Showing 27001 words to 30000 words out of 142761 words

Chapter 10 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Friday 31/12/2021*

*Typing................*

"Meyasa ba zaka barni na gani ba.?" Ya girgiza kai yana wani gajeran murmushi, "a'a wannan sorrina ne shi yasa ba zaki gani ba." "Him fad'a min wani abu dawa kake chart.?" Yayi wani lallausan murmushi sannan ya amsa mata, "ina magana da Auntyn ki ne." Kallonsa kawai take yayin da ta gagara furta masa komai shi ma haka kallonta yake, sun samu shiru na jim kad'an sannan ya anbaci sunanta. "Ahlam dare yayi sosai sannan kuma gurin nan yana da sanyi sosai, to ina ga ya kamata ki shiga ciki domin ki kwanta sai da safe." Har zuwa wannan lokacin kallonsa take ba kuma tare data furta masa komai ba, sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ta amsa mashi. "Kana buqatar na tafi domin kaci gaba da chart da wannan matar? Ba zan dakatar da kai ba amma dai ka daina kiran ta da Aunty na, sabo da ni ba zan ta'ba zama qanwarta ba amma k'ila na iya zama yayarta. Yanzu ka tashi mu shiga ciki sabo da ba zai yiyu ka kwana a nan ba, sabo da sanyin gurin zai iya cutar da kai da kuma lafiyar ka, to yaron mu yana buqatar mu sosai zamu iya tafiya yanzu sannan kuma zaka dakatar da wannan chart d'in mu tafi."

"Amma." Tayi saurin dakatar da shi ta hanyar rufe masa baki tare da girgiza masa ka a lamar a'a, da sauri ya wani zaro ido yana kallonta ita ma haka kallonsa take ya janye hanun ta da yake kan bakinsa tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam karki wani damu ni zan kula da kai na sosai sannan kuma zan kasance lafiya insha Allah to zaki iya yarda da ni." Sam bata amsa shi ba sai ma tashi da tayi tare da riqa hanun sa ya tashi sun shiga ciki, tayi masa nuni da wata kujera sannan taci gaba da magana. "zaka iya kwanciya a kan wannan kujeran ni kuma zan kwanta tare da yarona to sai da safe." Ya jinjina mata ka yana wani gajeran murmushi ita kuwa kallonsa kawai take daga bisani kuma ta nufi gado domin ta kwanta. Ya bita da kallo har ta kwanta shi ma kwantawa yayi tare da d'aukar wayar sa, yana dannawa daga bisani kuma ya d'ora wayar a kan kunnan sa, bayan wani lokaci ya fara magana cikin kyakkyawan yanayi yake magana yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa sosai.

"Barka da dare rabin raina fatan ban tashe ki daga barci ba? Kiyi hak'uri muna cikin charting na sauka qanwata ce ta zomin da wani uzuri, to ina fatan ba kiyi fishi ba sannan kuma zaki yafemin dan Allah." Cike da unci bak'in ciki tare da tarin damuwa Ahlam ta tashi ta nufi inda yake, sai wani sauri take har kamar zata fad'i tana k'oqarin amsar wayar yayi saurin janye wayar daga kunnan sa, tare da tashi zaune ya anbaci sunan ta tayi saurin dakatar da shi cike da 'bacin rai take magana wanda shi ma ya fahimci hakan. "Yaya Ahmad kamar dai na fad'a maka cewar ka kashe wayar ka to amma mai yasa baka yi hakan ba? Ka sani ni sam ba zan d'aukar maka hakan ba to ya kamata ka san da wannan yanzu ka kashe wayar sannan ka kwanta." ta juya zata tafi yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da zaunar da ita kusa da shi kusa sosai, sai wani kallonta yake kallo sosai ita ma abin da take yi kenan sun jima a haka sannan ya fara magana. "Ahlam mai ya saka kike yi kamar kina bani umurni bayan kuma ni ina gaba dake? Sannan kuma mai ya saka kika damu da abin da nake shin ke kina da matsala ne da hakan? Kin hana ni chart nayi shiru yanzu kuma kina k'oqarin dakatar da ni kar nayi waya da ita. Mai yasa fad'a min mai ya saka kike yin duka wannan fad'a min kina da matsala da hakan ne.?"

Sam bata iya furta masa komai ba sai kallonsa kawai take yayin da take jin soyayyar sa tana dad'a shigarta, a gefe ďaya kuma tana jin kamar ta rasa shi lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. Ta yunk'ura domin ta tashi yayi saurin dakatar da ita, "Ahlam shin da akwai matsala ne dan Allah ki sanar da ni? Mai yake faruwa da ke mai ya saka kike kuka ki sanar da ni gaskiyar please.?" "Ta girgiza ka tare da sakin wani saban kuka da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata ka, ya janyo ta jikinsa ya shiga rarrashin ta cikin sannu a hankali yake furta mata kalmar. "Ya isa haka karki tashi *Adyan* barci ya kamata ya huta, to yanzu fad'a min mai yake faruwa dake.?"

Shiru bata yi magana ba domin kuwa tin lokacin da yayi hugging d'in ta, ta manta da duk wata damuwar ta sai wani farin ciki yake ta shigarta sosai, sai wata soyayyar sa take ji tana qara shigarta shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai. "Ahlam mai ya saka ba zaki sanar da ni gaskiyar ba hak'iqa kina 'boye min wani abu, ya kamata ki sanar da ni gaskiyar domin na san da abin da zan iya taimaka maki, ina fatan karki jima sosai a cikin wannan yanayin sabo da hakan zai yi matuqar cutar dake sosai." Ya shiga anbatar sunan ta amma bata amsa ba ganin idanuwanta a rufe yasa yayi tinanin cewar barci take. Nan yaci gaba da danna waya daga bisani kuma barci ya d'auke sa bama tare da sanin sa ba, kukan da *Adyan* yake ne ya tashe su daga barci lokaci d'aya suka bud'e idanuwan su, cikin hanzari sun tashi dukansu sun nufi gurin yaronsu Ahmad ne wanda ya d'auke sa ya shiga rarrashin sa. Hakama Ahlam abin da take yi kenan Ahmad yace da Ahlam ta kira doctor ta amsa da to ta juya ta fita, ba jimawa ta dawo tare da likita ya duba shi ya kuma sanar dasu cewar yana samun sauki sannan ya juya ya fita.

Bayan tafiyar doctor Ahmad ya kai kallonsa ga Ahlam tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam ki samu kiyi salla sai ki rungumasa nima nayi salla ki tafi yanzu lokaci ya tafi sosai." Ta amsa da to ta tashi ta nufi toilet ba jimawa ta fito ta fara salla, bayan ta idar tayi azkar sannan ta tashi ta nufi gurin su ta fara gaisawa da Ahmad sannan ta kar'bi *Adyan* daga hanun sa. shi kuma ya tashi ya shiga toilet bayan wani lokaci ya fito ya fara salla, bayan ya qarasa ya tashi ya fita bai wani jima sosai ba ya dawo tare da kayan abinci. Ahlam ta had'a musu break past haka dai *Adyan* yaci gaba da samun kulawar doctor dama iyayen sa, ya samu tsayin mako d'aya asibiti sannan ya samu sallama zuwa gida. Da dare suna zaune a parlour Ahlam ta sauke kallonta ga *Adyan* tare da fad'ar sunan sa. "Masoyi dare yayi sosai to ya kamata mu tafi ka kwanta ka ji ko." Kafin ya amsa ta Ahmad yayi mata rigagi, "Ahlam karki manta cewar yau *Adyan* tare da ni zai kwana to ki dena wannan zak'ewar kinji ko." "A'a Yaya Ahmad sai dai kawai na baka hak'uri sabo da dani zai kwanta." "Ba zai yu ba Ahlam kawai dai ki amince da gaskiyar kinji ko." Nan kuwa suka shiga gardama *Adyan* sai kallonsu yake sai daga bisani ya fara magana. "Appa Ammie dan Allah ko zaku dena duka wannan? Ni zan kwanta da dukanmu ukun zamu yi barci a tare wannan ne k'arshe dan Allah."

Dukansu wani irin kallo suke yi masa kallo sosai, Ahlam ce take amsa shi yayin da Ahmad ya rufe su da ido. "Shikenan masoyi zamu yi hakan dukanmu zamu yi barci a tare, yanzu mu zamu tafi Appa zai zo daga baya to mu tafi." "A'a dukanmu zamu tafi a tare Appa mu tafi ina san zanyi barci." Ya jinjina masa ka tare da furta masa to sun tashi dukansu sun nufi d'akin Ahlam, suna haka Ahlam ta nufi toilet Ahmad kuma ya nufi gado da *Adyan* sun kwanta. Ahmad ya rungumasa jikin sa yana wani jijjigasa ba jimawa yayi barci, bayan wani lokaci Ahlam ta fito daga toilet wanda kuma wanka tayo, k'arar da yaji ne yasa shi kai kallonsa gareta tsaye take daga ita sai wani k'aramin towel, wanda tsayin sa iya cinya rabin k'irjin ta duk a waje sannu a hankali take tafiya tana wani motsa jiki har ta isa gaban madubi.

Taja kujera ta zauna ta fara shirin ta, sam ya kasa jure ganin ta a hakan wanda wannan dalilin ne yasa ya tashi zai fita. Sannu a hankali yake janye *Adyan* daga jikinsa ya shinfid'esa sannan ya tashi ya fita daga d'akin, ta bisa da kallo har ya fice ba kuma tare data furta masa komai ba, taci gaba da shirin ta inda ta shirya cikin wata kyakkyawar shiga ta wata ar riga, wadda tsayin ta bata kai guiwa ba iya cinya rigar shara-shara take tayi kwance jikin ta tare da bai yana surar ta. Ta feshe jikin ta da tirare ya had'u da humra sun had'u sun ba da wani daddad'an k'amshi mai dad'in shaqa, ta fito ta nufi bedroom d'in Ahmad kwance yake idanuwansa a rufe ga a lama tinani yake, ya jima a haka sannan daga bisani ya koma kiran layin Hayatee yana haka sai ga Ahlam ta shigo har zuwa wannan lokacin idanuwansa a rufe suke, wanda shi yasa bai iya ganin ta ba tayi tsaye sai kallonsa take cike da unci da bak'in ciki tare da tarin damuwa ta nufi inda yake.

Takun tafiyar ta yasa shi bud'e idanuwansa lokaci d'aya yayi tozali da kyakkyawar faskar ta, wani irin kallo yake yi mata kallo sosai har ta isa inda yake ta kai hanun ta, ta fizge wayar sa wanda bama ya san tayi ba tana k'oqarin fasa wayar ta hanyar yin jifa da ita yayi saurin dakatar da ita. "A'a dan Allah karki yi naro e karki fasamin waya please ki dawomin da waya ta dan Allah." Ya shiga rarrashin ta yana lalla'bata har ya samu ya iya ba shi wayar sa ya kar'ba tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam qlau kike kuwa mai ya saka kike cikin fishi sosai haka shin wani abu na faru dake ne.?" Magana yake yayin da ya rufe ta da ido yana kallonta kallo sosai, yayin da yake jin tana birgesa matuqar birgewa sosai. "Kai ne nan damuwa ta kuma kai ne wanda yake saka ni fishi sosai, haka kawai ka fito daga ďakin kazo nan nayi shiru ne sabo da nayi tinanin ko kana san ka watsa ruwa ne, a she sam ba haka bane kawai ka zonan domin kayi waya da wannan 'yar iskar yarinyar, ya kamata ka dawo da hankalin ka jikin ka domin kuwa ni sam ba zan ta'ba baka damar da zaka kasance tare da ita ba na har abada. Ina fatan Allah ya d'auke ranta a daran yau kafin safe ta yanda ku biyun zaku rabu na har abada."

Yayi saurin dakatar da ita ta hanyar kifa mata wani wawan mari wanda sai da ta kife a qasa, yasa hanun sa ya riqo ta ta tashi cike da fishin zuciya yake magana. "Idan kika qara fad'ar haka ni da hannayena zan kashe ki ita rayuwa ta ce to dan haka ya kamata ta rayu, ina matuqar masifar qaunar ta sosai wannan yasa nake kiran ta da rayuwata wato Hayatee na. Sabo da ita ne yasa har yanzu nake raye to dan haka yana da kyau ki girmamata sannan kuma kiso ta kinji ko." Wani irin kallo take yi masa mai cike da jin mamakin sa sosai yayin da take kuka kuma a haka take magana. "Kai mugu ne mai yasa kake cutar da ni sosai har haka to kawai ma ka kashe ni, sabo da a yanzu rayuwata bata da wani sauran anfani kuma kai ne nan wanda ya tarwatsa ni da kanka. To garama kai ka kashe ni da kanka ko kuma ni na aikata hakan da kai na kuma ba zan ta'ba barin ka dakatar da ni ba, kawai dai zan sanar da kai wani abu kafin na mutu abin shi ne ka kulamin da yarona sosai, sannan kuma ka fad'a masa cewar Ammie tana matuqar masifar qaunar sa sosai."

Kuka yaci k'arfin ta wanda wannan dalilin ne yasa ta yin shiru, ta kama aikin kuka ta juya domin tafiya da sauri ya ri e hanun ta tare da riqa kafad'ar ta ya juyo ta, sai wani kallonta yake kallo sosai ita ma abin da take yi kenan yayin da take kuka kuma kuka sosai. "Ahlam shin da akwai matsala ne fad'a min wani abu shin da akwai wani abin da kike 'boye min a game da ke? Ahlam ni kawai na damu ne a kan Hayatee na sabo da abin da kika fad'ar mata, Ahlam gaskiyar ita ce ni ina matuqar qaunar Hayatee na hakama ina buqatar kasancewa a tare da ita sosai, amma kuma ke kina k'oqarin ganin kin nisan ta ni da ita Ahlam ni sam ba zan iya jure wannan ba, sabo da hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai Ahlam dan Allah." A'a ta fad'a da k'arfi tana d'aga murya cike da unci ta daki bango tare da watse kayan dake kan madubi, yayin da take wani irin kuka abar tausayi sosai kuma a hakan take magana. "Kai mugu ne sam baka damu da kowa ba hakama ba ruwan ka da damuwar kowa sai taka, ka damu sosai a kan karka rasa wannan banzar amma kuma ka amince da ni na rasa ka na har abada."

"Yaya Ahmad ni qanwarka ce kuma matarka uwar yaronka amma duk da kasancewa haka kai baka ta'ba sona ba ko da kuwa na rana d'aya ne, nayi duk abin da zan iya domin kai kaso ni amma ka kasa tilassawa zuciyarka taso ni. Yaya Ahmad gaskiyar ita ce ni d'in nan ina matuqar masifar qaunarka sosai fiye ma da yanda nake sanka, amma abin takaicin shi ne kai da kuma zuciyarka wata daban kuke qauna hakan yana da matuqar zafi sannan kuma da k'una sosai, Yaya Ahmad ni ba zan tilassa maka a kan kaso ni ba amma ka sani idan har kai kayi nasaran yin aure da wata daban to wallahi tallahi ka rasa ni na har abada ni da kuma d'ana. Kuma ni ba zan ta'ba canja hakan ba to kana da lokacin da zaka yi tinani domin yanke hukuncin daya dace." Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i wanda kuma har zuwa wannan lokacin kuka take kuma kuka sosai, shi kuwa sai wani irin kallo yake yi mata kallo sosai mai cike da jin mamakin abin da take fad'a, cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana tamkar wani mara lafiya.

"Ahlam wai da gaske ke kina so na sosai har haka? Gaskiya ni sam na kasa yarda da hakan amma tabbas tin da jimawa ni na san cewar kina matuqar buqatar wani abu daga gareni. A ko yaushe kina nuna san na kusance ki kamar dai yanda yake a yanzu kinyi wannan shigar ne sabo da kija hankali na, Ahlam ni wannan ne abin dana sani kuma wannan sam ba soyayya ba ce to ya kamata ki amince da gaskiyar, Ahlam gaskiyar ita ce ke d'in nan baki ta'ba sona ba bama ki san ta yanda zaki so ni ba na jima da sanin hakan na kuma amince da gaskiyar, to dan haka ka da ki dakatar da burina ni ina san Hayatee na sosai kuma da ita kawai ne zan rayu ko da mai zai faru wannan alkawari ne kuma ba zan canja hakan ba. Ahlam to kawai ki amince da gaskiyar abin da nima nake yi kenan."

"A'a Yaya Ahmad wannan ba gaskiya bane ni ba kamar yanda kake tinani ba ce, eh gaskiyar ka fad'a ni d'in nan ina tare da buqatar ka sosai amma kuma hakan sam bai ya nufin cewar bana sanka. Yaya Ahmad da a ce buqatar ka kawai nake ji to da jimawa na baiwa kai na magani zansa kayi hakan ko da ba a cikin haiyacinka ba, ni sam ban damu ba idan har zan samu abin da nake so, amma kuma dai banyi hakan ba sabo da ni ina san ka kusance ni cikin qauna da soyayya, ta yanda zan gansu da abin da nake buqata daga gareka. Ba zanga laifin ka ba sabo da har yanzu kai baka san gaskiyar ba, amma kuma a yau ďin nan kuma a yanzu ni Ahlam Al'ameen zan sanar da kai duka gaskiyar. Daga nan kuma zan nuna maka irin abin da zan iya aikata wa kai na a lokacin da ni na rasa ka to ka kalla da kyau domin ka gani.................





*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/3, 11:00 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 12*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login