Showing 123001 words to 126000 words out of 142761 words

Chapter 42 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

yake suka nufa.
Sun shiga ciki sun samu *Adeel* yana ba shi abinci a baki, cike da d'aukin ganin su yake fad'ar sunayen su, ya tashi ya nufi inda suke cike da qauna yayi hugging d'in Mum. ita kuwa sai wani sunbatarsa take su *Adyan* kuwa sai kallonta suke, bayan sun sake juna ya gaisa da dukansu bayan sun gaisa, Mum taci gaba da magana da shi.

*"Adeel* lokaci ya tafi sosai to ya kamata kaci abinci, ni zan baka da kai na to mu tafi." "Mum shin ba zai yu naci abincin a nan ba dan Allah.?" "Rabin raina ni kawai ba zan jure zama a nan ba, amma zanyi hakan sabo da kai zan baka a nan." Yayi murmushi sosai tare dayi mata godiya murmushi kawai tayi masa ba tare data furta masa komai ba. Sun zauna Mum ta fara ba shi abinci su *Adnan* sai kallonsu suke, daga bisani kuma suka mai da kallonsu ga Prof, wanda shi kuma su Mum yake kallo sun juya sun nufi inda yake, hakan yasa ya dawo da kallonsa garesu lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna. Cike da izza da gadara tare da nuna isa yake musu magana.

"Mai kuma kazo yi nan? Bayan na fad'a maka cewar ka fita daga rayuwar d'ana, idan ma Adam ne ya sake turoka garemu to ka koma ka fad'a masa cewar ni bana buqatar ku, bawai Adam kawai ba ko dama kuwa a ce Kakar ka ce ta turoka gareni sabo da." Ya isa Prof kayi shiru haka karka ce zaka yi magana a kan ahalina, musamman Papa domin zan manta dangantakar da take tsakanin ku na hukunta ka. Ka gode Allah daka samu k'ani kamar Papa duk da irin zunubin ka, ina ta ya Papa takaicin samun ka a matsayin Yayansa da kuma *Adeel* da yazo matsayin ďanka. Dama wasu yaran da kayi sanadin salwantar rayuwarsu, Prof kai mugu ne kuma azzalumi kaci amanar mutane da dama kuma dukansu ahalinka ne."

"Da fari Maman ka k'anin ka yaranka matarka da kuma d'ayan ďanka. A dalilin ka ne Kaka ta ta rasa ranta Papa kuma ya rayu cikin k'unci, bayan wani lokaci kuma kai da hanayenka ka kashe yaranka, bama tare da mahaifiyar su ta gansu ba sannan kuma kayi wa kowa k'arya cewa d'a d'aya ka aifa a madadin uku. Ni na riga da na san duka gaskiyar amma kuma duk da irin wannan mummunan zunubin naka, kana kiran mahaifina mai laifi kai baka tab'a san kowa ba musamman ma *Adeel.* Da Mum kayi musu k'aryan cewa kana qaunar su amma kuma daga k'arshe ka cutar dasu sosai, kaci amanar Mum ta hanyar kashe mata yara kasa an cire mata mahaifa, a dalilin ka kuma ta kamu da cutar hauka ka sake ta a lokacin da take buqatar taimakon ka."

"Sannan kuma ka raba ta da d'ayan ďanta, wai kai wane irin mutun ne mai yasa kaddara ta sanya ka a cikin ahalinmu? Prof wallahi naso a ce wannan hatsarin da kayi bai barka ka rayu ba, ta yanda ahalinmu ba zasu yi k'unci ba amma yanzu sabo da kai duka ahalin suna tare da k'unci sosai. Prof wallahi ba zan tab'a yafe maka zunubin daka aikata ba na har abada nayi matuqar tsanar ka sosai." Magana yake cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa sosai, yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai.

Hakama *Adyan* abin da yake yi kenan, cike da jin mamakin abin da suka ji ya fad'a Mum take magana. *"Adnan* wai gaskiya ne abin da kake fad'a kuwa.?" "Eh Mum zama ki iya tambayar sa duka gaskiyar amma kawai kiyi magana da shi." Ta amsa shi da to tana wani jinjina ka shekaru ashirin da biyu kenan, ya d'auke su basu yi magana da juna ba, ta juya kallonta garesa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi ma kallonta yake cikin mutuwar jiki da sanyin murya take magana da shi...........................






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/15, 12:14 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 50*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Friday 11/03/2022*

*Time 05:43pm*

*Typing.................*


"Bani da wani zab'i sabo da kaddara ta riga da ta k'ara bani damar da zanyi magana da kai, nayi fatan a ce ni d'in nan ban k'ara ganin ka ba, amma mun k'ara had'uwa sabo da *Adeel* yanzu ka fad'a min wani abu, shin gaskiya ne abin da *Adnan* ya fad'a kai ka kashe min yara.?" Magana take cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai. Shi kuwa banda kallonta ba abin da yake wanda kuma hakan ne, ya hana masa iya furta mata komai sai ma mai da kallonsa ga, *Adnan* da yayi tare da fad'ar sunan sa cike b'acin rai yake magana. *"Adnan* a zahirin gaskiya ka aikata min babba kuma mummunan zunubi sosai, waye ya baka damar da zaka yi binkice a kai na ba tare da sani na ba? Ka fara da rashin amsa shari'a ta sannan kuma Abokinka, yayi k'oqarin mallakar duk wani abin dana mallaka. Ya kuma k'ara da rashin duba ni ba jimawa kuma mahaifin ka ya baiya a matsayin k'anina, yanzu fad'a min dalilin da yasa kayi binkice a kai na mai ya saka kake shiga rayuwata.?"

"Prof tin bayan da ni na sake had'uwa da *Adeel* na buqaci da na san waye ka, bayan kuma na had'u da Mum yanayin rashin lafiyar ta, yayi matuqar d'aga hankalina sosai sai bayan data samu lafiya ne, sannan na fara binkice a kanka kuma nayi nasaran samun duk abin dana nai ma. Sabo da nayi nasaran had'uwa da Dr Salim sannan kuma ya kai ni can gidan marayun, amma nayi nasaran sa'a sabo da sun tabbatar min da cewar, yaran sun mutu tin suna jarirai sabo da basu da lafiya sosai. Kai d'in gaba d'aya baka da sa'a shi yasa ka kasance a haka." Cike da k'unci bak'in ciki b'acin rai tare da tarin damuwa ta k'arasa inda yake, lokaci d'aya ta shiga kai masa tafi sai kai masa mari take tana kuka. "Mugu azzalumi kai wane irin uba ne wanda zai kashe yaransa da hanayensa? Auran ka da nayi shi ne babban qalubale na a rayuwa, hak'iqa nayi matuqar nadamar auran ka da nayi, na aure ka da zuciya ďaya amma kuma kai dame ka saka min? Kawai sai ka zab'i daka cutar da ni har ma da yaranmu ka daka a ciki, bama tare daka bani damar da naga yaran ba a matsayina na uwa. Wallahi tallahi ba zan tab'a yafe maka wannan ba na har abada."

Magana take tana kuka wanda kuma har zuwa wannan lokacin dukansa take, *Adyan* ya k'arasa inda take tare da rungumata jikin sa ya shiga rarrashinta. Lokaci ďaya kuma ta sulale a k'ara ta sume, cikin hanzari dukansu sun nufi gunta suna fad'ar sunan ta, amma sam ba wata a lama wacce ta nuna cewa zata farka. Nan kuwa *Adyan* yasa a ka kai ta d'aki na musamman wanda kuma shi ne da kansa yake duba ta, dukansu ukun suna tare da ita ďakin yayi shiru ba mai magana, *Adnan* ya anbaci sunan *Adyan* tare da furta masa su koma gefe. Ya amsa da to ya tashi sun fice daga d'akin sun samu wani guri daban sun zauna, bayan sun zauna *Adnan* yaci gaba da magana.

"Aboki ina ga kamar lokaci yayi wanda Mum zata san duka gaskiyar, ko kuma dai wannan yanayin nata yayi tsanani sosai, Aboki ita d'in mahaifiyar mu ce to ba zata tab'a yin abin da zai cutar damu ba. Zata fahimce mu sannan kuma zata amince da k'udirin mu, to ya kamata muyi abin daya dace dan Allah mu amince da gaskiyar sabo da farin cikin Mum." "Aboki ni kawai na damu ne a kan ahalinmu sabo da bana san wani abu ya cutar dasu, amma shikenan na amince da hakan sabo da Mum." "Na gode sosai daka iya fahimta na." "Aboki shin ko zaka dena wannan godiyar please.?" Murmushi kawai yayi masa mai tare da dariya shi ma abin da yake yi kenan, lokaci ďaya kuma suka samu kansu da yin hugging juna, bayan wani lokaci suka sake juna suka tashi suka koma ciki. Sun samu Umma zaune a kusa da ita yayin da *Adeel* yake ta aikin kai komo, su kuwa sai wani kallonsu suke cikin hanzari *Adeel* ya anbaci sunan *Adyan.* *"Dr Adyan* mai yake faruwa da Mummy na kuma yaushe zata farka.?"

Yayi shiru na jim kad'an sannan daga bisani ya amsa shi. *"Adeel* dukanmu a nan mun san irin abin da yake faruwa da Mum idan har tayi fishi sosai, to kawai tana buqatar hutu sosai sannan kuma ba zan iya sanin lokacin da zata iya farkawa ba. Zata iya jimawa sosai ko kuma a kasin haka to kawai mu jira tashin ta." Ya jinjina masa ka a lamar to tare dayi masa godiya kallonsa kawai yayi ba tare daya furta masa komai ba, ya juya ya fita dukansu sun bisa da kallo har ya b'ace, yana fita kai tsaye d'akin da Prof yake ya nufa. Ya shiga ciki ya same sa cikin wani irin yanayi mara dad'i, kallo ďaya tak zaka yi masa ka fahimci cewar yana tare da k'unci sosai, yanayin daya gansa ciki yayi matuqar d'aga hankalin sa sosai, yana k'oqarin fad'ar sunan sa yayi saurin dakatar da shi yana cewa.

"Dady gaskiyar Barrister ne kai ba zaka tab'a san kowa ba, sannan kuma yayi gaskiya daya kira ka da maciji sabo da kana cutar da ahalinka, Maman ka k'anin ka yaranka matarka da kuma ni. A kan me zaka kashe min 'yan uwa? Sannan kuma kayi wa kowa k'aryan cewa ni kad'ai ka aifa, na tabbata kayi hakan ne kawai sabo da wani buri naka, gaskiya ka cutar da Mum da yawa kuma har yanzu abin da kake yi kenan. To bara ka ji wallahi tallahi idan wani mummunan abu ya faru da Mummy na, ni da kai na zan hukunta ka to kayi fatan ta samu sauki cikin sauri, a dalilin ka ne na rasa Kaka ta sannan na ni santa da Kawu wato Papa, ka kuma kashe abokan aihuwa ta sannan kuma ka shiga tsakanina da Mummy na. Dady ni kuwa wane irin zunubi na aikata da a ka hukunta ni da samun uba irin ka, Dady ni ji nake kamar ban tab'a sanin ka ba sabo da k'arya kawai kake fad'a min, amma yanzu da ni na san duka gaskiyar wallahi tallahi."

Da sauri Dady ya dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar. "A'a ďana a'a dan Allah karka fad'i komai eh na amince da duka abin daka fad'a, na san cewar nayi ma k'arya a kan komai amma soyayya ta a gareka gaskiya ce, ina sanka ďana wallahi ina matuqar masifar qaunarka sosai. Ko da a ce zanyi k'aryan komai to banda soyayyar ka, hakama ko da a ce zan iya cutar da kowa to banda kai, sabo da kai d'ana ne kuma ina qaunarka sosai dan Allah ka yarda da ni wallahi ina qaunarka sosai." "Dady amma kuma kai ka kashe wasu daga cikin yaranka, to mai yasa nima ba zanyi tunanin cutar lokaci kake jira domin ka cutar da ni ba.?"

"A'a rabin raina ni ba zan tab'a cutar da kai ba, sabo da kai ne abin da nafi so fiye da komai sabo da kai kad'ai ne d'an da nake da shi. To dan Allah karka barni naro e ka ka da ka barni please." "Dady Ubangiji ya baka yara uku a lokaci ďaya a maimakon ka gode masa, sai ka zab'i daka butulce masa ina ma a ce bani bane wanda ka zab'a ba, ta yanda ba zan fuskanci wannan mummunan ranar ba. Mai yasa ka zab'e ni a cikin ukun mai yasa sai ni.?" "Rabin raina bani bane wanda ya zab'e ka ba kaddara ce ta zab'a min kai, na kuma yi matuqar farin ciki da hakan sosai sabo da kayi daidai da ra'ayi na. *Adeel* gaskiya ita ce ni banma ga wa 'yan can yaran ba, sabo da farin cikin had'uwa da kai masoyi ni dama d'a ďaya kawai nake da kwad'ayin na aifa kuma kai ne, na gaji wannan a gurin Kakar ka ita ta zab'i k'anina fiye da ni. Tana ba shi abinci ta hana ni daga k'arshe kuma ta kai ni makaranta almajiranci, na kasa jurewa shi yasa na gudu nayi tafiya ta, na had'u da wani mutum wanda ya zama uban gida na. shi ne wanda ya koya min yanda zanyi kasuwanci, daga bisani kuma na shiga makaranta ďana tin daga ranar da, Mama ta kai ni almajiranci na shafe babin ta ita da ďanta. Ban kuma k'ara wai wayar su ba har kawo yanzu da muke magana, to ya kamata kayi min adalci dan Allah karka barni please."

"Bani da wani zab'i sabo da Mum tana buqata na a yanzu, to zan tafi gareta ka kula da kanka sosai sai na dawo." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyar sa gurin Mum, ya samu su Umma a tare da ita shi ma ya mai mi guri ya zauna, misalin k'arfe 08:00pm Mum ta farka daga dogon suman da tayi, cikin hanzari sun shiga yi mata sannu kallonsu kawai take ba tare data amsa su ba. Kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, cike da kulawa Umma take magana da ita. "Aisha na san cewar wannan yanayin yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai, amma baki da wani za'bi sabo da ba zamu iya canja gaskiyar ba. To ya kamata kiyi hak'uri ki jure sabo da ba zan iya jure ganin ki, a cikin irin wannan mummunan yanayin ba domin hakan yana matuqar cutar da ni sosai."

"Umma ta ya zan iya mantawa da wannan cikin sauki? Ta ya Prof zai aikata min haka ni uwa ce to bai kamata ya aikata min haka ba, ta ya zai rabani da yarana bama tare dana saka su ga idanuwana ba? Umma ta ya ma Prof zai yi tunanin cutar da ni sosai har haka? Ya kasa bani damar da zan kasance tare da yarana, ya kuma hana ni damar kasancewa uwa ta gari a garesu, hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai, wallahi tallahi ba zan tab'a gafarta masa wannan ba na har abada."

Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da take kuka kuma kuka sosai, Umma ta shiga rarrashin ta tana bata magana hakama *Adeel* abin da yake yi kenan. Su *Adyan* kuwa sai kallonsu suke kallo mai cike da jin tausayin Mum sosai, *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. "Aboki ina ganin cewar yanzu ne lokacin daya dace Mum ta san gaskiyar." Ya jinjina masa ka tare da furta masa kalmar ok shi ma ya jinjina masa ka, tare da mai da kallonsa gasu Umma ya nisa tare da jan numfashi, ya k'ara da sauke a jiyar zuciya sannan ya anbaci sunan *Adeel.*

*"Adeel* ina ga ni da Aboki zamu iya daidai komai insha Allah." Kafin ya amsa shi Mum tayi masa rigagi. "A'a *Adnan* kawai ku bari haka na gode da kulawa, amma ba abin da zaku iya yi sabo da ba zaku dawo min da yarana ba. Na riga na rasa su ba tare dana ga ko fuskarsu ba, wannan ne abin da yafi cutar da ni fiye da komai, na tabbata wannan k'uncin zai d'auke ni na har abada." Kuka yaci k'arfin ta tayi shiru ta kama aikin kuka kuma kuka sosai, cike da tausayin ta sun tashi dukansu sun nufi kusa da ita, sun zauna sai wani kallonta suke kallo sosai lokaci ďaya kuma suka shiga share mata kwalla, yayin da suma kwallar suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. *Adnan* ya kama hanayen ta tare da fad'ar sunan ta, magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan sanar daku shi ba.

"Mum ni zan iya dawo maki da wannan." Cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. *"Adnan* shin wai kai ka fita haiyacinka ne? Ta ya zaka dawo da yaron da suka riga suka mutu.?" "Eh Mum ni zanyi hakan sabo da akwai buqatar kiyi farin ciki, sannan kuma da ina lokaci yayi wanda zaki rayu tare da duka yaranki. Mum gaskiyar ita ce har yanzu yaranki suna raye, sannan kuma dukansu biyun sun kasance kamar yanda kike fata. Mum gaskiya ke kina da matuqar sa'a sosai a rayuwa, kina samun duk abin da kika yi fata wannan ma farin nasaran ki ne. Ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login