Showing 18001 words to 21000 words out of 142761 words

Chapter 7 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

kuma sun shiga d'akin da Aisha take, sun same ta kwance duk an sanya mata wasu na'ura a jiki har a kai wanda kuma hakan ne ya tabbatar musu da cewar bata cikin kyakkyawan yanayi.

Da gudu *Adeel* ya nufi inda take yana fad'ar sunan ta da sauri Umma ta riqo hanun sa tare da kai kallonta ga Prof tana tambayar sa mai yake faruwa da Aisha. "Karki wani damu Umma zata samu lafiya insha Allah to kawai ki yarda da ni kinji ko." Ta jinjina masa ka a lamar to ya mai da kallonsa ga *Adeel* wanda yake ta fitinar sai ya tafi gurin Aisha, ya d'auke sa yana rarrashin sa sai wani lalla'basa yake har ya samu ya dena kuka daga bisani kuma yayi barci bayan kwana biyu.....................




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/28/2021, 9:34 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘

*THREE BROTHER'S*

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ‘‘

*Page 8*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*wΜΆΜΆΡ” Ξ±rΜΆΜΆΡ” Π²Ρ”Ξ±rΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟƒ gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ” wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓ­tΜΆΜΆΡ” Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓ­dΜΆΜΆΓ­ΟƒuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ‡ pΜΆΜΆΡ”rΜΆΜΆcΜΆΜΆΡ”Γ­vΜΆΜΆΡ” nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟƒ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓ­cΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡ”Ξ±tΜΆΜΆΓ­vΜΆΜΆΡ” gΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆΜΆ* ✍ *,Π²Ρ”hΜΆΜΆΟƒlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟƒdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟƒfΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡ”nΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟƒuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟƒrΜΆΜΆ Γ­tΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓ­lΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ” Ρ‡ΟƒuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟƒ pΜΆΜΆΞ±Γ­nΜΆΜΆ.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖ™ata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζ™ara mana Ζ™arfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Monday 27/12/2021*

*Time 09:06pm*

*Typing..............*

Kwance take Dr Anisa ta shigo domin ta duba ta, ta isa inda take ta duba ta Alhamdulallah tana samun sauki, ta juya domin tafiya Aisha ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "Doctor dan Allah ko zamu iya yin magana yanzu.?" Ta jinjina mata ka tare da furta eh tayi wani gajeran murmushi sannan taci gaba da magana. "Likita dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake damuna? Sabo da ina jin wani irin mummunan yanayi a tare da ni ina jin kamar zanyi hauka wani lokaci, musamman idan ina jiyo sautin kukan wad'an nan yaran ko kuma dai in nayi mafarki dasu. Kai na yana d'aukan zafi sosai sannan kuma ina fita haiyacina na tsayin wani lokaci, likita na san cewar kuna kan binkice a kan lafiya ta to dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da ni kinji.?" Doctor Anisa ta zauna daga gefen ta sai wani kallonta take kallo sosai mai cike da jin tausayin ta sosai a tare da ita, sun samu shiru na muntuna kad'an sannan ta amsa ta cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana.

*"Maman Adeel* ya kamata ki kwantar da hankalin ki domin tafiya ta samu damar shigarki, sabo da sam ba a san kina yawan shiga firgici, unci, bak'in ciki, da kuma damuwa sabo da hakan barazana ce ga lafiyar ki. To ya kamata ki dena unci sannan kuma ki jure kuna karki yanke qauna ga samun lafiyar ki kinji ko, to ki kula sosai ni zan tafi Allah ya baki lafiya." Ta yunk'ura domin ta tashi Aisha ta dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta. "Likita fad'a min gaskiya shin ni ina tare da juna biyu ne.?" Wani irin kallo take yi mata mai cike da jin mamakin abin data fad'a cike da rud'ani take amsa ta. *"Maman Adeel* kamar kina magana a kan juna biyu haka ne.?" Ta jinjina mata ka a lamar eh cike da jin mamakin abin data fad'a Dr Anisa take magana.

*"Maman Adeel* gaskiya naji mamaki sosai da naji kinyi magana a kan juna biyu, ko dai ke kin manta am ina nufin ta ya zaki aihu bayan kuma babu mahaifa a tare da ke.?"Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data fad'a take magana. "Likita wai mai kike fad'a ne ta ya ni na rasa mahaifa a tare da ni? A'a hakan sam ba zai faru ba da ni ba zan ta'ba barin hakan ta faru da ni ba, sam ba zai yu na rasa mahaifa a jiki na ba ni gaskiyar nake fad'a ki yarda da ni sabo da gaskiyar nake fad'a." *"Maman Adeel* dan Allah ki kwantar da hankalin ki sabo da kin fara fita haiyacinki, hakan kuma mummunan a lama ce a tare da ke to ya kamata ki natsu kinji ko dan Allah." Lokaci d'aya kuma ta fara fita haiyacinta sai wani irin abu yake yanayin ta ne yasa dole Dr Anisa tayi mata alluran barci. Ba jimawa sosai tayi barci Dr Anisa kuwa sai wani kallonta take yayin da tausayin ta yayi yawan gaske a tare da ita, tana haka sai ga Umma ta dawo Dr Anisa ta gaishe ta sannan ta tashi ta fice. Umma tayi isa inda take ta zauna sai wani kallonta take kallo mai cike dajin tausayin ta sosai a tare da ita, da yamma lis suna zaune tare da ita sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, sai wani kallonsu take ba kuma tare data furta musu komai ba dukansu sun shiga yi mata sannu amma bata amsa ba.

Lokaci d'aya ta tina da zancan da tayi da Dr Anisa kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai. Prof ya tashi daga inda yake ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, zai yi magana tayi saurin dakatar da shi ta hanyar d'aga masa hanu tare da juya masa baya cike da jin mamakin ta yake magana. "Aisha wai mai yake faruwa da ke ne haka dan Allah ki sanar damu kinji please.?" Shiru bata amsa shi ba sai ma kuka da take ya juyo da fuskar ta tare da fad'ar sunan ta, kafin ya furta komai tayi saurin dakatar da shi ta hanyar da bai ta'ba tinani ba, kamar a mafarki Aisha ta sauke masa mari biyu masu kyau a fuska. Cike da firgici da rud'ani Umma take fad'ar sunan ta amma bata amsa ba cike da jin mamakin ta sosai yake magana.

"Aisha yau kuma ni kika mara? Eh lallai kin tabbatar da cewar kin fara hauka to ya kamata na nai mi mafuta ko dan sabo da yarona, domin sam ba zanso ki cutar da shi da wannan haukan naki ba." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin da yake fad'a Umma take magana. "Prof wai mai kake fad'a ne haka sam na kasa fahimtar ka shin wani abu yana faruwa da Aisha ne dan Allah ka sanar da ni.?" Kafin ya furta komai tayi masa rigagi, "kai mugu ne na tsane ka kawai ka bar nan ka fita daga rayuwa ta data yarona gaba d'aya." Cike da rud'ani Umma ke magana, "Aisha qlau kike kuwa shin kinji irin lafazin da yake fitowa daga bakin ki kuwa? Ta ya zaki buqaci mujin ki ya rabu da ke cikin sauk'i mai ya saka zaki cutar da kanki har haka Aisha fad'a min mai yake faruwa da ke ne kuma gaskiyar zaki fad'a.?"

"Umma shi yasa an cire min mahaifa ba tare da amince wa ta ba, shi ya cutar da ni sosai sam bai kamata ya aikata min haka ba amma." Lokaci d'aya suka ga ta ri e k'irji tana fad'in wash da sauri suka shiga anbatar sunan ta, amma bata amsa ba sai ma wani irin abu da take lokaci d'aya kuma ta suma, cike da firgici Prof ya fita ba jimawa ya dawo tare da doctor ganin yanayin ta ne yasa a ka buqaci dasu fita. Prof ya fara d'aukan *Adeel* da yake kwance a kan kujera yana barci sannan suka fice daga d'akin, nan kuwa su Dr Anisa suka nufa kanta sun jima a tare da ita sannan daga bisani suka fito, cikin hanzari Prof ya shiga tambayar su jikin ta sun samu shiru na jim kad'an sannan Dr Salim ya amsa shi.

"Prof a zahirin gaskiya matarka sam bata cikin kyakkyawan yanayi, Prof kamar dai mun fad'a maka cewar matarka bata buqatar unci, bak'in ciki, 'bacin rai tinani, ko damuwa. Sabo da hakan yana matuqar cutar da ita sosai sannan kuma zai iya zama barazana ga lafiyar ta, to ya kamata ku kula da ita sosai ku saka ta farin ciki sosai sabo da hakan ne zai taimakawa lafiyar ta, Prof gaskiyar ita ce idan har irin haka yana faruwa da Madam to fa komai zai lalace zata rasa tinanin ta gaba d'aya, zata koma hauka ko kuma dai ku iya rasa ta gaba d'aya to da akwai buqatar ku kula da ita sosai please."

Yana kai k'arshen maganar sa ya juya ya nufi office hakama su Dr Anisa suma tafiya suka yi, cikin hanzari Prof ya juya ya nufi office ďin Dr Salim Umma kuma ta nufi d'akin da Aisha take. Zaune yake sai dai ba abin da yake Prof ya turo ofa ya shigo ya isa inda yake sai wani kallonsa yake cike da unci da damuwa ya kifa masa wani wawan mari tare da fad'ar sunan sa. "Dr Salim ni d'in nan nayi matuqar yarda da kai sosai to amma mai ya saka kai kaci amana ta? Na baka duk wani abin daka buqata daga gareni har ma qari na yima, amma kuma duk da haka shi ne kai ka za'bi da kaci amana ta mai yasa fad'a min mai ya saka kai ka yaudareni.?" Magana yake cikin fishi sosai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, Dr Salim kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai mai cike da jin mamakin sa kuma a haka yake magana. "Prof wai a kan me kake magana? Ni sam na gagara fahimtar komai daga cikin abin da kake fad'a, ya kamata ka fito min a mutum ta yanda zan iya fahimtar ka fad'a min a kan me kake magana.?"

Mst yaja tsaki sannan yaci gaba da magana, "Dr Salim ta ya a kai Aisha ta san cewar babu mahaifa a tare da ita? Karka fad'a min cewar wai ba kai bane ya sanar da ita gaskiyar ba sabo da sam ba zan yarda da hakan ba, fad'a min mai ya saka ka yaudareni ta hanyar sanar da ita gaskiyar.?" Cike da jin mamakin abin daya fad'a Dr Salim yake magana. "Prof wai mai kake fad'a ne haka taya kake tinanin cewar ni ďin nan zan iya yaudaranka har haka? A'a ni sam ban aikata abin da kake tinani ba wallahi tallahi ni ban sanar da ita komai ba to zaka iya yarda da ni." Cike da unci ya wani shak'o wuyan sa cikin fishi sosai yake magana.

Mai ya saka za kayi k'arya? Bayan kuma ni gaskiyar nake fad'a, ni dai ne kawai muka yi wannan zancan na biyaka kamar dai yanda ka fad'i farashin ka, har ma nayi ma qari amma da abin da zaka sakamun kenan wannan ne sakamakon da zaka ba ni? Yanzu sabo da kai matata sam bata cikin kyakkyawan yanayi sannan kuma ka d'ora alhakin hakan a kai na, ta hanyar fad'a min cewar ban kula da ita yanda ya kamata ba kai har kama isa, to bara ka ji bawai sabo da ka san sirrina ba sam ban damu da wannan ba sabo da hakan sam ba zai dakatar da ni daga hukunta ka ba idan naso hakan. Kud'i kawai zan ba da nan take za a yi man duk abin da nake so kamar dai yanda kai ma kayi, to yanzu ka fad'a min mai yasa kaci amana ta sannan kuma ka yaudareni gaskiyar zaka fad'a.?"

"Prof ni gaskiyar nake fad'a wallahi tallahi ban sanar da Madam komai a game da wannan ba, to ta ya ma ni zanyi tinanin aikata maka haka bayan kuma na san dani a kayi komai a'a ni ba zan ta'ba aikata maka haka ba. Prof ya kamata ka yarda da ni sabo da ni gaskiyar nake fad'a sam ban aikata abin da kake tinani ba, kuma komai lalacewa ta to ba zan ta'ba yiwa rantsuwa a kan k'arya ba to yana da kyau kai ka yarda da ni dan Allah." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana, "Dr Salim to idan ba kai bane wanda ya sanar da Aisha gaskiyar ba to waye? Ka fad'a min waye wanda zai iya aikata hakan wanda ya san da sirrin sabo da dole da akwai wani wanda ya san da wannan zancan, dan haka ni ba zan ta'ba yarda da kai ba har sai idan ka sanar da ni duka gaskiyar waye cikon na ukun mu wanda ya san da wannan zancan kuma gaskiyar zaka fad'a.?" "Prof ni na riga dana sanar da kai duka gaskiyar ban sanar da kowa ba to mai ya saka ba zaka yarda da ni ba."

"Wai kai kana magana a kan yarda? To ka sani ka riga daka rasa yarda ta ba kuma zan qara yarda da kai ba, daga k'arshe kuma lallai ya zame maka dole ka gano wannan wanda yake ri e da wannan sirrin, ko kuma dai kai ka san irin abin da zan iya aikata wa a kanka kuma kayi hakan cikin sauri." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa yayin da unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare da shi sosai, Dr Salim ya bisa da kallo har ta fice ya nisa tare da jan numfashi ya qara da sauke a jiyar zuciya ya zauna yana cewa. "To waye kuma wannan wanda yake k'oqarin 'ballomin ruwa ta ya ma a kai wannan zancan ya futa bayan kuma mu biyu ne kawai a gurin, ina matuqar mamaki sosai da hakan ta faru lallai ya zame min dole dana gano ko waye wannan eh zanyi hakan kuma nan kusa insha Allah."

Ai kuwa haka Dr Salim ya shiga binkice a kan gado wanda ya sanar da Aisha zancan cire mahaifa, amma sam bai yi nasaran gano komai ba sabo da sam bai ta'ba tinanin cewar Dr Anisa ba ce. Haka dai Aisha tayi ta samun cikakkiyar kulawa daga gurin doctor ta jima sosai asibiti sannan daga bisani ta samu sallama, amma sam bata yarda da koma wa gidan ta ba sabo ta kasa yafe wa Prof abin daya aikata a gareta. Wani yammaci Prof yazo domin tafiya da ita gida ranar gaba d'aya bata cikin kyakkyawan yanayi, zaune take ta had'e kai da guiwa tasa pillow ta toshe kunnan ta yayin da bakinta yake ta anbatar kalmar a'a Umma na daga bayan ta rungume da ita. Da sauri Prof ya nufi gurin ta har yana gudu hakama *Adeel* abin da yake yi kenan yayin da yake fad'ar sunan ta Mummy, yana k'oqarin hawa jikin ta ta ture sa har ya fad'i da sauri Prof ya riqo sa yana rarrashin sa shi kuwa sai kuka yake, ya jima yana rarrashin yaronsa har sai da yayi shiru sannan ya mai da kallonsa ga Umma tare da fad'ar sunan ta.

"Umma shin tin yaushe take cikin wannan yanayin sannan kuma yau tasha maganin ta kuwa.?" Cike da unci da tarin damuwa take magana, "ta jima sosai a haka tana magana a kan wasu yara daban gaba d'aya yau bata cikin kyakkyawan yanayi, nima bana tare da natsuwa sabo na damu sosai a kanta na sha'afa shi yasa na manta da bata magani. K'ila shi yasa jikin ta yayi zafi sosai Prof naro e ka dan Allah ka taimaki Aisha ta samu lafiya dan Allah." Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "Umma gaskiyar ita ce Aisha ta riga data samu matsalar ta'bin hankali ko na ce tana tare da ciwon hauka, wannan ne abin da likita ya sanar da ni a kanta nayi shiru ne sabo da ban yarda da abin daya fad'a ba. Amma yanzu da nake ganin a salin gaskiyar to ba zai yu nayi shiru ba, Umma ba zan 'boye maki ba gaskiya ba zan iya ci gaba da zama da 'yarki ba, sabo ba zata yi man wani anfani ba sai dai kawai ta cutar da ni da kuma yarona kinga abin data aikata a yanzu."

K'oqarin cutar da shi take to mai kuma kike tinanin zai faru idan ya kasance cewar su biyu ne? To duba da wannan yasa dole zamu rabu tabbas ina san Aisha sosai, hakama nayi ta burin na rayu da ita na har abada amma yanayin ta ya canja komai, a gaskiya ni ba zan iya jure wannan yanayin nata ba sabo da yana da hatsari sosai ita yanzu abar tsoro ce. To bani da wani za'bi wanda ya wuce wannan dole mu biyun zamu rabu sabo da a yanzu ni da ita sam bamu dace da juna ba, Umma kiyi hak'uri da irin abin da nake fad'a sabo da bani da wani za'bi ne shi yasa dole sai hakan ta faru, Umma ni Prof Abas Muh'd na saki matata Aisha Salisu saki d'aya ina fatan wata rana ta samu lafiya sai an jima." Ya tashi tare da riqa hanun *Adeel* domin su tafi da sauri ya cire hanun sa yana fad'ar a'a. Yayi kwance jikin Aisha yana fad'ar sunan ta Mummy shiru bata amsa ba, Prof ya riqo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login