Showing 114001 words to 117000 words out of 142761 words
Chapter 39 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
ka duba Dady na please." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da yake kuka. Lokaci d'aya tausayin sa ya shigesu sosai sun samu shiru na jim kad'an, sannan daga bisani *Adyan* ya amsa shi. *"Adeel* ina mai baka hak'uri a kan abin da ya faru da Prof, sannan kuma ina mai k'ara baka hak'uri sabo da ni ba zan iya duba Prof ba, hakama ba zan iya baka wani kud'i ba idan har zaka taimaki Prof da shi. Amma zan iya yin komai sabo da kai Umma da kuma Mum, to kawai saidai ni na baka hak'uri fatan zaka fahimci mai nake nufi.?"
Ya jinjina masa ka a lamar eh ya mai da kallonsa ga fuskar *Adnan,* kafin ya furta komai yayi masa rigagi ta hanyar fad'ar sunan sa. "Kayi hak'uri *Adeel* sabo da ba zan iya canja abin da Aboki ya fad'a ba, amma dai ka da ka tab'a manta cewa dukanmu biyu muna nan domin ka, kuma zamu iya yin komai sabo da kai Umma da kuma Mum, ba zamu tab'a barin wani daga cikin ku ya cutu ba zamu kare ku iya rayuwarmu. Wannan alkawari ne kuma zamu tabbatar da cewar mun cika alkawarin mu insha Allah." Yayi shiru kad'an sannan yana nazari sannan daga bisani ya fara magana. "Na san cewar kun taimake ni da yawa sannan kuma kun kula dani sosai da ma ahalina. Kunyi matuqar damuna sosai a kai na Mummy na da kuma Kaka ta, hakan yana matuqar yi min dad'i sosai shi yasa na fara yi muku kallon ahalina. Amma kuma ni na rasa dalilin da yasa kun kayi matuqar tsanar Dady na sosai, na san cewa Dady na ya aikata laifuka da dama a rayuwarsa, musamman cutar da Mummy na da yayi to amma kuma ku bai wani cutar daku ba, amma kuma duk da haka kunyi matuqar masifar tsanarta sosai, amma kuma duk da haka ni ina alfahari daku sosai ni zan tafi sai munyi magana ina godiya sosai da kulawa."
Ya tashi jiki a san yaye ya tafi dukansu sun bisa kallo har ya fice, bayan tafiyar sa *Afnan* ta mai da kallonta garesu, sai wani kallonsu take kallo mai cike da jin mamakin su sosai, cike da jin mamakin abin da suka yi take magana. "Besty wai mai kun ka aikata ne haka? Ta ya ma zaku yi tunanin cutar da *Adeel* har haka? Shi kamar ahalinmu ne yana da kirki sosai sannan kuma yana mutunta ku sosai, dukanku biyun kuna da damar da zaku taimake sa to amma mai ya saka ba zaku taimake sa ba? Hakan sam bai dace ba ya kamata kuyi abin daya dace ina nufin ku taimake sa dan Allah." Kallonta kawai suke yayin da suka gagara furta mata komai, *Adeel* ya fito domin tafiya ya samu Papa tsaye gefen k'ofa, zai fad'i sunan sa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar girgiza masa ka. Ya janyo hanun sa sun nufi wani guri daban Papa ya anbaci sunan sa yana cewa. *"Adeel* na riga da naji komai a game da Dadyn ka, kayi hak'uri da abin dasu *Adnan* suka fad'a a game da Dadyn ka, ni zan kula da komai to yanzu zamu iya tafiya can asibitin ni zanyi duk abin daya kamata." "Na gode sosai Papa Allah ya saka da alkhairi Amin." Ya amsa da Amin yana murmushi sun juya sun nufi mota ko wannan su ya shiga motar sa sun tafi.
Sun isa asibitin Papa ya had'u da Dr Sauban sunyi magana a game da aikin, Papa ya biya duka kud'ad'en na komai da komai, *Adeel* ya saka hanu a kan takardar aikin bayan wani lokaci suka shiga da shi d'akin tiyata. Bayan an shiga da shi d'akin tiyata Papa ya sauke kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* dan Allah ko zaka iya sanar da ni wani abu a game da Dadyn ka.?" "Papa ni ban san wani abu a game da shi ba bayan shi karan kansa. Shi kad'ai yake ba shi da kowa sai ni mu biyu kawai muke da junanmu." Cike da jin mamakin abin daya fad'a Papa yake magana. *"Adeel* shin Dadyn ka bai sanar da kai komai a game da shi ba? To kawai ka sanar da ni cikakken sunan sa da garin sa.?" "Eh na san wannan sunan sa Prof Abas Muh'd Kankiya." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Mine Abas Muh'd Kankiya.?" *Adeel* ya jinjina masa ka a lamar eh Papa ya ci gaba da magana. *"Adeel* shin bai tab'a sanar da kai komai a game da ahalinsa ba? Sannan kuma bai sanar da kai komai a game da K'ank'ara ba.?"
"A'a sam bai sanar da ni komai ba a game da K'ank'ara ba. To amma mai ya saka kake tambaya wannan.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Am dama da naji ka fad'i cikakken sunan sa sai na ji kamar na san sunan tin da jimawa, amma shi wanda na sani a K'ank'ara yake sannan kuma yana da k'ani, na jima sosai ina nai man sa amma sam ban samu had'uwa da shi ba, to ina fatan Dadyn ka ya kasance mutumen da na jima ina nai ma." "Amin Papa ina yima fatan samun mutumen daka jima sosai kana nai ma, to amma mai ya saka kake nai man wannan mutumen.?" *"Adeel* ina nai mansa ne sabo da na had'a shi da k'anin sa. Wanda a kullum kuma a ko yaushe yake kukan rashin sa tare da fatan sake had'uwa da shi."
"Allah sarki gaskiya ya bani tausayi sosai ina fatan ya had'u da Yayansa cikin sauri." Papa ya jinjina masa ka yana wani gajeran murmushi shi ma abin da yake yi kenan. Bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka tare da shi a d'akin tiyata, sun fito cikin hanzari dukansu sun isa ga Dr Sauban, tare da tambayar jikin Prof yayi shiru kad'an sannan ya amsa su. "Mun kai shi d'akin hutu domin ya huta." "Doctor to ya yanayin samun saukin sa shin yana samun sauki sosai.?" "Ba zan iya sanar daku komai ba a game da wannan, sabo da har yanzu baya cikin kyakkyawan yanayi duk da cewar ya fita cikin hatsari, amma zai samu lafiya insha Allah to zaku iya duba shi yanzu." Ya mai da kallonsa ga wani nurse wanda yake tare da shi ya fad'a masa cewar ya kai su d'akin da Prof yake, ya amsa shi da to Dr Sauban kuwa ya juya ya nufi office ďin sa, su kuma sun nufi d'akin da Prof yake sun isa d'akin tare da shiga ciki, da sauri *Adeel* ya k'arasa inda yake sai wani kallonsa yake kallo sosai, lokaci ďaya kuma ya saki kuka kuma kuka yake sosai.
Cike da jin tausayin sa Papa ya k'arasa inda yake ya shiga rarrashin sa, sai wani lalla'basa yake yana ba shi magana yayin da tausayin sa yayi yawa a tare da shi sosai. Bayan wani lokaci ya sake sa ya nufi gurin Prof yake kallo sosai, ya sauke kallonsa ga gefen kafad'ar sa sai wani kallon gurin yake kallo sosai. Ya mai da kallonsa ga fuskar sa sai wani kallonsa yake kallo sosai, lokaci ďaya kuma ya samu kansa da zubar da kwalla cike da jin mamakin sa *Adeel* yake magana. "Papa mai ya saka kake zubar da kwalla shin qlau kake kuwa.?" "Ba komai d'ana kawai dai ina farin ciki ne shi yasa har nake zubar da kwalla." "Papa mai ya saka kake farin ciki sosai har haka.?" "ina farin ciki ne sabo da Dadyn ka shi ne mutumen dana jima ina nai ma." "Mine ta ya a kai ka gane shi cikin sauk'i haka.?" *"Adeel* hakan yana da matuqar sauk'i sosai a gareni idan har zan gansa, sabo da nayi matuqar sanin sa sosai duba nan kaga."
Ya kai kallonsa ga gefen kafad'ar Prof inda yayi masa nuni da shi, yayi tozali da wani k'aramin tabo ya mai da kallonsa ga Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin kai ka san wani abu a game da wannan tabon.?" "Eh ďana amma zamu magana a game da wannan wani lokaci." Ya jinjina masa ka a lamar to ganin ya jima sosai bai dawo ba yasa *Adnan* kiran layin sa ba jimawa ya d'aga. "Papa kana ina? Lokaci ya tafi sosai amma har yanzu baka dawo gida ba, shin qlau kake kuwa gaskiyar zaka sanar da ni dan Allah.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Rabin raina ina lafiya kawai na d'an biya ta wani guri ne, amma yanzu zan dawo gida insha Allah to ka kula da duka gidan ka ji ko." "Eh Papa zanyi amma dan Allah ka dawo gida yanzu sabo da munyi kewarka sosai, sannan kuma ka kula da kanka sosai dan Allah." "Eh zanyi masoyi Allah ya ma albarka ďana." Ya amsa da Amin da kuma haka suka yi sallama.
Bayan sun k'arasa waya Papa ya kai kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* ka kula da Dadyn ka sosai idan da akwai buqatar nazo to kawai ka kira layi na, ni kuma zanzo nayi alkawari insha Allah to zan tafi sai na dawo ka kula sosai ka ji ko." Ya amsa shi da to tare dayi masa godiya Papa murmushi kawai yayi masa ba tare daya furta masa komai ba. Sai ma tashi da yayi ya fita domin zuwa gida ba jimawa da tafiyar su *Alishart* Papa ya dawo gida, bayan sun gaisa sun tashi sun nufi tebur sunci abinci, bayan sun k'arasa sun koma parlour sunci gaba da fira, ba kuma tare da Papa ya sanar dasu komai a game da Prof ba. Sun d'an jima a parlour suna fira sannan daga bisani suka tafi suka kwanta, washe gari bayan sunyi break past dukansu sun tashi sun nufi office.
Tin daya fita gida take aikin kiran layin sa amma har safe layin sa baya tafiya, hakan yayi matuqar d'aga hankalin ta sosai wanda ko barci bara iya yi ba, tin da sassafe ta kira layin *Adnan* amma bai tafi ba sai daga bisani, sannan ta iya samun sa yana k'oqarin shiga office wayarsa ta d'auki ruri, ganin wacce take kiran sa yasa shi d'aga kiran bayan sun gaisa taci gaba da magana. *"Adnan* dan Allah ko kayi magana da *Adeel?* Tin yammacin jiya nake kiran layin sa amma baya tafiya, *Adnan* dan Allah ka sanar da ni gaskiyar inda yarona yake.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta. "Mum ina ga kamar ni na san gunda za a iya samun sa, to sam ba buqatar kici gaba da d'aga h ki sosai yanzu zanso na kai ki inda yake." Ta amsa shi da to sunyi sallama ya juya ya nufi office ďin Papa, abin da yafi ba shi mamaki shi ne rashin samun Papa a office, cike da jin mamakin rashin ganin sa ya ciro waya ya shiga kiran layin sa, cikin rashin sa'a layin yak'i tafiya haka ya hak'ura ya juya ya nufi gidan Mum.......................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/9, 3:48 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 47*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Sunday 06/03/2022*
*Time 03:19pm*
*Typing................*
Ya isa gidan Mum tare da shiga ciki ya same ta a cikin wani irin yanayi, sai kai kawo take yayin da tunanin inda zata ga yaronta yayi yawan gaske a tare da ita. Umma sai rarrashin ta take tana bata magana cikin hanzari, *Adnan* ya isa inda take yana fad'ar sunan ta ya janyo hanun ta ya zaunar da ita sannan ya fara magana. "Mum mai yake faruwa dake ne haka shin qlau kike kuwa dan Allah ki sanar da ni.?" *"Adnan* ni kawai na damu ne a kan *Adeel* tin yammacin jiya daya fita, har yanzu ban k'ara jin komai ba daga garesa ba, kuma layin sa baya tafiya sannan kuma shi bai kira ba, *Adnan* ni ina tsoron kar wani abu ya faru da shi sabo da ba zan iya jure ba domin." Da sauri *Adnan* ya dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a Mum sam ba abin da zai faru dake shi ma zai kasance cikin k'oshin lafiya sosai, to zaki iya yarda da ni amma kinyi kalaci kuwa.?" Ta girgiza masa ka tare da furta a'a yaci gaba da magana. "Mum lokaci ya tafi sosai zuwa yanzu ya kamata a ce kinci wani abu, yanzu ni zan had'a maki break past bayan kin kammala sai mu tafi gurin *Adeel.* Idan kuma kika ce a'a to da zanyi fishi kuma fishi sosai."
"Shikenan zanci na gode sosai da kulawa Allah ya ma albarka." Ya amsa da Amin yana murmushi ya kuma ci gaba yana cewa. "Mum zanyi farin ciki sosai idan kika saka wa Abokina albarka shi ma ina nufin *Adyan."* Tayi murmushi sosai tare da shafar fuskarsa. "Shikenan ďana zanyi hakan Allah yayi muku albarka dukanku." Ya amsa da Amin yana murmushi sannan ya tashi ya nufi kicin, bayan daya gaisa da Umma yana cikin aiki sai ga Mum ta isa inda yake, tare da fad'ar sunan sa ya amsa yana murmushi yaci gaba da magana. "Mum mai yasa kika zo nan.?" "Nazo ne domin na ta ya ka aiki ta yanda zamu kammala cikin sauri." "Shikenan ina farin ciki sosai da zanyi aiki tare dake." Murmushi kawai tayi masa mai tare da dariya shi ma abin da yake yi kenan. Ba jimawa suka kammala sun shirya komai a kan tebur sannan daga bisani suka fara break past, bayan sun k'arasa ya d'auki Mum sun fita zuwa asibiti domin had'uwa da *Adeel.* Zaune suke yayin da suka saka Prof gaba da ido turo k'ofar da a kai ne, yasa su kai kallonsu ga k'ofa dan ganin mai shigowa sunyi ido biyu da fuskar Dr Sauban.
Ya k'arasa ciki bayan ya duba jikin Prof sannan ya basu takardar magani, Papa ya karb'i takardar maganin ya fita domin ya kawo maganin. *Adeel* ya shiga yi masa godiya murmushi kawai yayi masa sannan ya juya ya tafi, ba jimawa da tafiyar Papa ya ji a na buga masa k'ofa ya tashi ya nufi k'ofa, ya bud'e k'ofar kamar a mafarki ya samu Mum da *Adnan* tsaye a bakin k'ofa. Cike da d'aukin ganin sa yayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa, bayan sun sake juna ya mai da kallonsa ga fuskar, *Adnan* wanda shi ma kallonsa yake sun samu shiru na jim kad'an sannan *Adeel* ya fara magana. "Mai kuma kake yi a nan mai yasa kazo nan.?" *"Adeel* ni nazo nan ne sabo da Mum, ita d'in ta damu ne sosai a kanka ba kamar kai ba, tin yammacin jiya ka tafi amma kuma baka kira ka sanar da ita wani abu a game da kai ba. Hakan yasa ta damu sosai har ma ta gagara cin abinci, *Adeel* wannan babban kuskure ne ka aikata sannan kuma."
"Ya isa haka *Adnan* karka ce zaka koya min yanda zan kula da mahaifiya ta, ita d'in Mummy na ce kuma na san ta yanda zan kula da ita sosai, na san cewar kai ka taimake ni sosai dama duka ahalina musamman Mummy na. Amma kuma na rasa dalilin da yasa kai kayi matuqar tsanar Dady na sosai, na san cewar Dady na ya aikata kuskure sosai a rayuwar sa, musamman ma ta yanda ya cutar da Mummy na, amma kuma ku biyun bai cutar daku ba hasalima bai tab'a sanin ku ba, amma kuma kuna cutar da shi sabo da kune yake cikin kyakkyawan mummunan yanayin. Da a ce kai ka yarda da ka amshi shari'ar sa to da duka wannan bai faru ba, amma sai kak'i dalilin haka yasa yayi hatsari sannan kuma *Dr Adyan* ya gagara duba shi. A baya har na fara tinanin cewar ni daku 'yan uwan juna ne har ina kiran mu da ahali ďaya, amma kuma da hakan ta faru sai na fahimci a salin gaskiyar waye ni a gareku, amma kuma duk da haka ina mai alfahari daku sosai, tare da nuna godiya ta a gareku ina godiya sosai hakama ka isar da sakon godiya ta ga *Dr Adyan."*
Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, kafin *Adnan* ya furta komai Mum tayi masa rigagi. *"Adeel Adnan* shin ku ukun kuna fad'a ne.?" "A'a Mum sam ba kamar yanda kike tinani bane, sam bama fad'a da juna *Adeel* ne kawai bai fahimce mu ba, amma wani lokaci zai fahimci komai to ni bara na tafi sai an jima." Ta jinjina masa ka tana murmushi *Adeel* kuwa sai kallonsa yake, ya juya