Showing 51001 words to 54000 words out of 142761 words

Chapter 18 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

min to kawai ka dena, daga k'arshe kuma ni *Amna Anas* na amince da kai a matsayin mujin da zan aura insha Allah, ina sanka *Adeel* wallahi ina matuqar masifar qaunarka sosai fiye ma da yanda nake sanka to zan aure ka insha Allah." "Na gode *Amna* na gode sosai." "Godiya kuma to a kan me.?" "A kan komai." Murmushi kawai tayi masa ba tare data furta masa komai ba sai daga bisani ta anbaci sunan sa. *"Adeel* ko zaka dena wannan yawan godiyar dan Allah.?" Kallonta kawai yake yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi, ita ma abin da take yi kenan bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin suci abinci. Sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa suka tashi suka fita zuwa wani guri daban, wanda ya d'auke su na tsayin wani lokaci sai dare sannan suka dawo gida. *Adeel* ya samu tsayin kwana hud'u sannan ya koma gida,

*England*

Zaune yake yana dannar waya yaji a na buga masa k'ofa daga ciki ya amsa da shigo, sannu a hankali take turo k'ofar har ta bud'e ta shigo tare da isa inda yake ya a jiye wayar tare da kai kallonsa gareta. "Ki zauna." Ta amsa da to ta zauna yaci gaba da magana, "mai yake tafe dake? Amma ki fara da fad'ar sunan ki." Magana take cikin wani irin yanayi na rashin lafiya, "am sunana Ahlam." Kafin ta qarasa ya sauke mata tafi cike da 'bacin rai yake magana. "Ke har kinma isa ki shigo har cikin office d'ina sannan ki zagen? Ki bar nan tashi ki fita tashi man ko baki ji bane nace ki bar nan." Magana yake cikin fishi sosai cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. "Doctor wai a kan me kake magana yaushe ni na zageka? Ni kawai nayi abin daka fad'a ne ka tambayi sunana na kuma amsa ma da Ahlam amma." Saukan marin data koma ji ne yasa ta yin shiru, "nace ki tafi to mai ya saka har yanzu kike zaune a nan kawai ki tafi ki bar nan." Ya fad'a tare da buga tebur ďin da yake kusa da shi magana yake cikin fishi sosai, wanda har waje a na jiyo ihun sa nurse ďin dake wajen office ďin sa sun shiga ciki dan ganin abin da yake faruwa.

Sun same su suna ta sa in sa Jams ya fita da sauri ya nufi office ďin Appa ya sanar da shi abin da yake faruwa, da sauri ya tashi sun dawo tare sun kuma samu har zuwa wannan lokacin fad'a yake da ita. *"Adyan* mai yake faruwa ne a nan.?" "Appa ni ina ta k'oqarin ganin na taimake ta amma ita kuma zagina take, shi yasa nace ta tafi kuma tak'i sai ganin laifi na take sabo da na mare ta." Cike da firgicin abin daya fad'a Appa yake magana. *"Adyan* wai mai ka aikata ne haka taya ma har zaka yi tinanin marin ta? Sam bai kamata kai kayi hakan ba amma har yanzu kana da dama to kawai kai ka bata hak'uri ka ji ko." Wani irin kallo yake yiwa Appa mai cike da jin mamakin sa sosai ya girgiza ka yana cewa. "Appa taya ma wai kai zaka fad'i haka? Ita fa Ammie na ta zaga amma kuma duk da haka sai kake tinanin cewar ni zan bata hak'uri, a'a ni sam ba zan ta'ba hak'uri ba da a ce ita ďin bata zagi Ammie na ba to da duka wannan bai faru ba." "Shikenan karka bani hak'uri amma ka sani zanyi k'aran ka to kawai ka shirya wa hukuncin ni zan tafi." Ta juya zata tafi yayi saurin dakatar da ita ta hanyar rik'o hanun ta yana cewa.

"Wai ke barazana kike yi man? Kin kuwa san da wanda kike yiwa barazana shin kin san da wanda kike tsaye gaban sa a yanzu? To ki sani barazanar ki ba zata yi wani tasiri a tare ni ba, idan har a game da Ammie na ne to a shirye nake da d'aukan ko wane irin hukunci to yanzu zaki iya tafiya." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake mata hanu tana k'oqarin tafiya Appa ya dakatar da ita ta hanyar shan gaban ta yana cewa. "A'a dan Allah karki yi ni zan baki hak'uri a madadin sa shin hakan ya maki.?" Da sauri *Adyan* yace, "a'a Appa hakan ba zai faru ba ni ba zan ta'ba barin kai ka aikata hakan ba to ni zanyi zan bata hak'uri." Nan kuwa ya shiga bata hak'uri ya kuma qara da cewa, "tabbas wata rana sai kinyi matuqar nadama sosai a kan hakan, na tabbata ranar zata zo kuma zaki fad'i a kan qafata sannan kuma ki bani hak'uri, to yanzu zaki iya tafiya sannan kuma ki jira zuwan ranar kinji ko."

"Taya ni zan tafi ba kuma tare daka duba ni ba, zan tafi ne kawai idan har kai ka duba ni." Sam bai iya amsa ta ba sai ma juya wa da yayi ya fice daga office ďin, Appa ne wanda ya duba ta tare da qara bata hak'uri sannan ta tafi, bayan tafiyar ta shi ma tashi yayi ya nufi gida domin yana da tabbacin cewa yaronsa yana gida. Tsaye take tana shirya abinci a kan tebur lokaci d'aya taji a na buga mata k'ofa cike da d'auki ta nufi k'ofar tare da bud'e wa, ta samu Appa tsaye a gefen k'ofa sun rungumi juna tare da sunbatar juna sannan ya shiga ciki. Kai tsaye bedroom d'in *Adyan* ya nufa da sauri har yana gudu yayin da bakin sa yake fad'ar sunan sa, cike da firgici da rud'ani tare da jin mamakin Ahlam ta isa inda yake tana fad'ar sunan sa..............





*BY B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/16, 12:26 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 21*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Friday 14/01/2022*

*Time 07:10pm*

*Typing................*

"Yaya Ahmad wai mai yake faruwa ne ina *Adyan.?"* Wani irin kallo yake yi mata mai cike da jin mamakin abin da ta tambaya. "Ahlam karki fad'a min cewar *Adyan* bai ya gidan nan.?" Ta jinjina masa ka tare da furta eh, "miye to yana ina wane gun ya tafi kuma? Hakan yana nufin cewar yayi fishi sosai, *Adyan* mai ya saka ba zaka fahimci abin da nake nufi ba? Ni kawai bana san ka shiga a matsala ne amma kuma kai sam ka gagara fahimta na. Yanzu kana ina ya kamata na had'u da kai to amma kuma ban san inda kai ka tafi ba, *Adyan* kana ina? Dan Allah ka dawo gareni sannan kuma ka dena fishi da ni haka." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Ya ciro wayar sa ya shiga kiran layin sa sai dai kuma yayi rashin sa'a domin kuwa zuwa wannan lokacin wayar sa a kashe take, hakan ya qara d'aga hankalin sa sosai. "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un *Adyan* mai ya saka zaka kashe wayar ka? Sam bai kamata kayi hakan ba ya kamata na nai meka ina fatan nayi nasaran ganin ka." Ya juya zai fita da sauri Ahlam ta dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa cike da damuwa take magana. "Fad'a min ina *Adyan* sannan kuma mai ya faru da shi.?" Ba shi da wani za'bi shi yasa ya sanar da ita gaba d'aya gaskiyar, "wallahi tallahi ba zan ta'ba gafarta mata ba idan har wani abu ya faru da yarona." "Ba abin da zai faru da shi na maki alkawari zan dawo da shi gida cikin k'oshin lafiya insha Allah, to zaki iya yarda da ni kinji ko to ki kula sosai sai na dawo."

Ta jinjina masa ka shi kuma ya juya ya fita ita kuwa ta bisa da kallo har ta fice, yayin da tinanin yaronta yayi yawan gaske a tare da ita sosai, lokaci d'aya damuwa ta shigeta sosai bata ankara ba idanuwan ta suka fara zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo ta d'auki wayar ta nan ta shiga kiran layin Kamela. Ba jimawa ta d'aga tare da gaishe ta ta amsa taci gaba da magana. "Kamela shin kina tare da *Adyan* ne.?" "A'a Ammie ba jimawa na ga ya fita cikin fishi sosai, nayi k'oqarin bin bayan sa amma sai ya dakatar da ni ya tafi shi kad'ai." "Kamela amma baki san wani gurin da zai iya tafiya.?" "A'a gaskiya ban sani ba." "Shikenan na gode sosai." Da kuma haka suka yi sallama, Ammie tayi shiru sai nazari take da tinani ta shiga kiran layin Appa ba jimawa ya d'aga. "Hellow Yaya Ahmad shin ka samu had'uwa da *Adyan* kuwa.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa ta, "a'a har yanzu amma zan gano sa insha Allah zaki iya yarda da ni please." "Yaya Ahmad to mai yasa ba zamu sanar da 'yan sanda ba.?"

"A'a ba zamu sanar da 'yan sanda ba sabo da bai kamata su san da gaskiyar ba." "Amma Yaya Ahmad nifa ina jin tsoro kar wani abu ya faru da shi, ka riga da ka san komai a game da shi da kuma lafiyar sa to ya kamata mu san inda yake. Ya kamata ya dawo gida ina buqatar yarona ya dawo gida ina buqatar sa sosai." Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa ta, "Ahlam nima abin da nake buqata kenan zanyi komai domin ganin yaronmu ya dawo gida kinji ko." Ta amsa shi da to sunyi sallama tayi zaune tana kuka, haka Appa yayi ta yawo yana nai man yaronsa, ya jima sosai yana nai man sa daga bisani Jey ya kira layin Appa ya sanar da shi cewar ya ga *Adyan* cikin rawar murya yake amsa shi. "Jey yana ina.?" "Yana gurin kallon boll." "Na gode sosai Jey." Da kuma haka suka yi sallama Appa ya juya ya nufi inda zai had'u da yaronsa, ya isa gurin tare da shiga ciki sai wani zaran ido yake yana fad'ar sunan yaronsa ya jima a haka sannan daga bisani ya iya ganin sa. Cikin hanzari ya isa garesa cike da d'aukin ganin sa yayi hugging d'in sa sai wani sunbatarsa yake fuska zuwa wuya, shi kuwa sai wani kallonsa yake bayan ya sake sa ya anbaci sunan sa yana cewa.

"Rabin raina shin kai kana fishi da Appa ne.?" Shiru bai amsa shi ba sai kallonsa kawai yake shi ma kallonsa yake kallo sosai, *"Adyan* shin ba zaka yi man magana ba? Dan Allah karka cutar da ni ta wannan hanyar sabo da ba zan iya d'auka ba, masoyi shin zamu iya tafiya gida yanzu domin muyi magana a can dan Allah.?" Sam bai iya amsa shi ba sai dai ya jinjina masa ka a lamar to, "Yauwa rabin raina yaron kirki mu tafi." Ya fad'a tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar ina sanka sosai yarona. Ya rungumasa jikin sa har bakin mota sai da ya shiga mota sannan ya tafi ya shiga tashi motar suka tafi, sun isa gida tare da shiga ciki sun samu Ammie cikin wani irin yanayi mara dad'i, cike da d'aukin ganin sa ta nufi inda yake tana fad'ar sunan sa tana isa inda yake tayi hugging d'in sa tana sunbatarsa fuska zuwa wuya. *"Adyan* qlau kake kuwa fad'a min shin kai kana lafiya kuwa? Ni na damu sosai a kanka na gode Allah da ba wani abin daya faru da kai, yanzu fad'a min wani abu shin qlau kake kuma gaskiyar zaka fad'a.?"

"Ammie ni ina lafiya ina san zan shiga ciki zamu yi magana an jima." "Shikenan ďana ka kula sosai sannan kuma idan kana buqatar wani abu to kawai ka sanar da ni ka ji ko." Ya jinjina mata ka a lamar to ya juya ya nufi bedroom d'in sa Appa ya dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa, *"Adyan* shin wai har tsayin wane lokaci zaka d'auka kana fishi da ni sosai haka? *Adyan* na fad'a maka cewar ni ba zan iya d'aukar wannan ba to dan Allah ka yafemin please." Ya mai da kallonsa ga Appa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna ya nufi inda yake yana fad'ar sunan sa. "Appa ni sam bana fishi da kai sannan kuma ni ba zan ta'ba hukunta ka ta wannan hanyar ba, Appa ni kawai naji wani iri ne sannan kuma naji ba dad'i sosai daka saka na bata hak'uri. Ita ta zagi Ammie na amma kuma duk da haka kai ka saka ni na bata hak'uri hakan yayi matuqar saka ni takaici da k'unci sosai, amma kuma hakan sam bai ya nufin cewar ni ina fishi da kai, a'a ni ba zan ta'ba aikata wannan mummunan zunubin ba, ka yafemin da nasa ka ji wani iri sosai a kan hakan kayi hak'uri." Da sauri Appa ya rufe masa baki yana girgiza masa ka tare da furta.

"A'a rabin raina sam ba buqatar ka bani hak'uri sabo da ba kayi komai ba, *Adyan* na san cewar kai ka damu sosai a kan ni da kuma Ammie kana matuqar qaunar mu sosai. Amma kuma hakan ba zai saka mu canja gaskiyar ba, ita wannan matar sunan ta kawai ta fad'a to sam bai kamata kayi fishi ba, ko ba komai hakan zai iya cutar da lafiyar ka sosai wanda kuma hakan zai cutar damu sosai. Masoyi gaskiyar ita ce mu mun damu sosai a kanka da kuma lafiyar ka dalilin da yasa nake duka wannan kenan, *Adyan* kai ďana ne kuma abin da nafi so fiye da komai to zanyi komai sabo da kai, ina sanka sosai yarona kai ba kawai d'ana bane a'a kai rayuwata ne gaba d'aya, kai ne a salin farin ciki na k'uncin ka shi ne babban rashin hankali kuma qalubale ga rayuwa ta. To ina fatan zaka fahimce ni sannan kuma kayi min uzuri a game da abin dana saka ka aikata a yau ďin nan please."

Cike da qaunar sa yayi hugging d'in sa yayin da bakin sa yake furta, "ina sanka Appa ina matuqar masifar qaunarka sosai fiye ma da yanda nake sanka ina qaunarka sosai Appa." Abin da yake ta fad'a kenan shi ma haka tare da qara saka shi jikin sa yana sunbatarsa, Ahlam tana daga gefe tana kallonsu yayin da take jin suna birgeta sosai, ta isa inda suke tare da shiga jikin Ahmad tare da sunbatar yaronta tana furta masa kalmar ina qaunarka ďana. Ya amsa ta yana murmushi sun jima a haka sannan suka sake juna suna k'oqarin zama Ahlam ta dakatar dasu ta hanyar fad'ar sunan *Adyan.* "Rabin raina yanzu lokacin cin abinci ne to kawai mu tafi muci abinci Yaya Ahmad mu tafi." lokaci d'aya *Adyan* ya 'bata fuska yana fishi kafin ya furta komai tayi masa rigagi. "Kayi hak'uri na dena ba zan k'ara kiran sa da wannan sunan ba, nayi alkawari insha Allah to zaka iya yarda da ni please."

Magana take tana wani shafar kansa zuwa fuskarsa tare da sunbatarsa, Ahmad yana daga gefe yana kallonsu yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa sosai, ya jinjina mata ka a lamar to yana murmushi sun juya dukansu sun nufi tebur domin suci abinci. Sun isa ga tebur Ahlam taja musu kujera sun zauna ta fara zuba abincin sannan ta zauna suka fara cin abinci, bayan sun qarasa *Adyan* ya nufi bedroom d'in sa sun bisa da kallo har ya shige suna murmushi, sun dawo da kallonsu ga juna lokaci d'aya suka sakarwa juna murmushi mai tare da dariya. *"Abban Adyan* ko nace Appa kai kana da kirki sosai kuma zan iya kiran dana musamman, hak'iqa kai alkhairi ne a gareni dama rayuwa ta gaba d'aya ina qaunarka sosai Mujina *Abban Adyan."*

Cike da d'auki yayi hugging d'in ta ya k'ara da sunbatarta, "abin da nake koqarin fad'a maki kenan sai kuma ke kika yi min rigagi, amma duk da haka da akwai buqatar na sanar dake wani abu, abin shi ne har kawo yanzu zuciyar Ahmad tana qaunar ki sosai kamar dai a ranar farko, alkawarin da zanyi maki shi ne ni Ahmad Aliyu zanci gaba da sanki tare da baki cikakkiyar kulawa sosai, har zuwa lokacin da zanyi numfashi na na k'arshe." "Na gode sosai Mujina am ko zamu iya shiga ciki sabo ina buqatar wani abu daga gareka yanzu.?" Ya jinjina mata ka a lamar eh yana murmushi ita ma abin da take yi kenan sun juya sun shiga ciki, yana shiga ciki ya nufi inda laptop ďin sa ya d'auka ya nufi gado ya kwanta. Ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login