Showing 54001 words to 57000 words out of 142761 words
Chapter 19 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
nai man *Adnan* amma bai yi nasaran ganin sa ba mst yaja tsaki yana 'bata fuska, ya kai hanun sa ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin *Alishart* ya samu a na anfani da wayar mst ya koma jan tsaki ha!!! *"Adnan* bai ya online ita kuma *Alishart* tana anfani da waya ko dawa take waya oho? Bara na gwada layin *Adnan* na ga ko zai shiga ina fatan layin sa ya shiga."
Nan kuwa ya shiga kiran layin *Adnan* yayi sa'a layin ya shiga ba jimawa ya d'aga. *"Adyan* barka fatan kana lafiya to ya kake.?" Yayi shiru kad'an tare da jan numfashi sannan daga bisani ya amsa shi. *"Adnan* 'yar damuwar kad'an ce to kai fa ya kake.?" "Subhanalillah fad'a min miye damuwar domin naji da abin da zan iya taimaka wa.?" "Dama a office ne wata ta 'batan rai sosai, bayan na dawo gida kuma na duba ka online amma ban same ka, wannan yasa na koma kiran layin *Alishart* ita kuma tana tana waya da wani daban. Hakan ya qara min damuwa sosai amma yanzu ina lafiya sabo da na same ka." *Adnan* yayi murmushi kad'an sannan ya amsa shi.
"Eyya afuwan d'an uwa kayi hak'uri a game da wannan matar, a game da ni kuma ina mai baka hak'uri ina a bakin aiki ne shi yasa ban iya hawa online ba. Sannan kuma a game da qanwata ka san bata da wata, da wayar Mamie kuke magana to ina jin Mamie ce take anfani da wayar bawai qanwata ba. Fatan ka fahimci mai nake nufi sannan kuma zaka dena fishi da dukanmu.?" *"Adnan* nifa bana fishi da kai musamman *Alishart* kawai dai ni na damu ne da ban samu nayi magana daku ba. Amma yanzu komai daidai yanzu kawai kayi aikin ka, idan ka koma gida ka had'a ni da *Alishart* muyi magana dan Allah." "Muna godiya sosai karka damu zan had'a ka da qanwata nayi alkawari insha Allah, amma kafin nan kai kuma zaka yi man alkawarin cewa ba zaka yi k'unci ba." Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "eh nayi alkawari ba zanyi k'unci ba insha Allah, na gode sosai da kulawa to kai ma ka kula sosai ka ji ko." Ya amsa shi da to yana dariya shi ma abin da yake yi kenan, da kuma haka suka yi sallama bayan kwana biyu..............
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/17, 4:01 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
*THREE BROTHER'S*
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
*Page 22*
β *β GΜΎOΜΎLΜΎDΜΎEΜΎNΜΎ PΜΎEΜΎNΜΎ WΜΎRΜΎIΜΎTΜΎEΜΎRΜΎSΜΎ AΜΎSΜΎSΜΎOΜΎCΜΎIΜΎAΜΎTΜΎIΜΎOΜΎNΜΎ* ββ
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*wΜΆΜΆΡ Ξ±rΜΆΜΆΡ Π²ΡΞ±rΜΆΜΆΡrΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟ gΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓtΜΆΜΆΡ Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓdΜΆΜΆΓΟuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ pΜΆΜΆΡrΜΆΜΆcΜΆΜΆΡΓvΜΆΜΆΡ nΜΆΜΆΟ pΜΆΜΆΞ±ΓnΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓcΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡΞ±tΜΆΜΆΓvΜΆΜΆΡ gΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ* β *,Π²ΡhΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟfΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟrΜΆΜΆ ΓtΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓlΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ ΡΟuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟ pΜΆΜΆΞ±ΓnΜΆΜΆ.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ΖUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ΖARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζara mana Ζarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Saturday 15/01/2022*
*Time 07:58pm*
*Typing..............*
*Nigerian.*
Kwance take amma ba barci take ba ta wani lumshe ido, baitin wak'ar dake ratsata ne yasa har take wani rufe ido, lokaci d'aya ta ji Mamie tana kiran ta, ta amsa da k'arfi tare da tashi ta fita zuwa parlour da sauri har tana gudu. Ta fito ta samu Mamie zaune ta isa inda take tare da furta mata gani, *"Alishart* tin da kika qarasa exam kika d'aura aure da sauraran wakokin wannan secret super star Δin, baki da aiki sai sauraran wak'ar sa ni kuma ki banni da aikin gida, kar'bi nan tin d'azu *Adyan* yake kira yana san zaku yi magana." da sauri ta kar'bi wayar tare da furta mata kalmar. "Kiyi hak'uri Mamie ni kawai ina jin dad'in wakokin sa ne, shi yasa ko yaushe nake sauraran sa sabo da yana saka ni nishad'i sosai, sannan kuma ina k'ara fahimtar turanci sosai, karki wani damu sabo da zanci gaba da taya ki aikin gida insha Allah sannan kuma." Ringing Δin wayar da take hanun ta ne ya saka ta yin shiru ta juya ta nufi d'akin ta, Mamie ta bita da kallo tana girgiza ka yayin da take magana. "Yarinya sai d'an banzan surutun tsiya idan ta fara magana sam bata jin ta gaji, Allah ya k'ara shirya mana zuri'a Allahumma Amin."
Da gudu ta shiga d'aki ta fad'a gado tare da amsa wayar. "Kin kyauta sosai sai yanzu kike amsa min waya." "Kayi hak'uri *Yaya Adyan* wayar tana hanun Mamie ne shi yasa fatan zaka dena fishi da ni.?" "Waya fad'a maki cewar ina fishi dake a'a bana yi kuma ba zanyi ba." "Na gode Yayana." *"Alishart* wai har yanzu kina sauraran wak'ar wannan secret super star Δin.?" "Eh *Yaya Adyan* sabo da ina sansa sosai sannan kuma yana saka ni nishad'i sosai. Ko k'unci nake da zaran na saurare sa sai na fara nishad'i shi Δin na musamman ne, ya san ta yanda zai ja hankalin mutane sabo da ya iya dad'ad'an lafuzza masu matuqar dad'i sosai da sanyaya zuqata. Gaskiya ina matuqar qaunar sa sosai shi ne jarumi na ina fatan had'uwa da shi." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarta sosai, yayi shiru sai sauraran ta yake har ta qarasa jin shirun yayi yawa ne yasa ta fad'ar sunan sa. *"Yaya Adyan* shin kana jina kuwa.?" Shiru bai amsa ba taci gaba da magana, *"Yaya Adyan* dan Allah ka amsa ni shin qlau kake kuwa mai yasa baka san kayi magana? Shin ni na aikata wani zunubi ne fad'a min shin da akwai wani abin da ba daidai ba dan Allah kayi min magana.?" Still bai yi magana ba sai daga bisani sannan ya amsa ta.
*"Alishart* mai ya saka kike san abin da babu shi? Shi wannan mutumen ba mutum bane shin ke baki ga hakan ba? Ya kamata a ce kin fahimci haka tin daga sunan sa babu wani wanda ya san shi balantana wanda ya ta'ba ganin sa, ko a cikin wak'ar sa sam bai ya barin wata a lama wacce zata sa a fahimci a salin waye shi. Amma kuma duk da haka ke kike qaunar sa har haka mai ya saka kike san shi sosai ke kina san shi da yawa mai yasa.?" *"Yaya Adyan* nima ban sani ba abin dana sani shi ne kawai ina qaunar sa sosai to ba zan iya canja gaskiyar ba, sannan kuma sabo da kai ne ni na fara sauraran sa da fara ina k'ara iya turanci, hakan ne yake bani damar da nake yin magana da kai sosai, sannan kuma shi Δin ya fad'i cewa a k'asar England yake ka ga k'asar ku Δaya kenan. Daga k'arshe kuma yana saka ni nishad'i sosai hakan yasa na fara sansa." Ya nisa tare da jan numfashi sannan ya amsa ta.
"Eh gaskiyar kika fad'a a nan k'asar England yake amma kuma ba wani wanda ya san shi, amma kuma duk da haka ya tara tarin masoya da mabiya wakokin sa sun zaga duka duniya gaba d'aya. Hakan yasa ko ina na duniya zancan sa a ke waye shi ba wanda ya sani, *Adnan* ya iya turanci sosai to mai yasa ba zaki koya daga garesa? Sam bai kamata ki fara san mutumen da baki san komai a kansa ba." *"Yaya Adyan* da a ce tin farko kai kana jin hausa to da duka wannan bai faru ba, amma idan kana so to ni zan koya ma." "Da gaske ke zaki koya min.?" "Eh zanyi kawai ka sanar da ni idan ka shirya wa hakan." "Na shirya zamu iya fara wa yanzu." "Ba zai yu yanzu ba." "Mai yasa.?" "Sabo da ina san zanyi anfani da laptop d'in Yayana yayin da nake koyar da kai sabo da zaka fi fahimta na."
*"Alishart* shin zan iya tambayar ki wani abu.?" "Eh ina jin ka." *"Alishart* shin kina da ra'ayin waya da laptop naki na kanki.?" "Eh amma mai ya saka ka tambaya.?" "Ba komai zamu yi magana an jima, k'ila kuma kafin na ki ganni a gaban ki." Cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. "Miye kana ina karka fad'a min cewar ka shigo Nigerian.?" "A'a ina England amma zan iya zuwa yanzu kawai sabo da na ganki na jima ina mafarkin hakan." "Ai kana gani na ko yaushe idan muna video call." "Wannan kawai a waya ne to ba zai wani wadatar ba, shi yasa nake san na domin had'uwa dake k'ila nazo yanzu." "Sam bai kamata naji mamaki ba, sabo da kai na musamman ne Kakan ka ina nufin Abba shi ne shugaban k'asar nan, sannan kuma d'ayan Kakan ka ina nufin Abbu shi ne gwamnar kaduna, to kana da damar da zaka yi duk abin da kake so kai d'an gata ne sosai." *"Alishart* ko zaki iya yin shiru haka? Sabo da maganar ki ta fara yawa sosai." "Shikenan nayi shiru." Ta fad'a tana 'yar dariya shi ma abin da yake yi kenan, sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama.
Suna gama waya *Adyan* ya shiga kiran layin Ameer ba jimawa ya d'aga, bayan sun qarasa gaisa wa *Adyan* yaci gaba da magana. "Am Ameer dan Allah wani taimako nake buqata a gareka." *"Adyan* kawai ka fad'i koma miye ni kuma zanyi nayi alkawari insha Allah." "Na gode sosai am Ameer shin kasan aboki na *Adnan* wanda yake a nan kaduna sannan ka san gidan su.?" Ya amsa shi da eh yaci gaba da magana, "Ameer to zan turo ma da kud'i zaka siyi waya laptop da tap masu kyau sosai, sannan zaka siyi layin waya da kuma katin waya kar yayi k'asa da dubu hamsin. Ragowar kud'in ko nawa ne ka siyi chocolate biscuits da alawa, ka shirya komai yanda zai yi kyau sosai kuma ya k'ayatar sai ka tafi gidan su *Adnan Alishart* zaka baiwa qanwarsa. Duka sakon nata ne fatan ka fahimce ni sosai.?" "Eh na fahimta sosai." "Ok zan turo ma miliyan uku Δaya taka ce ladan ka biyun kuma na siyayyar ne, idan kuma kud'in bai isa ba to kawai ka sanar da ni Ameer amma zaka iya kai mata sakon yau.?"
"Eh zan iya yin komai a yau sannan kuma ina godiya sosai Allah ya bar zumunci ya kuma bar qauna Amin." Shi ma ya amsa da Amin da kuma haka suka yi sallama. *"Alishart* wai zaki fito daga Δakin nan ko kuwa.?" Da sauri ta tashi ta fita har tana gudu ta isa parlour tare da isa inda take tana furta mata gani. "Bani waya ta sannan ki tashi mu shiga kicin, rana tayi bana san *Adnan* ya dawo gida ban kammala girki ba to mu tafi." "Mamie hakan yana da sauk'i sosai sabo da shi madara ce abin da yafi so." "Eh haka ne sannan kuma shi Δin yana matuqar san samosa sosai da juice d'in kwakwa, to abin da zamu shirya masa kenan to mu tafi." "Mamie to Papa fa mai zai ci.?" "Zaici duk abin dana ba shi kuma bana buqatar wata tambaya bayan wannan to mu tafi." Ta amsa da to ta tashi sun nufi kicin sun fara aikin samosa, *Alishart* na shafa fulawa Mamie tana nad'ewa ba wani d'aukan lokaci suka qarasa, sun kuma koma ta gurin juice Δin kwakwa bayan sun qarasa sun shirya komai a kan tebur. Sannan daga bisani suka shiga ciki *Alishart* na shiga ciki ta fad'a gado tayi kwance sai wata gajiya take ji a tare da ita, ba jimawa sosai wani barci yazo d'auke ta bayan Mamie ta qarasa shirin ta tsab ta fito, rashin ganin *Alishart* a parlour ya tabbatar mata da cewar tana Δakin ta.
Ta juya ta nufi can ta shiga ciki ta same ta kwance tana ta sharan barci tayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan ta. *"Alishart* kenan 'yar laushi yanzu wannan samosar da muka yi ita ta gajiyar dake, har dasu barci kamar wadda tayi duka aikin gidan nan ai kuwa haka zaki ci gaba har ki saba. Ke macace to ya zama dole da ki iya duk wani aiki na mata, kafin lokacin da zaki tafi gidan mujin ki wato siriki na ina sanki 'yata Allah yayi maki albarka Amin." Ta shafi fuskarta tare da sunbatarta sannan ta juya ta fita, *Alishart* ta jima tana barci sannan ta farka kai tsaye toilet ta fad'a tayi wanka tare da d'ora alwala ta fito, ta fara gabatar da salla sannan ta shirya cikin wata kyakkyawar doguwar riga, shigar ta amsheta sosai ta juya ta fita zuwa parlour. Ta samu Mamie ita kad'ai tana k'oqarin zama taji a na buga k'ofa ta juya ta nufi k'ofa tare da bud'e wa, ta samu Papa da *Adnan* tsaye a bakin k'ofa lokaci d'aya ta saki wani kyakkyawan murmushi, cike da d'aukin ganin su take fad'ar sunayen su tare dayi musu sannu da zuwa sun amsa tare da shiga ciki.
Cike da d'aukin ganin su Mamie ta shiga yi musu sannu da zuwa Papa yake amsa ta yayin da *Adnan* ya nufi tebur, tafiya yake k'amshin yana k'ara kusa da shi ha!!! Ya nisa sosai tare da lumshe ido yana wani rawa da ka, yaja kujera ya zauna tare da bud'e kayan abincin dake gurin yayi tozali da abin da yafi so wato samosa. Nan kuwa ya fara cin ta Mamie ta shiga tambayar Papa *Adnan* kafin ya furta komai *Alishart* ta saki dariya sannan ta amsa ta. "Mamie ki duba tebur kiga mebi zaki iya samun sa a nan." Lokaci d'aya dukansu suka kai kallonsu ga tebur sun hangi *Adnan* zaune yana aikin cin samosa, lokaci d'aya suka saki wani kyakkyawan murmushi mai tare da 'yar dariya sun nufi inda yake. Sai wani kallonsa suke kallo sosai Mamie ta shafi kansa zuwa fuskarsa tare da sunbatarsa tana fad'ar sunan sa, *"Adnan* shin kana farin ciki da wannan samosar.?"
Ya shafi hanun ta da yake kan fuskar sa tare da sunbata cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Eh Mamie farin ciki sosai na gode sosai ina sanki Mamie ina matuqar masifar qaunarki sosai I LUV U SO MUCH Mamie." Ya fad'a tare da yin kwance jikin ta ita kuwa sai sunbatarsa take, "nima ina qaunarka sosai d'ana soyayyar da bata da na biyu kai ne abin dana ina sanka sosai." Magana take cikin kyakkyawan yanayi tare da k'ara saka shi jikin ta tana sunbatarsa. Papa yazo ta bayan ta yayi hugging d'in su tare da *Alishart* yana cewa, "wannan rashin adalci ne zaku rungumi juna kubar mu biyun a ware, ya kamata a ce dukanmu ne muka rungumi juna kamar dai haka." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi, suma abin da suke yi kenan sun jima a haka sannan suka sake juna sun juya zasu tafi, *Adnan* ya dakatar da *Alishart* ta hanyar fad'ar sunan ta.
*"Alishart* ki tafi kiyo man kiran Besty ki ce tazo yanzu kinji ko." "Yayana amma duka gidan muna buqatar samosa to amma kuma." *"Alishart* ki tafi ki kira man Besty karki bari na k'ara maimaita maki abin da nake buqata daga gareki kinji ko." Ta amsa da to ta juya ta nufi hanyar fita su Mamie sun bita da kallo suna murmushi, shi ma abin da yake yi kenan su Papa sun shiga ciki shi kuma yaci gaba da cin samosa, *Alishart* ta shiga gidan su *Afnan* tare da sallama ta samu *Afnan* tana k'oqarin hawa sama, ta fara da gaisawa dasu Abba sannan ta mai da kallonta ga *Afnan* tare da fad'ar sunan ta. "Aunty d'an dakata kad'an Yayana yace nazo na kira ki." Tayi murmushi sosai tare da furta mata kalmar mu tafi ta amsa da to sun sanar dasu Ummu sannan suka tafi.
Sun isa gida tare da shiga ciki kai tsaye tebur suka nufa gurin *Adnan,* ya tare su da murmushi tare da yiwa *Afnan* ta yin gurin zama, ta amsa tana murmushi ta zauna suna haka sai ga Mamie ta fito wanda kuma kicin ta nufa, *Afnan* ta gaishe ta ta amsa tana murmushi ta nufi kicin ba jimawa ta fito ta nufi bedroom *Alishart* ta anbaci sunan ta. "Mamie ki bani wayan ki da akwai abin da zanyi da ita." *"Alishart* gaskiyar ita ce ina san zanyi anfani da kud'in da yake waya na to kiyi hak'uri." Ta juya zata tafi da sauri *Alishart* ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "Mamie ni ba wanda zan kira kawai fa zanyi Game ne shi ne kawai to zaki iya yarda da ni please."
*"Alishart* nace a'a to kawai ki hak'ura kinji ko." Lokaci d'aya ta saki wani kukan shagwa'ba da sauri *Adnan* ya tashi ya nufi inda take, ya shiga rarrashinta yana lalla'bata tamkar wata k'aramar yarinya. "Ya isa haka qanwata kar'bi ga waya na ga kuma laptop d'ina kiyi duk abin da kike so, amma dan Allah ki dena wannan kukan bana so kinji please." Ta amsa da to tana murmushi tayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa sannan ta kar'bi wayar tare da d'aukan laptop ta nufi d'akin ta, sun bita da kallo suna murmushi Mamie ta girgiza ka ta juya ta nufi bedroom