Showing 39001 words to 42000 words out of 142761 words
Chapter 14 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
hanyar daya dace ba, to ba buqatar ka damu sabo da ita qanwata daban ce a cikin mata, zata kasance yarinyar kirki sosai kuma zan tabbatar maka da hakan insha Allah." "Ina fatan haka Allah ya amince mana Amin." Suna haka suka ji a na buga masu k'ofa lokaci d'aya *Afnan* ta saki wani kyakkyawan murmushi tare da fad'ar sunan *Adnan.* Ta tashi da sauri har tana gudu ta isa ga k'ofa tare da bud'e wa ta kuwa samu *Adnan* tsaye a k'ofa tare da *Alishart,* sun tari juna da wani lallausan murmushi abin birgewa ga wanda ya gani. "Na gode Allah daya kasance cewar kin qarasa shirya wa yanzu zamu iya tafiya, Papa da Mamie suna jiranmu karmu makara to mu tafi na fara gaisawa dasu Abba sai mu tafi."
Ta amsa da to sun dawo ciki tare ya fara gaisawa dasu Ummu, sannan suka tashi dukansu suka fita domin tafiya, sun fito sun samu su Mamie a nan waje bakin mota suna jiran fitowar su *Adnan.* Sun fara gaisawa dasu Abba sannan su *Afnan* suka shiga mota suka tafi, zaune suke suna break past cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa suka fara shirin tafiya gurin taron su Amir. Umma da Ummi zasu tafi ne domin amsa gaiyatar Anisa da Abdulrahim, Abba da Abbu kuma zasu tafi ne domin amsa gaiyatar shugaban makaranta da yayi musu, ya gaiyace sune sabo da kasancewar su manyan mutane sannan kuma gasu 'yan siyasa masu ri e da manyan muqamai. Abba yana matsayin Sanata ne yayin da Abbu yake a matsayin ďan Majalisa, bayan sun qarasa dukannin wani shiri nasu sun tashi sun kama hanyar zuwa gurin taro. Bugun k'ofar da a kai ne yasa shi tashi ya nufi k'ofa tare da bud'e wa, ya kar'bi abincin da yake hanun mutumen da yake tsaye bakin k'ofa tare da furta masa na gode, ya amsa da to ya juya ya tafi shi kuma ya dawo ciki ya a jiye abincin a kan tebur sannan ya nufi gurin yaransa, ya tafi kusa da shi ya zauna sai wani kallonsa yake ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa sannan ya anbaci sunan sa.
*"Adeel* mu tafi muyi break past lokaci ya tafi sosai zamu iya makara zuwa gurin taron, kuma hakan sam bai dace ba to ya kamata muyi break past yanzu dan Allah." Magana yake masa cikin qauna da soyayya yayin da yake rungume jikin sa, sai wani sunbatarsa yake ya tashi tare da tashin sa sun nufi tebur domin suyi break past. Sunyi break past cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa sunci gaba da shirin tafiya gurin taro, kasancewar sa sananne matashin mai kud'i yasa shugaban makaranta ya aika masa da sakon gaiyata har garin Bauchi. Sun qarasa shirin su sunyi kyakkyawan shiri sun tashi sun fice zuwa gurin taro, wani babban holl ne wanda a ka k'awata shi da ado gurin yayi kyau sosai. Holl ďin ya tara manyan mutane ne sosai na daga ko ina kama daga 'yan siyasa, 'yan kasuwa, ma aikatan gwamnati, da sauran jama'ar gari na daga ko ina na sassan k'asa. Yara 'yan makaranta sai nishad'antar da gurin suke da wasanni iri daban-daban, hakan yayi matuqar saka yaran dake gurin nishad'i sosai bayan wani lokaci a ka fara cin abinci.
"Afra ta tashi ko ina zata oho ta kai kallonta ga *Adyan* tare da tashin sa tana cewa. *"Adyan* mu tafi ka raka ni." Ahlam ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a Afra kawai ki tafi." "Haba Aunty Ahlam dan Allah karki dakatar da ni daga tafiya da shi please." Kafin ta furta komai Umma tayi mata rigagi, "eh Ahlam ki barta su tafi dan Allah." "Shikenan Umma zasu iya tafiya Afra ki kula da shi sosai dan Allah kinji ko." Ta amsa ta da to Ahlam ta mai da kallonta ga *Adyan* tayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa sannan suka tafi. Ta bisu da kallo har suka fice tafiya suke yayin da idanuwan *Adyan* suke a kan yaran da suke wasan boll, sai jin yake yana san ya tafi ya kai kallonsa ga Afra kafin ya furta komai wayar ta ta d'auki ruri, ta d'aga tana wani lallausan murmushi *Adyan* ya zame hanun sa cikin mata ya nufi gurin wasan boll da sauri har yana gudu. Ya shiga cikin wasan ba tare da wani ya dakatar da shi ba hakan yayi matuqar yi masa dad'i sosai, bayan wani lokaci ta qarasa waya ta kai kallonta ga gunda *Adyan* yake, amma tayi rashin sa'a domin kuwa da jimawa *Adyan* ya bar gurin cike da firgici ta shiga anbatar sunan sa. Amma bata yi nasaran ganin sa ba cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ta juya ta nufi gurin su Ummi.
Sun jima sosai suna buga wasan boll wanda hakan ne yasa *Adyan* yayi matuqar gajiya sosai, lokaci d'aya jikin sa ya mutu sai wani irin abu yake ji a tare da shi wanda zamu iya kira da kasala. Ya koma daga gefe ya zauna sai wani lumshe ido yake tamkar mai jin barci, kallo d'aya tak zaka yi masa ka fahimci cewar ba qlau yake ba ko ba shi da lafiya, *Adnan* na daga gefe ya hangesa cikin hanzari ya isa garesa yana furta masa kalmar. "Baka da lafiya to amma mai ya saka kai ka shiga wasan? Kai kana da irin cutar da take tare da ni dalilin da yasa nima ban buga wasan ba kenan. Yanzu fad'a min ina maganin sabo da akwai buqatar ka sha magani yanzu to fad'a min ina maganin ka yake.?" Kallonsa kawai yake domin kuwa kalma ďaya bai fahimta ba ga abin da yake fad'a, kasancewar hausa yake shi kuma turanci kawai ya iya cikin wata 'yar murya yake furta masa kalmar. "Bana jin abin da kake fad'a." "Mine hakan yana nufin bai ya jin hausa? Shikenan idan shi bai ya jin hausa ni kuma ina jin turanci to ya kamata na taimake sa."
Nan kuwa ya canja harshe ya koma turanci, "am sunana *Adnan Adam* kai baka da lafiya jikin ka yayi zafi sosai fad'a min ina maganin ka yake? Ya kamata ka sha maganin ka yanzu sabo da zai taimaka maka ka damu lafiya sosai." *"Adnan* dan Allah ka taimaken please." Wannan kalmar ce kawai iya fad'ar masa daga nan kuma ya suma, *Adnan* ya shiga jijjigasa yana furta masa kalmar ya tashi amma sai shiru yake ji yana haka ya hangi wani yaro zai wuce, yayi saurin dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar. "Kai zonan zo da sauri." Ya isa inda yake sai wani kallonsa yake ya qara da furta masa kalmar. "Kai mai ya saka kace nazo nan? Sannan kuma ka kira ni da kai fad'a min mai ya saka ka kira ni.?" "Karka yi fishi brother kawai ina san zaka taimaki abokina shi ďin ya suma ne." "Sunana *Adeel Abas* to yanzu fad'a ta yanda a kai shi ya suma.?"
"Am ni kuma sunana *Adnan Adam* kayi hak'uri dana dame ka, ba shi da lafiya ne jikin sa yayi zafi sosai to sai kawai ya suma." *Adeel* ya dukursa sai wani kallon *Adyan* yake kallo sosai, daga bisani kuma ya mai da kallonsa ga *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* muyi wani abu kawai yanzu kawai ka sanar da iyayen sa cewar ba shi da lafiya domin a kai shi asibiti." "Eh gaskiyar kane ya kamata nayi hakan yanzu kai ka tsaya nan tare da shi, ka kula da shi sosai ba zan jima ba zan dawo gareku ka ji ko." "Eh zanyi ni zan kula da shi sosai nayi alkawari to zaka iya yarda da ni sai ka dawo." "Na gode sosai brother sai na dawo." Ya fad'a tare da shafar kansa yana wani gajeran murmushi shi ma ya mayar masa da murmushi, da kuma haka suka rabu *Adnan* ya tashi ya tafi *Adeel* ya bisa da kallo har ya fice, bayan tafiyar ya mai da kallonsa ga fuskar *Adyan* sai wani kallonsa yake yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare da shi sosai...................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/9, 2:50 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 16*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Saturday 08/01/2022*
*Time 09:17am*
*Typing................*
Fira suke cikin raha wasa da dariya sai ga Ahmad ya sauke kallonsa ga fuskar Ahlam tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam ina *Adyan* fatan ya ci abinci, amma me yasa baya nan.?" Cike da firgicin abin daya tambaye ta take magana, "am shi ya fad'a min cewar madara kawai zai sha idan mun koma gida, sannan kuma shi ďin ya fita tare da Afra ya raka ta wani guri amma." Yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu, "ya isa haka amma kin fita hayyacinki ko? To taya ma har zaki yi tunanin aikata hakan? Kin baiwa Afra shi sun fita ba tare da kinyi tunanin sanar da ni ba, kin kuwa san irin girman zunubin da kika aikata a yanzu? To ki sani wallahi tallahi ba zan taɓa gafarta maki ba idan har wani abu ya faru da yarona." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa ta shiga anbatar sunan sa, amma bai amsa ba ya kuma dakatar da ita daga bin bayan sa. Su Umma sun bisa da kallo cike da jin mamakin sosai lokaci d'aya Ahlam ta saki kuka.
"Kin gani ko Umma dalilin da yasa tin farko ban yarda Afra ta fita da shi ba, ga shi yanzu Yaya Ahmad yana matuqar yin fishi da ni kuma fishi sosai. Gaskiyar sa ne sam bai kamata na bari ta fita da shi ba na amince ne sabo kinyi magana, Umma ni ban san wane irin hukunci zanyi wa kai na ba idan har wani mummunan abu ya faru da yarona ba. Ni na damu sosai a kansa hakama ina jin wani irin yanayi a game da shi ina fatan zai yana lafiya." Su Ummi sun shiga rarrashin ta suna bata magana ta tashi ko ina zata tafi oho Umma ta shiga tambayar ta. "Ahlam ina kuma zaki tafi.?" Ta girgiza ka tare da furta, "ban sani ba Umma amma dai bai kamata a ce ina nan banyi komai ba, zan tafi domin naga ko zan gansu." Ahmad na k'oqarin fita sai ga Afra ta shigo cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau, yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali Ahmad ya riqo hanun ta tare da tambayar *Adyan.* "Afra ina *Adyan.?"* "Yaya Ahmad nima ban san yana ina ba sabo da." Bata qarasa zancan ta ba ya kifa mata wani wawan mari biyu masu kyau sosai, wanda sai data kife a qasa ta saki kuka ya tashe ta ya kuma shiga fad'a da ita fad'a yake mata sosai.
"Ke kin haukace ne da har zaki kalli cikin idanuwana sannan ki fad'a min cewar wai baki san inda *Adyan* yake ba? Taya ma har zaki yi tinanin fad'a min haka ki fad'a min ta yanda a kai yaron ya rabu dake.?" Cikin muryar kuka take magana yayin da tsoron Ahmad yayi yawan gaske a tare da ita sosai. "Yaya Ahmad yana tare da ni na ri e hanun sa sai a ka layi na, shi ne sai na koma gefe ina amsa waya bayan na qarasa ne naga bai ya nan tare da ni." Cike da k'unci da bak'in ciki ya qara kifa mata tafi, "Afra yanzu kina san ki fad'a min cewa sabo da amsa waya kika rasa *Adyan?* Shin ke ba zaki iya kulawa da shi ba kuma kika buqaci fita da shi fad'a min wani abu shin amsa wayar ki tafi yaron muhimmanci ne da baki tsaya kin kula da shi sosai ba? To bara kiji wallahi tallahi idan har wani abu ya faru da yarona to sai kin biya, sabo da ni ba zan ta'ba gafarta maki ba na har abada to karki ta'ba mantawa da wannan kinji ko." Lokaci d'aya kowa ya kai kallonsa ga Ahmad wanda yake ta faman fad'a da Afra, cikin hanzari Abba da Abbu sun isa gurin hakama su Ummi Abba ya shiga tambayar abin da yake faruwa Umma ta sanar da shi komai.
A zahirin gaskiya hankalin su Abbu yayi matuqar tashi sosai da jin labarin cewar *Adyan* ya 'bata. Abba ya sanar da security a kan su tafi nai man sa sun amsa da to sun fice, Ahmad ma fita yayi domin nai man yaronsa Abba ya sanar da shugaba abin da yake faruwa. Lokaci d'aya dukansu jama'ar dake gurin sun saki salati suna taslima, sun shiga jajanta musu Ahlam kuwa sai wani irin kuka take kuma kuka sosai tana fad'a da Afra. Cike da firgici Prof ya anbaci sunan *Adeel* tare da mi e wa tsaye ya fita daga holl ďin da sauri har yana gudu, yayin da bakinsa yake ta anbatar sunan *Adeel* hakama Mamie ta shiga anbatar sunan *Adnan* ta kai kallonta ga *Afnan* tana cewa. *"Afnan ina Adnan* mai ya saka bai ya tare dake.?" "Mamie shi yama fa riga ni fitowa bayan mun qarasa wasan, to gaskiya ni sam ban san yana ina ba amma zan iya tafiya yanzu domin na duba shi." Ta girgiza mata ka tare da furta, "A'a 'yata ki barshi ni zanyi wannan tare da Papa to kawai ki huta kinji ko." "Mamie nan fa school ďinmu ne to ni na san ko ina na school ďin shi yasa zan iya gane sa kawai ki yarda da ni sai na dawo." Ta tashi da sauri har tana gudu tayi tafiyarta Mamie ta shiga anbatar sunan ta amma bata amsa ba Ummu ta amsa da cewa. "Karki wani damu su biyun zasu dawo tare insha Allah to zaki iya yarda da ni." "Maman Anwar nima ina fatan hakan."
Ba jimawa a ka tashi taron a kaci gaba da nai man *Adyan* a nan cikin school dama wajen school, *Adnan* yayi nisa sosai cikin tafiya ya hangi Ahmad yana tafiya ya nufi gurin sa yana kiran sa da Uncle. "Uncle dan Allah ka taimaki abokina shi ďin ya suma ne." Da sauri Ahmad ya tsaya tare da kai kallonsa garesa cikin wata sarkakiyar murya yake magana. "Miye ya suma waye shi kuma taya a kai ya suma.?" "Ni ban san sunan sa ba shi yasa nake kiran sa da abokina, a game da yanayin sa kuma shi ďin ya buga wasan boll ya gaji sosai shi yasa ya suma. To dan Allah ko zaka iya taimaka masa zuwa asibiti please.?" Ya jinjina masa ka tare da furta, "eh sabo da ni ne Abban sa shi ďin ďana ne tin d'azu nake nai mansa to mu tafi ka kai garesa." Ya amsa da to sun nufi gurin su *Adyan* yake sun same sa kwance yayin da kansa yake a kan cinyar *Adeel.* da sauri Ahmad ya d'auke sa yana k'oqarin tafiya *Adnan* ya dakatar da shi yana furta masa kalmar, "dan tsaya kad'an Kawu dan Allah." Ahmad ya jinjina masa ka a lamar to shi kuwa ya bud'e jakar sa ya d'auko photon sa inda yake tare da *Alishart,* ya juya bayan photon ya rubuta number Mamie da Papa sannan ya ba shi photon yana furta masa kalmar.
"Uncle ka ba shi wannan idan ya farka kace da shi daga *Adnan* dan Allah." "Eh zanyi hakan insha Allah *Adnan* kai aboki na gari ne naji dad'in had'uwa da kai sosai." Ya shafi fuskar sa zuwa kansa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar Allah yama albarka, ya amsa da Amin yana dariya Ahmad ya mai da kallonsa ga *Adeel* tare da furta masa kalmar. "Kai ya sunan ka.?" "Ni sunana *Adeel* ne." "Na gode sosai *Adeel* Allah yama albarka." Ya fad'a tare da shafar kansa zuwa fuskarsa tare da sunbatarsa ya amsa da Amin yana dariya, Ahmad kuwa wani gajeran murmushi yake ya juya ya fice zuwa mota domin ya kai yaronsa asibiti bayan tafiyar sa sun kai kallonsu ga juna *Adnan* ya dafasa tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* na gode sosai da kai ka yarda ka taimaki abokina ina godiya sosai, gaskiya kai yaron kirki sosai na tabbata Maman ka tana yawan fad'a maka haka." "Karka wani gode min sabo da ni kawai nayi abin daya dace ne, sannan kuma karka yi magana a kan Mama na sabo da ta tafi, *Adnan* Mama na ta za'bi ta mutu ba tare data yi tinani a kai na ba. *Adnan* ni fa ban ta'ba sanin fuskar Mama na ba kawai ta tafi ta barni sai Dady na, shi kad'ai yake sona kuma shi kad'ai nake da