Showing 30001 words to 33000 words out of 142761 words

Chapter 11 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Saturday 01/01/2022*

*Time 09:27pm*

*Typing............*

Yana kai k'arshen maganar sa ta juya tayi tafiyarta, shi kuwa ya bita da kallo yayin da mamakin ta dama abin da take fad'a yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Cikin hanzari ya bita a baya yana fad'ar sunan ta amma bata amsa shi, yana k'oqarin shiga ciki ita kuma tana har suka yi karo da juna kad'an ta fad'i yayi saurin riqo ta, lokaci d'aya suka saki a jiyar zuciya ya d'ago ta lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna. Wani irin kallo suke yiwa juna wanda ban san ta yanda zan sanar daku shi ba, sun jima sosai a haka sannan daga bisani ta fita daga jikin sa, ta tafi ta zauna ba tare data furta masa komai ba ya bita da kallo har ta zauna. Cikin sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, cikin mutuwar jiki da sanyin murya ya anbaci sunan ta kafin ya furta komai tayi saurin dakatar da shi, ta hanyar d'aga masa hanu tare da girgiza masa ka a lamar a'a taci gaba da danna waya daga bisani ta fara magana.

"Abbu kayi hak'uri dana kira layin ka yanzu, kawai dai ni naji ina san nayi magana da kai ne." "Na fahimce ki 'yata shin a kan Yayan ki ne.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "eh Abbu amma karka wani damu sabo da zan iya jure zafin duk da cewar yanayin yana cutar da ni sosai." "Ahlam wai har tsayin wane lokaci zaki d'auka kina 'boye gaskiyar? 'Yata zuwa yanzu ya kamata Ahmad ya san gaskiyar cewa kina qaunarsa sosai, Ahlam wannan fa ya jima na tabbata idan ya san gaskiyar to komai zai yi daidai. Ahlam ke kin fara san Ahmad ne tin a lokacin da baki da wayo, ke kin rayu ne gaba d'aya da soyayyar sa Ahlam to ya kamata ya san gaskiyar kawai ki sanar da shi kinji dan Allah." Tayi shiru na wani lokaci wanda kuma kuka take daga bisani kuma ta amsa shi. "Shikenan Abbu zanyi hakan na gode sosai sai da safe asuba ta gari ka gaida Ummi na." "Sai da safe 'yata Allah yayi maki albarka ki gaishe da Ahmad da jikana."

Ta amsa da to da kuma haka suka yi sallama ta tashi domin tafiya, da sauri Ahmad yayi saurin tashi ya sha gaban ta tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam bai kamata ki tafi ba sabo da akwai buqatar mu biyun muyi magana yanzu dan Allah." "Kayi hak'uri dare yayi sosai sannan kuma yarona zai iya buqata na, to a yanzu kana da damar da zaka kasance tare da abar qaunar ka to kayi farin ciki sosai sai da safe." Ta juya gefe taci gaba da tafiya da sauri ya ri e hanun ta tare da janyo ta, ta fad'a jikin sa ya mata wata kyakkyawar runguma sosai sai wani kallon juna suke kallo sosai. "Ni ka sake ni ka barni na tafi." Ya girgiza mata ka tare da furta, "a'a ba zan sake ki ba sannan kuma ba zan barki ki tafi ba, sabo da akwai abin daya kamata ki sani mu tafi d'aki na yanzu." "Shin ka shirya gabatar da ni a gurin budurwa ka ne? To ni ban shirya amince wa hakan ba dan haka ka barni na tafi dan Allah." Magana take cike da unci da tarin damuwa sosai yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai.

Shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai ya shiga girgiza mata ka, "a'a ba abin da zanyi ba kenan ni ba zan ci gaba da cutar dake ta wannan hanyar ba, bayan da na gano a salin gaskiyar Ahlam amma mai ya saka ke baki ta'ba sanar da ni gaskiyar ba.?" Shiru bata yi magana ba ya janyo ta sun tafi sun zauna yaci gaba yana cewa. "Ahlam dan Allah ki amsa ni mai ya saka baki ta'ba sanar da ni gaskiyar ba.?" "Taya ni zan sanar da kai gaskiyar bayan kuma kai kayi zurfi sosai cikin tsana ta, a ko yaushe tsana kake nuna min baka ta'ba nuna min soyayya ba ko da na zama kujera ďaya ce, a duk lokacin da kai ka rungumi *Adyan* ko ka sunbacesa ji nake ina ma a ce nima zan samu hakan daga gareka. Amma kai sam babu tinanin hakan a tare da kai sabo da wannan sakaryar yarinyar da kake kulawa, yau ka d'ora hanun ka a kan fuskar sabo da ita sannan kuma ka tsaya a gaba na ka fad'a min cewar ba zaka ta'ba barin ta ba. Kai ka za'beta fiye da ni da kuma yaronmu dan haka ni ba zan saurari komai daga gareka ba, to kawai ka sake ni ina san zan tafi na kwanta yarona zai buqace ni a tare da shi sosai." Magana take cikin fishi sosai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo.

Wani irin kallo yake yi mata mai tare da so ya qara saka ta jikin sa tare dayi mata kyakkyawar runguma sosai. Lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin ya shiga share mata kwalla ya tashi tare da tashin ta sun nufi d'akin sa, "a'a ni ba zan shiga ciki ba to kawai ka sake ni dan Allah ka barni please." Tayi tsaye tak'i shiga ciki ya girgiza ka tare da jinjina sa lokaci d'aya ya d'auke ta ya shiga da ita ciki, ya fara zaunar da ita a kan gado sannan ya tafi ya rufe k'ofa ya dawo ciki, ya nufi durowa ya bud'e ya d'auko wata 'yar qaramar jaka ya nufi gurin ta ya zauna tare da kai kallonsa gareta, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take sun jima a haka sosai. Sannan daga bisani ya mai da kallonsa ga jakar ita ma haka dan ganin mai zai yi, ya bud'e jakar tare da ciro abin da yake cikin ta gaba d'aya ya mai da kallonsa gareta tare da fad'ar sunan ta. "Zaki iya duba wa dan Allah ki duba please." Ta kai hanun ta tana duba photon da suke gurin ta d'auki wata takarda tana karantawa.

"Hayatee na soyayyar ki rayuwata ce ba zan rayu ba sai dake, wanda wannan dalilin ne yasa nake kiran da rayuwata. Ina fatan zuwan lokacin da zaki fara sona duk da cewar hakan yana da matuqar wahala sosai, sabo da kinyi matuqar tsana ta a cikin ranki dama zuciyarki gaba d'aya. Tina hakan kawai yana matuqar cutar da ni sosai sabo da ni dake kawai nake fatan na rayu rayuwa kuma ta har abada." Haka taci gaba da karanta takardun dake gurin tare da kallon photon dake gurin, daga bisani kuma ta mai da kallonta garesa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar shi ma kallonta yake kuma kallo sosai. Cikin mutuwar jiki da sanyin murya take furta masa kalmar, "Shin wannan ita ce Hayateen ka.?" Ya jinjina mata ka tare da furta mata eh, "Yaya Ahmad wai gaskiyar kake fad'a min kuwa.?" "Eh qanwata ke ce nan Hayatee na rayuwata kenan, Ahlam ina matuqar masifar qaunarki fiye ma yanda nake sanki ina qaunarki sosai. A kullum a ko yaushe tinanin samun ki nake yanda zaki zamo tawa ta har abada, amma bani da wani za'bi dole sai na 'boye gaskiyar a gareki, sabo da ni da zuciyata mun yarda da cewa kina tare da tsana ta sosai shi yasa ni na 'boye gaskiyar a gareki. Bama iya ke kawai ba har da ahalina Umma na ce kawai ta san da gaskiyar, Ahlam ni na kasa yarda a ce muna matuqar qaunar junanmu amma kuma a zahiri muna nuna wa juna tsana. Munyi matuqar cutar da juna ta irin wannan mummunan zunubin amma Alhamdulallah yanzu komai yayi daidai insha Allah qanwata ki yafemin a kan komai kinji dan Allah."

Magana yake yayin da yake ri e da hanayenta yana wasa da faratanta, ita kuwa sai wani kallonsa take kallo mai tare da so yayin da farin ciki yake ta shigarta ta ko ina jikinta, ta cire hanunta daga nasa ta kai hanun ta a kan fuskar sa ta shafi fuskarsa tare da d'ago fuskarsa wadda ta kasance a sunkuye. Lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna sai wani kallon juna suke kallo sosai, sun jima sosai a haka sannan daga bisani ta fara magana. "Ba buqatar ka fad'i haka kai baka yi komai to sam ba buqatar ka bada hak'uri, Yaya Ahmad abin farin cikin shi ne har yanzu mu biyun muna tare daga k'arshe kuma mun fahimci juna. To wannan kawai ya isa kawai muyi farin ciki ina sanka sosai soyayyar ka ta isa ta biya duk wani kuskuran daka aikata a gareni, to sam ba buqatar ka damu sosai a kan hakan sabo da soyayyar ka ta biya komai hakan ya isa to kawai muyi farin ciki." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa ga wanda ya gani, hakan yasa ya rufe ta da ido yana kallonta yayin da yake jin tana birgeta sosai.

"Hayatee na hak'iqa nayi matuqar sa'a dani na same ki, kafin yanzu a kullum kuma a ko yaushe cikin fargaba nake sabo da ina ganin kamar wata rana zan iya rasa ki, hakan ke sawa na shiga k'unci mai girman gaske wanda har nake zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Hayatee wallahi ke kad'ai nake so kuma ke kad'ai zanso har k'arshen rayuwata insha Allah wannan alkawari ne to zaki iya yarda da ni." "Eh na yarda da kai amma kuma da akwai abin da nake san ka sanar da ni." "Miye wannan.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "Yaya Ahmad da wa kake waya a ko yaushe sannan kuma kuke charting.?" Yayi murmushi sosai mai tare da 'yar dariya cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Ba kowa kawai sabo dake nake domin ki fahimci cewar bani kad'ai bane, Ahlam gaskiyar ita ce bana d'ora waya a kan kunne na sai a lokacin da kike tare da ni, haka kuma wani lokaci Game nake a waya amma sai na fad'a maki cewar ina chart da Hayatee na. Dalilin da yasa bana barin ki kar'bi waya na kenan sabo da zaki iya gano a salin gaskiyar, Hayatee na zaki iya yarda da ni sabo da ni gaskiyar nake sanar dake ina qaunarki sosai."

Wani irin kyakkyawan murmushi take mai tare da dariya wanda ya hana mata fad'ar komai. shi ma abin da yake yi kenan sun jima a haka sannan daga bisani ya furta mata kalmar, "Ahlam shin zan iya yin hugging d'in ki dan Allah kinji please.?" Ta girgiza ka tare da furta a'a da sauri ya wani zaro ido yana kallonta kafin ya furta komai tayi masa rigagi. "Eh ba buqatar sai ka tambaya kawai ka ai watar nima zanyi farin ciki sosai da hakan." Cike da d'auki yayi hugging d'in ta lokaci d'aya kuma ya shiga sunbatarta ta ko ina fuska zuwa wuya, daga bisani kuma ya dira a kan bakinta cikin wani salo da dabara yake tsotsar le'benta da ma harshen ta. Daga zaune sun kai kwance wai abin nai ma ya samu matar direba ta aifi sitari, nan kuwa suka ci gaba da jin dad'i da juna wanda daga bisani komai yaci gaba da wakana a tsakanin su, wanda a wannan ranar kuma a wannan lokacin Ahmad yayi nasaran kusantarta hakan yayi matuqar yi musu dad'i sosai. Bayan wani lokaci suka tashi suka nufi toilet sunyi wanka sun fito sun shirya daga bisani suka tashi suka nufi gurin yaronsu, sun kwanta tare da rungumasa jikin su dukansu kuma tin daga wannan lokacin rayuwarsu ta canja suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki sosai.

Bayan wani lokaci wani Yammaci zaune yake a parlour yana kallon labaru Ahlam ta fito, qarar rufe k'ofar da yaji ne yasa shi kai kallonsa gareta ya tashi ya nufi gurin ta yana fad'ar sunan ta. "Ahlam zonan ya kamata ki huta fatan kina lafiya.?" tayi murmushi sosai mai tare da dariya cikin kyakkyawan yanayi take magana. "Yaya Ahmad ina lafiya to ba buqatar ka damu sosai ka ji ko." "Duk da haka yanzu mu tafi ki zauna kar yarinya ta ta gaji da yawa." Murmushi kawai take ba tare data furta komai ba ya riqa ta sun tafi sun zauna, ya kai hanun sa ya shafi cikin ta tare da sunbata murmushi ya qaru ta anbaci sunan sa ya amsa taci gaba da magana. "Yaya Ahmad cikin wata biyar ne kawai to zan iya kulawa da kai na sosai, yanzu fad'a min mai zaka ci ya kamata na d'ora girki.?" "Qanwata ni zanci gaba da kulawa da dukanku na har abada sannan kuma na kareku iya rayuwata, to ba buqatar ki dakatar da ni sabo da alhaki ne da yake kai na kuma zan iya, yanzu kawai ki fad'i duk abin da kike so nima shi zanci nayi alkawari."

"Shikenan zan tambayi *Adyan* naji mai yake so yanzu fad'a min yana ina.?" "Ya fad'a min cewar zai tafi filin wasa to yana can." Da sauri ta wani zaro ido tana kallonsa cikin rawar murya har tana sarkewa take magana. "Yaya Ahmad kuma ka barsa ya tafi amma mai yasa.?" "Ahlam ki kwantar da hankali kafin ya tafi sai da ya min alkawarin cewa shi ba zai yi wasan boll ba sannan kuma ba zai yi gudu ba, Ahlam ni na yarda da yaronmu sosai shi yasa ban dakatar da shi ba yau yana cikin kyakkyawan yanayi to sam bana san na dakatar da farin cikin sa. Ahlam ki yarda da ni zai kasance cikin k'oshin lafiya sosai kuma ba abin da zai faru da shi insha Allah to zaki iya yarda da ni please." Ta jinjina masa ka a lamar to tare da furta masa kalmar, "nima ina fatan haka amma duk da haka ni zan tafi na duba shi." "Shikenan zamu tafi tare." "A'a zan kula da kai na to kawai ka jira a nan yanzu zamu dawo insha Allah." "Shikenan to ki kula sosai dan Allah." "Eh zanyi insha Allah nayi alkawari." Ya jinjina mata ka tare da sunbatarta sannan ta tashi ta fita shi kuwa ya bita da kallo har ta fice, tin daga nesa ta hangi *Adyan* yana lilo ta nufi gurin sa tana wani lallausan murmushi mai had'e da dariya.

Kad'an ta qarasa kai wa garesa ta hangi zomo yana zuwa inda yake ga shi kuma yana matuqar tsoransa sosai, wannan yasa ta qara sauri tana fad'ar sunansa amma bai jiyo ta ba, lokaci d'aya *Adyan* ya ga zomon ya tin kari inda yake nan kuwa ya saki ihu yana kururuwa da nai man taimako. Sai gudu yake yana kuka sosai zomon kuma sai binsa yake Ahlam ta shiga anbatar sunan sa wanda ita gudun take, hayaniyar su ce ta fito da Ahmad tana cikin gudu qafarta tayi tinti'be da wani dutse lokaci d'aya ta kife a qasa ta fad'i, yayin da bakinta yake anbatar sunan *Adyan* wanda da gangara ta qarasa kai wa inda yake tare da janyo sa jikin ta. Lokacin yayi daidai da fitowar Ahmad da sauri ya qarasa inda suke har yana gudu yayin da bakin sa yake fad'ar sunayen su, amma cikin rashin sa'a ko da ya qarasa inda suke dukansu sun suma cike da firgici ya d'auke su zuwa asibiti......




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/3, 10:25 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 13*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*Sister 'yar gata kwana biyu na dena jiyo ki, to ina fatan dai lafiya Allah yasa Amin ya hayyu ya kayyum.*

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login