Showing 81001 words to 84000 words out of 142761 words

Chapter 28 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Sunday 30/01/2022*

*Time 04:33pm*

*Typing................*


Kwance suke rungume da juna wayar sa ta d'auki ruri ya kai hannun sa, ya d'auki wayar ganin mai kiran sa ne yasa shi d'aga wayar tare da fad'ar sunan ta. "Ammie mai yasa kika kira.?' *"Adyan* kana ina? Kowa sai neman ka yake duka ahalin suna san had'uwa da kai, to ya kamata ka zo yanzu kuma ka zo tare da *Alishart* kafin wasu daga cikin su tafi, sannan kuma Ameer yana ta tambaya na fad'a min kina ina.?" "Ammie na fita ne tare da *Alishart* zamu yi siyayyar kayan zuwa dina anjima, amma karki damu zamu zo yanzu kin ji." Ta amsa da to da kuma haka suka yi sallama, ya mai da kallonsa ga *Alishart* wacce take kwance jikin sa, yayi wani kyakkyawan murmushi mai tare da 'yar dariya ya shafi fuskar ta tare da sunbatarta, cikin wata lallausar murya mai dad'in sauraro yake fad'ar sunan ta. Ta d'ago fuskarta ta kallesa tana murmushi wani irin kallo suke yiwa juna mai tare da so. "Masoyiya Ammie tana jiran sabo da zata gabatar damu ga duka ahalin, to ya kamata mu shirya mu tafi yanzu." "Ta jinjina masa ka tare da furta to ya tashi tare da tashin ta sun nufi gurin wanka.

Ba jimawa suka fito sun shirya tsab cikin kyakkyawar shiga sannan suka tashi suka nufi gurin Ammie, sun isa gidan nan kuwa Ammie ta shiga gabatar dasu duka ga ahalin, kasancewar shekaru goma kenan da basu shigo Nigerian ba. Duka ahalin sunyi farin ciki sosai da had'uwa dasu biyun, haka suka ci gaba da shagalin biki har zuwa lokacin da Amarya ta tare a gidan Angon ta. Su Appa kuwa watan nin su uku suka koma England wanda kuma tare da, *Alishart* suka tafi kafin zuwan lokacin da zata fara zuwa makaranta, wani yammaci tsaye yake yana had'a coffee a kicin lokaci ďaya wayar sa ta d'auki ruri, ya kai hanun sa ya d'aga tare da karawa a kunne bayan sun gaisa sunci gaba da magana. "Prof barka da wannan lokacin fatan kana lafiya kwana biyu ina *Adeel.?"* "Lafiya qlau Prof Bashir yarona yana lafiya to kai fa ya naka ahalin suke.?"

"Suna lafiya Prof Abas lokaci ya tafi sosai amma har yanzu baka shirya yin wani aure ba, ya kamata a ce kayi aure ko ba komai zaka samu wacce zata kula da kai da kuma yaronka. Ko kuma dai kayi k'oqarin dawo da *Maman Adeel* ina ga kamar hakan zai fi, ko ba komai yaron zai yi farin ciki sosai sannan kuma zai kula da ita sosai, kaga a hakan zai samu albarkar ta to ya kamata kayi hakan dan Allah." "A'a Prof Bashir ni ba zanyi hakan ba ina nufin ba zanyi aure ba, sabo da ba zanso wata ta cutar min da yaro ba sannan kuma ba zan ta'ba kuskuran, sanar da shi *Adeel* komai a game da mahaifiyar sa ba, sabo da zan iya rasa shi gaba d'aya domin kuwa yana san Maman sa da yawa, duk da cewar bai yaru da ita ba hasalima ni na boye ta daga garesa, ta hanyar sanar da shi cewar ta mutu ta yanda ma ba zai yi tunanin ya rayu da ita ba."

"Prof Bashir ban san ya yarona zai ji ba yayin da shi ya san a salin gaskiyar cewa mahaifiyar sa na raye, duk da cewar hakan zai matuqar wahala shi ba zai ta'ba sanin gaskiyar ba. Sabo da ni ba zan ta'ba barin na rasa yarona ba wannan alkawari ne." "Shikenan fatan nasara ďan uwa." Haka suka ci gaba da magana na tsayin wani lokaci sannan daga bisani suka yi sallama. Abin da bai sani ba shi ne duk abin da yake fad'a a kan kunnan *Adeel* wanda da jimawa ya dawo, amma ko wani gajeran motsi bai yi ba wanda zai sa ya fahimci cewar yana kusa da shi. A zahirin gaskiya ya shiga firgici rud'ani da kuma tashin hankali sosai, da irin abin da yaji Dadyn sa na fad'a lokaci d'aya ya saki wani irin ihu tare da sakin kuka. Ihun sa ne ya fito da Prof daga kicin cikin hanzari ya isa garesa yana fad'ar sunan sa. *"Adeel* mai yake faruwa da kai ne haka mai ya saka kake irin wannan kukan haka.?" Cike da k'unci bak'in ciki 'bacin rai tare da tarin damuwa yake magana. "Dady wannan shi ne karo na k'arshe da ni zan tambiye ka, to kawai dai yanzu ka fad'a min a salin gaskiyar ina Mummy na take.?" Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana.

*"Adeel* wai mai kake fad'a ne haka? To har sau nawa kake san ni na fad'a maka cewar Mummyn ka ta mutu? *Adeel* Mummyn ka ta mutu to ya kamata ka yarda da gaskiyar, ta yanda zaka dena tambaya na ita ka ji ko." "A'a wannan sam ba gaskiya bane sabo har yanzu Mummy na tana raye, to kawai ka sanar da ni gaskiyar ina Mummy na.?" *"Adeel* ni fa sam na gagara fahimtar abin da kake fad'a amma qlau kake kuwa.?" "Dady shin ko zaka dena wannan wayancewar haka dan Allah? Sabo da na riga da naji komai daga gareka, kai da bakin ka ne kake fad'ar cewar Mummy na tana raye, amma kuma ka 'boye ta gareni sabo da kawai karka rasa ni. Dady mai yasa kayi haka tsawan rayuwata begen Mummy na nake tare da kukan rashin ta a tare da ni, ko yaushe kana fad'a min cewar kana qauna ta sosai to amma ta ya ka iya jure ganin yaronka, a cikin irin wannan mummunan yanayin duk da cewar kana da mafutar damuwar sa? Dady gaskiyar ta bai yana cewa kai kawai cutar da ni kake sabo da wani buri na ka. Shi yasa ni na kasance a haka kamar wani mara gata ban san komai ba na rayuwa, kai ba abin daka ko ya man ko da kuwa addini na, na gode Allah daka had'u da *Adnan* wanda shi ne ya fara ko ya min yanda zanyi rayuwa. Musamman yanda zanso Mummy na wanda kai kuma tsanarta ka sanya min a zuciya ta, Dady ka fad'a min mai yasa kai kayi hakan ta ya cikin sauk'i ka za'bi cutar da ni ta wannan hanyar.?"

"Dady naro e ka ka sanar da ni dalilin ďaya wanda yasa ka raba ni da Mummy na? Ba tare da ka ji tausayi na ba sannan kuma daga k'arshe ina san ka fad'a min inda Mummy na take dan Allah." Magana yake cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau yayin da, damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai sai kuma aikin kuka yake kuka sosai, tamkar wani k'aramin yaro cike da jin tausayin sa sosai yake magana. "Kayi hak'uri d'ana ni kawai bana san rabuwa da kai dalilin da yasa na b'oye maka gaskiyar kenan, *Adeel* a lokacin kana yaro sosai shekarun ka uku ne kawai san da muka rabu, na za'bi kasancewa da kai ne sabo da ita ďin ba zata iya kulawa da kai ba. Kayi hak'uri d'ana amma Mummyn ka ita tana cikin halin rashin lafiyar hauka, ina nufin ita ďin mahaukaciya ce har ma tayi k'oqarin cutar da kai. *Adeel* ni bani da wani za'bi ne sabo da ba zan iya ci gaba da zama da ita ba, sabo da ita ďin mahaukaciya ce sannan kuma." *Adeel* ya dakatar da shi cikin k'unci ta hanyar furta mata kalmar A'a yaci gaba da magana. "A'a ka dena kiran Mummy na da wannan mummunan sunan ita ba mahaukaciya ba ce, ita ďin ba kamar yanda kake tinani ba ce to yanzu ka fad'a min ina Mummy na take.?"

*"Adeel* ni na raine ka yanda zan iya na baka duka soyayya ta, sannan na so ka da duka zuciya ta dama rayuwa ta gaba d'aya. Amma ta wannan hanyar zaka saka min? *Adeel* koma dai miye ni na aikata maka to nayi shi ne sabo da ina qaunarka sosai, sannan kuma sam bana san na rasa ka domin kai ne kawai ahalin da nake da shi. *Adeel* duk da cewar kai ka san gaskiyar amma kuma ba zan ta'ba sanar da kai inda Mummyn ka take ba, sabo da ba zan ta'ba baka damar da zaka tafi ka barni ba. Kawai zaka ci gaba da zama a tare da ni na har abada, to garama ka dena wannan shirmen naka ka dawo haiyacinka, zanyi ma wata alfarma d'aya kawai kai zaka kasance tare da Mummyn ka a photo, wancan photon daka ta'ba tambaya wacece to Mummyn ka ce, kayi hak'uri da ban sanar da kai ba kawai dai ni bana san ka ji wani iri ne, amma yanzu tin da ka san gaskiyar zaka iya anfani da shi. Baka cikin kyakkyawan yanayi to ya kamata ka huta yanzu ka sha magani ka ji ko."

Yana k'oqarin ba shi magani ya ya juya yayi tafiyarsa yayin da yake kuka kuma kuka sosai, Prof ya bisa da kallo har ya shige yayin da tausayin sa yayi yawan gaske a tare da shi sosai. Wanda zuwa wannan lokacin idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai, *Adeel* yana shiga bedroom kai tsaye durowa ya nufa ya d'auko jakar da take d'auke da photo nan Mummyn sa. Ya nufi gado ya zauna tare da ciro photo nan sai wani kallon photon yake yana kuka sosai, yayin da bakin sa yake fad'ar sunan Mummy lokaci d'aya ya fara fita haiyacinsa, Prof ya shigo ya same sa cikin wannan yanayin cike da firgici ya isa inda yake yana fad'ar sunan sa. Amma bai amsa ba Prof ya shiga rarrashin sa a kan ya yarda ya sha magani, "eh zan sha kawai sabo da Mummy na domin ina san na k'arasa rayuwata ta gaba da ita, to ka bani maganin na sha." Nan kuwa ya shiga ba shi magani ya sha ba jimawa sosai yayi barci, Prof ya rufe shi da ido sai kallonsa yake yayin da tausayin sa ya cika zuciyarsa sosai.

Bayan kwana biyu har zuwa wannan lokacin *Adeel* bin Prof yake a kan ya sanar da shi inda Mummyn sa take, amma sam yak'i ya sanar da shi komai a game da inda take hakan yasa, *Adeel* yake fishi da shi kuma fishi sosai wanda ko magana ya dena yi masa. Hakama ya dena ci da kuma sha sai azumi yake wanda ba sahur kuma ba bud'a baki, hakan tasa yake ta fama da rashin lafiya ko yaushe Prof ya shiga damuwa sosai da irin yanayin sa. Ba shi da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ya amsa shi da cewa Mummyn sa na katsina a garin Kankiya, ai kuwa nan ya fara shirin tafiya gareta amma mirsisi Prof ya dakatar da shi ya qara da fad'a masa cewa. *"Adeel* sai dai ka za'ba a tsakanin mu biyun idan ka zab'e ni to zaka ci gaba da yin rayuwa kamar sarki, amma idan ka za'bi kasancewa da Mummyn ka to fa zaka rayu ne kamar wani bawa mara gata. *Adeel* zaka bar komai da kake da shi a nan sabo da duk abin daka mallaka nawa ne, to dole a nan zaka barsa wannan shi ne hukunci na to yanzu zaka iya za'ba a tsakanin mu biyun."

"Dady ka san me ni na kasa gane kai wane irin uba ne a gareni? Da fari ka raba ni da Mummy na sannan kuma ka raine ni cikin k'arya, yanzu kuma kana goranta min a kan duk wani abin da kayi min. A baya nayi tunanin cewa kai uba na gari ne a gareni, amma kuma a'a kai kawai uba ne mai tilassa wa yaron sa a kan ra'ayin sa, shikenan zan za'ba kamar dai yanda ka buqata daga gareni kayi hak'uri domin kuwa a halin yanzu, Mummy na tana buqata sannan kuma ni ina matuqar buqatar kasancewa a tare da ita sosai. To kawai ka sanar da ni adres na inda zan same ta.?" Cikin rawar murya har yana sarkewa yake magana. *"Adeel* hakan yana nufin cewar kai ka za'bi kasancewa da Mummyn ka fiye da ni Dadyn ka.?" "A'a Dady ni ba zan iya za'ba a tsakanin ku biyun ba, kawai dai ni nayi abin daya dace ne ba kamar kai ba daka za'bi kud'in ka fiye da yaronka. Naso a ce yanda ka bani soyayyar ka kayi k'oqarin kasancewa uba na gari a gareni, amma duk da haka ina yima godiya sosai yanzu ka fad'a min Kankiya a wace unguwar kuma a wane layi Mummy na take.?"

Kallonsa kawai yake ba tare daya furta masa komai ba, sai ma juya da yayi ya fice daga d'akin ganin yanda ya k'osa a kan tafiya gurin Mummyn sa, yasa Prof ya dena barin sa fita ko ina ko da kuwa Campany gurin aiki, yayin da shi kuma zai fita sai ya rufe sa ta yanda ba zai iya fita ba. Amma kuma hakan sam bai canja masa ra'ayi daga tafiyar ba wata safiyar litinin bayan Prof ya fita zuwa office, ya tashi yayi duk wani shiri nasa na tafiya ya d'auki duk wani abin buqata. Ya nufi bayan gida ya tashi gobara ya koma k'ofa yana ihu iya k'arfin sa, ganin yanda wuta ke tashi cikin gidan yasa Audu ya nufi k'ofar tare da bud'e wa kasancewar yana da mukulli. Kafin su ankara gidan ya cika da mutane sosai masu kawo d'auki Audu ya kira layin Prof ya sanar da shi, Prof ya fara kiran layin masu kashe gobara sannan ya nufi gida, a nata ruguntsumin kashe gobara a daidai wannan lokacin ne *Adeel,* ya samu damar sulalewa ya fita ya bar gidan ya nufi Kankiya.

Ba jimawa sosai sai ga Prof ya k'araso cike da firgici yake anbatar sunan yaronsa, sai k'oqarin shiga ciki yake an ki e sa tare da sanar da shi cewar yaronsa ya tsira. Suna haka sai ga motocin kashe gobara sun fara aikin su yayin da Prof yake ta nai man yaronsa, amma ina sam bai yi nasaran ganin sa ba sabo da ya riga daya tafi. A zahirin gaskiya hankalin sa yayi matuqar tashi sosai domin yana da tabbacin cewa ya tafi Kankiya, *"Adeel* mai yasa baka kashe ni ba a maimakon aikata min haka? Ta ya kake tunanin cewa zan iya fara sabuwar rayuwa babu ka? Bayan kuma kai ne a salin farin ciki na abin da nafi so ina qaunarka sosai d'ana, na so ka da duka zuciya iya yarda zan iya na baka duka soyayya ta gaba d'aya to amma mai yasa ka za'bi ka tafi ka barni.?"

Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawa a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma kwalla ce take bin fuskar sa mai tsananin zafi da k'una sosai. Bayan an kashe gobarar ya shiga ciki sai wani kallon gidan yake kallo sosai, bayan wani lokaci ya rufe gidan ya nufi wani gidan daban kasancewar yana da gidaje da dama, yayin da tunanin yanda zai dawo da yaronsa yayi yawan gaske a tare da shi sosai. *Adeel* kuwa yana fita kai tsaye tashar mota ya nufa ba b'ata lokaci ya shiga mota suka kama hanyar Kankiya...............






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/3, 11:09 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 34*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/



*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Monday 31/01/2022*

*Time 03:12pm*

*Typing.................*


Da yamma lis ya sauka garin Kankiya yayi tsaye bakin hanya yayin da yake magana da zuciyarsa. "Na iso garin Kankiya amma kuma ban san ta ina zan fara nai man Mummy na ba, ya Ubangiji ka nunan hanya cikin sauk'i ka had'a ni da Mummy na." Maganar da d'an a cab'a yake ne ya tsinke tunanin sa, "Malan tafiya ne.?" "Eh tafiya ne amma ina san zan tambiye ka wani abu.?" Ya jinjina masa ka a lamar to shi kuma yaci gaba da magana. "Am dan Allah ko ka san wani mutum mai suna Prof Abas Muh'd? Shi ďin yana da kud'i sosai hakama yana tare da manyan 'yan siyasar k'asar nan. Shi a salin d'an garin nan ne amma ya bar nan ba tsayin lokaci ka ga photon sa." Ya nuna masa photon sa ya girgiza ka sannan ya amsa shi, "A'a ban san shi ba amma zaka iya tambayar wani daban, to yanzu fad'a min ina zamu tafi.?" Yayi shiru kad'an sannan ya jinjina ka tare da furta masa, "kawai ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login