Showing 93001 words to 96000 words out of 142761 words
Chapter 32 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
zaki ci gaba da kira na da hakan.?" Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, cike da jin mamakin sa sosai take magana. "Masoyi kenan hakan yana nufin cewar kai ne wannan d'an wasan da yake wasan tsere.?" Ya jinjina mata ka tare da furta eh taci gaba da magana. "Masoyi amma su Appa sun san da hakan kuwa.?" Ya girgiza mata ka tare da furta a'a ta nisa tare da jan numfashi sannan taci gaba da magana.
"Masoyi hakan bai dace ba sabo da zai iya cutar da kai sosai da kuma lafiyar ka, na tabbata wannan ne dalilin da yasa ka b'oye wasu Ammie gaskiyar. Masoyi k'ila dai yanzu lokaci yayi wanda zaka sanar dasu duka gaskiyar, sannan sai ka dena wasan gaba d'aya idan kaso kuma zaka iya sanar da masoyan ka, waye a salin *Adlishart* na tabbata zasu yi matuqar farin ciki sosai da hakan, musamman idan suka san cewa *Dr Adyan* shi ne jarumin su kuma masoyin su, to farin cikin su zai k'aru sosai to kawai kayi hakan dan Allah." Wani irin kallo yake yi mata mai tare da so cike da qaunar ta yayi hugging d'in ta, sai sunbatarta yake yana furta mata lafuzza masu tsananin dad'i sosai, yayin da yake jin tana dad'a shiga ransa cikin kyakkyawan yanayi yake magana.
*"Adlishart* ke kina da kirki sosai na gode da tunasarwa kuma zanyi duk abin da kika fad'a, sannan kuma daga k'arshe zan had'a ki da secret super star nayi alkawari insha Allah." Murmushin ta ya k'aru sosai tare da k'ara shigewa jikin sa, shi kuwa yayi mata wata kyakkyawar runguma sosai yana sunbatarta. Hakan kuwa ta kasance ya sanar dasu Appa gaskiyar cewa shi ne *Adlishart,* sannan kuma ya nai mi afuwar su tare dayi musu alkawarin ya dena. Sun amsa shi da ba komai tare da sanya masa albarka, yayi farin ciki sosai da ganin basu yi fishi da shi ba, bayan mako d'aya wani dare kwance suke rungume da juna ya anbaci sunan ta.
*"Adlishart* gobe ne secret super star yake taron bai yana kansa ga d'inbin masoyin sa, to ina ga dukanmu zamu kasance a gurin har dasu Ammie, sabo da dukanmu masoyan sa ne kuma masu yi masa fatan alkhairi. To ya kamata dukanmu muyi shiri na musamman domin had'uwa da shi." "Gaskiya ina farin ciki sosai domin burina na had'uwa da super star ya cika, na jima ina mafarkin had'uwa da shi na gode sosai *Adlishart."* Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarta sosai, shi kuwa sai wani kallo yake yi mata mai kama da harara ta shiga tambayar. "Masoyi mai ya saka kake harara na shin ni na aikata wani zunubi ne.?"
*"Adlishart* ni ďin nan sai na ciro harshen ki na cinye, ta yanda zan dakatar dake daga zancan wasu maza, kamar irin secret super star sabo da ina kishi sosai, *Adlishart* gaskiyar ita ce ina sanki sosai ina matuqar masifar qaunarki sosai. Shi yasa nake matuqar kishin ki so zo nan." Ta k'ara matsawa kusa da shi tana dariya shi kuwa murmushi yake ya k'ara saka ta jikin sa, yana sunbatarta ita kuwa sai dariya take sosai cike da nishad'i, sun samu farin ciki na wani lokaci sannan daga bisani suka yi barci....................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/7, 12:45 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 38*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Saturday 05/02/2022*
*Time 08:02pm*
*Typing................*
Yau garin London cike yake da mutane masu tarin yawa, wad'anda suke daga ko ina na duniya domin ganin fuskar, wannan b'oyayyen mutumen wanda ya tara tarin masoya masu yawan gaske, wato Secret Super Star mutumin da kowa yake fatan ganin fuskar sa. Bayan ta k'arasa shirin ta tsab ta mai da kallonta ga *Adyan* wanda yake ta sharan barci, ta tashi ta nufi gado ta zauna daga gefe tare da fad'ar sunan sa, amma sam bai yi yunk'urin tashi ba ta shiga buga pillow da yake kwance, idanuwansa na rufe yake magana. *"Adlishart* shin kina buqatar wani abu daga gareni? Shikenan zaki samu duk abin da kike so zo nan." Ya shiga laluba ta jin bai jiyo ta bane yasa shi bud'e idanuwansa, ya hangeta zaune gefen gado ya matsa kusa da ita tare da janyo ta, yayi hugging d'in ta tare da sunbatarta yana k'oqarin janye towel d'in da yake jikin ta, tayi saurin dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa tare da girgiza masa ka. "A'a ka tashi ka shiga wanka lokaci ya tafi sosai zamu iya makara to ya kamata ka shirya yanzu."
"Ke d'an dakata mai yasa yau baki jira ni ba kika yi wanka ba tare da ni ba? Gaskiya dole zaki canja wannan wankan sabo da ina da kwad'ayin nayi wanka dake, ko kuma dai mu fasa tafiyar gaba d'aya naga iya wannan rawar k'afar naki." Lokaci d'aya ta wani b'ata fuska tana wani turo baki, shi kuwa sai wani kallonta yake yana murmushi mai tare da dariya, ta k'ara b'ata fuska kamar zata saki kuka ya kamata fuskar ta yana cewa. "Karki yarda ki min kuka sabo da kin san mai zai faru kawai zan janye wannan towel d'in, sannan kuma ka kin fini sanin abin da zai faru damu, to yanzu zaki iya fara kukan ni kuma zan rarrashe ki yanda ya kamata nayi alkawari." Lokaci ďaya ta gyara fuskarta har da wani lallausan murmushi sannan ta amsa shi. "Masoyi nifa ba kuka zanyi ba to yanzu zamu iya tafiya, domin na saban ta wanka na zamu yi wanka a tare kamar dai kullum." "Masoyiya wannan duk sabo da buqatar had'uwa da secret super star ne.?" "A'a sabo da kayi farin ciki ne ka yarda da ni sabo da gaskiyar nake fad'a." "Shikenan zamu iya tafiya yanzu."
Ya tashi tare da tashin ta sun nufi band'aki ba jimawa suka fito suka fara shirin tafiya. Sun shirya cikin wata kyakkyawar shiga sunyi matuqar yin kyau sosai, sun fito babban parlour wanda fitowar su tayi daidai data su Appa, sun tari juna da murmushi sun isa ga juna sun fara runguma juna sannan suka zauna. sun gaisa gaba d'aya sannan suka nufi tebur suka yi break past, bayan sun gaisa sun tashi sun nufi babban studio domin had'uwa da secret super star. Sun isa gurin wanda gurin a cike yake da jama'a sosai zaune suke wayar sa ta d'auki ruri, ya tashi ya fita domin amsa waya bayan wani tsayin lokacin da suka d'auka suna jiran isowar sa, ya k'araso tafiya yake sannu a hankali kamar wani sarki, doguwar rigar da take jikin sa ita ta hana kowa ganin fuskar sa kasancewar tana ta hula.
Ya isa kyakkyawan gurin da a ka tanadar masa ya zauna, yayin da idanuwan kowa suke kansa nan kuwa 'yan jarida suka fara aikin su, ko wannan su sai jefa masa tambaya yake ya dakatar dasu yana cewa. "Kuyi tambayar ku cikin natsuwa ďaya bayan d'aya ni zan amsa ku kun ji ko." Sun amsa shi da to nan kuwa suka fara, "ranka shidad'e shin ko zaka iya sanar damu dalilin da yasa kake kiran kanka da secret super star.?" "Abin shi ne kawai bana san kowa ya san waye ni." "Amma mai yasa baka san a san waye kai bayan kuma kana da tarin masoya sosai? Ko dai kana jin tsoron wani daban ko akwai wanda kake ganin zai iya cutar da kai.?" "A'a bana tsoro sannan kuma ba wanda zai iya cutar da ni, kawai dai wannan ra'ayina kenan bana san kowa ya san waye ni." "Sir wasu na fad'ar cewa wai kai ba kyakkyawa bane shi yasa kake b'oye fuskar ka ga kowa shin hakan gaskiya ne.?" Lokaci d'aya ya saki dariya kuma dariya yake sosai sai daga bisani ya amsa ta.
"Ni ba zan amsa wannan ba nafi da san ku tabbatar wa idanuwan ku gaskiyar." "To ka fad'a mana cewar baka san kowa ya san waye kai, to amma mai ya canja ra'ayin ka yanzu har ka buqaci bai yana kanka ga masoyan ka.?" "Matata ita ce wacce ta canja min ra'ayi, a kullum kuma a ko yaushe zancan ta ďaya na ganin secret super star, tana matuqar sansa sosai ko yaushe cikin sauraran wakokin sa take. Ta damu sosai na rashin sanin waye shi wani lokaci har tana fishi da ni wai na kasa had'a ta da shi, to na damu sosai da yanayin ta wanda wannan dalilin ne yasa na shirya bai yana fuska ta ga masoyana." "Sir kenan hakan yana nufin cewar ko matar ka bata san cewar kai ne secret super star ba.?" "Eh bama iya ita kawai ba A'a har da iyaye na." "Gaskiya Madam tayi matuqar sa'ar samun ka ina ta ya ta murna." "A zahirin gaskiya ni ne wanda yayi matuqar sa'a sosai dana same ta, domin da bata amince da aure na ba to tabbas da ban rayu ba. Sabo da ni na rayu ne da soyayyar ta shi yasa zan iya kiran ta da rayuwata."
"Sir kana san Madam sosai haka ne.?" "Eh fiye ma da yanda kike tunani." "To ko zaka iya bai yana mana ita domin muyi magana da ita? Sannan kuma muga wace macace wacce da matuqar sa'a sosai har haka shin zaka bai yana mana ita.?" Yayi 'yar dariya tare da furta a'a, "mai yasa ba zaka bai yana ta a garemu ba.?" "Sabo da ita ďin sirrina ce ba kuma wanda zan bawa damar had'uwa da ita, musamman mazajen da suke a nan sabo da ina da matuqar zafin kishi sosai." "To kace ita ma ta zama secret." Ya fad'a yana dariya shi ma abin da yake yi kenan tare da jinjina masa ka a lamar eh. "Sir to ina ga lokaci yayi wanda zaka bai yana fuskar ka ga duk wani masoyi naka daya zo nan domin had'uwa da kai." Ya amsa da to tare da mi e wa tsaye ya cire rigar da take jikin sa wadda ta hana a ga fuskar sa, amma still fuskar sa tana sanye da fice max irin shigar dake jikin sa, lokaci d'aya gurin ya rika amsa sunan *Adlishart* ya jinjina ka a lamar eh, cikin rawar murya 'yan jarida sunci gaba da jefa masa tambaya bayan daya zauna.
"Sir lokuta da dama munyi ma tambaya ko *Adlishart* da secret super star mutun d'aya ne, amma ka sanar damu cewar ko wannan su daban ne, amma kuma yanzu ka fito a matsayin *Adlishart* mai yasa.?" "Eh kamar dai yanda na fad'a a baya kawai bana san a san a salin waye ni." "Sir gaskiya kana da wayo da yawa to yanzu mun shirya wa ganin a salin fuskar ka, shin to ko zaka iya yaye wannan mayafin fuskar domin cika alkawarin ka ga masoyan ka.?" "Eh na riga dana shirya wa hakan." Nan kuwa ya cire mayafin fuskar sa yayin da idanuwan kowa suke kansa, cike da mamakin ganin sa suke anbatar sunan sa. *"Dr Adyan* kai ne.?" "Eh wannan mutumen secret super star da kuma *Adlishart* ba kowa bane face *Dr Adyan Ahmad.* Na san cewa da yawan ku a nan zaku ji mamaki sosai musamman Appa Ammie da kuma *Adlishart,* kasancewar ban tab'a nuna kai na ga kowa ba sai yau na gode sosai masoyana, secret super star da kuma *Adlishart* dukansu biyun suna tare daku nima ina matuqar masifar qaunar ku sosai. Ni naku ne kuma ina alfahari da hakan sosai na gode Allah ya bar qauna Amin." Nan kuwa masoya suka shiga yi masa fatan alkhairi wani d'an jarida ya shiga tambayar sa.
"Sir mai yasa kake kiran kanka da sunan *Adlishart.?"* Murmushin sa ya k'aru sosai ya nisa tare da jan numfashi sannan ya amsa shi. "Wannan sunan yana da matuqar muhimmanci sosai a gareni, sabo da sunana ne dana matata na had'a guri d'aya *Adyan da Alishart* sai ya ba da *Adlishart."* "Sir muna maka fatan alkhairi tare da duka masoyan ka." "Na gode sosai." Da haka kuma tattaunawar su tazo k'arshe wasu daga cikin masoyan sa sun shiga ba shi kyauta, sai photo na suke tare dayi masa fatan alkhairi shi kuwa sai godiya yake musu. Su Appa suna daga gefe suna kallonsa yayin da farin ciki yake ta shigarsu sosai, *Alishart* kuwa sai wata soyayyar sa take ji tana qara shigarta sosai, sun jima sosai a nan gurin sannan daga bisani suka nufi gida. Bayan sun dawo ya anbaci sunan *Alishart* yana cewa. *"Adlishart* fad'a min wani abu yanzu kina farin ciki da kika had'u da secret super star.?" "Masoyi ni ba zan iya sanar da kai irin girman farin cikin da nake cikin sa ba, sai dai kawai nace da kai ina farin ciki gaskiya nayi sa'ar samun ka, a matsayin mujina kuma abokin rayuwata ina qaunarka sosai masoyi."
Magana take cikin kyakkyawan yanayi lokaci d'aya ya samu kansa da yin hugging d'in ta tare da sunbatarta, su Ammie sai kallonsu suke suna murmushi bayan wani lokaci ta tashi domin shiga ciki, tana cikin tafiya lokaci d'aya ta ji kanta ya sara da k'arfi, da sauri ta dafe kai tare da furta wash lokaci d'aya dukansu suka furta mata kalmar qlau kike. Ta jinjina musu ka tana furta eh ina lafiya taci gaba da tafiya nan kuwa ta fara ganin jiri, bata ankara ba ta kife a k'asa ta suma da sauri dukansu suka isa gareta suna fad'ar sunan ta, amma bata amsa ba Appa yace su tafi asibiti da sauri *Adyan* ya amsa shi da a'a. Cike da jin mamakin abin daya fad'a Ammie take magana. *"Adyan* mai ya saka baka san mu tafi asibiti duk da cewar bata da lafiya.?" Yayi shiru na wani lokaci sannan ya amsa da ba komai, *"Adyan* shin kai kana b'oye mana wani abu ne.?" Shiru bai yi magana ba.
*"Adyan* ka amsa ni shin da akwai abin da kake b'oye wa wanda baka san mu sani gaskiyar zaka fad'a.?" Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan fad'e sa ba. "Kuyi hak'uri dan Allah ku yafemin sannan kuma karku yi fishi da ni please ku yafemin." *"Adyan* wai mai yake faruwa da ita ne kawai ka sanar damu? Sannan kuma mai ya saka kake bamu hak'uri kawai ka sanar damu abin da yake faruwa dan Allah.?" "Appa ita d'in tana tare da juna biyu ne." "Mine *Adyan* shin wai ka ji abin daka fad'a kuwa? Ta ya hakan zata kasance sam bai kamata a ce kai ka kusanceta ba, balantana har ta iya samun juna biyu *Adyan* har yanzu ita yarinya ce, shekarun ta sha biyar ne kawai to sam bai kamata hakan ta faru da ita ba. Idan ta samu lafiya to fa dole zamu bar nan zamu koma gida a can ne zata aihu, ta hakan ne kawai zan iya kare ka a matsayi na na uba, sannan kuma ina fatan kar wani mummunan abu ya faru da ita."
"Na gode Appa na gode Ammie na gode ma dukanku." *"Adyan* kai d'an mu ne to zamu iya yin komai domin mu kare ka to ba buqatar ka gode mana ka ji ko." Kallonsu kawai yake ba tare daya furta musu komai ba, lokaci d'aya dukansu suka yi hugging d'in sa tare da sunbatarsa ba jimawa suka sake sa, sun mai da kallonsu ga *Alishart* Appa ya d'auke ta sun shiga ciki domin ya duba ta, kasancewar suna da kayan aiki a gida ya duba ta tare dayi mata Scan domin ganin lafiyar Babyn. Abin farin cikin shi ne Babyn yana cikin k'oshin lafiya sosai, bayan wani lokaci ta farka daga suman da tayi haka dai su Ammie suka ci gaba da kulawa da ita sosai, kuma Alhamdulallah tana samun sauki sosai wani dare.
*Adnan* ya kira layin sa ya d'aga bayan sun gaisa yaci gaba da magana. "Aboki da akwai abin daya kamata muyi magana a kai." "Aboki kawai ka fad'i koma miye ina sauraran ka." Ya amsa shi da to nan kuwa ya shiga sanar da shi komai a game da Mummyn *Adeel.* "Aboki mai yasa sai yanzu kake sanar da ni? Shikenan zan kula da wannan yanzu zanyi magana da Kaka na Abuja zan koma kiran ka." Ya amsa shi da to sunyi sallama bayan wani lokaci ya koma kiran layin *Adnan,* ba jimawa ya d'aga nan kuwa ya shiga sanar da shi cewar yayi magana da Abba. "Aboki nayi magana da Abba za a shirya wa dukanku visa zaku shigo nan da kwanaki biyar insha Allah. To ya kamata ku fara shirin tafiya amma kana farin ciki kuwa.?" "Aboki kana da kirki sosai Allah ya saka da alkhairi Amin zan sanar da *Adeel*