Showing 105001 words to 108000 words out of 142761 words
Chapter 36 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
da wannan amma zan kasance d'a na gari a gareki nayi alkawari, ke uwa ta gari ce a gareni to ina alfahari da hakan sosai ina matuqar masifar qaunarki sosai Mummy na." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take d'auke da wani lallausan murmushi, ita kuwa sai kallonsa take kallo sosai cike da qaunar sa tayi hugging d'in sa tana sunbatarsa. Farin cikin sa ya qaru sosai su Umma sai kallonsu suke, lokaci ďaya su *Adnan* suka ji wata soyayyar Mummmyn su tana shigarsu sosai, tausayin ta ne yafi yawa a tare dasu sosai sai ji suke kamar su tafi su rungumata.
Cike da k'unci da b'acin rai *Adyan* ya cire hanun sa cikin na *Adnan* ya nufi hanyar fita, *Adnan* ma juyawa yayi yabi bayan sa suna k'oqarin fita Umma tayi saurin dakatar dasu, sun tsaya tsak ba tare da sun amsa ba *Adnan* ne wanda ya juyo da kallonsa gareta, yayin da *Adyan* yake ri e da k'ofa kafin Umma ta furta komai *Adeel* ya mata rigagi. "Mum wad'an nan sune wad'an da suka taimaka min sosai gurin ganin kin samu lafiya, Mum *Adyan da Adnan* su ba kawai abokaina bane a'a su ďin na musamman ne a gareni. Sabo dasu ne na samu damar kasancewa a tare dake yanzu su sunfi kowa kirki, suna bina bashin da ban san dame zan biyasu ba, sai dai kawai naci gaba dayi musu addu'ar fatan alkhairi kamar dai ko yaushe." Nan ya shiga sanar da ita komai daya faru duk wani abin da suke fad'a *Adnan* yana sanar da *Adyan* da turanci.
Sabo da ba komai ne yake fahinta ba hakan tasa yake fahimtar komai, Mum tayi kiran su sun tafi kusa da ita sun zauna sai wani kallonsu take kallo sosai, suma haka kallonta suke kallo sosai mai tare da shauk'i sosai. "Na gode muku sosai Allah ya saka muku da alkhairi wannan kalmar ce kawai zan iya fad'ar muku, hak'iqa iyayen ku sunyi matuqar samun yaran kirki sosai Allah yayi muku albarka, ya kuma sanya wa rayuwarku albarka ku biyun kuna da kamanni da yarona sosai, kamar dai 'yan uwan juna ko ahali ďaya shin zan iya runguma ku jiki na? Sannan kuma zan iya kiran ku da yarana dan Allah.?" *Adnan* sai wani kallonta yake yayin da shi kuma *Adyan* ya rufe sa da ido yana kallonsa, *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* tare da sanar da shi abin da take fad'a, yayi shiru yana nazari *Adnan* ya shiga jinjina a lamar eh shi ya jinjina masa ka a lamar eh.
*Adnan* ya mai da kallonsa ga Mum tare da furta mata eh, murmushin ta ya k'aru sosai lokaci ďaya kuma tayi hugging d'in dukansu biyun. Ta k'ara da sunbatarsu tana furta musu kalmar Allah yayi muku albarka sun amsa da Amin, ba jimawa ta sake su bayan wani lokaci suka tashi suka fita, wanda kuma office ďin *Adyan* suka nufa sun shiga ciki *Adnan* ya sauke kallonsa ga, fuskar *Adyan* wanda yake ta hawa yana sauka ya gama fahimtar cewa cikin fishi yake sosai, shi ma yana tare da k'unci amma zai iya cewa damuwar *Adyan* tafi tasa yawa, ya nisa sosai tare da jan numfashi sannan ya fara magana.
"Aboki shin har yanzu kana tare da tsanar Mum sosai.?" "A'a Aboki ni kawai tausayin ta nake sosai tare da jin tsanar Prof a tare da ni sosai, shi ne abin da nafi tsana a rayuwata dan haka ya zama dole ya fuskanci hukunci daga gareni." "Aboki ciwon namu duka iri d'aya ne to tare zamu yi komai ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to da dare su Ammie suka shigo duba ta, wanda kuma tare suke dasu *Afnan Adeel* ya gabatar dasu ga Mum. Ta shiga yi musu fatan alkhairi sun amsa ta tare dayi mata godiya, haka dai Mum tayi ta samun cikakkiyar kulawa sosai har jikin ta ya warware gaba d'aya. bayan mako d'aya ta samu sallama zuwa gida, zuwa wannan lokacin cikin su *Alishart* yana da watanni hud'u, har ya fara bai yana hakan yasa suka fara shirin tafiya k'asa Nigerian, sunyi duk wani shirin su na tafiya Appa yayi musu visa bayan mako biyu jirginsu ya tashi......................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/16, 12:02 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 43*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Saturday 12/02/2022*
*Time 07:48pm*
*Typing...............*
*Nigeria.*
A garin Abuja suka sauka kasancewar su Abbu daga Abuja sun kawo masu Abba ziyara. Su Ummi sai wani d'aukin zuwan su suke inda suka shiga yi musu sannu da zuwa, bayan sun gaisa sun huta gajiya tare da cin abinci sun shiga yiwa Mum ya jiki, ta amsa da Alhamdulallah tare dayi musu godiya sosai, murmushi kawai suka yi mata tare da furta mata ba komai. Su *Adeel* sun samu kwana biyu a garin Abuja gidan Abba sannan suka fara shirin tafiya, ai kuwa a nan ne gizo ke sak'a domin kuwa *Alishart* ta shiga kukan sai ta tafi tare dasu *Afnan.* A zahirin gaskiya dukansu basu so tafiyar ta ba, amma ganin yanda take k'unci yasa Abba yace su Appa su barta ta tafi, basu da wani zab'i wanda wannan dalilin ne yasa suka amince da tafiyar ta. Suna ta shirin tafiya Abba da Abbu sunyi musu sha tara ta arziki, wanda visa ma a kayi musu Abuja to kaduna *Adyan* yayi musu rakiya, har Airport bayan sunyi sallama suna k'oqarin tafiya *Adyan* ya anbaci sunan *Adnan* yana cewa.
"Aboki ka kula da *Adlishart* sosai da kuma duka yaran ka ji ko." "Eh zanyi nayi alkawari amma bayan su baka buqatar na kula da kowa.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Shikenan ka kula da Mum sosai yanzu kana farin ciki.?" "Eh hakan yayi kuma ni zan kula da dukansu nayi alkawari, insha Allah to zaka iya yarda da ni ka ji ko." Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, daga bisani kuma suka yi hugging juna su Umma suna daga gefe suna kallonsu. Ba jimawa suka sake juna *Adnan* ya kai bakinsa daidai kunnansa ya rad'a masa cewa. "Aboki akwai buqatar ka rungumi Mum, Kaka, da kuma *Adeel* sabo da dukanmu ahali ďaya ne, wannan ce gaskiyar kuma hakan ba zai canja ba to kawai kayi hakan dan Allah." Kallonsa kawai yake ba tare daya amsa shi ba sai daga bisani ya jinjina masa ka a lamar to, *Adnan* yayi murmushi sosai tare da sunbatarsa a ka yana furta masa kalmar. "Ina sanka Aboki ina qaunarka sosai zanyi matuqar yin kewarka sosai." "Nima haka Aboki ina matuqar qaunar ka sosai ba zamu jima a nan ba, zamu shigo kaduna a wannan lokacin zamu k'ara kasancewa a tare."
Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, sun k'arasa gurin su Mum ya bisu ďaya bayan d'aya yayi hugging d'in su, kamar dai yanda *Adnan* ya buqata daga garesa ya anbaci sunan *Adeel.* *"Adeel* ka tabbatar daka kula da Mum sosai idan akwai buqatar nazo to kawai ka kira ni ka ji ko." "Na gode sosai *Dr Adyan* Allah ya saka da alkhairi Allah kuma ya bar tare Amin." Dukansu sun amsa da Amin *Adyan* ya mai da kallonsa ga *Alishart* tare da fad'ar sunan ta. *"Adlishart* dan Allah ki kula da kanki sosai da kuma yaronmu kin ji ko *Afnan* kema haka kin ji ko." Sun amsa shi da to suna murmushi da kuma haka suka yi sallama, suna fice ba jimawa sosai jirginsu ya tashi zuwa kaduna.
Misalin k'arfe 05:00pm jirginsu ya sauka *Adnan* ya tare musu taxy sun nufi gida, kai tsaye gidan Papa suka nufa Mamie na zaune a parlour tare da, Amal yarinyar Anwar ta kawo mata fira bugun k'ofar da a kai ne yasa ta tashi ta nufi k'ofa, ta shiga tambayar waye kamar a mafarki ta ji muryar *Adnan* yana fad'ar sunan sa. Cike da d'auki ta bud'e k'ofar yayin da bakinta yake anbatar sunan *Adnan,* "ďana ka dawo gareni sannu da zuwa rabin raina." Magana take yayin da take rungume da shi a jikin ta sai wani sunbatarsa take. "Nayi kewarka sosai yarona I really miss you so much my sweet son." Ta fad'a tare da qara sunbatar sa, "I miss you too Mamie nima nayi matuqar yin kewarku sosai ina matuqar masifar qaunarki sosai Mamie na." Ya fad'a tare da sunbatarta su Umma sun rufe su da ido sai kallonsu suke suna murmushi. Sai kuma zuwa wannan lokacin ne Mamie ta shiga yi musu sannu da zuwa, bayan data kammala da yaronta ta tafi ta shirya musu tebur da kayan abinci.
Sannan ta dawo garesu ta d'auke kallonta ga *Afnan,* wacce take rungume da Amal tare da fad'ar sunan ta. *"Afnan* masoyiya to ya kike ya mai gida na? Ya tafi na tsayin wata biyu ya barni da kewarsa sosai to fatan dukanku kuna cikin k'oshin lafiya sosai.?" Cike da jin kunya da nauyi take amsa ta, "Mamie muna lafiya sannan kuma muna tare da kewarku sosai." Hakan yayi kyau sosai." Ta mai da kallonta ga Mum tare dayi mata ya jiki ta amsa da Alhamdulallah, ta gaisa da Umma da *Adeel* sannan ta sauke kallonta ga fuskar *Alishart* tare da fad'ar sunan ta. "Rabin raina hak'iqa nayi matuqar yin kewarki sosai sabo da mun jima sosai bama tare, sai dai a waya amma kuma yau kinzo garemu nayi matuqar farin ciki da hakan sosai ina sanki 'yata ina qaunarki sosai."
Ta fad'a tare da sunbatarta ta k'ara da yin hugging d'in ta, bayan wani lokaci suka tafi suka ci abinci sannan suka tafi domin su shirya. Bayan sun shirya sun fito sun nufi gidan Abba har da *Alishart* suka tafi, sun kuwa samu dukansu a parlour nan kuwa su Yaya Anwar suka shiga yi musu sannu da zuwa. Sun amsa suna murmushi mai had'e da dariya bayan sun gaisa sunci gaba da fira cikin raha wasa da dariya, sun kasance a nan wanda sai dare sannan suka tafi gida sun samu Papa ya dawo, nan kuwa ya shiga yi musu sannu da zuwa sun amsa suna murmushi mai had'e da dariya, sun zauna sunci gaba da fira bayan wani lokaci *Alishart da Afnan* suka tafi domin su kwanta. Bayan tafiyar su ne *Adnan* yake sanar dasu Mamie cewar *Alishart* na tare da juna biyu, sun cika da mamakin hakan sosai daga bisani kuma suka yi mata addu'ar sauka lafiya, ganin dare yayi sosai yasa suka yiwa juna sallama tare da sai da safe, suka nufi d'akin barci su Mum sun samu tsayin kwana biyu a nan gidan Papa sannan suka tafi nasu gida.
Bayan mako d'aya *Adnan* ya shirya tsab ya nufi garin Kankiya, wata safiyar litinin zaune yake a office ya ji a na buga masa k'ofa, daga ciki ya amsa da cewa shigo ciki ba jimawa ya shigo, bayan ya zauna sun gaisa Dr Salim ya shiga tambayar sa mai yake tafe da shi, yayi shiru na jim kad'an sannan daga bisani ya amsa shi. "Am ko kai ne Dr Salim.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh *Adnan* yaci gaba da magana. "Am ni sunana *Barrister Adnan Adam Muh'd* nazo nan ne domin nayi magana da kai, a game da wani muhimmin abu to fatan zan samu had'in kanka.?" "Miye wannan sannan kuma a kan me zamu yi magana.?" "A game da Prof Abas ne."
Da sauri ya wani zaro ido yana kallonsa kallo sosai, sannan kuma daga bisani ya amsa shi. "Waye shi kuma mai yasa zamu yi magana a game da shi.?" "Ina san na san gaskiyar da kai da shi kuma birne shekaru ashirin da biyar da suka wuce." "Mai yasa kake tunanin cewa ina da sani a kan abin da kake fad'a.?" "Dr Salim na san cewar Prof Abas ya biyaka kud'i mai yawa sosai, ta yanda ba zaka sanar da kowa ba wannan sirrin amma na tabbata basu kai, rayuwar jikar ka ba wacce a yanzu haka bata makaranta. Sannan kuma bata gida Allah sarki 'yar talika ko tana ina? Gata kuma bata da lafiya to ko mai zai faru da ita yanzu? Zunubin Kakan ta ne ya shafe ta amma k'ila Kakan ta zai iya ceton rayuwar ta, ko kuma dai ya cutar da ita ta hanyar rashin fad'ar gaskiyar abin dana tambiye sa. Ni zan tafi ga kati na idan ka shirya magana to sai ka kira ni sai an jima."
Ya yunk'ura zai tashi da sauri Dr Salim ya dakatar da shi. "A'a karka saka jikata a cikin wannan ita ďin bata da lafiya sosai, sannan kuma d'ana ba zai jure ganin 'yarsa cikin k'unci ba, ya jima sosai kafin ya aihu yana san 'yarsa sosai. To naro e ka ka da ka cutar da ita dan Allah." "Eh na san da duka wannan amma kuma ni a gurin ka na koyi wannan, yanda a ke raba uwa da yaranta to kawai ka shirya yanda zaka fuskanci yaronka sai an jima." "A'a dan Allah yanzu fad'a min mai kake so.?" "kawai ka sanar da ni gaskiyar abin da yake tsakanin ka da Prof Abas." Ba shi da wani zab'i wanda wannan dalilin ne yasa dole ya sanar da shi komai. "Shikenan yanzu zamu tafi can gidan narayun domin na tabbatar da abin da kake fad'a."
Ya amsa shi da to sun tashi sun nufi gidan marayu, sun isa gidan ba jimawa suka had'u da shugaban gidan, bayan sun gaisa Dr Salim yaci gaba da magana. "Alh Mansoor munzo ne a kan wasu yara wad'an da ni na kawo su nan." Nan kuwa ya shiga sanar da shi komai ya jinjina ka sannan daga bisani ya amsa shi. "Eh na tuna da komai amma tin a cikin satin wasu ma'aurata suka d'auki yaran raino, to gaskiya ba zamu iya sanar daku komai a game da yaron ba kuyi hak'uri." Cikin hanzari *Adnan* ya amsa shi da cewa. "Am dan Allah ko ka san address ďin gidan su dan Allah ka sanar damu please.?" Ya amsa shi da eh nan kuwa yasa a ka duba musu address ďin tare da sanar dasu.
Sunyi masa godiya sannan suka tafi suka fita kai tsaye gidan su Anas suka nufa, sai dai sunyi rashin sa'a sabo da an sanar dasu cewar, sun bar nan tin shekaru ashirin da biyar da suka wuce, ba kuma wanda ya san inda suka koma suna tsaye jikin mota Dr Salim ya anbaci sunan *Adnan.* *"Barrister Adnan* to zuwa yanzu ya kamata ka sanar da ni inda jikata take.?" *Adnan* yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Dr Salim ni ba kamar kai bane da kake cutar da yara ba ta hanyar raba su da mahaifiyar su, jikar ka tana gida ni kawai nayi anfani da raunin ka ne domin na san gaskiyar, yanzu zaka iya magana da yaronka domin ka tabbatar da gaskiyar sai an jima."
Yana kai k'arshen maganar sa ya juya ya shiga mota, hakama Dr Salim shi ma zagawa yayi ya shiga mota sun fice, *Adnan* ya sauke shi office sannan ya wuce ya koma masauki. Inda kuma ya shiga sanar da *Adyan* komai daya faru ya amsa shi yana cewa. "Am Aboki ya kamata mu had'u da wannan matar sabo da ita kawai ce bata sanar damu, gaskiyar gaba ďaya ina nufin yanda a kayi mu biyun muka rabu da juna, da kuma yanda iyayenmu suka had'u damu dole ita kad'ai ce zata amsa mana wannan." "Eh Aboki nima ina tare da burin haka zanci gaba da nai man ta." Sunci gaba da magana na wani lokaci sannan daga bisani suka yi sallama, washe garin ranar *Adnan* ya koma gida bayan kwana biyu, wani yammaci zaune suke suna fira *Adeel* ya kai kallonsa ga *Adnan* tare da fad'ar sunan sa.
*"Adnan* da akwai abin da nake san na nai ma a gurin ka." *"Adeel* kawai ka sanar da ni koma miye." *"Adnan* dan Allah idan kana da dama ina san gobe zaka raka ni jigawa, zamu tafi na had'aka da *Amna* ita ďin budurwa ta ce, to ina fatan zaka amince da wannan tayin nawa dan Allah." *Adnan* yayi murmushi sosai mai tare da dariya sannan ya amsa shi. "Shikenan zamu tafi tare insha Allah." Yayi murmushi sosai tare da furta masa kalmar na gode sosai, murmushi kawai yayi masa ba tare daya furta masa komai ba. Hakan kuwa ta kasance washe gari suka kama hanyar jigawa gurin *Amna,* sunyi nasaran sauka lafiya *Amna* ta shiga yi musu sannu da zuwa, sai wani nan-nan take dasu yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare da ita, bayan sun gaisa *Adeel* ya shiga gabatar da *Adnan* gareta.
Sun k'ara gaisawa