Showing 96001 words to 99000 words out of 142761 words
Chapter 33 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
wannan." "Aboki karka gade min kawai kayi farin ciki sabo da zamu samu damar kasancewa tare, wannan shi ne abin da yake da matuqar farin ciki sosai." Sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama.
Haka su Appa suka shiga tarban zuwan su *Afnan Adnan* ya sanar dasu Papa, sam basu yi yunk'urin dakatar da shi ba yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare da, *Adeel* ya kira layin *Adyan* yayi masa godiya ya amsa shi da ba komai. Haka suka ci gaba da shirin tafiya bayan kwana biyar jirginsu ya tashi zuwa k'asar England........
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/8, 4:05 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 39*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Sunday 06/02/2021*
*Time 10:35pm*
*Typing................*
Suna fitowa Airport suka samu *Adyan da Alishart* suna jiran fitowar su, cike da d'auki *Alishart* ta isa gurin Yayan ta tare da fad'a wa jikin shi, shi kuwa ya runguma ta tare da sunbatar ta bayan sun sake juna, ta koma ta gurin *Afnan* sun rungumi juna.
Bayan sun sake juna sun k'arasa gurin *Adyan* wanda yake ta aikin furta musu sannu da zuwa, cike da d'auki suka yi hugging juna bayan sun sake juna ya sauke ta ga *Adeel,* yayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan sai ya amsa yana murmushi. *Adyan* ya ba shi hannu suka gaisa, ya mai da kallonshi ga su Umma, yaci gaba da yi musu sannu da zuwa tare da furta musu su tafi, sun nufi mota suna cikin tafiya *Adnan* ya dafa shi tare da fad'ar sunan shi. "Abokina amma qlau kake kuwa gaskiyar zaka fad'a.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh yana murmushi shi ma ya mayar masa da murmushi, sun nufi mota sun fara saka kaya both sannan suka tafi, sun isa gida su Appa sun shiga yi musu sannu da zuwa sun amsa suna murmushi.
Bayan sun zauna sun gaisa Ammie tayi musu ta yin abinci sun tashi sun nufi tebur, dukansu suna cin abinci amma banda *Adyan* sai wasa kawai yake da cokali, Ammie ta anbaci sunan ta tare da tambayar sa. "Rabin raina qlau kake kuwa.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh taci gaba da magana. "Rabin raina to mai ya saka baka cin abinci.?" Ya amsa ta da ba komai tare da tashi ya nufi wani gurin daban, Appa na k'oqarin binsa *Adnan* ya dakatar da shi ya tashi ya bisa a baya. Ya same sa tsaye gurin flowers yayi shiru ga a lama tunani yake, *Adnan* ya k'arasa inda yake sai wani kallonsa yake kallo sosai yana wani girgiza ka, ya dafasa tare da fad'ar sunan sa kallonsa kawai yake ba tare daya amsa ba *Adnan* yaci gaba da magana. "Aboki kallo d'aya nayi ma na fahimci cewar ba qlau kake ba, amma kace da ni a'a Aboki naro e ka dan girman Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake damunka please.?" Yayi shiru sai kallonsa yake kallo sosai yana girgiza ka, ya nisa sosai tare da jan numfashi cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Ka yafemin Aboki sannan kuma karka yi fishi da ni dan Allah." "Aboki wai mai kake fad'a ne haka ni baka yi min komai ba to mai yasa kake bani hak'uri.?"
"Aboki dama a game da *Adlishart* ne." Da sauri cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. "Aboki shin wani abu ya faru da qanwata ne.?" "Aboki abin shi ne ita." Ya kuma yi shiru yana girgiza ka tare da furta a'a, *Adnan* kuwa sai wani kallonsa yake cike da firgici da rud'ani yake magana. "Aboki naro e ka dan Allah da girman Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da qanwata please.?" "Aboki ni na aikata babban zunubi wanda har ina jin kamar ba zan iya yafe wa kai na ba, sam bai kamata a ce ni na aikata hakan ba amma kuma na kasa jurewa, ko yaushe ji nake ina k'osawa sannan kuma ni na kasa dakatar da kai na, Aboki ni banda wani zab'i ne to ina fatan zaka fahimce ni sannan kuma zaka yafemin dan Allah." "Aboki har yanzu baka sanar da ni abin da yake faruwa ba, to kawai ka sanar da ni koma miye dan Allah ka ji please.?" "Aboki *Adlishart* tana tare da juna biyu na wata biyu."
Cike da firgici da rud'anin abin daya fad'a yake magana. "Miye Aboki wai gaskiyar kake fad'a kuwa.?" "Eh Aboki tin a satin da muka yi aure hakan ta faru dan Allah ka yafemin please." "Aboki kai baka aikata wani kuskure ba to ba zan kira wannan da zunubi ba, Aboki ni kawai na damu ne a kan qanwata sabo da har yanzu ita yarinya ce, sannan kuma tana da k'ananun shekaru a wad'an nan shekarun nata, tayi k'ank'anta da a ce ta aihu shekarun ta sha biyar ne kawai, to ya idan kuma wani abu ya faru da ita fa.?" "A'a Aboki sam ba abin da zai faru da ita dukanmu zamu kula da ita sosai, zamu yi komai sabo data kasance lafiya to zaka iya yarda da ni dama iyayena." Ya jinjina masa ka a lamar to *Adyan* yaci gaba da magana.
"Aboki amma zaka jima sosai kana fishi da ni.?" Ya girgiza ka yana murmushi sannan daga bisani ya amsa shi. "A'a Aboki ni sam bana fishi da kai kuma ba zan tab'a yin fishi da kai ba na har abada wannan alkawari ne." "Wai da gaske kai baka fishi da ni.?" Ya jinjina masa ka yana murmushi lokaci ďaya shi ma ya saki murmushi, cike da d'auki sunyi hugging juna ba jimawa suka sake juna. "Aboki amma qanwata ta san cewar tana tare da juna biyu kuwa.?" Ya girgiza ka tare da furta a'a, "Aboki ya kamata ka sanar da ita domin akwai buqatar ta sani ka ji ko." Ya jinjina masa ka tare da furta to bayan wani lokaci suka koma babban parlour, sun samu su Appa sun k'arasa cin abinci har sun kai su Mum masauki, *Adeel* ne kawai a parlour sun k'arasa gurin sa sun zauna shi kuwa sai wani kallonsu yake yana murmushi. "Sannun ku da dawowa fatan kuna cikin k'oshin lafiya sosai.?" "Eh muna lafiya kayi hak'uri da muka tafi muka barka a nan to ina su Umma.?"
"Ba komai sannan kuma su Mum an kai su masauki Umma na tare da Mum, *Alishart* kuma tana tare da Maman baby to zaka iya duba dukansu." Sun jinjina masa ka sun tashi sun koma ga tebur sunci abinci, bayan sun qarasa *Adnan* ya nufi gurin matar sa ba jimawa *Alishart* ta fito, ganin ta fito ne yasa *Adeel* tashi ya nufi gurin su Umma *Adyan* na dakatar da shi amma ya fice abinsa, bayan tafiyar sa suma tashi suka yi suka nufi d'akin su. *"Adlishart* da akwai abin daya kamata na sanar dake yanzu." "Ina jin ka masoyi zaka iya sanar da ni koma miye." Yayi shiru kad'an sannan yaci gaba da magana, *"Adlishart* dama a game da yaron da zamu aifa ne nake san muyi magana." Lokaci d'aya ta saki dariya kuma a haka take magana. *"Adlishart* to mai yasa zamu yi magana a kan abin da bamu san lokacin zuwan sa ba? Karfa ka manta cewa nan da wata biyu zan koma gida na fara zuwa makaranta. Sannan kuma zan aihu ne kawai bayan na kammala karatu na, kamar dai yanda kai kayi min alkawari to kama dena yi min zancan yaro yanzu ka ji ko dan Allah."
Shiru bai yi magana ba sai wani kallonta yake kallo sosai, ya nisa da k'arfi tare da jan numfashi sannan ya fara magana. "Kiyi hak'uri dan Allah ki yafemin sabo da ni na kasa cika maki alkawarin dana yi, Masoyiya abin shi ne ke kina tare da juna biyu na tsayin wata biyu amma." "A'a hakan sam ba gaskiya bane sabo da kai kayi min alkawari to kawai ka fad'a min cewar wasa ne ka ji ko dan Allah." "Ki yafe min Masoyiya sabida ba zan iya canja gaskiyar ba kina tare da juna biyu amma." "A'a hakan ba zai yu ba kai kmin k'arya ba zan k'ara yarda da kai ba." Magana take tana kuka yayin da take ta aikin dukan cikin ta, yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta yana furta mata, "ya isa haka ki dena zaki iya cutar da yaron kuma hakan sam bai dace ba sannan." "Kawai ni ka rabu da ni sabo da bana san nayi magana da kai." "Haba masoyiya dan Allah karki cutar da ni sosai haka sabo da." *"Adlishart* nace a'a to kawai ka rabu da ni dan Allah."
Tana kai k'arshen maganar ta ta tashi tayi tafiyarta, ya tashi da sauri ya bita yana fad'ar sunan ta amma bata amsa shi ba, ta nufi k'ofar su *Afnan* ta shiga buga musu k'ofa tare da fad'ar sunan Yayan ta, ba jimawa ya bud'e k'ofar ya shiga anbatar sunan ta dama na *Adyan.* Kafin ya furta komai sai gasu Ammie sun fito nan kuwa suka shiga tambayar su abin da yake faruwa. "Ammie to ita tana fishi da ni ne sosai sabo da na sanar da ita gaskiyar cewa tana tare da juna biyu, sam ta mak'i saurara na har tana k'oqarin cutar da yaronmu, sai dukan cikin ta take sannan kuma ta dakatar da ni daga yi mata magana. Appa ni ban san ya zanyi ba domin nasa ta fahimta sabo da tana fishi da ni sosai."
Kafin su Ammie su furta komai *Alishart* tayi musu rigagi ta hanyar amsa shi. "To mai yasa ba zaka fad'a musu duka gaskiyar ba? Ka fad'a musu cewar kai kayi min alkawarin cewa ba zan aihu ba har sai na kammala karatu na gaba d'aya. To amma mai kayi kai kama kasa cika min alkawarin da kayi min, dan haka ba zan k'ara yarda da kai ba sannan kuma ba zan k'ara yi maka magana ba." Tana kai k'arshen maganar ta ta juya ta nufi bedroom d'in su *Adnan Afnan* ta bita a baya tana rarrashin ta, Appa ya nufi inda yaronsa ya janyo hanun sa sun zauna ya shafi kansa tare da fad'ar sunan sa. "Rabin raina na san cewar hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai, amma dole zaka jure wannan har zuwa lokacin da ita zata dena fishi da kai, *Adyan* dole ka jurewa wannan sannan kuma kaci gaba da bata kulawa sosai, ta yanda ita da kuma Babyn zasu kasance cikin k'oshin lafiya sosai ka ji ko."
"Appa nima abin da nake koqarin yi kenan amma kuma tak'i ta amince da ni, ta mak'i bani damar da zan iya kulawa da ita da kuma yaronmu, ni kawai ina san na san yanayin lafiyar Babyn sabo da yanda tayi ta dukan cikin ta, amma kuma ta kasa bani damar da zanyi hakan na kuma kasa yin komai bani da anfani." "A'a ďana ka dena fad'ar haka ita kawai tayi fishi amma komai zai yi daidai insha Allah, sannan kuma ni zan duba yanayin lafiyar Babyn ina fatan ya kasance lafiya." Ya jinjina mata ka a lamar to *Adnan* ya k'arasa gurin da suke ya sauke kallonsa ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. "Aboki karka yi k'unci sosai ni zan daidai ta komai insha Allah, yanzu kawai tayi fishi ne sosai amma komai zai yi daidai insha Allah, to zaka iya yarda da ni ka ji ko." "Na gode sosai Aboki kai kana da kirki sosai ina farin ciki sosai da samun ka, a matsayin Abokina sannan kuma ina alfahari da hakan sosai ina godiya sosai a kan komai." "Aboki kai na kana da kirki sosai sannan kuma ina farin ciki da samun ka sosai."
Lokaci d'aya suka yi hugging juna suna murmushi hakama su Appa murmushi suke, dama *Adeel* wanda yake daga gefen k'ofa yana kallonsu, su Ammie sun tashi sun shiga ciki hakama *Adeel* juyawa yayi ya shige abinsa. Bayan wani lokaci suka tashi suka shiga gurin su *Alishart* suke, sun samu *Afnan* tana ta tausan ta tare da bata magana, nan kuwa *Adnan* shi ma yasa baki suka ci gaba da rarrashin ta sai wani lalla'bata suke tare da bata magana, wanda har sai da suka samu ta iya fahimtar su ta dena fishi da mai gidan ta. Bayan wani lokaci da komai ya daidai ta suka tashi suka koma d'akin su washe gari Ammie ce da kanta, ta duba lafiyar Babyn ta hanyar yi mata Scan Alhamdulallah Babyn yana cikin k'oshin lafiya sosai. Hakan yayi wa dukansu dad'i sosai bayan kwana biyu *Adyan* ya fara binkice a kan rashin lafiyar Mum, ya duba file ďin ta wanda duka record ďin rashin lafiyar ta yake ciki.
Wani yammaci zaune suke a wani kyakkyawan guri, wanda an yi shi ne musamman sabo da hutawa *Adyan* ya kai kallonshi ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* da akwai abin daya kamata muyi magana a kai."
"Shikenan zaka iya sanar da ni koma miye."
*"Adeel* a game da Mummyn ka ne shin da gaske tana da rauni a k'arkashin zuciyar ta.?"
"Eh shi yasa nima nake tare da wannan cutar."
*Adyan* ya jinjina ka yaci gaba da magana, "amma da gaske kai kad'ai ne d'an ta.?"
"Eh haka ne ni kad'ai ne d'an ta amma mai ya saka ka tambaya.?" "Ba komai kawai dai saboda naga yanda take magana a kan wasu yaran ne amma kawai ka manta, yanzu ka fad'a min wani abu wane irin abinci ko abin sha ita ďin tafi so?".
*"Adyan* Kaka ta ita ta fad'a min cewar Mummy na tana matuqar son madara sosai, ko yaushe ita ce kawai abin da take sha tana santa sosai Dady na kuma samosa ce abin da yafi so, shi yana da saurin fishi amma kuma baya jimawa yake sauka. Ina son Dady na sosai duk da irin girman zunubin da ya aikata a gareni, da kuma Mummy na amma hakan sam bai hana ni sonshi ba sai dai kuma ina matuqar yin fishi da shi sosai."
Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da idanuwan shi suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai, zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. *Adyan* sai wani kallonsa yake kallo sosai yayin da tausayin shi yayi yawan gaske a tare da shi, ya shiga rarrashin shi yana ba shi magana, ya k'ara da yin hugging d'in shi..............
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/9, 4:59 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 40*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Monday 07/02/2022*
*Time 41:29pm*
*Typing.............*
Zaune yake ya ji zaman ba dad'i ya tashi sai safa da marwa yake, yayin da tunani iri daban-daban yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Dafasa ďin da a kai ne yasa shi kai kallonsa garesa lokaci d'aya yayi tozali da fuskar *Adnan.* "Aboki qlau kake kuwa fad'a min abin da yake faruwa da kai? K'ila ba zan rasa abin da zan taimake ba to yanzu fad'a min miye damuwar.?" Yayi shiru sai aikin kallonsa yake yana girgiza ka sun tafi sun zauna, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallon *Adnan* yake, sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi. "Aboki