Showing 42001 words to 45000 words out of 142761 words
Chapter 15 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
shi yana masifar qauna ta sosai, shi yasa nake matuqar masifar qaunar sa sosai amma ita Mama na bata ta'ba sona ba. Bama ta bari ta rayu da ni ba shi yasa na tsane ta sosai kamar yanda ta min, Dady ya fad'a min cewar ita Mama na bata ta'ba sona ba ko da kuwa na rana d'aya ne dalilin da yasa na tsane ta kenan. Duk da cewar hakan yana saka ni k'unci *Adnan* hakan yana da zafi sosai, sannan kuma da matuqar k'una sosai amma karka damu da ni zan kasance lafiya."
Lokaci d'aya *Adnan* yaji tausayin yana shigarsa, duk da kasancewar yaro amma yana da kyakkyawan tinani sosai cike da jin tausayin yake magana. "Kayi hak'uri *Adeel* tabbas kana tare da k'unci sosai, sannan kuma ba laifin Maman ka bane data mutu a islamiya malamin mu ya fad'a mana cewar dole ne sai kowa ya mutu. Yayin da bawa ya mutu kuma to yana buqatar addu'a sosai daga gurin ahalinsa, kamar iyayen sa, Yayyen sa, Qannan sa, abokan sa, 'ya'yan sa dama duniya gaba d'aya. *Adeel* Maman ka tana sanka sosai kaddaran mutuwa ce kawai ta shiga tsakanin ku, to ya kamata kai ma ka sota sosai bawai kaci gaba da tsanan ta ba, *Adeel* a yanzu Maman ka tafi kowa buqatar ka to ya kamata ka biyata ta hanyar yi mata addu'a, malamin mu ya fad'a mana cewar yiwa iyaye biyayya tare da nuna musu soyayya wannan wajibi ne dole. *Adeel* na san kai ma ka san hakan amma mai yasa ka manta? *Adeel* kana da damar da zaka so Maman ka to kawai kayi hakan dan Allah, sannan kuma ka kasance mai yiwa Maman ka addu'ar samun rahma da gafara a gurin Allah, ta haka ne zaka kasance yaro na gari a gareta to ina fatan zaka yi anfani da duka shawara ta.?"
*"Adnan* ni duka ban san wannan ba sabo da bana zuwa islamiya, a baya kafin yanzu ina zuwa wata rana a kaman dukan makara shi ne na fad'a wa Dady na, ai kuwa yayi ta fad'a wanda har sai da yasa a ka rufe malamin a gidan kaso. To fa tin daga ranar na dena zuwa islamiya shi yasa ban san duka wannan ba, gaskiya naji dad'in had'uwa da kai sosai a k'alla na san yanda zanso Mama na na gode sosai." Cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adnan* yake magana. *"Adeel* gaskiya rayuwar ka tana da ban tausayi sosai, lallai ya kai kayi koma miye domin ka koma islamiya, domin ka san a salin waye kai addinin ka ne kawai zai fad'a maka haka." "Na gode *Adnan* gaskiya kai d'an uwa na gari ne, nayi alkawari zanyi anfani da duk abin daka fad'a min a yanzu insha Allah."
Lokaci d'aya kuma suka yi hugging juna sun d'an jima a haka sannan suka sake juna, *"Adnan* ni zan tafi kar Dady na yayi ta nai mana." "Shikenan zaka iya tafiya ina yima fatan alkhairi a ko yaushe." Da kuma haka suka yi sallama ya tafi shi tafiya yayi domin koma wa gurin ahalinsa, yana cikin tafiya bai ankara ba yaji an runguma sa ta baya, lokaci d'aya ya saki murmushi mai had'e da dariya yana anbatar sunan *Afnan.* Ta sake shi tare da fitowa ta gaban sa tana fad'ar sunan sa. *"Adnan* wai ina ka shiga ne.?" "Ba ko ina kawai ina zaga cikin school ne." "Shikenan mu tafi lokacin tafi gida yayi." Ya amsa ta da to sun fice sun samu su Mamie bakin mota sun shiga mota sun tafi, hakama *Adeel* ya samu Prof sun fice masauki wato hotel washe garin ranar suka kama hanyar Bauchi domin koma wa gida.............
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamin ne.*
[1/12, 8:22 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
*THREE BROTHER'S*
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
*Page 17*
β *β GΜΎOΜΎLΜΎDΜΎEΜΎNΜΎ PΜΎEΜΎNΜΎ WΜΎRΜΎIΜΎTΜΎEΜΎRΜΎSΜΎ AΜΎSΜΎSΜΎOΜΎCΜΎIΜΎAΜΎTΜΎIΜΎOΜΎNΜΎ* ββ
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*wΜΆΜΆΡ Ξ±rΜΆΜΆΡ Π²ΡΞ±rΜΆΜΆΡrΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟ gΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓtΜΆΜΆΡ Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓdΜΆΜΆΓΟuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ pΜΆΜΆΡrΜΆΜΆcΜΆΜΆΡΓvΜΆΜΆΡ nΜΆΜΆΟ pΜΆΜΆΞ±ΓnΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓcΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡΞ±tΜΆΜΆΓvΜΆΜΆΡ gΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ* β *,Π²ΡhΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟfΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟrΜΆΜΆ ΓtΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓlΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ ΡΟuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟ pΜΆΜΆΞ±ΓnΜΆΜΆ.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ΖUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ΖARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζara mana Ζarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Saturday 08/01/2022*
*Time 11:20pm*
*Typing.................*
Ya isa asibiti cikin hanzari nurse suka kar'bi yaron suka shiga da shi ciki domin a duba shi. "Am nima zan iya shiga ciki, ni ya kamata na duba sa, sabo da na san komai a game da rashin lafiyar sa, sannan kuma ni Δin likita ne to dan Allah kar ku dakatar da ni please." Da fari doctor bai yarda ba sai daga bisani sannan ya amince da buqatar sa. Sun shiga ciki nan kuwa Ahmad ya shiga duba sa tare da taimakon Dr Habib bayan sun qarasa duba sa, Dr Habib ya nufi office Δin sa hakama nurse Δin da suke tare da su su ma sun fice. Ahmad yayi zaune gefen sa sai wani kallonsa yake kallo sosai, ya shafi fuskarsa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar Allah ya baka lafiya Amin. A can gurin su Ummi kuwa sam basa cikin kwanciyar hankali sabo da rashin ganin *Adyan,* a zahirin gaskiya duk kansu suna tare da tashin hankali mai matuqar girman gaske sosai, ganin Ahmad ya jima bashi tare da su sannan bai nemi kowa ba yasa Abba ya fara shakkar ya anbaci sunan Abbu. "Al'ameen ni fa ina tunanin cewar Ahmad yana tare da *Adyan."* "Amma Yaya mai ya sa kake fad'ar haka.?"
"Al'ameen dukanmu a nan mun san yanda Ahmad yake matuqar masifar qaunar yaronsa sosai, kuma na tabbata Ahmad zai yi komai domin ya samu yaronsa ya dawo garesa, Ahmad ya jima sosai da fita amma har zuwa wannan lokacin bai nai mi ko Δaya daga cikin mu ba, wanda ya kamata a ce ya nai mi wani daga cikin mu domin yaji abin da yake faruwa. Dalilin da yasa na fahimci hakan kenan to ya kamata mu tafi gida domin had'uwa dasu." Sun amsa da to sun kama hanyar gida sun isa gida amma sunyi rashin sa'a domin kuwa basa nan, sun shiga tambayar security Ahmad ya dawo sun amsa su da a'a, hakan yayi matuqar d'aga hankalin su sosai musamman da layin sa bai ya tafiya. Sun qarasa ciki zaune kawai suke amma ba mai magana a cikin su, sun shiga nazari da tinanin ina Ahmad da *Adyan* suka shiga kuma mai ya saka layin Ahmad bai ya tafiya. Sun jima sosai a cikin wannan yanayin bugun k'ofar da a kai ne yasa dukansu suka kai kallonsu ga juna, da sauri Abbu ya tashi ya nufi k'ofa tare da bud'e wa ba tare daya tambaya ba, ya samu Jabir tsaye bakin k'ofa ya shiga tambayar sa mai ya amsa shi.
"Ranka shidad'e a game da mai gida Ahmad ne ina nufin *Abban Adyan."* Cikin rawar murya har yana sarkewa yake amsa shi, "Jabir shin kun samu wani labari ne a game da Ahmad to jikana fa ina *Adyan.?"* "Sir dukansu suna tare da juna suna asibiti ne." "Asibiti kuma mai kuma ya faru dasu.?" "Sir abin shi ne *Adyan* sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi shi yasa suke asibiti." "Subhanalillah Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un abin da nake yiwa gudu kenan, yanzu fad'a min wani abu suna wace asibiti.?" "Am suna Saudat Care hospital." "Shikenan zaka iya tafiya." Ya amsa da to ya juya yayi tafiyarsa Abbu kuma ya dawo ciki tare da sanar dasu Abba abin da yake faruwa, dukansu sun shiga anbatar kalmar Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un cikin hanzari sun tashi dukansu sun nufi asibiti. Zaune yake yayin daya saka *Adyan* a gaba sai kallonsa yake kallo sosai, yana haka yaji a na buga masa k'ofa ya tashi ya nufi k'ofa ya bud'e ba tare daya tambaya ba, ya samu su Abbu tsaye a gefen k'ofa kallonsu kawai yake ba tare da yayi magana ba. Cike da d'aukin had'uwa da yaronta ta nufi ciki da sauri Ahmad ya dakatar da ita ta hanyar rufe k'ofar zata yi magana yayi saurin dakatar da ita yana cewa.
"Baki da damar dake zaki had'uwa da d'ana to dan haka zaki iya tafiya." Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin sa sosai, "Yaya Ahmad wai mai kake fad'a ne haka taya ma kai zaka yi k'oqarin dakatar da ni daga ganin yarona? Hakan sam ba abu mai sauki bane a gareki dan haka ni ba zan iya amsa tayin ka ba. To kawai kayi hak'uri sannan kuma ba zan dakata daga ganin yarona ba wannan ce gaskiyar." "Da gaske wai ke kin damu a kan yaronmu? A'a ke sam baki wani damu a kan yaron ba, kamata yayi a ce yaron yana tare dake amma kuma sai kika za'bi da ki baiwa Afra shi sabo da wani dalili naki, da fari naso yaron ya kasance a tare da ni amma kika bani damar tabbacin cewar ke zaki kula da shi sosai. Na yarda dake sosai shi yasa ni na barki domin ki kula da shi sosai, amma kuma ke sam baki yi hakan ba kin barsa ya tafi tare da Afra duk da cewar kin san komai a game da yanayin sa. To sabo da sakacin ki shi Δin ya tafi ya buga wasan boll tare da sauran yara, dalilin da yasa yake cikin wannan yanayin kenan. Ahlam ke d'in nan ke ce wacce take da alhakin duka wannan sabo dake yanzu yaron bai ya cikin kyakkyawan yanayi, shi Δin yana kwance ba shi da lafiya kuma duka sabo da sakacin ki ne. To dan haka ni ba zan ta'ba baki damar da zaki ga yarona ba wannan shi ne hukuncin ki, kuma ni ba zan ta'ba canja wannan ba to yanzu zaki iya tafiya."
Dukansu wani irin kallo suke yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, "Yaya Ahmad wai mai kake fad'a ne haka taya ma kake tinanin wai ni zan aminta da abin daka fad'a? A'a ni sam ba zan ta'ba amince wa hakan ba lallai ya zama dole ni Δin nan na had'u da yarona. Yaya Ahmad shin kai a tinanin ka ina farin ciki ne da yanayin da yaronmu yake ciki? A'a k'unci nake sabo da na damu sosai a kansa ni Ammie sa ce kuma shi Δin Δana ne wanda nake matuqar so sosai, ko yaushe buri na shi ne yaronmu yayi farin ciki sosai sannan ya samu duk wani abin daya ke so, hakama ina ta k'oqarin ganin na kasance uwa ta gari a garesa dan haka ka dena hukunta ni haka, ni sam ba zan iya d'aukar wannan hukuncin ba to dan Allah karka dakatar da ni daga ganin yarona please." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da take kuka kuma kuka sosai, amma hakan sam bai saka shi amma sa ba sai ma juya wa da yayi domin tafiya Abba ya dakatar da shi.
"Ahmad karka cutar da ita har haka, sabo da ita sam ba zata iya d'aukan wannan ba to ya kamata ka daidai wannan dan Allah." "Abba ko zaku iya fita cikin wannan zancan dan Allah.?" "Amma Ahmad." "Abba dan Allah please." Abba zai qara magana Abbu ya dakatar da shi ta hanyar dafasa tare da girgiza masa ka a lamar a'a, sai kuma zuwa wannan lokacin ne Umma tayi magana. "Ahmad ka dena hukunta ta a kan zunubin da ni na aikata, Ahlam tayi ta k'oqarin dakatar da Afra daga fita da shi sai da nayi magana sannan ta barta suka tafi. Ahmad ita Δin bata aikata wani zunubi ba to dan haka babu dalilin da zai sanya ka hukunta ta, sannan kuma dukanmu a nan mun san cewa Ahlam tana matuqar qaunar *Adyan* sosai. Dukanku kuna qaunar juna sosai hakan abu ne mai kyau Ahmad to dan Allah ka bar komai ya wuce please." "Umma abin shi ne ita ta san komai a game da yaron wanda data sanar dake to da ke ma ba zaki aikata hakan ba. Umma koma dai mai zaku fad'a to ba zai canja gaskiyar ba Ahlam ita ce wadda take da alhakin duka wannan, dan haka ni ba zan bata damar da zata ga *Adyan* ba kuyi hak'uri dan Allah ku gafarce ni please."
Yana kai k'arshen maganar sa ya juya ya koma gurin yaronsa, su Ummi sun bisa da kallo cike da jin mamakin sa sosai yayin da kukan Ahlam yasa banta, su Umma sun shiga rarrashin ta Abba da Abbu sun shiga sun duba jikin sa hakama Ummi, yayin da Umma ta kasance tare da Ahlam ai kuwa kafin su ankara gurin ya fara ci kowa da mutane musamman 'yan siyasa mutanan su Abbu. Su Ummi sun kasance a nan har dare suna ta shirin tafiya gida amma Ahlam tak'i, sunyi iya yin su dan ganin ta tafi tare dasu amma tak'i dan dole suka tafi suka barta a nan, zaune take a kan kujeran dake gefen Δakin da *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin idanuwanta basu dena zubar da kwalla ba. Kukan yaron ne data ji yasa ta saurin tashi ta nufi d'akin amma ta samu k'ofar a rufe, ta shiga buga k'ofar tare da fad'ar sunan Ahmad. "Ahmad dan Allah ka bud'e k'ofar zuwa yanzu ya kamata na had'u da yarona ina buqatar hakan, Ahmad yaron kuka fa kuka yake to na tabbata yana buqata na sosai to dan Allah ka bud'e k'ofar please."
Haka ta shiga yi masa magiya tana rarrashin sa har ta samu ya iya bud'e mata k'ofa, cikin hanzari ta shiga ciki ta nufi gurin *Adyan* yayin da take fad'ar sunan sa, tana isa inda yake tayi hugging d'in sa tana sunbatarsa shi ma sunan ta yake fad'a Ammie. Ahmad yana daga gefe sai kallonsu yake ya juya ya fita ba jimawa ya dawo tare da doctor, nan kuwa ya shiga duba sa abin farin cikin shi ne yana samun sauki sosai ya sanar dasu cewar yana samun sauki sosai sannan ya juya ya fita. "Rabin raina fad'a min mai zaka ci yanzu na tafi na kawo ma.?" "Appa ni kawai zansha madara." "Shikenan yanzu zan tafi na kawo ka ji ko." Ya d'aga masa ka tare da furta ok, ya tashi domin tafiya Ahlam ta dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa tare da fad'ar sunan sa. "Yaya Ahmad shin ko zamu iya yin magana yanzu dan Allah.?" Kallonta kawai yake daga bisani kuma ya jinjina mata ka a lamar eh, ya koma ya zauna ta nisa tare da jan numfashi ta qara da sauke a jiyar zuciya sannan ta fara magana. "Yaya Ahmad dan Allah kayi hak'uri a kan komai, eh gaskiyar ka ne duka wannan laifi na ne k'ila ni ban kasance uwa ta gari a gurin *Adyan* amma."
Yayi saurin dakatar da ita ta hanyar rufe mata baki yana girgiza mata ka, "A'a Ahlam ba buqatar sai kin bada hakuri duk da cewar kin aika laifi, na san cewa kin damu a kan *Adyan* sosai sannan kuma ke uwa ta gari ce a garesa. Ahlam ni kawai na damu ne a kan yaronmu sabo da ba zan jure rasa shi ba, to dalilin da yasa ni aikata maki hakan kenan to ina fatan zaki fahimce ni sannan kuma ki yafemin dan Allah." "Yaya Ahmad kai kana da matuqar kirki sosai, ka kasance muji na gari a gareni kuma uba na gari a gurin yaronmu, Yaya Ahmad kai kayi abin daya dace to nice kai to abin da zanyi kenan, to sam ba buqatar ka bada hak'uri sabo da ba kayi komai ba to kawai ka manta ka ji ko." Ya jinjina mata ka lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin hugging d'in ta, ya qara da sunbatarta yana furta mata kalmar ina sanki ta amsa shi da ina qaunarka sosai, daga bisani kuma ya tashi ya fita domin kawo ma *Adyan* madara.
Zaune kawai yake amma bai ya tare da farin ciki, Mamie ta shafi fuskarsa tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* shin qlau kake kuwa.?" Ya girgiza ka tare da furta mata, "a'a Mamie ni kawai na damu ne a kan abokai na *Adyan da Adeel.* Sabo da dukansu basa cikin kyakkyawan yanayi *Adyan* ba shi da lafiya sosai, *Adeel* kuma yana tare da k'uncin rashin Maman sa data mutu, gaskiya suna matuqar bani tausayi sosai kuma ni nayi matuqar damuwa sosai a kan dukansu." Mamie ta girgiza ka tare da jinjina sa daga bisani kuma ta amsa shi, "masoyi kai yaron kirki ne ka damu sosai a kan kowa shi yasa nake qara qaunar ka, karka wani damu insha Allah dukansu zasu kasance lafiya to ka dena damuwa ka ji ko."
Ya d'aga mata ka a lamar to ta janyo sa jikin sa tare da sunbatarsa tana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona, ya amsa ta nima ina jin Mamie Appa yana daga gefe yana kallonsu yayin da yake wani lallausan murmushi abin birgewa sosai. Ya tashi daga inda yake tare da d'aukan *Alishart* ya nufi inda suke ya zauna