Showing 36001 words to 39000 words out of 142761 words

Chapter 13 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

isa gida, Prof ya fito ya zaga ya bud'e masa k'ofa tare da riqo hanun sa ya fito sun shiga ciki, sun fara zama a parlour Prof ya tafi ya kawo masa ruwa da juice ya girgiza masa ka a lamar a'a ya tashi yayi tafiyarsa. Prof ya tashi cikin hanzari ya bisa a baya yana fad'ar sunan sa amma bai amsa ba, ya same sa kwance a kan gado yana ta aikin kuka yayin da yake ta anbatar sunan Mama. Cike da jin tausayin sa ya isa inda yake ya zauna tare da d'ora kansa a kan cinyarsa yana rarrashin sa, yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare da shi sosai ya fad'a a zuciyarsa. "Kayi hak'uri *Adeel* domin kuwa ni sam ba zan ta'ba bai yana maka mahaifiyar ka ba, wannan yasa ni sai dai kawai na baka hak'uri ina fatan zaka yafemin a kan wannan. Ina sanka d'ana kai komai nawa zanma iya kiran ka da rayuwa gaba d'aya." Maganar zuci yake yayin da tausayin yaronsa yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Bayan wani lokaci ya dena kuka Prof ya anbaci sunan sa yana cewa, "rabin raina ya kamata ka shirya muci abinci dan Allah karka ce da ni a'a please."

Magana yake yana wani shafar kansa zuwa bayan sa tare da sunbatarsa ya jinjina masa ka a lamar to, Prof yayi wani gajeran murmushi sannan ya tashi ya shiga toilet ya had'a masa ruwan wanka, ya fito tare da sanar da shi ya tashi ya nufi toilet Prof ya bisa da kallo yana girgiza ka, bayan wani lokaci ya fito Prof ya taimaka masa ya shirya sannan suka fita. Kai tsaye tebur suka nufa yaja masa kujera ya zauna ya fara zuba abincin sannan ya zauna, wanda kuma shi ne wanda yake ba *Adeel* a baki yana ci, bai wani ci sosai ba ya tashi Prof ma tashi yayi ya nufi inda yake a zahirin gaskiya yana matuqar masifar qaunar yaronsa sosai. Wannan yasa yake matuqar shiga damuwa idan ya gansa cikin k'unci da 'bacin rai sosai, ya same sa zaune a kan kujera ya zauna sai wani kallonsa yake kallo mai cike da jin tausayin sa sosai. *"Adeel* dan Allah ka dena wannan fishin haka yayi yawa sosai kuma hakan zai iya cutar da kai da kuma lafiyar, *"Adeel* yanzu fad'a min kake so ni kuma zanyi ma nayi alkawari kawai ka fad'a min ka ji ko.?"

"Dady ni kawai Mama na nake so to kasa ta dawo gareni please." "Kayi hak'uri *Adeel* sabo da ni ba zan iya baka wannan ba, sabo da ita Maman ka ta riga data mutu kuma ita d'in bata ta'ba sanka ba, sabo da ta tafi ta barka kuma ita ba zata ta'ba dawowa gareka ba na har abada. To ya kamata ka fuskanci gaskiyar kawai kai ma ka manta da ita kamar yanda ita ma tayi gareka ka ji ko." "Eh gaskiyar ka fad'a kawai zan manta da ita kamar yanda ta tafi ta barni, Dady ina sanka sosai kamar dai yanda kai ma kake sona, kai ko yaushe kana tare da ni amma ita Mama kawai sai ta za'bi data barni, hakan yana da zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una. Amma duk da haka ni ina qaunarta sosai dan Allah ka nuna man ko da photon ta ne please." Magana yake yana kuka Prof kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai yayin da tausayin sa yake ta shigarsa, "kayi hak'uri yarona ka yafemin sabo da bani da photon Maman ka ina fatan ba zaka yi fishi a kan hakan ba.?" "Eh ba zanyi ba ina sanka Dady na." "Nima ina qaunarka sosai *Adeel* yanzu yana da kyau mu fita mu zaga gari, sabo da ka manta da wannan k'uncin naka ka ji ko."

Ya jinjina masa ka a lamar to ya tashi tare da tashin sa sun fita domin su zaga gari, misalin k'arfe 02:30pm jirginsu Ahlam ya sauka sun fito sun shiga taxy zuwa gida, wanda sunyi hakan ne kawai domin su yiwa su Abbu bazata. Kasancewar basu sanar dasu labarin zuwan su ba, sun isa gidan su Habu sun shiga yi musu sannu da zuwa tare da riqa musu kaya, sun amsa suna murmushi tare da sake musu fuska, sun shiga ciki wanda kuma kai tsaye part ďin Abba suka nufa. Zaune suke dukansu sai fira suke cikin kyakkyawan yanayi kamar diran mikiya suka jiyo sallamar su Ahmad, da sauri dukansu suka kai kallonsu ga k'ofa domin tabbatar wa idanuwan su abin da kunnan su yaji, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar suma kallonsu suke. Cike da d'auki suke fad'ar sunayen juna musamman ma *Adyan,* sun qarasa ciki cike da d'auki sun shiga yin hugging juna dukansu bayan sun zauna tare da gaisawa da juna Abba yaci gaba da magana. "Ahmad wannan wace irin bazata ne mai matuqar dad'i sosai haka? A zahirin gaskiya dukanmu muna farin ciki sosai da ganin ku kunyi matuqar saka mu farin ciki sosai. Amma duk da haka naso a ce ka sanar damu labarin zuwan ku ta yanda zamu shirya muku kyakkyawar tarba, musamman wannan abokin nawa tabbas dukanmu muna tare da kewarku sosai musamman *Adyan* to sannun ku da zuwa."

"Yauwa Abba muna godiya sosai sannan kuma mu kawai muna san muyi muku bazata ne, shi yasa bamu iya sanar daku labarin zuwan mu ba abin farin cikin shi ne dukanku kunyi matuqar farin ciki da hakan sosai, to wannan ma kawai ya isa shin baku ga yanda *Adyan* yake farin ciki da ganin ku ba? Shi d'in yayi matuqar yin kewarku sosai a kullum kuma a ko yaushe cikin zancan ku yake dalilin da yasa muke nan kenan." Abba ya kai kallonsa ga *Adyan* wanda yake zaune a kan qafafun sa ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana cewa. "Rabin raina muma munyi kewarka sosai amma yanzu muna farin ciki sosai sabo da dukanmu muna tare ahalinmu ya cika, kuma duk sabo da kai ne gaskiya kai yaron kirki ne sannan kuma zan iya kiran ka dana musamman." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi su Abbu suka sai wani murmushi suke mai tare da dariya, bayan sun sha ruwa da juice sun tashi domin su tafi su shirya Ahmad ya riqa hanun *Adyan* domin shiga ciki, Ahlam tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa.

"Yaya Ahmad *Adyan* zai tafi tare da ni part ďin Ummi, ni zan shirya sa to kawai ka barsa a nan please." Ahmad ya girgiza ka tare da jan numfashi sannan ya amsa ta, "Ahlam yaron zai zauna a tare da ni sannan kuma ni zan shirya sa ai na gware a hakan to zan iya kinji ko." "A'a Yaya Ahmad *Adyan* kawai a gurin Ammie zai tsaye to kawai ka amince da hakan ka ji ko please." "Ahlam karki yi taurin kai mana na fad'a maki cewar yaron a guri na zai tsaya, kuma ni ne nan wanda zai kula da shi to kawai ki amince da hakan kinji ko." "Yaya Ahmad gaskiya ni ba zan yarda da hakan ba kawai a guri na zai zauna hakan ba zai canja ba." "Shikenan zamu gani yanzu yaron shi da kansa zai za'ba wa kanka inda zai zauna, ni ina da imanin cewa yarona ba zai ta'ba barina ba to kawai muyi hakan." "Na amince wa hakan sabo da na tabbata yarona ba zai bani kunya ba." Magana suke cike da kwarin guiwa dukansu su Ummi sai kallonsu suke suna murmushi mai tare da dariya, lokaci d'aya suka kai kallonsu ga *Adyan* wanda shi ma kallonsu yake Ahmad ne yake magana da shi. "Rabin raina fad'a min wani abu shin zaka zauna da Appa ne ko Ammie.?"

Kallonsu kawai yake yayin daya gagara furta masa komai jin shirun yayi yawa yasa Ahlam magana. "Masoyi kawai ka za'ba dawa kake san ka zauna mu zamu amince da duk abin daka za'ba, to kawai ka fad'a dawa zaka zauna.?" Har zuwa wannan lokacin kallonsu yake kuma kallo sosai ya girgiza ka tare da furta musu kalmar. "Appa Ammie ni sam ba zan iya za'ba a tsakanin ku ba, sabo da dukanku kuna da matuqar muhimmanci sosai a gareni da kuma rayuwata ina matuqar qaunar sosai. Appa Ammie shin ba zamu iya zama dukanmu a guri d'aya ba? Ni zanyi matuqar farin ciki da hakan sosai dan Allah." Lokaci d'aya suka kai kallonsu ga juna ba jimawa suka mai da kallonsu garesa suna murmushi Ahmad ya amsa shi. "Shikenan masoyi zamu yi hakan dukanmu ukun zamu kasance tare da juna, to yanzu fad'a min wani abu shin kana farin ciki.?" Ya d'aga masa ka tare furta eh Appa. Lokaci d'aya kuma suka yi hugging d'in sa tare da sunbatarsa suna furta masa kalmar muna qaunarka sosai.

Su Abbu sai wani kallonsu suke suna murmushi sun tashi dukansu sun nufi bedroom d'in Ahmad. Su Abba sun bisu da kallo suna murmushi mai tare da dariya, "gaskiya yaranmu suna da matuqar birgewa sosai musamman ma jikana, yana k'oqarin qara had'e kan iyayen sa hakan yana da kyau sosai sai naji na qara qaunar sosai." Umma ta amsa ta da, "Eh Maman Ahlam gaskiyar kika fad'a jikanmu yana da birgewa sosai nima ina jin qaunar sa sosai a tare da ni." "Eh gaskiyar kuke fad'a dukanku to yanzu ku dakata da zancan haka ku tafi kusa a shirya musu tebur. Na tabbata zasu buqaci abinci bayan sun qarasa shirin su musamman *Adyan* to kuyi hakan cikin sauri." "Eh zamu yi Senoter musamman sabo da saban Angon mu daya kawo mana ziyara to zamu tafi yanzu." Wani irin kallo Abba yake yi mata mai kama da harara sannan ya amsa ta, "Maman Ahmad shin ko zaki dena kiran wannan yaron da Angon ku? Ko kuma dai ni nasa ya koma qasar England a yau ďin nan."

"Yaya ai ita Aunty gaskiyar ta fad'a mu ďin nan muna matuqar farin ciki sosai da zuwan Angon mu, sannan kuma zamu yi komai sabo da shi idan kuma kasa a ka mai da *Adyan* England, to fa ni da Aunty ba zamu qara yi muku magana ba ba zamu ci abinci ba sannan kuma daga k'arshe zamu yi fishi daku kuma fishi sosai." Wani irin kallo suke yi mata mai cike da jin mamakin ta sosai, sam basu iya amsa ba sai dai suka yi mata murmushi mai tare da dariya ita ma abin da take yi kenan. Ta tashi ita da Umma sun fice su Abbu sun bisu da kallo suna murmushi mai tare da dariya, su Ummi sun samu su Shamsiya a part d'in su sun sanar dasu cewar su tafi zasu shirya wasu Ahmad abinci. Sun amsa da to sun tashi sun nufi kicin dukansu domin yin aikin da yake gaban su, bayan wani tsayin lokacin da suka d'auka a ciki suna shirya wa sun fito dukansu cikin kyakkyawan yanayi, da kuma kyakkyawar shiga sunyi matuqar yin kyau sosai.

Su Ummi sun kawo musu ruwa da juice tare da kayan fruit sun shiga yi musu godiya murmushi kawai suka yi musu mai tare da dariya, bayan wani lokaci Shamsiya tazo ta sanar da Umma cewar sun shirya komai a kan tebur ta amsa da to ita kuma ta tashi ta fice. Suma tashi suka yi suka nufi tebur domin cin abinci, sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarsu sosai. Bayan sun qarasa sun dawo parlour sunci gaba da fira cikin kyakkyawan yanayi bayan kwana biyu Ahlam ta kai wa Kawun ta ziyara, wanda tare take da Ahmad da kuma *Adyan* sai fira suke abinsu cikin raha wasa da dariya Anisa ta anbaci sunan Ahlam tana cewa. "Ahlam gobe ne za a yi bikin qarewar su Amir to ina fatan dukanku zaku tafi.?" Ahlam ta kai kallonta ga Ahmad kafin ta furta komai yayi mata rigagi. "Eh Aunty zamu tafi insha Allah." Wunin ranar gaba d'aya a nan gidan suka yi sa *Adyan* sai wasa yake dasu Amir washe gari........




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/8, 8:32 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 15*

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Thursday 06/01/2022*

*Time 03:10pm*

*Typing.................*

Tsaye yake gaban madubi yana wani kallon Kansas, yayi kyakkyawan murmushi mai tare da dariya yana magana da kansa. "Gaskiya nayi kyau sosai na tabbata *Afnan* ma zata fad'a min haka, ya kamata na tafi na had'u da ita yanzu ina fatan ita ma ta qarasa shirin ta." Cike da d'auki ya juya domin tafiya lokaci ďaya yayi tozali da fuskar Mamie, wacce take tsaye jikin bango tana kallonsa sai wani lallausan murmushi take sosai. Shi kuwa dariya yake ya isa inda yake yana fad'ar sunan ta, ta amsa shi tana 'yar dariya shi ma abin da yake yi kenan. "Kayi kyau sosai yarona tabbas *Afnan* zata fad'a maka cewar kayi masifar yin kyau sosai, amma zaka tafi tare damu a can gurin bikin ka ji ko." "Eh Mamie kawai *Afnan* ce zata zo tare damu yanzu zan tafi na sanar da ita, sai mu dawo tare to yanzu fad'a min wani abu ina qanwata.?" Murmushin ta ya qaru sosai ta amsa, "Qanwarka tana parlour tare da Papa kai muke jira domin mu tafi gurin taron, lokaci ya tafi sosai mun kusa mu makara, to yanzu idan ka shirya mu tafi."

Ya amsa da "Eh" suka juya suka fita zuwa parlor, sun samu Papa zaune tare da *Alishart* yana ta ya ta wasa, *Adnan* ya isa inda take ya shafi kanta zuwa fuskar ta ya qara da sunbatarta. "Sannu da wasa qanwata kinyi kyau sosai cikin wannan shigr, na tabbata ke ce wacce zata fi kowa ce mace kyau a gurin taron, ina sanki sosai qanwata yanzu ki jira Yayan ki a nan, zan tafi na dawo tare da *Afnan* sai mu tafi kinji ko." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi. Ya qara sunbatarta sannan ya tashi ya sanar dasu Papa cewar zai shiga gidan su *Afnan* ya dawo, "Shikenan masoyi amma karka jima sosai kaga lokaci ya tafi sosai, zamu iya makara hakan kuma bai dace ba ka ji ko." "Eh Papa ba zan wani jima ba kawai zance da ita ta fito mu tafi shi ne kawai." "Shikenan amma ka kula sosai dan Allah ka ji ko?." "Eh zanyi nayi alkawari sai na dawo." Suka amsa da a dawo lafiya ya amsa da Amin sannan ya juya ya fita suka bisa da kallo suna murmushi, bai qarasa fita ba *Alishar* ta bisa a baya tana fad'ar sunan sa yayin da take kuka, da sauri ya isa inda take tare da d'aukan ta ya shiga rarrashin ta ba jimawa tayi shiru tare da furta masa, "Yaya nima zan tafi tare da kai." "Shikenan mu tafi."

Ya sauke ta tare da riqa hanun ta sun fice su Mamie sun bisu da kallo suna murmushi. *"Afnan* ki fito mu tafi lokaci ya tafi sosai." Ta fito sai fishi take tana wani turo baki fuskar ta awa zata yi kuka dukansu sai wani kallonta suke Yayan ta ya shiga tambayar ta. *"Afnan* mai yake faruwa dake ne haka.?" "Yaya to ba Ummu bace take ta san mu tafi ba tare da mun jira zuwan *Adnan* ba ni ina san na tafi tare da shi." "Haba qanwata yanzu sabo da wannan ne kike 'bata rai? To ki dena mu zamu jira zuwan *Adnan* kin fasan ke ce sarauniyar gidan, to zamu yi duk abin da kike so kinji ko to kiyi farin ciki sosai kinji ko zonan." Ta d'aga masa ka tare dariya tare da isa inda yake kamar dai yanda ya buqata daga gareta, ya shafi fuskarta tare da sunbatarta a ka dama gefen fuska cike da d'auki ta fad'a jikinsa, shi kuwa ya runguma ta yana wani shafar kanta a zahirin gaskiya yana matuqar qaunar qanwarsa sosai. Su Ummu sai wani kallonsu suke suna murmushi sai kuma zuwa wannan lokacin ne Abba yayi magana.

"Anwar a gaskiya kana sangarta *Afnan* sosai ina jin dad'in yanda kake san qanwarka tare da nuna mata kulawa sosai. Anwar soyayya da qaunar da kake nuna wa *Afnan* ko mu iyayen ta bama nuna mata, Anwar idan kaci gaba da sangarta *Afnan* haka kana shagwa'ba ta to abin zai yi yawa sosai sabo da." "A'a Abba ba abin da zai faru qanwata ta tantanci ta samu duka soyayya ta, ita qanwata ce to zan iya yin komai sabo da ita sannan kuma zata kasance yarinyar kirki sosai kamar dai yanda muke yi mata fata. Abba sangarta yaro bai yasa ya lalace sai idan har ba a yi hakan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login