon sa Meer yayi kasaƙe kamar bazaiyi magana ba, sai kuma yace wani tsoho nake nema wanda yayi parking ɗin wannan mashin ɗin,

Ɗan leƙowa mutumin yayi yana leƙen mashin ɗin tare da fitowa daga falon yana cike da rashin fahimta, yace wannan mashin ɗin ai nawane babu wanda yayi parking ɗin sa yanzu,

Wata uwar harara Meer ya jefe masa batare da yace koma ba,

Tuni kuwa cikin bawan Allah nan ya ɗuri ruwa dan ya tsorata da irin kallon da yaga Meer yana binsa dashi,

Cike da tsoro mutumin ya haɗiyi yawu a boye, yana muzurai ido yace "gaskiya na gaya maka wanann mashin ɗin nawa ne ba nawani bane, idan kuma baka yarda ba bari inkira maka wani anan shagon ka tambaye sa kaji yana faɗa yana shirin juyawa ya zaije shagon dake gefan sa,

Hannu Meer yasa ya dawo dashi baya, yana dawo dashi ya ɗaga hannu ya kira masa mari, tare da nuna sa da yatsa yace "kar ka nemi ka ɓata min loƙaci ranka zaiyi mummunan ɓaci, ka gaya min gaskiya ina mutumin nan yake,

Kuka bawan Allahn nan ya fashe dashi yana dafe gurin da aka mare sa, yace "nifa bansan wanda kake magana akai ba na gaya maka wannan mashin ɗina ne,yana maganar yana goge hawayen fuskar sa, yana faɗar haka ya ɗaga murya yace "Sulaiman! Sulaiman!! yakira sunan sa cike da rauni da muryar kuka,

Daga can cikin shagon na ciki ga amsa da "Na'am Bello, ya amsa tare da fitowa da sauri jin muryar maƙocin nasa ba kamar yanda yasaba jin ta,

Yana fitowa yaga abun dake faruwa ya tako da sauri yazo gurin yana kallon yace "Bello me yake faruwa naganka kana kuka, bawan Allah me yake faruwa, yafaɗa yana maida kallon sa kan Meer,

Cike da tsananin damuwa wanda aka kira da Bello yace "Sulaiman dan Allah wannan mashin ɗin waye,

Da mamakin tambayar da game masa yake kallon sa sannan yace "kamar ya wannan wace irin tambaya ce naka ne mana, ko haka akace na wanine,

"Eh gashin nan kagaya masa yazo ya sameni kawai yace wai sai na fito masa da wanda yayi parking ɗin mashin ɗin yake, nace masa ni babu wanda yazo shago na, mashin kuma nawa ne amma yaƙi yarda shine harda su marina, yaƙara sa maganar cike da taƙaicin marin da akayi masa,

"Allah sarki, bawan Allah wannan mashin ɗin sane nima kuma ina cikin shagon nan banji ƙarar wani mashin ba, da sai ince maka, ko wani mashin ɗin kake tunanin ya biyo ta nan, amma wannan muna tare babu wanda yazo, in kuma baka yarda ba, mushi ga ciki ka duba cikin shagon ka gani,

"Muje, Meer yafaɗa yanayin gaba,

Kallon kallon suka shiga yi a tsakanin su, cike da fargaba, da tashin hankalin abun da zai faru, cikin su duk ya ɗuri ruwa basu taɓa tunanin zai iya cewa suje ya duba ba, sun ɗauka idan suka gaya masa haka zai haƙura ya juya,

Saboda tsoro duk sun kasa ɗaga ƙafa su bishi, har saida Meer ya juyo yace "me kuka tsaya yi to, har suna gware wajen juyawa suka shiga tafiya da sauri wanda aka kira da Sulaiman yana cewa "a'a babu komai muje muje na tsaya ne inayi masa sannu yace gurin da ka mare sa zafi yake masa,

Meer bai tanka masa ba ya juya, dan yagama karantar su basu da gaskiya duk yanda akayi,

yana taka ƙofar shagon Bello yayi saurin shan gaban sa yace "kaga nafa ce maka babu kowa aciki kar ka shigar min shago,

Ɗayan ma ya zagayo kusa dashi yace "Bello ka barshi mana ya shiga aidai bazai maka sata ba, iyakaci fa ya duba, yana faɗar haka ya janye Bello daga gaban Meer,

Meer ya girgiza kai yana ƙara tamke fuska dan hakan da yayi yaƙara tabbatar masa da bashi da gaskiya ɗin tsohon yana cikin shagon dan haka bai tsaya bi takan saba, yabarwa kansa idan ya kamo tsohon ya dawo yaci masa uwa akan ƙaryar da yayi masa,  sai kawai ya danna kai cikin shagon,

Zaro ido Bello yayi yana ɗora hannu akai, yaƙara yunƙurin zai bisa, Sulaiman yayi saurin riƙe sa, murya can ƙasa ƙasa yace "wai kai meye hakan karabu dashi mana duk kabi ka tashi hankalin ka meye idan yagani, yasan kane mtswww ni wallahi kama bani haushi,

na shiga cikin shagon yaga babu komai sai kayayyakin daga can lungu ya hango wani guri kamar an saka masa wani abu kamar buhu kamar fatar danƙo anyiwa wajen labule,

A hankali ya shiga takawa zuwa wajen yana zuwa yaɗaga hannun sa ya sauke akan labulen, yana shirin ɗaga sa kenan yajiyo wata siririyar muryar mace daga ciki tana cewa, baby wai me yake faruwa ne dan Allah kayi sauri kasan dai bazan iya tasowa ba, baka gama ba, wai waye ma yazo ya katse mana jin daɗin mu, dan Allah kayi haƙuri, wallahi a matse nake,

Jin hakan yasa Meer janye hannun sa daga kan labulen da sauri yana yarfar da hannu yaja wani wawan tsaki ya juya dan tundaga maganar yagama fahimtar komai, ji yayi duk haushi yagama cika sa, sai yanzu yagane dalilin sa, da yaso ya hanasa shigowa cikin shagon ashe iskanci yake,

Da yaso yashiga yaci mutuncin koma wace a ciki, ya jaɗasu gaba ɗayan su yaci mutuncin su, to dalilin da ya hanasa shiga gudun kallon abun da idon sa zai iya gano masa, baisan a wane irin yanayi zai tadda itaba, kuma baya so idon sa suyi masa mugun gani, shiyasa kawai ya haƙura ya juya cike da taƙaici ya fita daga shagon ko kallon inda suke beyi ba, yana ta tafam jan tsaki haka ya nufi wajen motar sa...,

A kusan tare suka sauke wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, sulaiman harda dafa ƙirjin sa, yace Allah mun gode maka,

Bello kwa da yagama ficewa hankalin sa ya kalli Sulaiman da mamaki ƙarara a fuskar sa yace "ya akai hakan ta faru, kaga fa ya tafi, kode bai shiga ciki ba,

juyawa sulamain yayi ya kalli inda motar Meer take yaga har ya tayar da motar ya juya ya tafi, sannan ya ƙara sauke ajiyar zuciya yace "waya sani zo mushiga muga, yaja hannun sa suka shiga cikin shagon,

Suna shiga shima na fitowa daga cikin ɗakin,  da mamaki suka tsaya suna kallon sa, cike da ruɗani Bello yace "baba ya akai haka ta faru ba shigo ɗakin bane,

Dariya tsohon ya saka yana kallon su yace duk kun gama tsorata ko? kun yi tunanin zai ganni, ai bazai ganni ba, tunda na riga na shigo nan, daman nasan dole sai ya biyo ni shiyasa na shirya tun kan ya ƙaraso,

Sulaiman yace "Baba me ka shirya nagafa yazo wajen ƙofar,

Dariya baba ya kuma yi sannan yace "baza ku gane ba, nasan shine sosai shiyasa loƙacin da naga zai shiga nayi masa muryar mata, hakan ne kawai zai hanasa shiga dan baya son mace bare kuma ayanda nayi masa maganar nasan bazai taɓa shiga ba,

Sai yanzu Bello ya samu ƙarfin magana  wallahi baka ji yanda hankali na ya tashi ba, har marina fa yayi gaskiya wannan yaron masifaffe ne, Allah ya taima ke ni ma bai haɗa min da duka ba, duk yanda nake tunanin sa yafi haka,

Sulaiman yace kai ai dan baka taɓa ma ganin sa yana duka ba ai yayi maka da sauƙi ma, nima ai duk a tsorace nake nasan tsaf zai iya haɗawa dani, dan ba tausayi ya cika ba, akwai shi da saurin fushi idan ya rufe ido baya ji baya gani,

"Amma da kasan da haka ka turani kenan yafara takaina,  cewar Bello,

Dariya sulaiman yayi yace aide iya mari ne saika godewa Allah,

Nan tsohon yace to dukkan ku kuyi haƙuri sannan nagode muku da taimakon da kuke min, komai ya Kusan zuwa ƙarshe in sha Allah, ni zan wuce ku kula sosai dan nasan zai iya dawo wa gurin ku, kuma koda wasa dan Allah kar ku nuna kunsanni ko kunsan inda nake, taimakon da kuke yi min kuci gaba da yi min, dan yaron akwai kaifin tunani yanzu idan yaje ya nutsu zai iya canzawa ya dawo gurin ku,

Nan sukayi sallama ya fito daga shagon, bayan ya fito ya nufi wajen mashin ɗin ya ɗauki jakar sa dake jiki ya saƙala ta a wuya, sannan ya kuma ce musu ku shiga da mashin ɗinnan ciki, ni zan tafi sai ankon biyu,

Sai ya dawo suka ce masa, daga nan ya ɗauki wata siririyar hanya, ya nusa cikin dajin inda gidan sa yake.....,

Suma zama sukayi suna ci gaba da tattaunawa akan abun da ta faru da taya da taya tsohon da addu'ar Allah ya kawo masa ɗauki yabar cikin dajin nan, ya dawo ya cigaba da rayuwa kamar kowa.......,

__________Meer cike da taƙai ci yake tafiya yana tafiya yana faman sakin tsaki ba adadi, amma kuma wani ɓangare na zuciyar sa yakasa yarda da gaske mutumin baya gurin, koma dai meye tunda yaga inda yayi, zai ƙara komawa ko kuma zaisa asaka masa ido agun, indai tana gurin dole wataran za agansa koda wucewa ne za agansa,

A haka ya ƙarasa gida koda ya shiga gida bai bari kowa ya gansa ba, inda Allah ya taimake sa loƙacin da ya shiga falon babu kowa sai kawai ya shige ɗakin sa tare da saka muƙulli ya ƙulle ƙofar.......,

Agurguje..........✍️

      *BAYAN KWANA BIYAR....*


........acikin kwana biyar ɗinnan har yau Meer da Ameesha basu ƙara haɗuwa ba, duk inda yasan zata haɗu dashi bata bari su haɗu daɗin daɗawar ma har anfara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login