Showing 141001 words to 142761 words out of 142761 words
Chapter 48 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
a na buga masu k'ofa *Amna* ta yunk'ura zata tashi, da sauri Mum ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a 'yata k'ila mujin nawa yana buqatar hutu sosai to ya kamata ya huta, ni zanyi wannan da kai na to kawai ki huta kin ji ko masoyiya." Cike da jin kunya ta jinjina mata ka a lamar to ita kuwa sai murmushi take, mai tare da 'yar dariya hakama su Mama abin da suke yi kenan. Mum ta tashi ta nufi k'ofa domin ganin waye, ta isa k'ofar tare da bud'e wa ba tare data tambaya waye ba, ta samu Prof tsaye a gefen k'ofa ta ja numfashi tare da furta masa kalmar. "Kai ne to mai kuma kake yi a nan.?" Murmushinsa ya k'aru sosai cikin kwantar da murya yake magana. "Ina ga ba zai zama laifi ba idan nazo gurin uwar yarona, sannan kuma wacce zata k'ara kasancewa matata nan kusa kuma kusa sosai insha Allah."
"Prof to komai saurin unguwar zoma zata jira nak'uda, eh gaskiyar ka ne ni ce nan mahaifiyar *Adeel* na ji mamakin da baka manta hakan ba. To ka gode Allah daya kasance da akwai d'a a tsakaninmu, da k'ila mu biyun ba zamu koma kasancewa tare da juna ba na har abada. Amma yanzu sabo da girmama farin cikin yarona na amince zan koma gareka, to yanzu zaka iya tafiya sabo da bana buqatar ka nan." "Shikenan zan tafi amma zan koma dawowa, yanzu ki kasance cikin farin ciki sosai sai na dawo." Ya juya ya tafi kamar dai yanda ta buqata ita kuma ta koma ciki, Umma ta shiga tambayar waye yazo ta sanar da ita, bayan muntuna biyu ta tashi ta shiga ciki sun bita da kallo har ta shige. Bayan kwana biyu Prof ya had'u dasu Abba su Abbu sun yi masa nasiha sosai tare da jan hankali, inda kuma daga bisani suka saka musu ranar mako biyu, a zahirin gaskiya Prof da *Adeel* suna farin ciki sosai, hakama Papa ganin yanda Yayansa yake ci gaba da zama mutumen kirki. Ta b'angaran *Adnan da Adyan* kuma sam basa farin ciki sai ma ji suke, tamkar su dakatar da faruwar hakan amma sam basu da wannan damar, hakan kuwa ta tabbata suna ji suna gani bayan mako biyu a ka d'aura auran Prof da Mum.
Umma kuma ta koma gidan Abbu da zama gaba d'aya, kasancewar Mum a nan gidan ta ta tare haka dai Prof yayi ta, k'oqarin kasancewa muji na gari a gareta kuma uba na gari a gurin *Adeel.* Mum ta yi masa gwaji da dama amma yayi nasaran tsallakewa, wanda kuma hakan ne ya tabbatar mata da cewar ya canja, ya dawo mutumen kirki sosai shi yasa ita ma ta yanke shawaran kasancewa mata ta gari a garesa. Sunci gaba da zama cikin kyakkyawan yanayi hakan ya k'ara yiwa *Adeel* dad'i sosai, wani yammaci Prof ya samu *Adeel* zaune wani kyakkyawan guri tare da *Amna,* bayan sun gaisa Prof ya sauke kallonsa ga fuskar *Amna* tare da fad'ar sunan ta. *"Amna* dan Allah ko zaki iya bamu guri ina san zanyi magana da shi." Ta amsa shi da to ta tashi ta fice bayan tafiyar ta ya zauna tare da fad'ar sunan *Adeel.*
*"Adeel* ďana ina san zamu yi wata magana mai matuqar muhimmanci sosai, to ina fatan zaka bani had'in kai sosai sannan kuma zaka sanar da ni gaskiyar gaba ďaya." "Eh Dady kawai ka sanar da ni koma miye kuma zan sanar da kai gaskiyar idan har na sani." Yayi shiru kad'an sannan yaci gaba da magana. *"Adeel* dama a game da *Adnan da Adyan* ne zuciyata tana fad'a min wani abu a game dasu." Cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. "Dady mai zuciyarka take fad'a maka a game dasu ne.?" Ya nisa sosai tare da jan numfashi ya k'ara da sauke a jiyar zuciya, sannan daga bisani yaci gaba da magana. *"Adeel* ban san ya zaka d'auki abin ba, amma gaskiyar ita ce ina jin wani irin abu sosai a tare dasu, sannan kuma zuciyata tana fad'a min cewar su ne yarana da a ce sun mutu sabo da." "A'a Dady sam karka amince da abin da zuciyarka take fad'a maka, sabo da ba gaskiya bane kawai yaudarar ka take ya kamata ka fuskanci hakan."
*"Adeel* amma kuma komai a bai yane yake dukanku ukun, kuna tare da irin ciwo ďaya wanda kuma mahaifiyar ku ce take da wannan cutar, sannan kuma dukanku kuna matuqar san samosa da madara sosai, kai kafi kowa sanin irin yanda nake matuqar san samosa sosai, Mummyn ka kuma ba abin da take so fiye da madara sosai. Amma kuma ku duka biyun kuke so kuma sosai, ďana wannan ma ya isa ya tabbatar da gaskiyar, sannan kuma dai dukanku ukun kuna da kamanni da juna sosai, hakama kuma dukanku kuna matuqar qaunar junanku sosai. *Adeel* wannan ba zai faru haka kawai ba abin da yawa sosai, ni ina ganin kamar zuciyata gaskiya take fad'a min lallai ya kamata na yi wani abu. Amma kafin nan d'ana shin da gaske baka b'oye min komai dan Allah.?" "A'a Dady ni na riga dana sanar da kai duka gaskiyar to ya kamata ka yarda da ni please." "Shikenan na gode sosai zan tafi." Ya jinjina masa ka a lamar to da kuma haka suka rabu, cikin hanzari *Adeel* ya tashi ya nufi gurin Mum ya sanar da ita abin da yake faruwa.
"Mum ina ga kamar lokaci yayi wanda ya kamata Dady ya san a salin gaskiyar, to ni zanyi magana dasu a kan su amince da gaskiyar su bai yana kansu ga Dady, idan har su da kansu suka sanar da shi gaskiyar to zai iya fahimtar su, amma idan kuma shi da kansa ya gano gaskiyar to fa komai zai lalace ne." "Eh gaskiyar ka ne ya kamata ni nayi magana dasu zance su zo nan yanzu." Nan kuwa ta shiga kiran layin *Adnan* ta sanar da shi cewar suzo tana san ganin su yanzu, ya amsa ta da to sunyi sallama abin da basu sani ba shi ne, duk abin da suke fad'a a kan kunnan Prof ya fad'a a zuciyarsa. "Zuciyata tayi gaskiya ba shakka wannan dalilin ne yasa suka tsane ni sosai, tabbas na cancanci hakan daga garesu zan jira zuwan su domin mu fuskanci juna. Ina fatan zasu yafemin sannan kuma su karb'e ni a matsayin mahaifinsu ta yanda ahalinmu zai k'ara cika."
Ba jimawa sosai sai gasu *Adyan* sun k'araso zuwan su a kan idanuwan Prof, ba jimawa da shigarsu ciki shi ma ya shiga ciki, ya same su suna magana basu da wani zab'i a wannan lokacin. Wanda wannan dalilin ne yasa su sanar da shi gaskiya, yayi matuqar farin ciki sosai tare da nai man gafaran su, yana mai kaskantar da kansa yayin da yake zubar da kwalla. Mai tsananin zafi da k'una sosai sun kuwa yafe masa hakan yayi wa yi masa dad'i sosai, bayan kwana biyu dukansu zaune suke a tebur domin cin abinci, samosa ce da madara Mum ta had'a cikin hanzari dukansu suka kai hanayensu, ga samosa da sauri Dady ya dakatar dasu yana cewa. "Wannan ta ni kad'ai ce to kawai ku sha madara kun ji ko." "A'a Dady mu ba zamu yarda ba." Sun shiga yi masa magiya ganin kamar ba zai basu ba, yasa suka shiga wasoso tamkar wasu rana Mum sai dariyar su take, cike da soyayya da qauna Prof ya rungumasu jikin sa tare da sunbatarsu, yana furta musu kalmar yana qaunar su sosai bayan ya sake su, ya tashi ya nufi gurin Mum ya zauna k'asa da ita, tare da kama hanayenta sannan ya fara magana.
"Na gode sosai da kika shiga rayuwa ta, hak'iqa ke alkhairi ce a gareni dama rayuwa ta gaba d'aya. Da a ce baki dawo gareni ba to dana shiga uku na lalace, k'ila dai da ba zan rayu ba ko kuma nayi mak'ask'anciyar rayuwa, sabo da na jima da mutuwa amma kika k'ara raya ni, ke ce nan wacce ta sake bani sabuwar rayuwa na gode sosai Allah ya saka maki da mafi alkhairi, Allah ya sanya wa rayuwar yaranmu albarka data yaransu ita kuma *Amna* Allah ya sauke ta lafiya Amin." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai, ita ma haka murmushi take sosai wanda ya hana mata iya fad'ar komai, ya sunbaci hanayenta da suke cikin nasa tare da furta mata kalmar i love you. Cike da d'auki su *Adeel* sun k'arasa inda suke lokaci ďaya suka yi hugging juna, bayan sun sake juna suka tashi suka koma tebur suka fara cin abinci, haka dai suka ci gaba da rayuwa cikin kyakkyawan yanayi, dukansu yaran suna farin ciki sosai tare da duka ahalinsu. Ba kuma tare da sun bar wata kafa wadda zata bari wani ya san gaskiyar ba, bayan wasu watanni *Amna* ta aihu ta aifi twin's duka mata, farin ciki gurin su Prof abin ba zai fad'u ba sai dai na ce suna farin ciki sosai.
Bayan suna da wata biyu su Appa suka fara shirin tafiya England, su Mum sai ji suke kamar su dakatar da shi amma sam basu da wannan damar, haka suka ci gaba da shirin tafiya bayan mako biyu jirginsu ya tashi, sun samu rakiyar duka iyayensu Mum da Prof Abba da Mama Papa da Mamie da kuma su Kaka wato Abbu. Sun rungumi juna cikin qauna da soyayya sannan daga bisani suka yi sallama, su Umma sun bisa da kallo suna d'aga musu hanu har suka b'ace, suma abin da suke yi kenan har suka fice ba jimawa sosai jirginsu ya tashi, su *Adnan* sun bi jirgin da kallo suna murmushi tare da yi musu bye-bye. Sai bayan jirgin ya tafi ne sannan su *Adeel* suka shiga mota zuwa gida.........................
*To Alhamdulallah kuma a daidai wannan gabar ce na kawo k'arshen, wannan littafin nawa mai taken suna THREE BROTHER'S. Ina fatan abin dana fad'a ba alkhairi Allah ya bani ladarsa, inda kuma na samu tintib'en harshe Allah ya gafarta min, sannan kuma Allah yasa muyi anfani da darasin dake ciki Amin. Da kuma haka nake cewa sai mun had'u daku a wani sabon littafina, sai an jima ma'assalam.*
*Godiya gareku tarin masoyana mabiyana, masu yi mani fatan alkhairi ina godiya sosai Allah ya bar qauna Amin. Jinjina ga k'ungiya ta wacce ta taimaka min sosai gurin ganin nayi duk wani abin daya kamata, to ina godiya sosai Allah ya k'ara d'aukaka ta ya kuma sanya mata albarka Amin.*
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*