Showing 111001 words to 114000 words out of 142761 words

Chapter 38 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

yayi jim kad'an sannan ya amsa shi. "Hakan yayi kyau ina fatan kar yayi nasara a kan wannan shari'ar, Allah ya hana masa gaske ya k'ara masa duhu fiye da wanda yake tare da shi sosai." "Amin Aboki nima wannan ne fatana to Allah ya amince mana Amin." "Amin bro ka shirya wa gobe domin zamu tafi gurin shari'ar, domin ganin yanda Prof Abas zai fad'i sabo da ba zai tab'a yin nasara ba." "Shikenan Aboki zan shirya wa hakan insha Allah." Magana suke cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar su, take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa ga wanda ya gani. Sun jima sosai a nan tare sannan daga bisani *Adnan* ya masa sallama ya tafi.

Cikin rashin sa'a ya dawo masaukin Dady, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi, cikin hanzari Dady ya shiga tambayar sa abin da yake faruwa da shi, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Kayi hak'uri Dady sabo da *Adnan* ya kasa yarda da tayi na, sam yak'i amincewa da buqata na ya fad'a min cewar ba zai iya taimaka maka ba. Ba kuma tare daya sanar da ni wani dalili ba, Dady *Adnan* yana da matuqar kirki sosai amma ban san dalilin da yasa yayi haka ba, amma koma miye na tabbata yana da k'wakk'waran dalili wanda yake da matuqar girma sosai. Naso a ce na san gaskiyar ta yanda zan iya saurin fahimtar sa, Dady ni yanzu ban san ya zanyi ba amma ina ganin a yanzu mafia ďaya muke da shi. Dady kawai ka siyar da wasu daga cikin kadarorin ka, k'aramin Campany, Restaurant, ko ďaya daga cikin makarantu ta yanda zaka samu kud'ad'en da zaka biya su da shi."

"A'a *Adeel* ni sam ba zanyi hakan ba ba zan rabu da komai nawa na, sabo da hakan sam ba laifi na bane ni sam ban aikata wani kuskure ba, to bai kamata su hukunta ni ta hakan ba, ďana ko da mai zai faru da ni to ba zan rabu da wani abu daga cikin kadara ta ba, nayi aiki tuk'uru sannan na sha wahala sosai kafin na gina kai na, *Adeel* kai kad'ai kake da hak'i da wannan duniyar tawa, kai kad'ai kake da mallakin duk wani abin dana mallaka, to ba zan tab'a barin na rasa duk wani abin da yake nawa ba wannan ce gaskiyar." "Dady ni kawai zan rayu cikin farin ciki ne idan kana farin ciki, kai nafi buqata fiye da duk wani abin daka mallaka, dan haka kawai kayi abin daya dace dan Allah karka bari su Uncle Bashir suci zarafin ka."

Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawa a tare da shi, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. Prof ya shiga rarrashin sa yana ba shi magana haka suka kasance, na tsayin wani lokaci sosai sannan daga bisani suka kwanta, washe gari misalin k'arfe goma na safe suka shiga kotu, bayan sauraran ko wane b'angaran na lauyoyi Al'qali ya yanke hukuncin cewa, Prof Abas zai biya su Prof Bashir duka kud'ad'ensu cikin mako biyu. A haka shari'ar ta tashi hankalin Prof Abas ya tashi sosai da hukuncin da Al'qali ya yanke, hakama *Adeel* shi ma yana tare da k'unci sosai tsaye suke jikin mota, suna tinanin mafua sai gasu *Adnan* bayan sun gaisa *Adyan* yaci gaba da magana.

"Prof Abas Muh'd ya kamata muyi magana yanzu." "Waye kai kuma mai ya saka kake san kayi magana da ni.?" "Kana magana da *Adyan Ahmad Aliyu* to ya kamata ka saurare ni, sabo da zan iya taimaka wa ga buqatar ka to ya kamata, ka saurare ni sabo da a yanzu ni ne kawai wanda zai iya taimakon ka." "Waye kai da kake magana da ni haka cikin gadara.?" Kafin ya furta komai *Adeel* ya amsa shi ta hanyar sanar da shi waye shi, Dady ya jinjina ka tare da mai da kallonsa ga fuskar *Adyan* yana fad'ar sunan sa.

*"Adyan* a kan me kake magana kuma wane taimako zaka yi min.?" "Prof Abas na san cewar a yanzu haka kana matuqar buqatar kud'i sosai, sabo da ka biya su Prof Bashir kud'ad'ensu to ni zan baka idan kana da buqata." *"Dr Adyan* wai da gaske kai zaka bawa Dady na wad'an kud'ad'en.?" "Eh *Adeel* zan ba shi duka kud'ad'en idan har zai siyar min da duka kadarorin sa." Da sauri har yana sarkewa Prof yake magana. "A'a ba zai yuba ni ba zan siyar da komai nawa na." "Shikenan kaci gaba da ri e kadarorin ka amma ka sani kawai zaka k'are ne a gidan yari." Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa *Adeel* yake magana. *"Dr Adyan* mai ya saka kake yiwa Dady na magana haka.?" *"Adeel* ni kawai ina tausayin Dadyn ka ne sannan kuma ina buqatar na taimake sa, amma kuma na gama fahimtar cewa shi sam baya buqatar hakan shikenan ni zan tafi." Ya juya domin tafiya da sauri *Adeel* ya dakatar dasu ta hanyar anbatar sunan *Adyan.* *"Dr Adyan* dan Allah d'an dakata kad'an." Ya jinjina masa ka a lamar to shi kuwa ya mai da kallonsa ga Prof tare da fad'ar sunan sa.

"Dady zuwa yanzu bamu da wata mafua to na ro e ka daka siyar da duka abin da kake da shi, ka biya su Uncle Bashir kud'ad'ensu sabo da ba zan jure ganin ka a gidan kurkuku ba. Hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai to dan Allah karka bar hakan ta faru please." Magana yake cikin wani irin yanayi na damuwa sosai, yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Su *Adnan* sai wani kallonsa suke kallo sosai mai cike da jin tausayin sa sosai, sai sun bar abin a zuciyarsu ba tare da sun nuna ba cike da damuwa Prof yake magana. "Shikenan ďana zanyi hakan sabo da kai to ka dena kuka ka ji ko." Magana yake yana wani shafar fuskarsa tare da sunbatarsa, ya mai da kallonsa gasu *Adnan* tare da fad'ar sunan *Adyan.* *"Dr Adyan* zan siyar ma da makaranta da Restaurant amma banda k'aramar ma'aikata." "A'a ni duka ukun nake so musamman ma ma'aikatar ita ce abar da nafi so." "A'a ni ba zan iya rasa wannan campaning ba, sabo da shi ne kawai abin daya ragemin dan haka sai dai kawai na baka hak'uri." "Shikenan kawai mu fasa hark'allar ka ga sai ka shirya wa zama gidan kurkuku."

"A'a hakan sam ba zai yu ba Dady naro e ka daka amince da buqatar sa, sabo da wannan ita kawai ce mafutar mu a yanzu." "A'a ďana ya kamata na bar wannan campaning sabo da kai, domin kai ne kawai wanda zai mallaki wannan campaning, sabo da ba zai yu na b'ata rayuwar yarona ba da hanayena. *Adeel* kai ďin ďana ne to zanyi komai sabo da kai ina sanka sosai yarona zo nan." Ya wani janyo sa jikin sa yana sunbatarsa su *Adnan* kuwa sai kallonsu suke. Bayan sun sake juna Prof ya sauke kallonsa ga fuskar *Adyan* yaci gaba da magana. *"Adyan* kawai ka bani kud'in na amince sabo da wannan buqatar yarona ce." Sai zuwa wannan lokacin ne *Adnan* yayi magana. "Prof Abas ga a lama kana qaunar yaronka sosai shin haka kake qaunar sauran yaran naka.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Ni yaro ďaya kawai nake da shi d'an da nake matuqar alfahari da shi, ba kuma kowa bane face *Adeel* shi ne d'an dana mallaka a rayuwata. Shi yasa nake matuqar masifar qaunar sa sosai shi yasa zan iya yin komai sabo da shi."

"Hakan yayi kyau sosai, to yanzu sai ka had'a duka takardun guri ďaya ni kuma zansa a shirya kud'ad'en, sannan kuma kazo da mutanan da zasu zame maka shaida nima zanso da nawa shaidun. To muyi hakan zuwa yamma fatan ba zaka canja hakan ba.?" "Shikenan kawai ka sanar da *Adeel* inda zamu had'u da kuma lokacin da zamu had'u." "Hakan yayi kyau sosai ku zame ni gidan Abbu *Adeel* zai kai ka gidan, to ba zaka wahala gurin had'uwa da ni ba kazo k'arfe 05:00pm hakan yayi." Magana yake cikin isa tare da nuna gadara Prof sai wani kallonsa yake ba tare daya furta masa komai ba, sai dai *Adeel* ya amsa shi magana yake cike da k'unci tare da tarin damuwa sosai. *"Dr Adyan* koma dai miye wannan Dady na ne to zanyi farin ciki sosai idan ka mutunta shi, shikenan zamu zo gurin kamar yanda ka fad'a sannan kuma muna godiya sosai."

Dukansu kallonsa suke yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare dasu, *Adyan* ya amsa shi ta hanyar jinjina masa ka a lamar to da kuma haka suka yi sallama. Dukansu suka nufi gida sun isa masauki Prof sai kai kawo yake yana huci *Adeel* ya anbaci sunan sa yana cewa. "Dady dan Allah ka dena wannan yawan damuwar sabo da yanayin zai iya cutar da kai sosai." "D'ana dole zan damu a kan hakan sabo da narasa komai a lokaci ďaya, *Adeel* na jima sosai ina shirya wa rayuwarka amma lokaci ďaya narasa komai. Sam ba zanso ka rayu kamar yanda ni na rayu ba, ina yi ma fatan ka rayu cikin kyakkyawar rayuwa ga shi kuma lokaci ďaya, komai ya lalace dan Allah ka yafemin na san cewa na cutar da kai da yawa to ina fatan zaka yafemin."

"Dady shin ko zaka dena fad'ar haka? Ni kai na fiso fiye da duk abin daka mallaka, abin farin cikin shi ne kai ka bani duka soyayyar ka to wannan kawai ya isa, sannan kuma ina alfahari da hakan sosai ina sanka sosai." Cike da soyayyar juna sunyi hugging juna Dady sai wani sunbatarsa yake, bayan wani lokaci suka sake juna nan kuwa Dady ya shiga had'a takardu. Sun shirya duka takardun tsab yayin da k'unci da damuwa suka yi yawan gaske a tare dasu, haka yake ko a gurin su *Adnan* suna isa gida *Adyan* ya fara shirya kud'ad'en, misalin k'arfe 05:00pm daidai su *Adeel* suka iso gidan Abbu. Ba jimawa suka had'u dasu *Adnan* ba wani d'aukan lokaci suka fara abin daya tarasu, bayan sun qarasa Prof Abas Muh'd ya bawa *Adyan* kundun takardu, shi kuwa ya ba shi kud'i an yi takardu sun saka hanu tare da duka shaidu. Bayan sun k'arasa kammala komai su Prof Abas sun tashi sun tafi, bayan tafiyar su sun mai da kallonsu ga juna *Adnan* ya anbaci sunan *Adyan* yana cewa.

"Aboki bana tunanin cewa *Adeel* zai iya jure wannan, sabo da yanayin yana da zafi sosai Mum sam ba zata iya jure ganin shi a cikin wannan yanayin ba, to ya idan kuma yanayin sa yayi k'oqarin cutar da ita fa? Aboki ya kamata muyi tunani a game da wannan ina nufin yanayin Mum, Aboki ni kawai na damu ne a game da Mum da kuma yanayin da zata iya shiga." "Na fahimce ka Aboki amma kuma ya kamata muyi hakan, sabo da na tabbata idan Mum ta ji labarin cewa Prof Abas ya rasa koman sa to zata yi farin ciki sosai. To sam bana tunanin wani abu zai faru da ita to sam bai kamata mu samu damuwa ba." "Ina fatan hakan to yanzu miye tsarin mu na gaba.?" "Yanzu dai ni bani da wani shirin komai to kai kuma fa.?"

"Aboki nima bani da wani shiri, amma kuma nayi matuqar damuwa sosai a kan *Maman Amna,* sabo da ita ďin tayi matuqar damuwa sosai a kanmu da kuma rayuwar mu, Aboki ni ina ganin kamar ya kamata muyi magana da ita, Aboki ina kamar akwai buqatar ita ta san gaskiyar a game damu, ko ba komai hankalin ta zai kwanta sannan kuma zata samu natsuwa." "Shikenan zamu yi magana a game da wannan wani lokaci." Ya fad'a yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan. Su Prof Abas sun isa masauki yayin da damuwa tayi yawa sosai a tare dasu, musamman ma Prof *Adeel* ya shiga rarrashin sa yana ba shi magana, har ya samu ya iya fahimtar sa haka yaci gaba da kasancewa tare da shi. Washe gari bayan sunyi break past *Adeel* ya sauke kallonsa ga Prof tare da fad'ar sunan sa.

"Dady ni ina san zan tafi na duba Mum to ka kula da kanka sosai dan Allah." "Eh zanyi na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka." Ya amsa da Amin yana murmushi lokaci ďaya suka yi hugging juna, bayan wani lokaci suka sake juna *Adeel* ya tashi ya fita, ba jimawa da tafiyar sa Prof shi ma ya tashi ya fita. *Adeel* na cikin fira dasu Umma wayar sa ta d'auki ruri ya d'aga tare da sallama, daga ciki an amsa shi an kuma ci gaba da magana. "Kana magana da Dr Sauban Dadyn ka yana asibiti yayi hatsari." "Mine wane asibiti.?" "Hamdala hospital." Ya amsa da ok sunyi sallama ya fara sanar da Mum sannan ya tashi ya tafi, su Umma sun bisa da kallo suna girgiza ka har ya fice....................




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/6, 12:48 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 46*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/



*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Friday 04/03/2022*

*Time 12:17am*

*Typing................*


Ya isa asibiti cikin hanzari tamkar wani zararre, nan ya shiga tambayar nurse inda Dadyn sa yake. Bai wani jima sosai ba ya samu isa d'akin da yake, Doctor's sun dakatar da shi daga shiga ciki ya shiga safa da marwa, bayan wani lokaci suka fito Dr Sauban ne yake magana da shi. "Kai ne yaronsa.?" Cikin hanzari har yana sarƙewa yake amsa mashi da eh Dr Sauban ya cigaba da magana. "Dadyn ka baya cikin kyakkyawan yanayi zan kuma iya cewa da kai, yanayin sa ya tsananta sosai yana matuƙar buƙatar taimakon gaugawa sosai." "Doctor dan Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da Dady na.?" "Am gaskiyar ita ce Dadyn ka ya samu karaya a duka k'afafun sa, ya zama dole a yi masa aiki yanzu sannan kuma yana buqatar jini sosai, sabo da ya rasa jini sosai yanzu ka biyo ni zuwa office sai muyi magana a can."

Ya amsa da to sun juya sun nufi office ďin Dr Sauban, sun isa office d'in tare da shiga ciki bayan sun zauna Dr Sauban yaci gaba da magana. "Yanzu zamu tafi ka cike takardun tiyata sannan kuma ka bamu jini naka ko na wani daban." "Doctor nawa ne kud'in aikin.?" "Abin da yawa to kud'in zai iya kaiwa d'ari uku da hamsin." Cike da firgici ya wani zaro ido yana kallonsa, cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Doctor dan Allah ko zaku iya yi masa aikin kafin na iya had'a muku kud'in please.?" "A'a sam hakan ba zai yuba kawai zamu yi masa aiki ne idan ka biya kud'in aiki." "Shikenan zan kawo kud'in yanzu bara na tafi na kawo kud'in." Dr Sauban ya amsa shi da to shi kuma ya tashi ya fita, zuwa wani gurin daban domin samo kud'in da za a yi masa aiki.

Tin a hanya yake kiran layin *Adyan da Adnan* amma layin yak'i tafiya, hakan tasa ya nufi gidan Abbu gurin *Adyan* a nan ma yayi rashin sa'a sabo da baya gida. An sanar da shi cewar ya fita tare da *Adnan* cikin hanzari ya juya mota ya nufi gidan Papa, ganin motar *Adyan da Adnan* ya tabbatar masa da cewar dukansu suna ciki, ya fito mota ya nufi ciki zaune suke suna fira cikin kyakkyawan yanayi tare da matayansu, lokaci d'aya suka ji a na buga masu k'ofa, *Adnan* ne wanda ya tafi ya bud'e k'ofar ya samu *Adeel* tsaye bakin k'ofa. Yanayin sa yayi matuqar tsorata sa sosai cikin hanzari ya shiga anbatar sunan sa, kallonsa kawai yake ba tare daya amsa shi ba *Adnan* ya janyo hanun sa sun shiga ciki. Lokaci ďaya dukansu suka shiga tambayar sa abin da yake faruwa da shi, magana yake cikin wani irin mummunan yanayi mara dad'i yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo.

*"Adnan Adyan* naro e ku da ku taimaki Dady na, shi yayi hatsari yana cikin mawuyacin hali sosai, ya rasa jini sosai sannan kuma dole sai an yi masa aiki. Suna buqatar dubu d'ari uku da hamsin, mun riga da mun bawa Al'qali duka kud'ad'en to sam bana tunanin zai bani kud'in da nake buqata. To zanso wani daga cikin ku ya bani a ron kud'in ni kuma zan biya kud'in daga baya, *Dr Adyan* dan Allah zanso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login