Showing 48001 words to 51000 words out of 142761 words
Chapter 17 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
da to yana murmushi.
Ya tashi ya shiga toilet ita kuma ta gyara masa d'aki sannan ta fice daga d'akin. Ta fito ta samu su Papa a parlour suna ta fira abinsu ta zauna Mamie ta shiga tambayar *Adnan,* "Mamie da kyar na samu ya iya tashi yanzu dai ya shiga wanka." *"Afnan* da baki tashe sa ba sabo na na qara masa lokaci wanda nake tinanin zai ishe sa." "Eh haka ya fad'a min bayan na tashe sa." "Shikenan hakan ma daidai ne." Bai wani jima ba ya fito ya shirya cikin wata kyakkyawar shiga ta qananan kaya, shigar tayi matuqar amsar sa sosai sai wani k'amshi yake mai dad'in shaqa ya d'auki rigar aiki da hula tare da takardu ya fita. Ya fito ya same su a parlour sai fira suke cikin raha wasa da dariya ya tafi ya zauna, bayan sun gaisa sun tashi sun nufi tebur domin suyi break past. Sunci abinci cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa su Papa sun fita zuwa office, Papa ya fara a jiye *Alishart* school sannan ya nufi kotu. Zaune take tana danna waya ga a lama charting take Abban ta ya fito ta shiga yi masa sannu da fitowa, ya amsa yana murmushi tare da sanya mata albarka yaci gaba da magana.
*"Amna* ina Maman ki.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi. "Abba tana bedroom ďin ta sannan kuma bata cikin kyakkyawan yanayi, ka riga da ka san komai a game da damuwar ta tana cikin k'unci sosai. Nayi ta k'oqarin kwantar mata da hankali amma daga k'arshe sai ta buqaci dana barta ita kad'ai, Abba bani da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa dole nazo nan na zauna." Yayi shiru yana nazari tare da girgiza ka daga bisani ya juya ya nufi bedroom d'in Mama. Zaune take jikin gado yayin data saka photon twin's da ma kayan su a gaba tana kallo, ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. tana cikin wannan yanayin Abba ya turo k'ofa ya shigo sai wani kallonta yake ya isa inda take ya zauna, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake cikin kwantar da murya yake magana.
"Maman twin's wai har tsayin wane lokaci zaki d'auka kina tare da wannan k'uncin? Abida wannan yanayin naki yana matuqar cutar damu sosai musamman ma *Amna.* Abida nima nayi matuqar damuwa sosai a kan twin's kawai dai hak'uri nake ina dannewa, Abida Allah shi ne wanda ya aiko mana da kaddaran rasa twin's sannan kuma ya bamu *Amna* a matsayin 'ya. Abida yarinyar mu tana matuqar buqatar ki sosai tana buqatar kulawar ki da kuma soyayyar ki gaba d'aya, Abida dan Allah ki bamu damar da dukanmu zamu rayuwa cikin farin ciki sosai please." Magana yake yana rarrashin ta cikin kasa-kasa da murya tare da tautasa take magana. "Abban twin's taya zanyi farin ciki ba tare dana san halin da yarana suke ba? Yaya Anas yau tsayin shekaru ashirin da uku kenan na d'auka ba tare da yarana na, Yaya Anas ni kawai na damu ne a kansu suna ina a wane irin hali ko yanayi suke ciki? Shin har yanzu suna tare da mutanan da suka sace su ko a'a shin har yanzu suna raye ko sun mutu? Abban twin's wallahi tallahi wannan tinanin yake hana ni sake wa nayi farin ciki, sabo da ni na damu sosai a kansu domin kuwa har yanzu su ďin yarana ne kuma ina sansu sosai. Hakama nayi matuqar farin ciki sosai da samun *Amna* na aife ta a lokacin da banyi tsammani ba, wallahi ina farin ciki sosai da samun ta amma kuma hakan ban saka ni mantawa da twin's ba. Sabo da ina sansu sosai ina matuqar masifar qaunar su sosai, ina fatan na sake had'uwa dasu ko da sau ďaya ne a rayuwa ta."
"Nima ina fatan hakan." Ya fad'a tare da rungumata jikin sa yana rarrashin ta daga bisani kuma suka tashi suka fita zuwa parlour, *Amna* ta shiga yi musu sannu da fitowa sun amsa suna murmushi Abida ta anbaci sunan ta taci gaba da magana. *"Amna* kiyi hak'uri da yanayi na ni kawai na damu ne a kan yayyan ki, *Amna* yanzu tsayin shekaru ashirin da uku kenan bama tare ban kuma san komai a game dasu ba, *Amna* hakan yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai. Ina fatan na sake had'uwa da twin's sabo da ahalinmu ya qara ciki ta yanda zamu rayu cikin farin ciki sosai." "Mama nima ina fatan had'uwa dasu ban san suba amma kuma ina tare da soyayyar ina qaunar su sosai." Tayi mata murmushi tare da sunbatarta yana furtamata Allah ya maki albarka, ta amsa da Amin tana murmushi mai tare da dariya bayan wani lokaci suka tashi suka nufi tebur domin suyi break past.
Bayan sun qarasa Abba ya nufi office hakama *Amna,* Abida kuma tashi tayi ta koma bedroom tana cikin yiwa yara darasi wayar ta ta d'auki ruri. Duk da cewar ta san mai kiran ta amma bata d'aga ba, taci gaba da yiwa yara darasi bayan ta qarasa ta fita sannan ta shiga kiran layin sa, sai da kiran ya kusa tsinkewa sannan ya d'aga ba kuma tare daya furta mata komai ba, tayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* shin wai kai kana fishi da ni ne.?" Shiru bai amsa ta ba jin shirun yayi yawa yasa taci gaba da magana. *"Adeel* mai yasa ba zaka amsa ni ba? Dan Allah kayi min magana ka ji please." Yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa ta. "Ni ban san cewar ke baki da lokaci na ba shi yasa na kira layin ki, amma yanzu na fahimci komai shi yasa ba zan sake kiran ki ba sai an jima."
Yana k'oqarin kashe wayar tayi saurin dakatar da shi, "a'a *Adeel* dan Allah karka kashe wayar ka d'an saurare ni mana, tabbas na ga kiran ka amma kuma a lokacin ina yiwa yara darasi shi yasa, to ina fatan yanzu zaka fahimce ni sannan kuma kayi min uzuri dan Allah." Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "shikenan amma da sai kiyi min ko da text ne ta yanda zan iya fahimtar ki amma kuma sam baki yi hakan ba, shikenan ba komai ya wuce yanzu fad'a min ya kike.?" "Gaskiya bana cikin kyakkyawan yanayi sabo da kai kana fishi da ni kuma fishi sosai." *"Amna* ni sam bana fishi dake kawai dai naji wani iri ne da baki d'aga kira na ba, amma yanzu komai ya wuce to kawai kiyi farin ciki kinji ko." "Shikenan masoyi ina godiya da kai ka iya fahimta na to miye labari.?" "Ke ce labari na nayi kewarki sosai rashin ki ba dad'i, gaskiya ina san ganin ki sosai ya kamata na shirya zuwa gareki, amma fad'a min wani abu shin ke kinyi kewata kuwa.?"
Tayi murmushi sosai tare da girgiza ka ta qara da jan numfashi, tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi. *"Adeel* wallahi ba zan iya sanar da kai irin yanda nayi kewarka ba, sabo da abin yana da matuqar girma sosai nake kewarka sosai. Yanzu fad'a min yaushe zaka zo gareni.?" "Karki wani damu sabo da abin da nake ta shiri kenan, zanzo inda kike nan kusa kuma kusa sosai insha Allah." "ina farin ciki da zuwan ka rabin raina zan fara shirin zuwan ka tin a yau ďin nan." Kafin ya furta komai sai ga Dadyn sa ya shigo yayi sallama da ita tare da fad'ar sunan Dady. "Sannu da zuwa Dady." "Yauwa rabin raina kana tare da sirika ta a waya.?" Yayi murmushi sosai mai tare da dariya sannan ya amsa shi, "eh Dady nayi kewarta sosai ina san na tafi gurin ta." Dady ya shafi fuskarsa zuwa kansa tare da hura sannan ya anbaci sunan sa.
*"Adeel* hakan yayi kyau sosai idan ka shirya tafi sai ka sanar da ni ka ji ko." "Na gode sosai My lovely Dad ina sanka Dady na." "Nima ina qaunarka ďana kai ne d'an daya fi kowa zo nan ďana." Ya fad'a tare da janyo sa ya runguma shi jikin sa yana sunbatarsa, sun jima a haka sannan ya sake sa ya anbaci sunan sa yana cewa. "Rabin raina lokacin tafi gida yayi ta idan ka shirya mu tafi. Ya amsa da to yayi shirin tafiya sun fice bayan kwana biyu da dare *Adeel* ya bud'a durowa komai zai d'auka oho, Allah ya kai hanun sa ga wata 'yar k'aramar jaka ya d'auki jakar ya koma kan gado ya zauna tare da bud'e jakar.
Ya ciro photo na masu yawa yawancin photo nan shi da Dadyn sa ne, sai wasu d'aid'ai ku da suke su uku shi Dadyn sa da kuma wata mata, wacce bai santa ba duka photo nan yana yaro ne sosai haka yaci gaba da kallon photo nan har ya gama, yaci gaba da kallon photon wannan matar kallo sosai yayin da yake magana da zuciyarsa. "Wacece wannan matar ko dai ita ce Mama na? To amma idan ita ce Mama na mai ya saka Dady na bai ta'ba nuna min photon ta ba mai yasa kuma mai hakan yake nufi? Lallai ya kamata nayi magana da shi domin ina san na san wacece wannan matar.?" Ya d'auki photon tare da tashi bai qarasa k'ofa ba sai ga Prof ya shigo yayi tozali da photo nan da suke watse a kan gado, ya wani zaro ido yana kallon photo nan sannan ya dawo da kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa........
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/15, 12:56 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 20*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Thursday 13/01/2022*
*Time 10:22pm*
*Typing................*
*"Adeel* mai kake yi ne haka mai ya saka ka d'auko wannan.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa mashi, "Dady wacece wannan matar ko dai ita ce Mama na.?" Da sauri ya kar'bi photon daga hannun sa sai wani kallon photon yake kallo sosai, ya nisa sosai tare da jan numfashi yayin da yake magana da zuciyarsa. "Ka gafarce ni *Adeel* domin kuwa ni sam ba zan iya sanar da kai asalin gaskiyar ba, domin idan har ka san gaskiyar to tabbas zaka buqaci had'uwa da ita, ni kuma ban shirya rabuwa da kai ba, sabo da kai ne abin da nafi so fiye da komai a rayuwa ta. Dan haka ya zame min dole dana 'boye maka gaskiyar na har abada." Sunan sa ne da *Adeel* ya fad'a da k'arfi tare da dafasa yasa shi dawo wa daga duniyar tinanin sa, ya d'ago fuskarsa tare da kai kallonsa garesa ba tare daya amsa ba, *Adeel* kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai daga bisani kuma yaci gaba da magana.
"Dady wacece wannan matar shin ita ce Mummy na.?" Da sauri ya shiga girgiza masa ka tare da furta, "a'a ďana wannan ba Mummyn ka ba ce, wannan wata ce daban ita ďin kamar qanwa take a guri na amma yanzu bata nan, to sam ba buqatar ka damu sosai a kanta ka ji ko dare yayi to ya kamata ka huta." "Dady ni nayi tinanin cewar ita d'in Mummy na ce, lokaci d'aya na fara santa yanzu kuma kana fad'a min cewar ita ba Mummy na ba ce, sai naji wani iri sosai k'unci na ya qaru sosai amma zanci gaba da jurewa kamar ko yaushe." Magana yake cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa sosai ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, cike da jin tausayin Prof ya janyo sa jikin sun tafi sun zauna ya wani rungumasa jikin sa yana rarrashin sa. Sai wani lalla'basa yake yana ba shi magana sun jima a nan tare sannan daga bisani ya tashi ya nufi d'akin sa, Dady ya bisa da kallo cike da jin tausayin sa sosai a tare da shi da ma zuciyarsa. Bayan tafiyar sa Prof ya mai da kallonsa ga photon da suke kan gado sai wani kallon photon yake yayin da yake magana da zuciyarsa.
"Aisha ina fatan ba zaki koma dawowa rayuwar mu ba, ban sani ba zuwa yanzu ko kin samu lafiya ko a'a, to koma dai miye ba zan ta'ba bai wa yarona damar da zai had'u dake ba na har abada. Wanda wannan dalilin ne yasa ma ni na fad'a masa cewar kin mutu ta yanda bama zai nai meki ba, amma kuma yanzu kina nai ma ki shiga rayuwar sa ni zanyi komai domin na kare ďana wannan alkawari ne." Ya kwashe photo nan ya mayar cikin jaka ya tafi ya a jiye jakar gurin da take, ya juya ya nufi toilet yayi wanka ya fito yayi shirin kwanciya ya tafi ya kwanta. *Adeel* kuwa ya shiga d'akin sa yayi zaune jikin gado sai tinani yake iri daban-daban, ya nisa sosai tare da jan numfashi yana magana da zuciyarsa. "Ni sam na kasa yarda da abin da zuciyata take fad'a min a game da wannan matar, wacece ita mai yasa Dady zai yi photo da ita kuma a tare da ni, sannan kuma yana rungume da ita a jikin sa amma ya fad'a min cewar ita d'in qanwarsa ce, to ina fatan gaskiyar ya fad'a min ta yanda ba zanyi zargin sa ba."
Ya tashi ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin shigar kayan barci ya kwanta, amma sam ya gagara barci ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin *Amna* ba jimawa ta d'aga, sunci gaba da waya na tsayin wani lokaci sosai sannan suka yi sallama suka kwanta. Bayan kwana biyu ya fara shirin tafiya jigawa gurin *Amna* yayi duk wani shirin sa ya kama hanyar, da yamma lis ya isa garin jigawa kai tsaye gidan su *Amna* ya nufa. Zaune suke a parlour suna fira yayin da *Amna* take ta aikin kallon agogo da k'ofa, tana ta takun jiran zuwan masoyin ta lokaci d'aya suka ji a na buga masu k'ofa, cike da d'auki take anbatar sunan sa ta tashi cikin hanzari ta nufi k'ofa tare da bud'e wa ba tare data tambaya ba, ta samu *Adeel* tsaye a gefen k'ofa cike da d'aukin ganin sa take anbatar sunan sa tare da yin hugging d'in sa. "Sannu da zuwa rabin raina." Ta fad'a tare da sunbatarsa a gefen fuska shi kuwa sai wani kallonta yake yana murmushi mai tare da dariya, ita ma haka murmushi take sosai sun jima a haka sannan daga bisani suka shiga ciki.
Abba da Mama sun shiga yi masa sannu da zuwa kasancewar dama suna da sani da shi. Ya amsa tare da gaishe su cikin girmamawa bayan sun gaisa Abba da Mama sun tashi sun shiga ciki, bayan tafiyar su *Amna* ta tashi daga inda take ta koma kujeran da yake zaune ta zauna kusa da shi kusa sosai. Shi kuwa sai wani kallonta yake kallo sosai yayin da yake jin tana birgesa matuqar birgewa sosai, ya kai hanun sa ya shafi fuskarta tare da sunbatarta a ka cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "masoyiya nayi kewarki sosai ba kiji ba wallahi abin ba dad'i sannan kuma da k'una sosai tin da muka kammala karatu kika dawo gida sai komai nawa ya tsaya, *Amna* ke ce jigona kin taimaki rayuwa ta sosai, *Adnan* wanda ya fara d'ora ni a kan hanya ke kuma kika qarasa, *Amna* ke ba kawai abar qauna ta ba ce a'a ke malama ta ce kuma ni ina alfahari da hakan sosai. Da badan na had'u dake ba k'ila da har yanzu ban samu damar dana sauke Al'qaur'an ba, amma sabo dake na sauke na kuma san wasu daga cikin littafai shi yasa a ko yaushe nake alfahari dake. *Amna* na fad'a ko a'a amma gaskiyar ita ce ke alkhairi ce a gareni da kuma rayuwata gaba d'aya shi yasa nake matuqar masifar qaunar ki sosai, *Amna* ina sanki sosai irin san da ba zan qara mafarkin yiwa wata 'ya mace ba na har abada. To ina fatan zaki amince da aure na duk da kasancewa ta d'alibin ki kuma wanda bai san komai ba, *Amna* yanzu fad'a min wani abu shin ke zaki aure ni.?"
*"Adeel* a rayuwa kowa yana da nasa anfani kai ma ka taimaken da dama fiye da abin da ni nayi ma, babban abin daka bani wanda yafi komai a gareni shi ne soyayyar ka kai ka so ni da gaba d'aya zuciyar ka. *Adeel* to wannan ma kawai ya isa to ba buqatar kaci gaba da gode