Showing 63001 words to 66000 words out of 142761 words

Chapter 22 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

a gurin, hakan yana matuqar yi masa dad'i sosai tare kuma da qara masa gwarin guiwa sosai. A zahirin gaskiya yana da tarin masoya da mabiya sosai duk da cewar basu san a salin fuskar sa ba, sabo da yana 'boye fuskar sa da fice max ga kuma hular kwano hakan yasa ba wanda ya san fuskar sa. Duk da cewar shi ne wanda yazo na k'arshe a tafiya amma kuma shi ne wanda yayi nasaran lashe wasan, ko yaushe shi ne wanda yake yi nasara a wasan hakan tasa ya tara tarin masoya da mabiya sosai. Sunan *Adlishart* ya zaga ko ina na duniya amma kuma ba wanda ya san fuskar sa, kamar dai tauraron mawak'in nan wanda yayi suna a k'asar England dama k'asashen duniya baki ďaya, wato secret super star wanda wasu mutane suke dan gan tasa da aljan.

Ya kar'bi kyautar sa kamar dai ko yaushe yayi photo da masoyan sa sannan ya tafi, wanda kuma kai tsaye office ya nufa a zahirin gaskiya yana tare da gajiya sosai, yana shiga ciki ya nufi firij ya d'auki rubar ruwa ya qarasa inda maganin sa ya sha magani, ya tafi yayi kwance a kan kujera sai wani irin yanayi mara dad'i yake ji a tare da shi ba jimawa sosai yayi barci.

*Nigerian.*

Gudu take iya k'arfin ta tana furta kalmar ku bani yarona yayin da take wani irin kuka abin tausayi, daga gaban ta kuma wasu yara ne suke tsokanar ta da teady a matsayin yaronta da take nai ma. Tana cikin binsu lokaci ďaya ta ji ta fad'a ruwa cike da firgici ta saki ihu tana kururuwar nai man taimako, yaran kuwa sai dariyar ta suke suna tsokanar ta yayin da ita kuma take kuka. "A'a ku dena nace ku dena a'a! A'a!! A'a!!!." Ihun sa ne ya tashi Prof daga barci ya shiga tashin sa ta hanyar buga pillow da yake kwance tare da fad'ar sunan sa, firgigit ya tashi wani a firgice yayin da bakin sa yake furta kalmar a'a cike da firgici ya fad'a jikin Dadyn sa, shi kuwa yayi masa wata kyakkyawar runguma sosai yana wani buga bayan sa, bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a haka *Adeel* ya fara magana. "Dady wacece ita kuma mai ya saka ko yaushe take zuwa a cikin barci na? Hakan yana saka wa naji wani iri sosai sannan kuma ina shiga k'unci sosai." "Ka dena damuwa yarona sabo da kawai a mafarki ne kuma mafarki ba gaskiya bane, ni ba zan ta'ba barin wani ya cutar da kai ba zanci gaba da kare ka iya rayuwa ta wannan alkawari ne." "Na gode Dady na." Ya fad'a tare da qara shigewa jikin sa shi kuwa ya runguma sa sosai jikin sa, sun jima a haka sannan daga bisani suka koma barci bayan kwana biyu suna cikin cin abinci Prof ya anbaci sunan sa. *"Adeel* ina san na shirya zuwan ka U. K makaranta ina san ka kammala karatun ka na zama Prof, zanyi farin ciki sosai idan har kai ma ka zama Prof to kawai ka fara shirin tafiya."

Yayi shiru kad'an yana nazari sannan daga bisani ya amsa shi, "Dady gaskiyar ita ce ni bana san na tafi ko ina, ka riga daka san komai a game da lafiya ta shi yasa ba zan iya yin nesa da kai ba. Dady kai kad'ai nake da shi to ba zan ta'ba barin ka ba na har abada, Dady ni wannan degree dana yi ya ishe ni sam bana buqatar na zama Prof sabo da ina da kai, sannan kuma ina tare da kai to wannan ma kawai ya isa kuma ina farin ciki sosai da hakan ina qaunarka sosai Dady na." "Karka damu *Adeel* sabo da ni zanyi komai sabo da kai ina qaunarka sosai d'ana, kai ne d'an da nafi so kai ne wanda na za'ba fiye da sauran sabo da kai ne wanda nafi so, ina sanka da duka zuciya ta dama rayuwa ta gaba d'aya shi yasa na baka duka soyayya, ina matuqar qaunar ka sosai d'ana." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai. Cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adeel* yake magana, "Dady nifa sam na kasa fahimtar abin da kake fad'a, shin wai kai kana da wasu yaran ne bayan ni.?"

Ya girgiza ka yana murmushi sannan ya amsa shi, "A'a ďana ba abin da nake nufi ba kenan ba, ina nufin kai ne kawai ďana sabo da tin bayan Mummyn ka ta mutu, ban k'ara tinanin nayi wani aure ba sabo da kai kad'ai nake so a matsayin ďana wannan ce gaskiyar ďana." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar ina qaunarka sosai d'ana, yayi murmushi sosai yayin da farin ciki yake ta shigarsa sosai, cike da farin ciki da d'auki ya fad'a jikin sa shi kuwa yayi masa wata kyakkyawar runguma sosai. Yana ta shirin fita sai ga Anwar ya shigo Abba ya koma ya zauna bayan sun gaisa Abba yaci gaba da magana. "Anwar dama kuwa da akwai abin da nake san na sanar da kai, jiya Baba ya saka ranar auran *Afnan* da Auwal ta mako hud'u insha Allah." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Abba ni sam na kasa fahimtar abin da kake fad'a Auwal fa kace to ta ya ma hakan zata kasance? Mai ya saka Kaka zai yi haka amma Abba ka sanar da shi cewar *Afnan da Adnan* suna tare.?" "Eh Anwar na sanar da shi amma kuma sam bai saurare ni ba." "Shikenan ni zan kula da wannan zanyi komai domin na dakatar da auran, ni ba zan ta'ba barin wani ya raba su biyun ba wannan alkawari ne, to dan Allah karka dakatar da ni please." "Anwar ina jin tsoro sosai sabo da Baba yana da zafi sosai." "Karka damu Abba kawai ni zanyi abin daya dace ne, to zaka iya yarda da ni please." Ya jinjina masa ka a lamar to bayan wani lokaci suka tashi suka fita ko wannan su ya nufi office ďin sa..................





*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/23, 7:33 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 26*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Friday 21/01/2022*

*Time 05:25pm*

*Typing...............*

Yana ƙoƙarin fita da mota sai ga Anwar ya shigo da mota ganin sane yasa shi fitowa, yayi tsaye jikin mota ba jimawa Anwar ya fito ya kuma nufi gurin sa kafin ya furta komai ya masa ƴar rige. "Sannu da zuwa abokina kuma siriki na, yanzu nake ƙoƙarin tafiya zan koma Jos ne gurin aiki, saura kaɗan ka samu bani nan, to mu shiga daga ciki domin kuwa na tabbata gurina ka zo." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai. "Auwal ni sam bana buƙatar shiga ciki domin yin magana da kai, kafin yanzu nayi tunanin cewa kai aboki na gari ne a gare ni, sannan kuma Yaya na gari a gurin *Afnan da Adnan* amma kuma nayi kuskure sabo hakan k'arya ne, Auwal kamar dai ni na fad'a maka cewar karka shiga rayuwar *Afnan da Adnan* sabo da hakan zai cutar da su sosai. Na kuma ja maka kunne a kan cewa kabar zancen iya mu biyu kawai, to amma mai ya saka ka sanar da Kaka wannan? Ta ya ma har zaka yi tunanin aikata hakan shin ka kuwa san irin girman zunubin da kai ka aikata kuwa.?"

"To ka sani wannan ba kuskure bane a'a wannan zunubi ne kuma ni zan hukunta ka a kan zunubin ka, Auwal wallahi tallahi koma mai zai faru to zanyi komai domin na dakatar da auran ka da qanwata. Ba zan ta'ba baka damar da zaka cutar da *Afnan da Adnan* ba su biyun kawai an aife sune sabo da junansu, to kuwa zasu ci gaba da kasancewa a tare na har abada wannan alkawari ne kuma zan na cika alkawari na insha Allah." Magana yake cike da fishi da 'bacin rai sosai Auwal kuwa sai kallonsa yake yana murmushi, "Anwar ni na baka damar a kan ka aikata duk wani abin da zaka iya, amma kuma ka sani wallahi tallahi ba zaka ta'ba yin nasara ba sabo da Kaka yana tare da ni. To babu wani abin da zai dakatar da aure na *Afnan* nan da mako hud'u kamar dai yanda Kaka ya saka, Anwar a baya na goyi bayan ka sosai da zaka auri qanwata, amma kuma kai baka san ni nayi aure da qanwarka mai yasa kawai sabo da *Adnan* ne? Shi fa kawai mak'ocin kune kuma bare ni kuma abokin ka kuma ahalinka." Anwar ya dakatar da shi cikin tsawa tare da d'aga murya, "ya isa haka Auwal karka k'ara fad'ar wani abu a kan qanina kuma ka sani *Adnan* ahalinmu, shi ahali bawai yana nufin jini ba a'a kyakkyawar halak'a ita zata canja zuwa ahali. Auwal kasancewar Kaka yana 'bangaren ka hakan baya nufin ka samu qanwata, a'a ni ba zan ta'ba barin hakan ta faru ba wannan alkawari ne kuma zan cika alkawari na insha Allah."


Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa Auwal ya bisa da kallo har ta fice, shi ma mota ya shiga ya fita wanda kuma kai tsaye gidan Kaka ya nufa inda ya shiga sanar da shi k'arya da gaskiya. Kaka ya shiga rarrashin sa tare da nuna masa cewar yana tare da shi sosai, hakan ya qara masa farin ciki sosai bai wani jima ba kasancewar a hanya yake, yayi sallama da Kaka ya tashi ya kama hanyar jos domin koma wa gurin aiki, bayan tafiyar sa Kaka ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin Abba, ba jimawa ya d'aga kafin ya furta komai Kaka ya masa rigagi ta hanyar furta masa kalmar, "kazo yanzu ina san ganin ka." Yana kai k'arshen maganar sa ya kashe wayar sa ba tare da jira ya amsa shi ba. Hakan yayi matuqar saka Abba cikin sark'ak'iya sosai cikin hanzari ya bar office ya nufi gidan Kaka. Ya samu Kaka cikin fishi sosai cikin hanzari tare da nuna kulawa yake tambayar sa mai yake faruwa, cike da 'bacin rai sosai tare da tarin damuwa Kaka yake magana.

"Abubakar ya kamata ka k'ara sauri sosai gurin duka shirin ka domin na dawo da auran Auwal da *Afnan* mako biyu insha Allah." cike da jin mamakin abin daya fad'a Abba yake magana. "Baba shin wani abu ya faru ne mai ya saka zaka dawo da ranar mako biyu? Shin ni na aikata wani zunubin ne da kake hukunta ni ta wannan hanyar dan Allah ka sanar da ni please.?" Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi, "a'a wannan kawai hukunci na kenan kuma ba zan ta'ba canja hakan ba, to ka tafi ka ci gaba da shirin ka yanzu zaka iya tafiya." "Baba shin kai kana fishi da ni ne dan Allah ka yafemin please." "Abubakar ni sam bana fishi da kai to ka dena bani hak'uri Allah yama albarka." Ya amsa da Amin bayan wani lokaci ya tashi ya koma office bakin aiki, yayin da tausayin *Afnan da Adnan* yayi yawan gaske a tare da shi sosai da yamma bayan ya dawo gida yake sanar da Anwar abin da Kaka ya fad'a masa. "Anwar shin ka tafi gurin Baba ne dan Allah ka sanar da ni gaskiyar please.?"

Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, "a'a Abba ban tafi ba amma nayi magana da Auwal." Nan ya shiga sanar da shi komai, "Anwar mai yasa kayi hakan na fad'a maka cewar Baba yana da tsauri sosai, yanzu kaga irin hukuncin daya yanke ya dawo da auran mako biyu, ban kuma san abin da zan iya yi ba a cikin mako biyu domin dakatar da auran. Anwar ni ban san ya zanyi ba duk da cewar hakan yana matuqar cutar da ni sosai, ta ya zan iya fuskantar *Afnan* da irin wannan mummunan labarin ba zan iya jure ganin k'uncin da zata shiga ciki ba." "Karka damu Abba ni zanyi komai domin ganin na dakatar da auran kuma zanyi nasara insha Allah, to kawai dai ka yarda da ni sannan kuma karka sanar da qanwata komai a game da wannan please." "Anwar ni ina jin tsoro sabo da Baba zai iya dawo da auran gobe to kawai ka barmin komai, ni zan kula da komai ina fatan nayi nasara a kan abin da muke fata." "Shikenan Abba ina fatan muyi nasaran dakatar da auran."

Ya jinjina masa ka a lamar eh suna haka sai ga *Afnan* ta shigo wanda kuma tare take da Amal, da gudu Amal ta nufi gurin Abban ta wato Anwar shi kuwa ya d'auke ta yana murmushi, *Afnan* ta gaishe su sannan ta nufi d'akin ta sun bita da kallo suna girgiza ka cike da jin tausayin ta. Bayan kwana biyu zaune take tana kallo taji a na buga mata k'ofa ta tashi ta nufi k'ofa, ta isa k'ofa tare da bud'e wa ta samu *Afnan* tsaye a gefen k'ofa tayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan ta. "Sannu da zuwa sirika ta kuma Amaryar mu shigo ciki." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai, ita kuwa sai kallonta take tana wani gajeran murmushi sun tafi sun zauna *Afnan* ta anbaci sunan ta. "Aunty wai a kan me kike magana ni sam na kasa fahimtar abin da kike fad'a? Sannan kuma kin kira ni da wani sabon suna mai ya saka kika kira ni da Amarya.?" Murmushin ta ya k'aru sosai sai wani kallon *Afnan* take daga bisani kuma ta amsa ta. *"Afnan* ki dena wani wayancewa sabo da nima na san gaskiyar, a kwana biyun nan zamu fara shirin auran ki amma dai ni ba zan kira ki da Aunty ba, sabo da kin jima kina kira na da Aunty amma k'ila na kira ki da matar Yaya."

Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin da taji ta fad'a take magana. "Aunty wai a kan me kike magana nifa sam na kasa fahimtar abin da kike fad'a, Aunty dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa mai ya saka kika kira ni da Amarya.?" *"Afnan* karki fad'a min cewar baki san cewar za a yi auran ki da Yaya Auwal ba.?" "Mine ni nayi aure da Yaya Auwal? A'a sam hakan ba zata ta'ba kasancewa ba har abada. Amma Aunty wai gaskiyar kike fad'a kuwa ko dai kina tsokanata ne.?" "A'a *Afnan* ni gaskiyar nake fad'a za a yi auran ki da Yaya Auwal nan da kwana sha biyu insha Allah." Cike da firgici take furta kalmar A'a ta tashi da sauri zata fita lokacin yayi daidai da shigowar Anwar, da sauri ya isa inda take yana tambayar ta abin da yake faruwa da ita. "Yaya ka fad'a min cewa ba gaskiya bane ni ba zan auri Yaya Auwal ba, ni bana san na aure sa to dan Allah ka dakatar da wannan auran please."

"Eh qanwata abin da nake ta k'oqarin yi kenan shi yasa ma ba kiji zancan daga garemu ba, *Afnan* har yanzu Yayan ki yana nan kuma zai yi komai sabo da farin cikin ki, to kawai ki yarda da ni kinji dan haka ki dena wannan kukan bana so kinji ko please." Ta jinjina masa ka a lamar to shi kuwa ya shiga share mata kwalla tare da sunbatarta, bayan wani lokaci ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata ta juya ta fita zuwa part d'in Abba, bayan tafiyar ta Anwar ya mai da kallonsa ga Anisa wacce ita ma kallonsa take, wani irin wawan kallo yake yi mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewar yana fishi da ita kuma fishi sosai. Ya juya ya nufi bedroom ita ma tashi tayi ta bisa a baya ta shiga ciki ta same sa sai safa da marwa yake, ta isa inda yake tare da fad'ar sunan sa amma bai amsa ba duk da haka taci gaba da magana. "Yaya Anwar lafiya mai ya saka kai baka san yi man magana.?" "Anisa dan Allah ko zaki iya fita daga nan? Kawai ki tafi ki bar nan duka wannan laifin Auwal ne kuma ni ba zan ta'ba barin yayi aure da *Afnan* ba, idan kin ga dama to zaki iya yarda da kowa wannan amma kuma daga k'arshe ni zanyi nasara."

"Yaya Anwar amma mai ya saka kai baka san su biyun suyi aure.?" "Anisa na fad'a maki ki bar nan to ki tafi jeki man ki tafi." Ta amsa da to ta juya ta fita shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login