Showing 21001 words to 24000 words out of 142761 words

Chapter 8 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

hanun sa tare da fad'ar sunan sa sannan yaci gaba da magana.

*"Adeel* ya kamata mu tafi gida karka damu zan siya maka ice cream da chocolate ai zaka sha ko.?" "A'a ni ina san na zauna tare da Mummy to ba zan tafi ba." *"Adeel* hak'uri kawai zan baka domin dole zamu tafi yanzu." Ya riqo hanun sa domin su tafi lokaci d'aya ya saki kuka yana anbatar sunan Mummy kuka yake sosai, haka kukan sa yayi ta mata yawo a ka da sauri ta janye pillow da yake kunnan ta tare da kai kallonta ga yaronta wanda yake ta fad'ar sunan ta. Da sauri ta tashi ta nufi inda yake ta wani ri e hanun sa ta qara da yin hugging d'in sa shi kuwa yayi kwance jikin ta yana fad'ar sunan ta, Umma sai wani kallonsu take hakama Prof shi ma kallonsu yake kallo sosai ya nisa tare da jan numfashi yana cewa.

"Aisha a haka kamar kin dawo haiyacinki amma kuma ba hakan bane, gaskiyar ita ce ba zaki iya kulawa da kowa ba dan haka dole zan tafi da *Adeel* ki yafemin a kan hakan dan Allah." Ya kai hanun sa ya janyo *Adeel* domin tafiya shi kuwa sai kuka yake kuka sosai hakama Aisha kuka take, haka cikin rashin tausayi ya d'auki *Adeel* suka fice yayin da yaron yake kuka, Aisha na k'oqarin binsu Umma tayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun tana girgiza mata ka a lamar a'a, ita kuwa sai wani irin abu take ta qara fita haiyacinta Umma ta shiga rarrashinta tana yi mata addu'a............




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/30/2021, 11:50 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 09*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Wednesday 29/12/2021*

*Time 02:07pm*

*Typing................*

Haka Umma tayi ta k'oqarin ganin ta kwantar mata da hankali, amma sam tak'i ta saurare ta da k'yar Umma ta samu ta iya bata magana, wacce kuma daga bisani barci yayi nasaran d'auke ta. Umma tayi zugum sai wani kallonta take kallo sosai yayin da tausayin ta yayi yawan gaske a tare da ita sosai, ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da ƙuna sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, haka suka kasance na wani lokaci a can gurin Prof kuma lokaci zuwa lokaci ya kan tafi da *Adeel* gidan Umma domin ya duba Mummyn sa. Wacce har zuwa wannan lokacin bata cikin kyakkyawan yanayi, bayan wasu ƴan watan ni Prof ya bar garin Katsina ya koma garin Bauchi da aiki. A kullum a ko yaushe *Adeel* cikin kukan ya kai shi gurin Mummyn sa yake, amma sai dai ya ba shi hak'uri yana rarrashin sa tin yana damuwa har ya fara sabawa da rashin ta, ya cigaba da rayuwar sa daga bisani kuma Prof ya saka shi school.

*England*

Zaune take tana ta aikin dannar waya ga a lama chart take k'arar da taji ne yasa ta saurin d'ago fuskarta, tayi tozali da fuskar Ahmad ya fito cikin wata kyakkyawar shiga ta k'ananan kaya shigar ta amshesa sosai, yayi matuqar yin kyau sosai sai wani lallausan murmushi yake wanda ya qara bai yana a salin kyan fuskarsa. Hakan yasa ta rufe sa da ido tana kallonsa kallo sosai lokaci d'aya ta sami kanta da jin yana birgeta matuqar birgewa sosai, shi kuwa ta gefen ido yake satan kallonta ganin ya doshi ofa ga a lama fita zai yi tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. Ya tsaya tare da juya wa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna sai wani kallon juna suke kallo sosai, wani irin kallo suke yiwa juna wanda suka gagara fahimtar mai suke nufi da shi, sun jima sosai a haka sannan daga bisani ya amsa ta.

"Ahlam kamar kin kira ni ko? To fad'a min miye sabo da ina sauri zan d'auko yarona daga makaranta.?" Ha!!! Ta nisa sosai tare da jan numfashi tana mai sauke a jiyar zuciya cikin tautasa murya tare da kwantar da ita take magana. "Am Yaya Ahmad shin zamu iya tafiya tare please.?" Magana take cikin wata irin murya mai dad'in sauraro, shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "shikenan zamu iya tafiya amma ki fara shiga ciki ki sauya wannan shigar da take jikin ki sai mu tafi." Ta kai kallonta ga jikin ta tana kallon kanta wata riga ce a jikin ta, wadda tsayin ta iya guiwa ne hakama rigar shara-shara take tayi kwance jikin ta, hakan yasa duk ta fito da surar jikin ta wanda kuma tana yin duka hakan ne sabo da taja hankalin ta a kanta. Dalilin ta na yin hakan kuma shi ne zuwa wannan lokacin ita ta fara san shi, ta mai da kallonta garesa tana wani lallausan murmushi tare da jinjina masa ka tana cewa, "shin wai ba zai yu ni na fita a haka ba.?"

Wani irin kallo yake yi mata mai cike da jin mamakin abin data fad'a. "Ahlam shin kin duba kanki da kyau kuwa ta yanda zaki tantance irin shigar da take jikin ki? to ki sani ni sam ba zan ta'ba baki damar da zaki fita a haka ba kawai ki zauna a gida sai na dawo." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa ba tare daya jira yaji mai zata fad'a ba, ita kuwa ta bisa da kallo har ya fice yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi. Yayin da take jin yana birgeta sosai ta juya ta nufi bedroom d'in ta yayin da take magana da zuciyarta, "Yaya Ahmad gaskiya kana buqatar birge ni sosai ina fatan ina da muhalli a cikin zuciyar ka dama rayuwar ka gaba d'aya." Tayi kwance tare da rufe idanuwan ta sai wani farin ciki take ji yana shigar ta sosai.

Bayan wani lokaci Ahmad ya dawo tare da *Adyan* sai dai basu sami Ahlam a parlour ba, da sauri *Adyan* ya nufi bedroom d'in ta har yana gudu yayin da yake fad'ar sunan ta Ammie. Ahmad ya bisa da kallo yana murmushi mai tare da ar dariya yayin da yake jin wata qaunar sa tana qara shigarsa. Ya shiga ciki ya same ta kwance da gudu ya hau gadon tare da fad'a wa jikin ta yana fad'ar sunan ta Ammie, da sauri ta bud'e idanuwan ta tayi tozali da kyakkyawar faskar sa tayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa, tana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona shi ma abin da yake fad'ar mata kenan. Duk abin da suke fad'a a kan kunnan Ahmad sabo da yana kallonsu yayin da yake jin suna birgesa sosai, ya juya ya shiga ciki yayi tsaye jikin ofa lokaci d'aya dukansu suka kai kallonsu garesa suna murmushi, *Adyan* ya shiga anbatar sunan sa ya tashi daga jikin Ahlam ya nufi inda yake, Ahmad ya dukursa tare da rungumasa jikin sa yana sunbatarsa tare da furta masa kalmar ina qaunarka sosai d'ana. "Appa mai ya saka kake tsaye a nan kazo ka kusa damu domin mu rungumi juna, hakan zai saka muyi farin ciki sosai to mu tafi gurin Ammie."

Magana yake cikin kyakkyawan yanayi shi kuwa sai wani kallonsa yake hakama Ahlam kallonsa take tana murmushi mai tare da dariya. "Gaskiyar ka ne yarona amma yanzu da akwai buqatar kaci abinci sannan kuma a shirya ka, to ina ga wannan ne abin daya fi komai dace wa a yanzu, to yanzu fad'a min mai zaka ci.?" "Appa yau naci abubuwa da dama a school to shi yasa yanzu ni sam bana jin yunwa." "Shikenan amma duk da haka dole zaka sha madara kuma sam ba zan yarda da kalmar a'a ba ka ji ko." "Eh Appa zan sha yauwa Appa da akwai abin da zan sanar da dukanku." Ahlam ta tashi daga inda take ta nufi inda suke ta zauna tare da shafar kansa ta qara da sunbatarsa tana cewa. "Rabin raina fad'a mana koma miye? Tabbas zamu yi matuqar farin ciki da duk abin da zaka sanar damu, to fad'a mana miye.?" Cike da d'auki yake sanar dasu, "Appa Ammie an d'auke ni cikin yaran da zasu yi wasan tseren keke da kuma kwallon k'afa, ina farin ciki sosai kuma ina fatan nayi nasara a cikin gasar amma kuna farin ciki kuwa.?"

Ahlam ce wadda take amsa shi yayin da Ahmad ya rufe shi da ido yana kallonsa, "eh rabin raina muna farin ciki sosai sannan kuma zaka yi nasara sabo da kai d'in na musamman ne, ina yima fatan nasara ďana." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi, a zahirin gaskiya tana farin ciki sosai yayi hugging d'in ta ita kuwa ta sunbacesa a ka dama gefen fuska, tana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona ya amsa ta da nima ina qaunarki sosai. Sun kai kallonsu ga Ahmad wanda yayi shiru tamkar da bai ya gurin sai wani kallon *Adyan* yake yayin da yake magana da zuciyarsa. "Kayi hak'uri ka yafemin yarona sabo da a yanzu sam ba zan iya baka abin da kake so ba, ina nufin ni sam ba zan barka ka shiga wannan gasar ba duk da cewar kana da buri sosai a kan hakan. Zanyi hakan ne sabo da lafiyar ka domin yin wannan gasar zai iya cutar da kai sosai da kuma lafiyar ka to ni sam ba zan ta'ba barin hakan ta faru ba, to ina fatan zaka fahimce sannan kuma ka iya fahimta na ina qaunarka sosai d'ana."

Dafashi d'in da tayi ne tare da fad'ar sunan sa da k'arfi yasa shi kai kallonsa gareta ba kuma tare daya amsa ta ba. "Yaya Ahmad qlau kake kuwa fad'a min mai kake tinani? Shin ka ji abin da *Adyan* ya fad'a kuwa amsa min shin qlau kake kuwa gaskiyar zaka fad'a.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "ki shirya shi ni zan had'a masa madara." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi domin tafiya da sauri *Adyan* ya ri e hanun sa yana cewa. "Appa baka yi man fatan nasara ba amma kana farin ciki kuwa.?" Ya dukursa tare da shafar fuskarsa ya qara da sunbatarsa, "eh masoyi ina farin ciki sosai sannan kuma ina yima fatan nasara, yanzu ka tafi Ammie ta shirya ka Appa kuma zai had'a maka madara ka ji ko." Ya jinjina masa ka yana dariya shi kuwa murmushi yake ya qara sunbatarsa sannan ya sake sa daga rungumar da yayi masa ya tashi ya fita, Ahlam tabi shi da kallo har ya 'bace sannan ta dawo da kallonta ga *Adyan* ta fara cire masa kayan jikin sa sannan ta rik'a hanun sa zuwa toilet.

Ba jimawa ta fito da shi ta shirya sa sun fito parlour sun samu Ahmad zaune ya tare su da murmushi, da gudu *Adyan* ya nufi inda yake ya zauna a kan cinyarsa Ahmad ya sunbacesa tare da fad'ar sunan sa. *"Adyan* bana fad'a maka cewar ka dena yin gudu ba amma mai ya saka kake yi.?" "I'm so sorry Appa please." "OK yanzu ka sha wannan." Nan ya shiga ba shi madara ya kuma sha sosai bayan ya qarasa ya tashi yana cewa. "Appa Ammie ni zan tafi nayi wasa." "Shikenan yarona kayi ko wane wasa amma banda kwallo, tsalle, da gudu ka ji ko to ka kula sosai." Lokaci d'aya ya 'bata fuska kamar zai saki kuka cikin hanzari Ahlam ta anbaci sunan sa ta kuma ci gaba da magana. "Karka wani damu rabin raina zaka iya yin ko wane irin wasa idan kana so, jeka kayi kwallo, tsalle, da gudu dama duk abin da kake so ka ji ko." Lokaci d'aya ya saki wani kyakkyawan murmushi cike da d'auki ya juya ya fita, Ahmad na kiran sa amma sam bai amsa ba ya fice abinsa Ahmad ya dawo da kallonsa ga Ahlam kafin ya furta komai tayi masa rigagi.

"Yaya Ahmad mai yasa kake haka mai yasa kake dakatar da yaron daga farin ciki? Yau yaronmu yana farin ciki sosai sabo da gasar da a ka za'besa amma kuma kai sam baka farin ciki da hakan, yanzu kuma kana k'oqarin dakatar da shi daga yin wasa Yaya Ahmad mai ya saka kake yin duka wannan shin da akwai wani abin da kake 'boye min a game da yaronmu.?" Shiru bai amsa ba sai ma yunk'urin tashi da yayi da sauri ta dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa, tare da zaunar da shi sai wani kallonsa take kallo sosai ta gama fahimtar cewa sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi, hakama da akwai unci da damuwa sosai a tare da shi ta nisa tare da jan numfashi tana anbatar sunan sa. "Yaya Ahmad dan Allah ka amsa ni shin kana 'boye man wani abu a game da *Adyan* gaskiyar zaka sanar da ni.?" Yayi shiru kad'an yana nazari daga bisani ya girgiza mata ka tare da fad'ar sunan ta. "Ba komai ni sam bana 'boye komai kawai dai ni sam bana da buqata da hakan, ina nufin bana buqatar naga yana irin wannan wasan to shi yasa nake dakatar da shi, Ahlam ni ina yin abin daya dace ne a kan yarona to dan Allah karki ce zaki dakatar da ni please."

Ya yunk'ura zai tashi da sauri ta dakatar da shi ta hanyar furta masa, "a'a hakan sam ba zai yu ba ni sam ba zan baka damar da zaka dakatar da farin cikin yarona ba, to ya kamata ka dakatar da wannan burin naka sabo da cikar burin yaronmu. Sannan kuma zai yi gasar kamar yanda a ka tsara hakan sam ba zai canja ba to kawai ka amince da hakan ka ji ko." Ya girgiza ka yana cewa, "Ahlam wannan ne abin da ba zai ta'ba yuwa ba ni ba zan ta'ba amince wa hakan ba na har abada, ni abu mai kyau nake sannan kuma rayuwa mai kyau nake baiwa yaronmu to ya kamata ki fahimci hakan sannan kuma dai karki yi yunk'urin dakatar da ni dan Allah." yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyarsa, da sauri ta tashi ta bisa a baya dan ganin inda ya nufa, yana fita kai tsaye gurin *Adyan* ya nufa domin ganin abin da yake.

Tin daga nesa ya hange sa yana aikin buga kwallo wanda yake had'awa da gudu, hakama ya gama fahimtar cewa sam ba shi da kuzari sosai da sauri ya nufi inda yake har yana gudu, kamar daga sama ya ga Ahlam ta sha gaban sa tare da fad'ar sunan sa, "Yaya Ahmad ni fa ba zan baka damar da zaka dakatar da shi ba to ya kamata ka fahimci hakan ka ji ko." "Ahlam ki janye min a hanya wai mai yasa ka sam bakya fahimtar abin da nake fad'a ta ya kike tinanin cewar zan cutar da *Adyan?* A'a ni sam ba zan ta'ba aikata hakan ba to kawai ki yarda da ni please sabo da ina yin abin daya dace ne, ya kamata na tafi sabo da akwai buqatar na dakatar da shi yanzu." "A'a ba zaka dakatar da shi ba har sai idan ka sanar da ni a salin gaskiyar. To yanzu fad'a min mai kake 'boye min a game da *Adyan.?"*

Shiru bai yi magana ba sai ma k'oqarin tafiya yake domin zuwa gurin *Adyan* amma ta hana shi, sai abu d'aya take maimaita masa ya nisa tare da jan numfashi yana mai sauke a jiyar zuciya. "Shikenan zan sanar da ke kamar yanda kika buqata daga gareni abin shi ne." Kafin ya furta komai ya hangi *Adyan* yana k'oqarin kife wa qasa, da sauri ya janye Ahlam gefe ya nufi gurin sa da sauri har yana gudu, da sauri Ahlam ta kai kallonta garesa cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ta nufi gurin da gudu yayin da take fad'ar sunan sa. Ahmad ya isa inda yake da sauri ya ri e sa ya fad'a jikin sa lokacin yayi daidai da zuwan Ahlam, sun shiga jijjigasa suna fad'ar sunan sa ganin yanayin sa ya soma tsananta sosai, yasa suka d'auke sa zuwa asibiti..................




Please ina buqatar addu'ar ku mura na damuwa sosai.





*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/30/2021, 9:22 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login