Showing 12001 words to 15000 words out of 142761 words

Chapter 5 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

ya kai kallonsa ga Ahmad tare da furta masa yazo ya amsa da to ya nufi inda yake, shi ma yayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa ya anbaci sunan sa yaci gaba da magana.

"Ahmad fad'a min wani abu shin kana farin ciki da buqatar qanwarka kuwa.?" Ya jinjina masa ka tare da furta, "eh Abba ina farin ciki sosai to zaka iya yarda da ni." "Hakan yayi kyau sosai yarona Allah ya albarkaci rayuwarku data yaronku gaba d'aya." Sun amsa da Amin suna murmushi Abbu sai kallonsu yake yana murmushi ya anbaci sunan Abba yana cewa, "Yaya gaskiya ina farin ciki sosai amma ya kamata mu d'auki *Adyan* zuwa kaduna, zamu kai shi Saudat Care Hospital na tabbata zai samu kulawa sosai a can sannan sai mu fara shirin tafiyar su wanda baifi kwana biyar ba." Abba ya jinjina masa ka a lamar to shi kuma zuwa wannan lokacin ne Abba ya sake su daga rungumar da yayi musu ya anbaci sunan Ahmad yana cewa.

"Ahmad ya kamata na had'u da likitan daya duba jikana." Ya amsa da to sun tashi sun nufi office ďin doctor har da Abbu bayan tafiyar su Ahlam ta sauke kallonta ga fuskar *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin barci yake. Ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana furta masa kalmar, "ina qaunarka yarona ina fatan ka samu lafiya cikin sauri ka zama jarumi, sannan kuma ka jure domin Ammie tana matuqar buqatar ka sosai, to ya kamata ka jure zafin sabo da ni da kuma Dadyn ka ka ji ko ina sanka sosai d'ana." Ta fad'a tare da sunbatarsa yayin da take jin soyayyar sa tana zaga ko ina lungu da sak'o na jikin ta, su Abbu sun isa office d'in doctor tare da shiga ciki bayan sun gaisa Abba yaci gaba yana cewa, "doctor a game da jikana ne shin zamu iya tafiya da shi zuwa gida kuwa? Zamu canja masa wata asibiti sabo da mu a kaduna muke to ya kamata a duba shi a can, to ko zamu iya tafiya da shi yanzu ka sanar damu.?"

"Shikenan zaku iya tafiya da shi amma yana matuqar buqatar kulawa sosai, sabo da yaron sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi sannan kuma yana da wani miki a zuciyar sa. Sam ba a san wani abu ya gajiyar da shi sabo da hakan zai cutar da shi sosai, to yana da kyau ku kula da shi sosai kunji ko." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali Ahmad yake magana. "Doctor to mai ya kamata a yi a game da yarona sabo da ya kamata ya samu lafiya kayi hakan cikin sauri dan Allah ka ji ko." "Kayi hak'uri sabo da a yanzu dai ni ba zan iya yin komai a game da wannan raunin na sa ba, sabo da wannan ciwon a na d'aukan sa ne daga gurin uwa mace wanda na tabbata dukanku sun san da wannan, sabo da dole Maman sa tana tare da wannan cutar shin gaskiya ni na fad'a kuwa.?" Lokaci d'aya dukansu suka jinjina masa ka tare da furta masa kalmar eh yaci gaba yana cewa.

"Amma da akwai wata ar mafuta amma tana da hatsari sosai, abin shi ne a na aikin wannan cutar amma aikin yana da hatsari sosai cikin goma ďaya ne kawai wanda yake rayuwa. shi yasa ba kowa bane yake amincewa da aikin ba sannan kuma a k'asar waje ne kawai a ke aikin ba a yi a nan, to idan kuna da buqata a kan aikin to zaku iya shirya fita da shi sabo da wannan ce kawai damar ku amma kafin nan zan ba shi magana wanda zai sha." Sun jinjina masa ka a lamar to nan ya rubuta musu magani tare da takardar sallama. Sun tashi sun fice sun dawo d'akin da babyn yake ko mu ce *Adyan* sunan da Ahlam ta ba shi, sun shigo ciki zuciyar su cike da tausayin yaron sosai a tare dasu, kallo d'aya tak Ahlam tayi musu ta fahimci cewar da akwai matsala cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali take tambayar su mai yake faruwa. "Abbu Abba Yaya Ahmad ku fad'a min wani abu yana faruwa da *Adyan* ne gaskiyar zaku fad'a please.?"

A zahirin gaskiya hankalin Ahlam yayi matuqar tashi sosai da ganin yanayin su, lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai sai kuka yayin da bakin ta yake anbatar sunan *Adyan.* Cikin hanzari tare da nuna kulawa Abbu ya runguma ta jikin sa ya shiga rarrashinta yana bata magana. "Ki dena kuka 'yata mu zamu kula da komai jikana yana tare da wata rashin lafiya amma zamu kula da komai insha Allah kinji ko." "Abbu mai yake faruwa da yarona dan Allah ka sanar da ni please.?" Shiru bai yi magana ba sabo da ba zai iya sanar da ita gaskiyar ba, jin yayi shiru ne yasa Abba yin magana, "am kinga 'yata ki kwantar da hankalin ki jikana zai samu lafiya sannan kuma sam ba abin da zai faru da shi to zaki iya yarda damu yanzu zamu tafi." Ta amsa da to ta hanyar jinjina masa ka nan suka fara shirin tafiya ba jimawa suka tafi. Tafiya suke cikin kyakkyawan yanayi har ya wuce kuma ya dawo tare da yin parking ya fito cikin sauri ita ma haka fitowa tayi, tare da isa inda yake sunyi shiru suna nazari lokaci d'aya kuma suka kai kallonsu ga juna cikin rawar murya har tana sarkewa take magana.

"Masoyi shin kai kaji abin da nake ji kuwa.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh taci gaba da magana, "Mujina ni fa kamar kukan yaro nake jiyowa shin kai ma ka ji da kyau kuwa.?" "Eh dalilin da yasa na tsaya kenan yanzu ki koma mota ni zan duba domin na tabbatar." "Shikenan amma dan Allah ka kula ka ji ko." Ya jinjina mata ka a lamar to ya juya ya nufi dajin dake gefen su ita kuma ta koma mota, ya d'an jima sannan ya dawo hannayen sa d'auke da yaro ya shiga mota tare da bata yaron. Ta kar'bi yaron tare da sakin salati tana taslima shi kuma ya ja mota sun tafi, "wace irin uwa ce wannan wadda ta aikata wa yaron ta irin wannan mummunan zunubin? Ta ya uwa zata yi tinanin cutar da yaron ta har haka bayan data riga ta aife sa ni sam na kasa yarda da hakan. Barrister yaron yana da zazza'bi jikin sa yayi zafi sosai ya kamata mu kai shi asibiti." Ya jinjina mata ka a lamar to yayin da ya gagara furta mata komai sai wani kallon yaron yake ita ma haka abin take yi kenan................




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/25/2021, 5:43 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page sex*

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Thursday 23/12/2021*

*Time 10:10pm*

*Typing.............*

Sun isa asibiti cikin hanzari nurse suka kar'bi yaron suka shiga da shi ciki domin a duba shi. Bayan sun shiga da shi Barrister ya d'auki wayar sa kowa zai kira oho Asma'u tayi saurin dakatar da ta hanyar fad'ar sunan sa, "Barrister wa kuma zaka kira.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "Asma'u ya kamata na sanar da an sanda wannan, to abin da nake qoqarin kenan." Da sauri ta furta masa kalmar a'a wani irin kallo yake yi mata cike da jin mamakin ta yake magana. "Asma'u mai kike k'oqarin dakatar da ni.?" Ta nisa sosai tare da jan numfashi cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana. "Barrister ni na dakatar da kai ne sabo da ya kamata muyi magana yanzu." "Magana kuma to a kan me fad'a min ina sauraran ki.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan taci gaba da magana.

"Barrister ni da ma ina idan ka amince mu d'auki rainon wannan yaron, masoyi tsayin shekaru biyar mu kayi aure amma har yanzu bamu aihu ba, to shi ne nake san ka amince da rainon wannan yaron dan Allah karka ce a'a please." Wani irin kallo yake yi mata sam ba zai yi mamakin ta ba sabo da yafi kowa sanin irin yanda ta damu sosai a kan taga ta aihu. Yayi shiru yana nazarin sannan daga bisani ya amsa ta, "shikenan masoyiya idan har hakan zai saka ki farin ciki to na amince da rainon sa." Cike da d'auki tayi hugging d'in sa tana furta masa kalmar. "Na gode sosai Mujina ina sanka ina qaunarka sosai." Yayi murmushi tare da sunbatarta ita kuwa ta qara yin kwance jikin sa, bayan wani lokaci doctor ya fito ya isa inda suke kafin ya furta komai sunyi masa rigagi har suna had'a baki. "Doctor to ya jikin yaronmu.?"

Yayi shiru kad'an sannan ya amsa su da cewar su same sa office, cike da firgici da rud'ani sun juya sun bisa a baya sun shiga office d'in bayan sun zauna doctor yaci gaba yana cewa. "A zahirin gaskiya yaronku sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi ina mai bak'in cikin sanar daku cewar, yaronku yana tare da wani miki a gefen zuciyar sa wanda kuma wannan cutar dole daga gurin Maman sa ya samu, sabo da a nan ne kawai a ke d'aukan wannan cutar shin gaskiya ni na fad'a kuwa.?" Lokaci d'aya suka kai kallonsu ga juna cike da unci bak'in ciki tare da tarin damuwa, Asma'u take amsa masa da eh hakama Barrister doctor yaci gaba da magana. "To yanzu ya kamata ku kula da yaran sosai sannan kuma ku dakatar da shi daga yin duk wani abin da zai gajiyar da shi, sannan kuma ya zama dole daku haka yaronku unci idan kuna so to za a iya yi masa aiki, amma aikin yana da hatsari sosai cikin goma ďaya ne kawai wanda yake rayuwa, shi yasa ba kowa bane yake amincewa da aikin ba sannan kuma ba a nan a ke aikin ba a k'asar waje ne kawai a ke yi, to zan iya cewa wannan ita kawai ce damarku ga yaronku."

Lokaci d'aya dukansu suka ji wani iri tashin hankali yana fuskantar su musamman ma Asma'u. Sun tashi jiki a san yaye sun nufi d'akin da yaron yake sun shiga ciki, sannu a hankali suke tafiya har suka isa inda yake sun zauna gefen sa sai wani kallonsa suke kallo sosai, mai cike da jin tausayin sa yayin da tausayin sa ya cika zuciyarsu sosai, ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana cikin kwantar da murya take magana. "Barrister wane suna ka baiwa yaronmu.?" Magana take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo yayin da tausayin yaron yayi yawan gaske a tare da ita sosai. Ya shiga share mata kwalla yana girgiza mata ka a lamar a'a daga bisani kuma ya amsa ta, "Asma'u sunan yaronmu *Adnan* ne fatan sunan yayi maki.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh yayin da take kuka amma kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da una sosai.

"Mai ya saka kike kuka.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "masoyi ni kawai na damu ne sosai a kan yaron ina nufin *Adnan* yanayin sa yayi tsauri sosai. Ina san na taimake sa wannan yasa nake san na kasance uwa ta gari a garesa, sabo da ta wannan hanyar ce kawai zamu iya taimakon sa ai ka shirya amince wa hakan ko.?" "Eh na amince da yaronmu to kiyi farin ciki nima abin da nake yi kenan, sannan kuma ki dena damuwa sabo da yaronmu zai samu lafiya insha Allah, ni zanyi komai domin ganin yaronmu ya fita daga hatsari to zaki iya yarda da ni kinji ko." Ta jinjina masa ka tana wani gajeran murmushi shi ma haka abin da yake yi kenan. Kwance take tana barci lokaci d'aya ta wani tashi cikin tsoro da firgici sosai nan kuwa ta shiga furta kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un. Tayi zugum sai tinanin abin data gani a cikin mafarkin ta take, ta sauke kallonta ga yaronta wanda yake kwance daga gefen ta yana barci ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yayin da take magana da zuciyarta.

"Su waye wad'an nan yaran mai ya saka a ko yaushe nake mafarki dasu? Yaron suna cikin garari sannan kuma suna matuqar buqatar taimako sosai, duk da cewar mafarki ne amma kuma ni ina tare da jin tausayin yaran sosai, ya Ubangiji ina fatan kar wannan ya zama gaskiya Allahumma Amin." Ta qara sunbatar yaronta tare da d'ora sa jikin ta tana mai furta masa kalmar ina qaunarka sosai *Adeel.* Ta rufe idanuwan ta ba jimawa barci ya d'auke ta, sunyi na saran isa garin kaduna lafiya kai tsaye Saudat Care Hospital suka nufa, sun had'u da Dr Bilal wanda shi ne shugaba a nan fannin yara, Abba ya sanar da shi komai a game da yaron amma ba a gaban Ahlam ba. "Karku wani damu insha Allah yaronku zai samu lafiya idan har yana nan a tare damu, sabo da 24hou doctor ne muke kulawa da duka yaran da suke nan to sam ba buqatar ku damu sabo da yaronku zai samu lafiya insha Allah." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi Abba ya amsa shi yana cewa.

"Muna godiya doctor Allah ya taimaka ya baiwa duka yaran lafiya." Dukansu sun amsa da Amin nan kuwa a ka fara baiwa *Adyan* taimakon daya dace da shi sunyi sallama da Dr Bilal suka fito, cikin hanzari tare da nuna kulawa Ahlam take tambayar su Abbu mai yake faruwa. "Karki damu 'yata *Adyan* yana samun kulawa sosai a nan, kuma zai samu lafiya insha Allah to zaki iya yarda da." Ta jinjina ka tare da furta masa kalmar, "Na gode Abba ina fatan *Adyan* ya samu lafiya cikin sauri."

"Eh Ahlam muma wannan shi ne fatan mu to Allah ya amince da hakan Amin." Dukansu sun amsa da Amin Ahlam da Ahmad sun shiga ciki sun duba yanayin jikin sa bayan wani lokaci suka fito sannan suka nufi gida. sun isa gida ko wannan su part ďin su ya nufa su Abba sun bisu da kallo Abbu ya anbaci sunan Abba yaci gaba da magana. "Yaya ni fa ina jin wani irin a game da wannan sabo da har yanzu Ahmad da Ahlam basa tare da juna. Kawai sun amince da junansu sabo da *Adyan* na rasa dalilin da yasa suke qaunar yaron sosai har haka, Yaya shin kai sam baka jin komai a game da wannan.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "ba buqatar ka damu Al'ameen sabo da su da kansu suka buqaci hakan to na tabbata ba zasu saka mu unci ba, Al'ameen gaskiyar ita ce ni farin ciki nake sosai to kai ma ya kamata kayi farin ciki, sannan kuma ni na yima alkawari insha Allah ba abin da zai faru to zaka iya yarda da ni ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to da kuma haka suka yi sallama kowa ya nufi part ďin sa.

Haka dai *Adyan* yayi ta samun cikakkiyar kulawa daga gurin doctor da kuma su Ahlam, yayin dasu Abbu suke ta shirin tafiyar su sunyi shirin su tsab na komai bayan kwana biyar jirginsu ya tashi. Zuwa qasar England tare da yaronsu *Adyan* wanda kuma har suka tafi iyayen su mata basu samu labarin komai ba a game da *Adyan,* kamar dai yanda su Abbu suka yi musu alkawari saidai sunyi farin ciki sosai da auran da a kayi wa yaran wato Ahmad da Ahlam hakan ya saka su farin ciki sosai. A can gurin su Barrister kuwa *Adnan* ya samu tsayin mako biyu asibiti sannan daga bisani ya samu sallama zuwa gida, sunci gaba da ba shi cikakkiyar kulawa sosai tare da nuna masa soyayya da qauna irin ta d'a a zahirin gaskiya suna san yaron sosai shi yasa suke ba shi kulawa sosai.

Zaune suke suna fira cikin raha wasa da dariya yayin da Prof yake rungume da yaron sa wato *Adeel,* lokaci d'aya Aisha ta wani toshe kunnan ta duka biyun tare da rufe ido da sauri ta bud'e idanuwan ta tana furta A'a. Da sauri ta tashi ko ina zata tafi oho Prof ya riqo hanun ta tare da zaunar da ita, domin kuwa ya gama fahimtar cewa sam bata cikin kyakkyawan yanayi zai ma iya cewa sam b as ta cikin haiyacinta gaba d'aya. Sai wani kallonta yake kallo sosai mai cike da jin mamakin ta cike da firgici da rud'ani yake magana. "Aisha qlau kike kuwa fad'a min mai yake faruwa da ke ne haka please.?" "Prof shin kai baka jin komai ni ina jin kukan yara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login