Showing 138001 words to 141000 words out of 142761 words

Chapter 47 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Monday 21/03/2022*

*Time 05:44pm*

*Typing..............*


A zahirin gaskiya ba zan iya sanar da ku girman farin cikin da yake tare da su ba, sai dai kawai na ce suna matuƙar farin ciki sosai, lokaci ďaya a ka fito da yaran nan kuwa suka shiga d'aukan yaran. Appa ya kira layin Abba da Abbu ya sanar dasu, take farin ciki ya shigesu sosai Mum ta kira layin Umma ta sanar da ita, kasancewar tana Abuja tare dasu Ummi haka suka shiga sanar da, 'yan uwa da abokan arziki bayan wani lokaci suka nufi gurin su *Afnan.* Dukansu a d'aki d'aya suke wanda kuma Appa ne yasa a ka had'e su d'aki ďaya, sun samu *Afnan* ido biyu yayin da *Alishart* take ta sharan barci. Su Mamie sun shiga yi mata barka da arziki murmushi kawai tayi ba tare data furta komai ba, sun mai da kallonsu ga *Alishart* tare da yi mata addu'ar Allah ya bata tafiya, *Afnan* tayi matuqar farin ciki sosai da ganin yaranta, dama yaran *Alishart* to balantana kuma su *Adyan* abin ba zai fad'u ba.

Misalin k'arfe 03:00pm *Alishart* ta farka kuma ta tashi cikin kyakkyawan yanayi sosai, sun shiga yi mata sannu da ya jiki ta amsa da Alhamdulallah tana samun sauki sosai. Tayi matuqar farin ciki sosai da kyautar da Allah ya bata, dama yaran Yayanta *Afnan* bata wani jima ba ta samu sallama, kasancewar tana lafiya *Alishart* kuma ta samu kwana biyar asibiti sannan ta samu sallama zuwa gida. Yanda a kayi bikin auran su a rana ďaya hakama bikin suna, duka ahalin sai hidima suke kwana biyu da aihuwa su Umma suka dawo, kafin ka ce haka gari ya d'auka inda labarin aihuwar ya zaga ko ina na duniya. Bayan mako biyu suka gabatar da walima a madadi bikin suna, da dare kuma suka yi Dina an rad'a wa yaran *Adnan suna Aarif da Aaryan, yaran Adyan kuma Aarfat da Aarfan* bayan suna da mako biyu su Appa suka nufi Abuja. Amma ba tare da *Alishart* ba sun barta a nan gidan Papa, bayan wasu watanni wani yammaci zaune take a part d'in Mama wato Abida, suka ji a na buga masu k'ofa *Amna* ce wacce ta tafi domin ta bud'e k'ofar, ta bud'e k'ofar ta samu *Adeel* tsaye a k'ofa lokaci d'aya suka saki murmushi, ta shiga yi masa sannu da zuwa ya amsa sun koma ciki su Mama sun shiga yi masa sannu da zuwa, ya amsa tare da gaishe su ya k'ara da fad'ar sunan Mum.

"Mum tare nake da Dady wai yana san zai yi magana dake yana bakin mota." *"Adeel* wai mai ya saka kake yi min irin haka a kan me zaka zo da shi nan? To ka tafi ka fad'a masa cewar ya bar nan kuma karya koma dawowa na har abada, sabo da ni sam bana buqatar sa a rayuwa ta ka ji ko." "A'a Mum dan Allah karki fad'i haka shi fa ya canja sosai wanda ke ma kin fahimci haka, Mum ai kin fad'a masa cewa kin yafe masa to mai yasa ba zai zo gurin ba? Mum nima ina san na kusance kamar *Adnan Adyan da kuma Amna,* suna rayuwa kamar sarki da sarauniya sabo da suna tare da duka iyayensu. Amma ni ban tab'a samun hakan ba Mum baki san iya yanda hakan yake cutar da ni ba, ko yaushe kukan zuci nake tin lokacin da ni nake yaro amma Mum baki tab'a amince da hakan ba, eh gaskiyar ni ne Dady ya cutar dake sosai amma kuma ya baki hak'uri har yana zubar da kwalla, sannan kuma kin fad'a masa cewar kin yafe masa duk da cewar har yanzu hukunta shi kuke. Mum ni ba zan iya b'oye maki gaskiyar ba ina san ku biyun ku k'ara kasancewa tare, wannan alfarma ce nake nai ma a gurin ki to ina fatan zaki amince da hakan please."

Kallonsa kawai take yayin da ta gagara furta masa komai, shi kuwa ya shiga rarrashinta yana bata magana, *Amna* ma ta ta ya shi amma duk da haka bata furta komai ba, Mama zata yi magana tayi saurin dakatar da ita ta hanyar girgiza mata ka tare da furta. "A'a ni ba zan iya wannan ba sam ba zan tab'a k'ara komawa garesa ba na har abada, kayi hak'uri ďana sabo da ba zan iya baka abin da kake so ba dan Allah ka yafemin." "Shikenan tin da kin zab'a wa yaronki rayuwar k'unci, bayan kuma kina da damar da zaki taimake sa, amma kuma banyi fishi ba to ke ma karki yi fishi da ni dan Allah. Yanzu zan tafi na sanar da shi sak'on ki sai na dawo." Ya tashi domin tafiya Mama ta shiga girgiza wa Mum ka a lamar a'a, ya bud'e k'ofa yana k'oqarin fita Mum tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa, lokaci ďaya Mama da *Amna* suka sauke a jiyar zuciya.

*"Adeel* ka fad'a masa cewa zanyi magana da shi, bayan na samu izini daga gurin ahalina amma ba yanzu ba dan haka ya jira wani lokaci." Cike da d'auki yake amsa ta, "eh zai jira har zuwa lokacin da zaki samu izini daga gurin Kaka, sannan kuma duk da haka yana godiya sosai sai na dawo." Ya juya ya fita su kuwa sun bisa da kallo har ya b'ace, ya fito tare da sanar da Prof abin data fad'a yayi wani gajeran murmushi yana cewa. "Shikenan zan jira ina fatan daga k'arshe ta amince da ni, dama su biyu ne nake fatan su amince da ni Mummyn ka sai kuma yaron k'anina. Alhamdulallah yanzu *Adnan* yana kira na da Kawu, hakama *Adyan* tin a ranar data bawa *Alishart* ya fara kira na da Kawu, yanzu sun fara bani girma *Adeel* ni ba sabo dasu na bata jini ba, amma ina farin ciki sosai da hakan ya zama silar da zasu ga girma na. To yanzu kuma Mummyn ka ce duk da irin nadamar da nayi amma sam ta kasa amincewa da ni, amma ba komai Allah ya fimu sanin daidai Allah ya zab'a mana mafi alkhairi Allahumma Amin."

*Adeel* ya amsa shi da Amin da kuma haka suka yi sallama, Prof ya shiga mota yayi tafiyarsa bayan tafiyar sa *Adeel* ma juya wa yayi ya nufi ciki. Bayan mako biyu zuwa wannan lokacin Abbu ya dawo daga Abuja, Umma ta sanar da shi buqatar *Adeel* ta Mum ta koma gidan Prof. "Asiya ni ba zance komai ba har sai nayi magana da Yaya, yanzu zan kira layin sa sai muji abin da zai fad'a." Ta amsa shi da to ya d'auki wayar sa ya shiga kiran layin Abba ba jimawa ya d'aga, sun fara gaisawa sannan Abbu ya shiga sanar da shi abin da Umma ta fad'a masa, yayi shiru na jim kad'an yana nazari sannan daga bisani ya fara magana. "Gaskiyar *Adeel* ba wani d'a wanda zai so yaga iyayensa basa tare, amma kuma na san cewar zai yi matuqar wahala sosai, Aisha ta iya amincewa komawa gidan Prof sabo da cutarwar da yayi mata. Duk da cewar yanzu yayi matuqar yin nadama sosai, ni na tabbata Aisha ba zata tab'a yin aure da wani namuji daban ba, sabo da ko yaranta ma ba zasu amince da hakan ba. To ni ina ga kawai ta amince da buqatar yaronta ko ba komai shi zai yi farin ciki sosai, idan kuma ta ce a'a to fa ba wani wanda zai tilassa mata a kan hakan."

"Shikenan Yaya zanyi magana da ita zaka ka ji duk yanda muka yi." Ya amsa ta da to da kuma haka suka yi sallama. Ta mai da kallonta ga fuskar Abbu ya jinjina mata ka a lamar eh, ita ma ta jinjina masa ka a lamar to da yamma bayan ta koma gida, take sanar da Mum abin da Abba da Abbu suka fad'a tayi shiru tana nazari, sai tinani take daga bisani ta anbaci sunan Umma. "Umma amma kina ganin su *Adnan* zasu amince da hakan kuwa.?" "Ban sani ba amma mai zai hana kiyi magana dasu domin ki ji ra'ayin su. Ta amsa ta da to ta d'auki wayar ta nan ta shiga kiran layin *Adnan,* ba jimawa sosai ya d'aga tare da sallama ta amsa ta kuma ci gaba da magana. *"Adnan* dan Allah idan kana da lokaci ina san zamu yi magana." "Shikenan sai na shigo." *"Adnan* qlau kake fad'a min wani abu mai ya saka ba zaka fad'i sunana ba.?" "Ina gida tare da Papa da Mamie." "Na fahimta sai ka shigo." Ya amsa da ok sunyi sallama bayan isha ya nufi gidan Mum, domin jin kiran da take masa ya isa gidan tare da shiga ciki bayan sun gaisa yaci gaba da magana.

"Mum mai kike san mu yi magana a kai.?" "Ba komai d'ana kawai dai ina buqatar ganin ka ne shi yasa na ce kazo." "Mum kiyi hak'uri wallahi yau mun jima sosai a office shi yasa muka gaji sosai, bayan mun koma gida kuma yau su *Aaryan* fitina suke bama su barni nayi barci ba. Baki ga yanda Besty take ta fama dasu ba dole sai da Mamie ta taimaka mata, kuma kin san qanwata na gida gasu *Aarfan* shi yasa ban iya fita zuwa ko ina ba bayan office." *"Adnan* idan irin haka ya k'ara faruwa to ka sanar da ni, sabo da na tafi na taimaka wa Mamie sannan kuma da akwai buqatar yaran su saba da ni. Ta yanda zan samu damar da zan kasance Kaka ta gari a garesu." Ya amsa ta da to yana murmushi ita ma abin da take yi kenan, suna haka sai ga Umma ta fito bayan ta gaisa da *Adnan* taci gaba da magana.

"Aisha kun yi maganar kuwa.?" "Umma ko yanzun ma magana muke." "Aisha a game da wancan zancan shin kin sanar da shi kuwa.?" Kafin ta furta komai yayi mata rigagi. "Umma mai yake faruwa ne ita ba abin data sanar da ni.?" Nan kuwa Umma ta sanar da shi abin da yake faruwa, ya mai da kallonsa ga fuskar Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum to ke wane hukunci kika yanke.?" "Am dama ni ina san na ji ne daga gareku, su Kawu sun amince dana koma ga Prof sabo da farin cikin *Adeel,* amma duk da haka ina buqatar na ji miye ra'ayin ku kai da *Adyan.?"* "Mum to idan kuma muka ce a'a fa.?" "Ban yi mamaki ba sabo da dama na san cewar amsar ku ba zata wuce a'a ba, a baya na yi tunanin cewar Dady shi ne kawai wanda yake da san kansa da yawa, amma gaskiyar ita ce yaransa ma haka suke gaskiya jinin sa yana da k'arfi sosai."

*"Adeel* wai mai kake fad'a ne haka.?" "Eh *Adnan* ni kawai gaskiyar nake fad'a, abin da nake cewa shi ne ku biyun ku yaushe kuna samun damar kasancewa tare da iyayenku, a kullum suna runguma ku jikin su sannan kuma su sunbace ku a lokaci ďaya, cikin qauna da soyayya tare da fad'ar muku cewar suna qaunarku sosai to amma ni kuma fa? Sam ban tab'a samun hakan ba ko sau ďaya a rayuwa ta, Mum da Dady basu tab'a shiga rayuwa ta a lokaci ďaya na, tin ina k'aramin yaro nake da burin samun kyakkyawar rayuwa kamar dai yanda yake kai da *Adyan.* Amma kuma mummunan kaddara ta bata bani wannan damar ba, dama ko a cikin ku ni ne mara sa'a shi yasa kaddara ta tazo min a haka, na yi tunanin cewar yanzu ne lokacin da nake jira yazo, amma sabo daku ba zan tab'a samun cikar burina ba. Shikenan tin da abin da kun ka zab'a min kenan ba komai zan ci gaba da jurewa na har abada." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya zai fita da sauri, *Adnan* ya dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa...................






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/23, 8:45 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 56*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶
s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Tuesday 22/03/2022*

*Time 06:14pm*

*Typing...............*

🔚🔚🔚🔚 Insha Allah.

*"Adeel* wai mai kake fad'a ne haka? Kai sam ka gagara fahimta ta ballantana ka iya gane abin da nake fad'a, *Adeel* ni na yi matuqar fahimtar ka sosai amma kuma abin da kake so yana da matuqar girma sosai. Kai ka fimu sanin waye Prof da kuma irin abin da zai iya aikata wa, mu kawai mun damu ne sosai a game da Mum, amma shikenan idan kana ganin komawar ta gidan Prof shi ne daidai. Ni ba zanso wannan yanayin naka yaci gaba da cutar da kai ba, sabo da hakan zai bawa shaid'an damar shiga zuciyarka, ya kuma saka maka wasuwasi a kai na da kuma Aboki, to ina ga kawai wannan lamarin ya k'are a yanzu. Ni da kuma Aboki mun baka damar cika burin ka, ina nufin mun amince da duka buk'atar ta to yanzu kana farin ciki.?"

Wani irin kallo yake yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a sosai, sam bai iya amsa shi ba sai dai ya nufi gurin sa yana zuwa, cike da d'auki yayi hugging d'in sa tare da sunbatarsa yana furta masa kalmar. "Ina sanka d'an uwa ina qaunarka sosai, kayi hak'uri da irin yanayi na ni kawai na k'osa ne sosai, shi yasa nake yin duka wannan amma kuma daga k'arshe burina zai cika, mafarki na zai zama gaskiya ina farin ciki sosai da hakan." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yayi yawan gaske a tare da shi sosai, sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake *Adnan* daga rungumar da yayi masa. Ya mai da kallonsa ga fuskar Mum tare da fad'ar sunan ta. "Mum shin ke kin shirya wa hakan kuwa.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh farin cikin sa ya k'aru sosai sai wani lallausan murmushi, yake sosai mai had'e da dariya dukansu sai wani kallonsa suke kallo sosai, bayan wani lokaci ganin lokaci ya tafi sosai yasa, *Adnan* yayi sallama dasu tare da sai da safe ta tafi, ya fara zuwa part d'in su Mama sun gaisa sun d'an tab'a fira kad'an, sannan yayi sallama dasu ya tashi ya tafi.

Tin a mota ya kira layin *Adyan* ya sanar da shi abin da yake faruwa, ba shi da wani zab'i a kan abin da *Adnan* ya fad'a, wanda wannan dalilin ne yasa ya amince da hakan. Cike da d'auki *Adeel* ya tashi ya fita duk da cewar dare yayi sosai, kai tsaye gidan Prof ya nufa ya isa gidan tare da buga masa k'ofa, ba jimawa yazo ya bud'e bayan da ya ji cewar waye cike da d'auki yayi hugging d'in Prof yana cewa. "Kayi narasa duka ahalin sun yarda sun kuma amince da cewar Mum ta dawo gareka, a gaskiya na wahala sosai kafin na iya samun amincewar su, sabo da suna yawan tunawa da baya wanda sam sun gagara mantawa, Dady ina ro e ka daka kasance muji na gari a gurin Mum. Ka saka ta farin ciki sosai kasa ta ji cewar tafi ko wace mace sa'ar samun muji a rayuwa, kasa ta manta baya gaba d'aya sabo da a yanzu zuciyar ta cike take da tsoro, firgici rud'ani da kuma fargaba tana ganin kamar zaka k'ara cutar da ita ne. Dady wane irin alkawari zaka yi min a game da Mum.?"

Kallon d'an nasa kawai yake yayin da ya gagara furta masa komai, sai wani kyakkyawan murmushi fuskar sa take fitarwa, cike da soyayya da qauna yayi hugging d'in sa yana sunbatarsa. "Na gode sosai d'ana Allah yayi ma albarka ya kuma albarkaci rayuwarka, hak'iqa kai d'a na gari ne a gareni ina matuqar alfahari sosai da hakan. *Adeel* nayi ma alkawarin kasancewa muji na gari a gurin Mummyn ka, zan tabbatar na saka ta farin ciki sosai, zan zame mata tamkar bawa har zuwa lokacin da zata 'yanta ni. Zanyi komai domin ganin na gyara duka zunubin dana aikata mata, wannan alkawari ne to zaka iya yarda da ni d'ana." "Na gode sosai Dady na ina qaunarka sosai Dady." "Nima haka ďana ina matuqar masifar qaunarka sosai, fiye ma da yanda nake sanka ina qaunarka ďana."

Lokaci ďaya suka k'ara runguma juna sosai, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna, ganin dare yayi sosai yasa yayi masa sallama ya tafi. Washe gari da yamma lis Prof ya isa gidan su Mum, kai tsaye part ďin su Umma ya nufa zaune suke a parlour dukansu, suka ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login