Showing 108001 words to 111000 words out of 142761 words
Chapter 37 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
bayan sun qarasa gaisawa *Adeel* ya shiga tambayar su Mama tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi. *"Adeel* ka riga da ka san komai a game da ita, kamar dai kullum yau ma sam bata cikin kyakkyawan yanayi, tin data samu labarin cewa an kashe wasu 'yan fashi, take cikin wannan mummunan yanayin wanda har sai da ciwan zuciyar ta ya tashi. Wanda har sai data kwana biyu asibiti jiya da yamma muka dawo gida, amma har yanzu bata cikin kyakkyawan yanayi Abba yana kulawa da ita sosai." Cike da jin mamakin abin data fad'a *Adnan* yake magana.
*"Amna* amma mai ya saka ta damu sosai a kan wad'an nan 'yan ta'addan da a ka kashe shin da akwai wanda ta sani ne.?" "A'a ita kawai ta damu ne a kan yayuna wad'an da 'yan fashi suka sace daga garemu." Nan kuwa ta shiga sanar da shi komai kamar dai yanda iyayen ta suka sanar da ita. *"Adnan* dukansu sun damu ne sosai sabo da muna tsoron kar twin's su kasance a cikin su, sabo da bamu da sani a game dasu wannan yafi komai cutarwa,, mun rayu ne tare da tunanin cewar wata rana zasu dawo garemu, amma har yanzu ba wani labari a game dasu suna raye ko a'a suna tare da 'yan fashin bamu sani ba.?"
"Shin sun samu kub'uta daga garesu idan sun kub'uta to suna ina dawa suke tare? Shin sun samu kyakkyawar rayuwa kuma ingantaciya suna farin ciki kuwa bamu sani ba? Tuna hakan kawai yana saka mu kuka sosai ni ban tab'a sanin yayuna ba sai a photo, amma kuma hakan sam bai hana ni sansu ba ina matuqar qaunar su sosai. Ina fatan zuwan lokacin da zasu dawo garemu ta yanda ahalinmu zai k'ara cika sannan kuma." Kuka yaci k'arfin ta tayi shiru ta kama aikin kuka, cike da qauna da soyayya tare da jin tausayin ta *Adeel* ya shiga rarrashin ta, cikin mutuwar jiki da sanyin murya tare da jin tausayin ta sosai *Adnan* yake magana............
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/28, 3:52 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: ✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 44*
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Wednesday 16/02/2022*
*Time 11:46pm*
*Typing............*
*Alhamdulallah munyi hidima lafiya mun k'arasa lafiya, Amarya da Ango Allah ya ba da zaman lafiya da zuri'a d'ayiba, Allah ya kau da shaid'an a tsakanin ku Allah yasa mutuwa ce zata raba Allahumma Amin ya hayyu ya kayyum.*
*To mu tai zuwa dan jin yanda zata kasance dasu.*
"Kiyi hak'uri amma kuna nai man yaran kuwa.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh yaci gaba da magana. "To amma wane ci gaba a ka samu.?" "Ba wani ci gaba sabo da har yanzu ba wani labari a game dasu." *"Amna* Shin ko zan iya ganin photon twin's dan Allah.?" Ta jinjina masa ka tare dayi masa nuni da gefen da photon yake, ya kai kallonsa ga inda tayi masa nuni da shi sai wani kallon photon yake kallo sosai. Ya tashi daga inda yake ya nufi gurin photon yake yayin da yake magana da zuciyarsa. Tabbas ni ne a cikin wannan photon hakan yana nufin cewar wannan Aboki ne, Allah sarki Mama ta rayu gaba d'aya cikin k'uncin rashin ni da Aboki, dukansu ahalin suna da kirki sosai suna qaunarmu fiye ma da yanda suke sanmu. Ya kamata na had'u da dukansu biyun Mama da kuma Abba a yanzu." Ya mai da kallonsa gasu *Adeel* lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar suma kallonsa suke kafin ya furta komai *Amna* ta anbaci sunan sa. *"Adnan* lafiya kamar dai kai baka cikin kyakkyawan yanayi shin qlau kake kuwa.?" "Eh *Amna* qlau nake kawai dai na damu ne a game da twin's sabo da sunyi matuqar bani tausayi sosai, *Amna* dan Allah ko zan iya ganin iyayen ki da akwai abin da nake san na tambiye su please.?"
*"Adnan* abin sam ba shi da sauki kamar yanda kake tunani, ita Maman twin's bata cikin kyakkyawan yanayi hakama Abba, to sam bana jin cewar su biyun zasu saurari wani abu daga gareni, amma duk da haka zan gwada insha Allah zan dawo yanzu." Ta tashi ta nufi bedroom d'in Mama su kuwa sun bita da kallo har ta shige, bayan wani lokaci ta fito tayi shiru kad'an sannan ta fara magana. *"Adnan* kayi hak'uri sabo da sam basu aminta da tayin ka ba." Yayi shiru kad'an sannan ta tashi ta nufi bedroom d'in sun bisa da kallo, *Amna* zata dakatar da shi *Adeel* ya shiga girgiza mata ka a lamar a'a, ya isa ga k'ofar tare da bud'e k'ofar ya shiga ciki.
Tare da kyakkyawar sallama lokaci ďaya ta suka kai kallonsu garesa, sunyi ido biyu da juna kasancewar shi ma kallonsu yake, sannu ahankali yake tafiya har ya k'arasa inda suke, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallon juna suke, kafin ya furta komai Abba yayi masa rigagi yana cewa. "Waye kai mai kuma kake a nan.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi cikin kwantar da murya yake magana. "Am sunana *Adnan Adam Muh'd* ni abokin *Adeel ne Amna* ta sanar da ni, komai a game da twin's to ina ga zan iya taimaka wa domin gano twin's. Sabo da har yanzu yaran suna raye sannan kuma daf suke dasu dawo gareku, to sam ba buqatar kuci gaba da kasancewa cikin wannan mummunan yanayin. Sabo da hakan yana matuqar cutar da masoyan ku sosai, to ya kamata ku dena wannan k'uncin domin ku samu ku rayu cikin farin ciki na har abada dan Allah."
Tin daya fara magana suke kallonsa har ya kai natsaya, cike da jin mamakin sa sosai Mama take magana. "Barrister shin kai ka san wani abu a game da yarana dan Allah ka sanar da ni please.?" "Eh na tab'a jin labarin wasu twin's da suka b'ata to ina fatan su kasance yaranku ne." "A wane gurin? Ya kamata mu tafi can yanzu sabo da ina buqatar na had'u da yarona." "Ba zai yu mu tafi yanzu ba sabo da ina san nayi binkice a kan lamarin, sannan kuma na k'ara sanin wani abu a game dasu, shin zaku sanar da ni wani abu a game da yaranku.?" Sun amsa shi da eh ai kuwa nan suka shiga sanar da shi komai, ta yanda suka rasa yaransu shi kuwa sai wani kallonsu yake, yayin da tausayin su yayi yawan gaske a tare da shi sosai.
"Karku wani damu ni nayi muku alkawarin cewa twin's zasu dawo gareku insha Allah." "Mun gode sosai Allah ya ma albarka ya kuma albarkaci rayuwarka Amin." Ya amsa da Amin yana wani gajeran murmushi ba jimawa suka tashi, suka fita babban parlour sun gaisa da *Adeel* sannan suka nufi k'aramin parlour, bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin cin abinci, suna cikin cin abinci *Adeel* ya sauke kallonsa ga fuskar *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* qlau kake kuwa.?" Ya girgiza masa ka tare da furta ba komai, *"Adnan* dan Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai.?" "Ba komai *Adnan* kawai dai na damu ne a game dasu Mama, yanayin su yana da matuqar ban tausayi sosai." *"Adnan* kai kana da kirki sosai sannan kuma ka damu da damuwar kowa, kai kana da halaiya masu kyau sosai na gode sosai da kulawar ka a kan iyayena." Yayi wani gajeran murmushi sannan ya amsa ta. "Ba komai Sister Mama da Abba kamar iyayena suke to zanyi komai sabo dasu insha Allah."
Murmushi kawai tayi masa hakama *Adeel* abin da yake yi kenan, bayan sun kammala sun koma parlour sunci gaba da fira cikin kyakkyawan yanayi, sai yamma sannan suka kama hanyar kaduna sunyi nasaran sauka lafiya. Kai tsaye gidan su Papa suka nufa *Adeel* ya sauke *Adnan* sannan ya nufi gida. Da dare bayan *Afnan* tayi barci *Adnan* ya kira layin *Adyan,* ya shiga sanar da shi komai a game dasu Mama wato iyayen *Amna.* "Aboki dukansu ahalin sun damu sosai a kanmu musamman ma Mama gaskiya na tausaya wa dukansu sosai. To yanzu mai ya kamata muyi shin zamu iya sanar dasu gaskiyar a game damu? Sabo dasu dena damuwa a kanmu domin ko ba komai zasu rayu cikin farin ciki sosai."
"A'a Aboki ba zai yu mu sanar dasu gaskiyar ba, sabo da hakan zai iya b'ata komai wanda kuma dukanmu ba zamu so hakan ba. To ya kamata kayi tunani a kan iyayenmu, sabo da wannan shi ne abin da yafi komai muhimmanci a garemu dan haka ya zama dole mu b'oye gaskiyar ka ji ko." "Amma Aboki yanayin su Mama yayi tsauri sosai kuma hakan yana matuqar cutar dasu sosai, Aboki su ďin fa masoyan mu ne to bai kamata mu barsu a cikin irin wannan mummunan yanayin ba, bayan kuma muna da damar da zamu iya taimaka wa to ya kamata muyi abin daya dace." "Eh Aboki gaskiyar ka fad'a amma zamu yi magana a game da wannan bayan na dawo, jibi zamu dawo kaduna insha Allah fatan kana kulamin da *Adlishart* sosai.?" "Eh ina yi ina farin ciki da zuwan ku Allah ya kawoku lafiya, Aboki shin ba zaka tambayi Mum ba.?" "Dama yanzu nake shirin na tambiye ta to ya take fatan tana tafiya.?"
"Eh tana lafiya." Haka suka ci gaba da fira na tsayin wani lokaci sannan daga bisani suka yi sallama, bayan kwana biyu su Appa suka dawo kaduna tin a ranar *Adyan* ya d'auki *Alishart* zuwa gidan Abbu. Wani yammaci zaune suke suna fira *Adeel* ya kai kallonsa ga Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum gobe zanyi tafiya insha Allah." "Rabin raina ina zaka tafi ne shin zan iya sani.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta. "Mum ina san zan tafi jos ne gurin Dady." Kallonsa kawai take ba tare data furta masa komai ba, shi ma haka kallonta yake ya nisa tare da jan numfashi sannan taci gaba da magana. "Mum dan Allah karki saka damuwa a ranki wani abu yazo ya faru dake, wanda hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai sannan kuma ba zan wani jima ba zan dawo gareki insha Allah."
"D'ana ni kawai na damu ne a kanka sabo da ina tsoron kar ya cutar da kai. Sabo da shi ďin tamkar maciji ne zai iya cutar da duk wanda ya rab'esa, to sam bana san ya cutar da kai kamar dai yanda ya min, musamman ma yanzu daya san cewar kana tare da ni d'ana ni na kasa yarda da zuciyata sabo da." "A'a Mum sam ba abin da zai faru da ni sabo da Dady na yana qaunata sosai, na tabbata ba zai tab'a cutar da ni ba to zaki iya yarda da ni dan Allah." Ta jinjina masa ka a lamar to yayi murmushi sosai tare da yin hugging d'in ta, Umma na daga gefe zaune tana kallonsu yayin da fuskar ta take fitar da murmushi. Sunci gaba da fira na tsayin wani lokaci sannan ya tashi ya fita, hakan kuwa ta kasance washe gari bayan sun qarasa break past *Adeel* ya kama hanyar Jos. Yayi nasaran isa garin Jos lafiya ya nufi gida ya isa gidan bayan sun gaisa da Audu yaci gaba da magana.
*"Adeel* Dadyn ka baya nan." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Audu ina kuma ya tafi.?" *"Adeel* labari ne mai tsayi bayan tafiyar ka komai ya lalace, babban campaning sa yayi gobara to ba wannan bane abin damuwar ba, *Adeel* wad'an da suke da hanun jari a campaning sun kasa amincewa da kaddaran data faru. Wanda har sunyi k'aransa a kan sai ya biyasu kud'ad'ensu." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Audu yaushe hakan ta faru yanzu fad'a min ina Dady na yake.?" "Yana kaduna a can ne suke shari'a." Ya fara da karb'ar number Dady ga Audu sannan ya juya ya shiga mota, ya kama hanyar komawa kaduna misalin k'arfe 08:00pm ya isa garin kaduna. Cikin hanzari ya shiga kiran layin Dady ba jimawa ya d'aga, ba tare daya furta komai ba cikin wata 'yar murya yake fad'ar sunan sa.
"Dady kana ina ya kamata mu had'u yanzu.?" *"Adeel* ďana da gaske kai zaka had'u da ni.?" "Eh Dady kawai ka sanar da ni kana ina.?" "Rabin raina ina Rahma hotel room 224." Ya amsa da ok sunyi sallama yaja mota ya fice, ya isa hotel ďin cikin hanzari ya nufi d'akin da yake, yana zaune ya ji a na buga masa k'ofa ya tashi ya tafi ya bud'e, kamar da wasa ya samu *Adeel* k'ofa cike da d'aukin ganin sa, Dady yayi hugging d'in sa yana sunbatarsa ya janyo sa sun shiga ciki. "Nayi matuqar yin kewarka sosai ďana nayi farin ciki sosai daka yanke shawaran dawowa gareni."
"Dady kayi hak'uri dan Allah ka yafemin, na san cewar na cutar da kai sosai da rashina amma." "A'a ďana karka bani hak'uri sabo da baka yi komai, to ba buqatar sai ka bani hak'uri to ya jikin Mummyn ka.?" "Ta samu sauk'i sosai sabo da zuwa yanzu ta dawo haiyacinta, Dady na ji duk abin daya faru a gurin Audu to ina san zan taimaka." "A'a ďana ni sam bana san ka shiga cikin wannan ka ji ko." "Dady ni ba zan zuba ido na barka ba tare da nayi komai ba, sam bai kamata su Uncle Bashir suyi maka haka ba, amma ba komai zamu samu mafuta insha Allah da akwai wani Abokina, shi ďin Barrister ne kuma yana da kirki sosai sannan kuma zai taimaka sosai insha Allah. To yanzu ya kamata na tafi nayi magana da shi sai na dawo." "Na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka." Ya fad'a tare da sunbatarsa shi kuwa ya amsa da Amin yana murmushi.
Ya tashi ya fita Dady ya bisa da kallo yana murmushi, tin a mota *Adeel* ya kira layin *Adnan* tare da tambayar sa yana ina, ya amsa shi da cewa yana gidan Abbu tare da *Adyan* ya amsa da ok sunyi sallama. Ya nufi can ya isa gidan ya same su wani kyakkyawan guri, wanda an yi sane musamman sabo da hutawa ya samu guri ya zauna, bayan sun gaisa *Adeel* ya sauke kallonsa ga fuskar *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. *"Adnan* ina buqatar taimakon gaugawa sosai daga gareka." *"Adeel* kawai ka sanar da ni koma miye ni kuma zanyi nayi alkawari fad'a min miye.?" Nan kuwa ya shiga sanar da shi buqatar shi garesa. Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, "kayi hak'uri *Adeel* sabo da ni ba zan iya taimaka wa Dadyn ka ba." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. *"Adnan* mai ya saka ba zaka taimaki Dady na ba.?" Ya girgiza ka tare da furta ba komai, "Shikenan na gode sosai sai an jima." Yana kai k'arshen maganar sa ya tashi yayi tafiyarsa, su kuwa sun bisa da kallo har ya b'ace............................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/3, 11:15 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 25*
*Sister Fatima Allah ya baki lafiya ya bawa Babyn ki lafiya.*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Monday 28/02/2022*
*Time 08:16pm*
*Typing.................*
Bayan tafiyar su sun dawo da kallonsu ga juna, *Adyan* ya shiga tambayar *Adnan* abin da yake faruwa. Yayi shiru kad'an sannan ya sanar da shi abin da yake faruwa, *Adyan*