Showing 66001 words to 69000 words out of 170049 words

Chapter 23 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7214

jiki gaba ɗaya,

Da wani irin kallon tsana Meer yake binta ji yake kamar ya kashe ta, dande kawai kisan kai ba kyau amma da tuni yayi mugun dukan da zai kashe ta loƙaci ɗaya,

Ƙafa yaƙara ɗagawa ya sauke ta akan gwaiwar ta da ƙarfi take ta bada wani irin ƙara, itama kanta saida tasamu dama Muryar ta tafito tayi ƴar ƙaramar ƙara, ɗayar ya sake ɗagawa zai sauke Amra tayi saurin tsugunnawa a wajen cikin kuka tace dan Allah ka rabu da ita mai tayi maka,

Tamke fuskar sa ya ƙara yi tare da daka mata tsawa yace ta matsa,

Da sauri ta matsa tare da ƙara fashewa da kuka suma su Ameeshan kuka suke sun nanne waje guda kuma sai kace anyi musu dole ance su tsaya agun sai sun gani sunƙi tafiya,

Meer ba fasa abun da yayi niya ba saida ya karya ɗayar ma, sannan ya ɗago yana kallon su ganin yanda suke kuka gaba ɗayan su hakanne kawai yasashi dakatawa dan sai yanzu da yayi wani tunanin yagano ashefa yaran jikokin tane, dole suyi kuka, ita kuma Ameesha ko uban mai yasa zatayi kuka sai yaji ma ta bashi haushi,
tsawa ya daka musu yace subar gurin gaba ɗayan su,

ba shiri suka tafi suna kuka kamar ƙananun yara.

"Kirasu su fita da ita, Meer ya faɗa yana kallon Khalid,

zaro wayar sa Khalid yayi, ya kara a kunne ana ɗagawa yace ku shigo, sannan ya sauke wayar,

yana saukewa saiga motar ƴan sanda nan ta shigo cikin gurin,

a gaban su tayi parking sannan ƴan sandan suka fito, suna fitowa duk suka ɗaga hannu suka sarawa Khalid tare da ƙamewa, shima sara musu yayi sannan yace 'arest har,

Matan cikin sune suka kamata suka yi mata kama kama suka sakata a bayan motar da ƙyar, bayan sun sakata suka ƙulle motat, ɗaya daga cikin su ce taje gaban su Khalid saida ta ƙara sara masa sannan tace "sir baza afara kaita asibiti ba ayi mata treatment kafin mu wuce can ɗin dan naga taji ciwuka da yawa, abun zaiyi hurting ɗin ta da yaw......, Bata ƙarasa ba Meer ya dakatar da ita tare da jefa mata wata muguwar harara, sannan yace ahaka za a rufe ta bance a taimaka mata da komai ba, in ba ruwa ba,

Sunkuyar da kai tayi tace ok sir sannan ta ƙara salute ɗin sa ta juya ta shiga mota suka tafi da ita,

Hannu Meer yasaka ya shafi fuskar sa tare da sakin wani ɗan ƙaramin tsaki yana sauke ajiyar zuciya na gajiya, sannan ya dubi, Khalid cike da gajiyawa da rashin ƙwarin jiki, yace masa "what next,

Khalid ya ɗanyi murmushi yasa yaɗan dafa kafaɗar sa yace congrats mutumi na next shine kaje ka gyara jikin ka, sai muje aji da sauran sai kasamu ka huta gajiyar duka, irin wannan duka gaskiya da soja ka dace da hakan zata faru nasan da masu laifuka da yawa baza suyi ba duk wanda ya haɗu dakai bazai so ku ƙara haɗuwa ba, Allah da hanya sai na kaika soja matsalar kawai shine sar......,

"Enough! Khalid banason irin wannan Allah ya kiyaye uban mai zanyi da aikin soja agarin wallahi ƙasar nan sam batayi ba,

"To ya zakayi kuma ɗan cikin tane zama dole bayanda zakayi, "Khalid ya basa amsa,

Meer yace hmmm dole kaf duniyar nan akwai wanda ya isa yayi min dole akan abun da banyi niyaba, shiru yayi kafin kuma Khalid yace wani abun ya ɗora cewa.....,
"kaga malam muje ni ba wani shiri da sanyi sai naba kowa gurin sa, hankalina zai kwanta, yana faɗa ya yi gaba bai jira jin ta bakin saba,

Ganin hakan yasa Meer yayi saurin binsa da sauri,

Loƙacin da suka shiga cikin fada nan ma ashe faɗa ake tsakanin Fulani da sauran ta hau masifa itama harda su duka tafara kai musu akan bazata haƙura da abun da sukayi mata ba sun cuceta da farko sun zalince ta sun juyar mata da mahaifa ita da ganin gudan jinin ta sai a lahira, gashi sun jawo mata zaman gidan ƙasa, gashi kowa yana mata kallon muguwa, taso tayiwa Ammah ma tas amma ganin Meer yasa ta rabu da ita iya nasama ya isheta,

Shiyasa yana fita tajawo hajiya Sarah tafara dukan ta saida kyar ka ƙwaceta, ana ƙwatar ta kuma sai ta koma kan wata daga duk wanda takama kawai duka take kai musu zagi kam sun shashi kamar zai fito ajikin su, saida ƙyar Abu ya dakatar da ita dan gurin ma gaba ɗaya haukacewa yayi da haya niya, ga masifar gwaggo itama ba abarta abaya ba,

shigowar Meer ne da yadakatar dasu shima da ƙyar sannan aka samu komai ya lafa,

guri yasamu ya zauna sannan ya kalli Papa yace "wane irin hukunci yake son a yanke musu, yanzu, dan gaba ɗayan su masu laifi ne, da farko yayi tunanin suma duk atarkata su akai su kotu, sai kuma yayi wani tunanin kafin akaisu dole sai sun fara hukuntasu sannan zasu kaisu a ɗaure su agidan yari gaba ɗayan su, babu wanda aka ɗagawa ƙafa,

Papa yabawa Meer dama yace ya yanke musu duk hukuncin da ya dace, dasu,

Ana agaban kowa Meera yace ya yanke musu hukunci zaman gidan yari na dindin daga nan har ƙarshen rayuwar su, sannan kafin afita dasu zasu fara amsar hukunci acikin gidan nan za akaisu ɗakin ƙasa kamar yanda suke sawa akwai wasu suma zasu shiga ciki a horasu horo mai tsanani sannan a fito dasu akaisu prison dan babu wanda yakamata yaci gaba da rayuwa cikin mutane domin zaman su aguri haɗarine kowa mummunar zuciya garesa, idan aka barsu nan gaba ma zasu iya yin son zuciyar tasu su kara cutar da al'umma,

Nan kowa yayi na'am da hukuncin nasa, sannan aka nemi inda wanda yake da magana yayi kafin zama yaƙare,

Kande ce tace tana da magan, aka bata izni,

Sannan tace dan Allah tana neman alfarma kafin a yanke mata hukunci tana so taga ƴaƴan ta anemo mata koda nan cikin gidanne ta gansa kafin ta tafi sannan tagaya masa abun da Ammah tace ya koma garin su, dan tasan batasan inda ɗayan yake ba, ta haƙura da ganin sa idan kuma Allah yayi haɗuwar su Allah yasa su haɗu,

Da farko Meer ƙin amincewa yayi saida Maama tasaka baki sannan, ya yarda, nan suka shiga tunanin mai irin siffofin da ta lissafo, amma duk da haka basu gano ba, a loƙacin Meer ya fita da kansa aka tara masu aikin gidan, ya shiga dubasu yana tambayar su amma aka rasa,

haka ya dawo cikin fadar yake sanar dasu ba'a samuba wata ƙil ƙarya take, har anyi shiru da maganar za afara wata, Sarki Salahudeen yace "yana da magana, nan aka bashi izni,

Cikin sanyin yanayi ya tashi ya fara da cewa "bana tunanin ƙarya take domin abubuwan da ta faɗa a halayen sa da kamannin sa a yanda tafaɗa akwai mai irin su agidan nan, sai yanzu naƙara tabbatar da hakan da nayi tunani, to amma abun mamakin anan shine, shi wannan mai halayen yana da mahaifiya indai kuma ba shima ƙarya akayi masa ba.....,

Da sauri Fulani ta tashi ta karɓeshi da cewa ƙwarai kuwa wallahi wanda kake zance shine ma duk yanda ta faɗa haka yaron nan yake ni zan baku labarin sa,

Wallahi wannan munafukar zaku tuhuma tasan komai, tunda tace ɗanta ne nidai tunda nake da ita ban taɓa ganinta da ciki ba, hasalima bata taɓa yin aure ba, wai amma loƙaci ɗaya tace min ɗanta ne alugunguma shegiya zo nan dan kutumar ubanki kiyi mana baya ni uban waya baki ɗa ta ƙarasa maganar tana jawo kan Hajiya Sarah ta dungurar da ita agun tana nuna ta da yatsa tace Wallahi itace wannan fa tafi kowa mugwar munafuka ce sheɗaniya anya ma nikam matar nan bata haɗa dangi da sheɗanu ba (oh Fulani da masifa mai hali baya fasa halin sa)

Nan kallo ya koma kan Hajiya Sarah da Fulani, Fulani ce ta ƙara dungurin ta tace "bazakiyi magana ba, shiru Hajiya Sarah tayi bata tanka mata ba,

Papa ne yayi mata magana da kansa sannan tace "Eh ɗanta yana cikin gidan nan ba ɗa na bane ɗanta ne, Ammah ce ta bani shi tace in riƙeshi har zuwa girman sa idan ya girma kuma zata karbesa ya shigo cikin masarautar amma bada sanin ko shi waye ba kawai zata na bashi kulawa ne sannan ba ko wane aiki zai ringayi ba agidan, daga nan kuma da yayi wayo sosai tasa nace masa ya daina yin komai sannan ya ringayiwa Fulani rashin mutunci duk ranar da tace zata yi masa wani abu yace mata yasan sirrin ta kuma zai tona idan taci gaba da abun da take anan zai ƙara samun damar yin duk abun da yaga dama, marabar sa da ƴan gidan kawai shi su suna part ɗin ƴan gida shi kuma yana part ɗin bayi masu aiki,

Duk abun da tabani ni kuma sai inbashi amatsayin sa na ɗana tunda tun yana ƙarami yake hanuna ni na ƙarasa rainon sa shiyasa yayi tunanin nice mahaifiyar sa,

Ranar da kuma yakira ni yace zasu kasheshi, duk tsarin mune saboda a loƙacinne burin kowa yake daf da cika ta haka kawai za asauke sa daga mulki su kuma su ɗora waɗanda suke so, shiyasa aka kamasa ranar da yarinyar ta shiga ɗakin sa mukuma mukayi amfani da wannan ranar muka tura mutane aka gaya wa sarki abun dake faruwa shi kuma ya ɗau zafi dalilin da yasa akayi musu wannan dukan kenan mutanen ma su suka shirya su, sukayi musu wannan dukan,

Shiyasa da ya kirani nazo dan in tona asirin kowa yaji hakan ma tsari ne, daga nan kuma sai abu ya taɓaɓɓare rishe ya juye da mujiya, dan a loƙacin so nayi ingudu sai kuma hakan bai yiyuba........,
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                   (DA ZAFI ZAFI)
                             By
               ❤️Yaya Azeema❤️
   
                      *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

Shiyasa da ya kirani nazo dan in tona asirin kowa yaji hakan ma tsari ne, daga nan kuma sai abu ya taɓaɓɓare rishe ya juye da mujiya, dan a loƙacin so nayi ingudu sai kuma hakan bai yiyuba........,

Tana gama rufe bakin ta, Kande tace "wai wa kike nufi kice min, kina nufin ɗana yana gidan nan dan Allah akira min shi, inganshi dam Allah kukirashi,

Meer ne ya tambaye ta sunan ɗan tagaya masa tayi shi kuma ya nufi hanyar fita, sannan yasa wani yace yaje ya kirawo masa Hamza,

Ba aɗau wani loƙaci ba, sai gashi an shigo da Hamza cikin gurin,

yana shigowa ya ɗauke kai daga gurin Hajiya Sarah saboda baya son ganin ta har yanzu haushin ta yake ji,

Gaban Papa ya ƙarasa tare da tsugunnawa agaban sa ya gaida shi saboda duk a tunanin sa ko akan batun Sam ne shiyasa aka kirasa,

Bayan sun gama gaisawa, Papa ya kirasa sunana sa, sannan ya fara sanar da shi abun dake faruwa tare da basa ɗan taƙaitaccen labarin tundaga farko har zuwa ƙarshe amma da aka gama bashi labarin aka nuna masa mahaifar sa, sai ya nuna ko in kula da jin nasa labarin idan ka kalle sa bazaka gane farin ciki yake ba ko baƙin ciki,

Hakan da yayi kuma ba ƙaramin mamaki yabawa wasu ba, har Saida Maama tayi masa magana akan baiji me akace bane yace yaji, kawai baida ra'ayin komai shi kawai arabu dashi yanda ya taso shi kaɗai zai ci gaba da zaman sa, a haka baya buƙatar wasu dangin na cikin masarautar sune dangin sa kuma zai ci gaba da zama dasu, mahaifayar sa kuma itama tasha bai taso da ita ba kuma bazai zauna da ita ba dan haka bai ɗauke ta matsayin uwa ba, tunda har ta nuna son zuciyar ta ta rabu dashi yataso cikin garari bata neme saba, dan haka shima baya nemanta yanzu acikin rayuwar sa, saboda acewar sa inda har da gaske ne badan son zuciya bane ai da tasan yanda tayi tagayawa wani halin da take ciki ai dole za'a kama ita Ammah ɗin amma tayi shiru da bakin ta suka ci gaba da zalintar mutane, idan kayi wani tunani ma gaba ɗaya kusan itace silar komai da batayiwa tifkar hanci ba tun loƙacin da ta gane gaskiya da ta dakatar da ita ta sanar da mutane abun dake faruwa da duk haka bata faru ba,

Dan haka shi ba wani farin ciki da yayi da hakan, ana gama maganar ma ya tashi yabar cikin fadar, uwar tana ta kuka tana kiran sa amma ko waiwaiwayon tama baiyi ba, ya fice abun sa, su papa ma babu wanda ya dakatar dasu sun rabu dashi zuwa wani loƙacin zasu kirasa suyi magana,

Kamar ranta zai fita haka Kande take kuka, tayi da nasani yafi cikin kwando ji take kamar tayi hauka ita bataga wani cigaba da ta samu a rayuwar ta ba ta rasa mijinta ta rasa ƴaƴan ta gashi ta tashi a tutar babu, babu wani cigaba da tasamu gashi ta jawa kanta zaman gidan yari na har abada, wannan masifa da mai tayi kama ga ɗanta yana gudun ta ko nuna yaji da daɗi ma da ganin ta baiyi ba, ya tafi yabarta tana roƙon sa amma yaƙi sauraron ta, haka ta ringa tunani kala kala, ita kaɗai,

Daga nan kuma aka rufe taro da addu'a kowa yakama gabansa su kuma aka kwashe su aka kaisu can gidan ƙasa kowa aka raba masa ɗaki babu wanda aka haɗa da wani,


_*Washe gari*_


Fulani ma ta koma sashenta babu wani hukunci da aka ƙara yi mata saboda duk abun da ya faru bayin kanta bane, shiyasa aka rabu da ita, inda Saida ta jira akayi masa gyare gyare aka dawo dashi tsaf kamar yanda yake ada sannan ta koma dan cigaba da sabuwar rayuwa,

momma ta koma nata part ɗin inda ta tara su twins ɗinta ta basu labarin komai sannan ta rungumi ƴaƴan tare da miƙa lamarunta ga Allah, Allah ya kawo mata sassauci akan abun dake samun ta, Sam kam shima ta ajiye batunsa a gefe tunda anyi neman duniya an rasa shi, wayar sa ma kuma bata shiga, amma bayan ko wace awa sai ta ƙara gwada Number ko zata shiga amma bata sa'a,

Sannan tun a ranar aka sa aka fito da komai na part ɗin Ammah, zuwa gobe za azuba wasu kayan aciki,

Papa da Maama suna sun koma nasu part ɗin inda suka yiwa Allah godiya da ya nuna musu ƙarshen maƙiyan su, yanzu basu da wata damuwa kuma sai neman baban Ameesha amma yanzu sun gama da cikin gidan saura kuma waje zasu fara bincika, hankalin su yanzu ya ɗan kwanta, saboda duk wani ma'aikacin gidan marar gaskiya saida aka kamasa aka ƙulle,

Sannan Papa yace "aje a lalubo wanda ya buge Maama shima sai ankama sa duk dade bada son ransa bane, amma shima yana da laifi na ƙoƙarin kisan kai da yayi,

Nan aka shiga neman sa amma aka rasa, da Maama batayi niyar faɗa ba saidaga baya tace tasan inda yake amma tana neman alfarmar a rabu dashi ta yafe masa saboda ba da son ransa yayi ba, kawai dai akirasa a haɗa da da ƙanin sa, su sasanta kansu, su san junan su, inyaso daga baya su tattara suma su koma can gidan su, su karɓi sarautar su,

Hakan kuwa akayi akaje aka kirawo baban Bossay sannan aka sanar dashi duk abun dake faruwa duk da yasan wasu abubuwan wasu kuma bai sani ba, da kuma abun da ake so suyi, aka haɗasa da Hamza aka gabatar dashi agaban sa, yanzu ba laifi Hamza yaji daɗin ganin yayan nasa yanzu bai nuna rashin amincewarsa da hakan ba,

Atake agun har suka ɗan saba Dadyn su Bossay ya nemi da su tafi tare su zauna acan gidan sa kafin komai yayi stalling, suje can garin nasu, A loƙacin dai ba ba samu damar hakan ba, Papa yace masa ba yanzu ba, shima kuma Hamzan bai amince ba yadai ce zaizo amma yanzu ba,

Haka Dady ya haƙura ya koma gida tare da tara gaba ɗaya iyalensa ya sanar dasu komai babu abun da ya ɓoye musu, nan suma suka shiga jin daɗin jin asalin mahaifin su,

Bossay kam saboda jin daɗi a loƙacin ya taho masarautar yazo wajen Hamza inda suka ringa tsokanar juna Hamza yace Bossay ɗan sane dan haka dole yace masa baba ko kuma yace masa uncle shi kuma bossay yace bazai faɗa ba Hamza zaici inyaga dama ya amsa inbaiga dama ba kuma kar ya amsa, hala sukai tayi, daga ƙarshe suka shiga hirar Sam yanda za'ayi anemo sa dan sun tausayawa mahaifiyar sa,

Bossay bai bar gidan ba saida yaje wajen Ameesha suka sha hira sannan yatafi gida,


Khalid ma tun ajiya bayan gama komai ya wuce gida,

Ya daɗe da dawowa amma baije gidaba sai yau, tundaga wajen gidan yake binsa da kallo sai yaga kamar ancanza komai na gidan haka yaci gaba da driving ɗinsa tare da yiwa mai gadi horn aka zuge masa gate ya shiga ciki,

A parking lot yayi parking sannan ya buɗe motar ya fito, tundaga sama har ƙasa yake ƙara bin gidan da kallo,

A tsanake ya shiga takawa zuwa falon gidan saboda yana so yayi musu surprise shiyasa bai sanar dasu dawowar saba,

Murɗa ƙofar yayi ya tura kai ciki ya shiga falon ba tare da yayi sallama ba,

zaune yaganta ta juya baya akan dinning tana cin abinci, ƙarasawa yayi inda take ta bayan ta yatsaya tare da zura hannuwansa ya rufe mata ido ta baya yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login