Showing 99001 words to 102000 words out of 142761 words
Chapter 34 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
kana matuqar san samosa da madara sosai ko? Sannan kana da saurin fishi amma kuma kana da saurin sauka, haka ne ko a guri na dama *Adeel* sannan kuma dai muna da kamanni da juna sosai, hakama dukanmu ukun muna da rashin lafiya iri d'aya. Ra'ayin mu da kuma halaiyar mu ko manmu iri d'aya ne, Aboki ni sam na kasa fahimtar wannan mai yasa hakan take faruwa damu? A baya sam bana jin komai amma a yanzu ina ta damuwa a kai, na jima ina tambayar kai na a game da hakan amma kuma sam na gagara samun amsar. Aboki dukanmu ukun muna yin mafarki iri ďaya hakan yana da matuqar rikitarwa sosai."
Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya fad'ar sa ba, amma zan iya cewa yana tare da tarin damuwa sosai *Adnan* ya shiga girgiza masa ka tare da furta. "A'a Aboki dan Allah karka bari tunanin hakan ya cutar da kai, wannan ba komai bane kawai ikon Allah da kuma k'arfin girman abotar mu. *Adyan* kawai ka kai da hankalin ka ga samun lafiyar Mum ka ji ko yanzu mu shiga daga ciki." Kallonsa kawai yake na tsayin wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi da to, sun tashi sun nufi ciki bayan kwana biyu zaune suke Umma tana tare da Mum, yayin da *Adeel* yake ta aikin chatting da abar qaunarsa wato *Amna.* suna haka sai ga *Adnan* ya shigo ya fara gaisawa da Umma sannan ya isa gurin *Adeel,* ya zauna tare da ba shi hanu sun gaisa *Adeel* ya shiga tambayar *Adyan.* *"Adeel* karka fad'a min cewar Aboki bai zo nan ba? Sabo da ya jima da fitowa kuma ya sanar da ni cewar office zai zo, ga shi kuma kai kana fad'a min cewar bai zo nan ba hakan yana nufin bai shigo ya duba jikin Mum ba? Shikenan zan tafi na duba shi a office ďin sa zamu dawo tare insha Allah."
*Adeel* ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, hakama Umma wacce take zaune gefen Mum *Adnan* ya tashi ya fita zuwa office ďin *Adyan.* Zaune yake amma ba aiki yake ba lokaci d'aya ya ji a na buga masa k'ofa, daga ciki ya amsa da shigo ciki ba jimawa sai ga Max ya shigo, ya k'arasa inda yake ya fara da gaishe sa sannan ya ba shi takardun dake hanun sa. Ya karb'a shi kuma ya juya ya fita bayan tafiyar sa shi kuwa ya shiga duba takardun domin ganin abin da yake ciki, lokaci d'aya ya ji k'irjin sa yana bugawa da k'arfi tare da zuciyar sa, kansa yana sarawa ya fara fita haiyacinsa sai wani irin gumi yake saukar masa. "A'a wannan k'arya ne hakan sam ba zata tab'a kasancewa ba, a'a wannan ba a salin result ďin bane to sam bai kamata na yarda da wannan ba." Ya tashi ya fita cikin sauri har kamar zai fad'i yana cikin tafiya Dr John ya rik'o hanun sa, tare da fad'ar sunan sa kallonsa kawai yake ba tare daya furta masa komai ba.
*"Dr Adyan* mai yake faruwa da kai ne haka.?" "Dr John dan Allah ka barni karka k'aran wani k'uncin bayan wanda nake tare da shi." *"Dr Adyan* k'ila dai zan iya taimaka wa domin ka fita a cikin wannan mummunan yanayin, yanzu ka biyo ni mu tafi zan kai ka inda zaka manta da gaba d'aya wannan k'uncin to mu tafi." Yayi shiru kad'an sannan daga bisani ya amsa shi da to sun juya sun nufi mota. *Adnan* ya isa office d'in *Dr Adyan* tare da shiga ciki sai dai bai yi nasaran samun sa a ciki ba, ya fito cike da jin mamakin rashin ganin sa yana sama ya hangesa tare da Dr John suna k'oqarin shiga mota, kallo ďaya tak yayi masa ya fahimci cewar ba qlau yake ba, da sauri ya juya ya nufi gunsu har yana gudu yana fitowa suna fice wa. Da sauri ya fad'a taxy tare da fad'a wa mai taxy d'in ya bayan motar Dr John, haka suka ci gaba da tafiya har zuwa inda su Dr John suka sauka, cikin hanzari *Adnan* ya fito tare da bawa mai taxy kud'in sa ya juya ya shiga ciki.
Wani irin guri ne wanda ya had'a tarin mutane maza da mata, wasun su sai rawa suke wasu kuma caca suke da dai ire-iren su, haka yayi ta dogon wuya yana zaran ido dan ganin inda zai gasu *Adyan.* Ya jima yana abu ďaya sannan daga bisani ya hangesu gurin wani tebur zaune, kamar a mafarki ya ga Dr John yana ba shi kofin da yake hanun sa, wanda kuma yana da tabbacin cewa giya ce a ciki da sauri ya k'arasa gurin yana fad'ar sunan sa. *"Dr Adyan* ya kamata ka sha wannan to duka k'uncin ka zai tafi." Ya jinjina masa ka a lamar to ya karb'i kofin tare da kai wa baki, ya fara sha da sauri ya a jiye kofin yana tari tare da furta, "a'a ba zan iya shan wannan ba ba dad'i sannan kuma yana da d'aci sosai." *"Dr Adyan* wannan ce kawai damar ka idan har kana buqatar ka rabu da wannan k'uncin, zaka iya yarda da ni to kawai ka sha ka ji ko please."
Ya amsa da to yaci gaba da sha yana cikin sha sai ga *Adnan* da sauri ya fizge kofin da yake bakin sa, ya a jiye a gefe yana fad'ar sunan sa kallonsa kawai yayi ba tare daya amsa ba, *Adnan* ya mai da kallonsa ga Dr John cike da k'unci bak'in ciki tare da b'acin rai yake magana. "Kai waye da zaka aikata masa haka? Shin ka kuwa san girman zunubin daka aikata kuwa.?" Dr John yayi wani gajeran murmushi sannan ya amsa shi, "sunana Dr John kuma ni Abokin sa ne nazo da shi nan ne sabo da ya samu farin ciki sosai, amma waye kai da kake k'oqarin dakatar da ni shin kai ďin Yayan sa ne? Ko a'a kai ďin twin's brother d'in sa ne sabo da naga kuna da kamanni da juna sosai.?"
"Wai da gaske kai Abokin sa ne? To amma kuma ni sam banga hakan ba, kai ba Aboki bane amma zan iya kiran ka da mak'iyi, to gargad'i daga yau karka yarda ka koma yin kuskuran cutar da shi sosai har haka, to ka tabbatar da ka kiyaye wannan sabo da zan iya aikata komai a kan Aboki na." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi *Adyan* sun fita Dr John ya bisu da kallo yana murmushi tare da girgiza ka, suna fitowa *Adnan* ya tare musu taxy sun shiga cikin wata 'yar murya yake magana. "Aboki karka kai ni gida dan Allah kawai ka sauke ni, a Beauty hotel ina da d'aki a can to kawai mu tafi can." Ya amsa shi da to tare da sanar da driver inda zai sauke su, ya amsa shi da to ya ja mota sun tafi sun isa hotel ďin cikin hanzari an kai su d'akin da yake.
Sun shiga ciki *Adnan* ya tafi ya kwantar da shi sai wani kallonsa yake. "Haba Aboki mai kake yi ne haka ta ya ma zaka yi tunanin cutar da kanka har haka? Miye damuwar shin wannan Abokin naka yafi Appa Ammie ni ko kuma *Adeel?* Kai ka zab'i sanar da shi damuwar ka fiye damu mai yasa? To shin ko zaka iya sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai k'ila ina da abin da zan taimaka.?" Magana yake cike da damuwa sosai *Adyan* kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai. Lokaci d'aya kuma ya fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, ban ankara ba sai kuka kuma kuka yake sosai sai wani irin abu yake, wanda har yana k'oqarin cutar da kansa da k'yar *Adnan* ya samu ya iya dakatar da shi. *"Adyan* dan Allah ka dena cutar da kanka haka, sannan kuma ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai miye matsalar.?"
"Aboki kawai ka barni na ji da wannan k'uncin da yake tare da ni, Aboki da a ce kai ka san a salin gaskiyar to da kai ma ka kasance a cikin irin wannan yanayin nawa. Aboki ciwon yana da matuqar girma sosai sannan kuma ba shi da magani, Aboki ni ina jin ina ma a ce mutuwa nayi ta yanda ba zan fuskanci irin wannan mummunan qalubalen ba, Aboki wannan matar muguwa ce sosai sannan kuma mak'aryaciya ce sosai, to ita d'in sam bata cancanci kulawar mu ba, shi yasa na yanke hukuncin cewa ba zan k'ara duba taba. Sabo na tsane ta matuqar tsana sosai sabo da." Lokaci ďaya kuma wani wawan barci yazo ya d'auke sa, *Adnan* kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai cike da jin mamakin abin daya fad'a. *"Adyan* zanso ka sanar da ni a salin gaskiyar abin da yake faruwa da kai, mai yasa kake fad'ar haka a kan Mum shin wani abu ya faru tsakanin sa da *Adeel* ne? Ya kamata nayi magana da *Adeel* yanzu ina fatan ya sanar da ni duka gaskiyar."
Ya ciro wayar sa ya shiga kiran layin *Adeel* ba jimawa ya d'aga. *"Adnan* kuna ina nazo office ďin amma ban same ka ba? Na kira layin ka baya tafiya *Adyan* kuma baya d'aga kira na, ni na damu sosai a kanku biyun sabo da ban san abin da yake faruwa daku ba, yanzu fad'a min kuna ina sannan kuma qlau kuke.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, *"Adeel* muna lafiya amma zanso na tambiye ka wani abu.?" *"Adnan* kawai ka sanar da ni koma miye." *"Adeel* shin kayi magana da Aboki a kan Mum.?" Ya amsa shi da eh tare da sanar da shi komai, *Adnan* amma mai ya saka ka tambaya.?" "Ba komai kawai ina san na sani ne amma kayi hak'uri." "Ba komai *Adnan* na gode sosai da kulawa." Ya amsa shi da ba komai daga bisani suka yi sallama. Ya mai da kallonsa ga *Adyan* yayin da yake magana da zuciyarsa.
"Aboki mai yake faruwa da kai ne haka mai ya saka ka tsani Mum haka? Ita bata da lafiya balantana na ce ko ta aikata masa wani abin, sannan kuma shi bai yi sa in sa da *Adeel* to mai yake faruwa ne ya kamata na sani to amma ta ya.?" Nan kuwa ya shiga tunani da nazari ya jima sosai a haka, ganin yanda kansa ya d'auki zafi sosai ga kuma damuwa tana k'oqarin yi masa yawa, yasa shi ciro maganin sa daga aljihu ya tafi ya d'auki ruwa ya sha magani, sannan ya nufi gado ya kwanta kusa da *Adyan* ba jimawa barci ya d'auke sa....
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/12, 1:32 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 41*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Wednesday 09/02/2022*
*Time 07:40pm*
*Typing...............*
Sun jima sosai suna barci sannan daga bisani suka tashi, *Adyan* ne wanda ya fara tashi motsinsa ne ya tashi *Adnan.* Lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar dukansu kallon juna suke, "Aboki ka tashi to ya yanayin naka fatan kana samun sauki.?" Kallonsa kawai yake ba kuma tare daya furta masa komai ba, lokaci d'aya kuma ya saki kuka cike da firgici *Adnan* ya tashi yana fad'ar sunan sa. "Aboki mai yake faruwa da kai ne haka? Naro e ka a kan ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai please.?" Ya shiga rarrashin sa yana yi masa magiya bayan wani lokaci ya fara magana.
"Aboki ni banma san ta yanda zan iya sanar da kai a salin damuwar ba, Aboki ciwon yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai, to ni sam ba zanso kai ma ka fuskanci irin wannan mummunan yanayin da nake ciki ba. To shi yasa bana jin zan iya sanar da kai a salin gaskiyar kawai sai dai na baka hak'uri." "Aboki ni kawai zan yafe maka ne idan har ka sanar da ni gaskiyar, ko kuma dai nayi fishi da kai kuma fishi sosai, sannan kuma zan dena yima magana na tsayin wani lokaci sosai, to kawai ka sanar da ni gaskiyar dan Allah please.?" Yayi shiru kad'an yana nazari sannan ya amsa shi. "Aboki abin shi ne ni kai da kuma *Adeel* ba haka kawai muke san juna ba, ba kuma haka kawai muke da ra'ayi iri ďaya na, sannan kuma ba a banza muke da kamanni da juna sosai ba. Aboki komai yana faruwa ne tare da dalili sannan kuma ba abin da yake faruwa haka kawai, Aboki gaskiyar ita ce dukanmu ukun abu ďaya, dalilin da yasa muke matuqar qaunar junanmu kenan amma kuma."
Yayi shiru tare da girgiza ka yayin da yake kuka kuma kuka sosai. "Aboki sam bai kamata hakan ya saka ka kuka ba, dukanmu ukun mun kasance abokai na gari ga junanmu, sannan kuma muna bawa junanmu kulawa sosai, hakan yasa muka kasance tamkar ahali ďaya to kawai kayi farin ciki, sannan kuma dan Allah da girman Allah kayi hak'uri ka sanar da abin da yasa ka tsani Mum? Shin kai kayi fad'a da *Adeel* ne ko a'a ita ďin ta aikata maka wani abin ne cikin rashin sani.?" "Aboki *Adeel* yana da kirki sosai amma kuma yana matuqar bani tausayi sosai, sabo da shi sam bai yi dace da iyaye na gari ba, a baya nayi tunanin cewa Dadyn sa ne kawai yake da butulci, amma yanzu na fahimci komai dukansu irin su ďaya sam basu da kirki, sannan kuma basu da godiyar Allah dukansu munafukai ne shi yasa na tsane su sosai." "Aboki naro e ka dan Allah da girman Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa please.?"
"Aboki tin da ka matsa shikenan zan sanar da kai duka gaskiyar, Aboki abin shi ne dukanmu ukun ni kai da kuma *Adeel* ahali ďaya ne, ina nufin dukanmu ukun iyayenmu ďaya." Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya ji ya fad'a yake magana. "Aboki wai mai kake fad'a ne haka shin wai kai ka fita haiyacinka ne? Am ina ganin cewar giyar daka kurb'a har yanzu bata gama sakin ka ba, to ya kamata ka kwanta ka huta na wani lokaci idan ka dawo haiyacinka zamu yi magana." "Aboki ni kawai gaskiyar nake fad'a wannan matar da take kwance asibiti, ita ce a salin mahaifiyar mu Aboki bayan da *Adeel* ya sanar da ni komai a game da iyayen sa, sai nayi dogon nazari da tunani a game damu biyun wanda wannan dalilin ne yasa, ni nayi mana gwajin halitta dukanmu ukun da kuma Mum, Aboki yau ne a ka kawon result bayan na duba sakamakon sai na ga duka iri d'aya ne. Wanda hakan ne yake tabbatar mana da cewar dukanmu 'yan uwan juna ne, sannan kuma *Maman Adeel* ita ce a salin mahaifiyar mu."
Da sauri *Adnan* ya dakatar da shi cikin tsawa har yana ďaga murya. "Ya isa haka Aboki ka dena fad'ar wannan shirmen ya kamata ka dawo haiyacinka, ka dena fad'a min abin da zuciyata ba zata iya d'auka ba, ta ya ma zaka kalli cikin idanuwana sannan ka sanar da ni cewar *Maman Adeel* wai ita ce a salin mahaifiya ta. A'a hakan sam ba gaskiya bane Mamie da Papa sune a salin iyayena, to kama dena fad'ar wannan shirmen ka ji ko." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, amma zan iya cewa yana tare da tarin damuwa sosai yayin da k'unci yayi yawan gaske a tare da shi sosai. "Aboki ni kawai gaskiyar nake sanar da kai, wallahi naso a ce duka wannan k'arya ne ko kuma a ce mafarki nake, ta yanda zan rok'i Allah a kan ya tashe ni daga wannan mummunan mafarkin da nake. Amma kuma hakan gaskiya ne sannan kuma ba zamu iya canja gaskiyar ba, Aboki dan Allah ko da mai zai faru to sam bana san kowa ya san da wannan zancan, ina san kayi min alkawarin cewa ba zaka tab'a sanar da kowa gaskiyar ba dan Allah."
Shiru bai amsa ba sai ma aikin kuka da yake kuma kuka sosai, haka shi ma abin da yake yi kenan lokaci ďaya suka yi hugging juna, cike da jin tausayin juna suke rarrashin junansu cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa *Adnan* yake magana. "Aboki duka iyayenmu suna matuqar masifar qaunar mu sosai, Aboki Papa da Mamie suna matuqar qauna ta sosai fiye ma da yanda suke so na. Ko yaushe suna k'oqarin saka ni farin ciki sosai hakama sam basa jure ganin duk wani