Showing 90001 words to 93000 words out of 142761 words
Chapter 31 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
komai a game da shi, cike da jin tausayin sa sosai yake magana. "Aboki hakan sam bai yi ba amma komai zai yi daidai insha Allah, yanzu zanyi magana da Kaka na kaduna ina nufin Abbu zan koma kiran layin ka."
Ya amsa shi da to sun tsinke kiran bayan wani lokaci *Adyan* ya koma kiran sa ya d'aga tare da fad'ar sunan sa ya amsa shi yana cewa. "Barrister nayi magana da Kaka yace gobe ka same sa a gida ka tafi tare da, *Adeel* sannan kuma ya tafi tare da takardun sa amma kana ganin zai iya ri e matsayin manager kuwa.?" "Doctor kai kana da kirki sosai Allah ya saka maka da alkhairi Amin, eh zai iya sabo da shi ne matsayin daya ri e a company Dadyn sa. Yana da kwarewa sosai a kan aikin company to zaka iya yarda da ni." "Aboki Dadyn sa yana da kud'i sosai har haka, amma yaronsa yake irin wannan rayuwar shi wane irin uba ne wace irin zuciya yake da ita haka? Ya ma kasa kasancewa uba na gari ga yaronsa tir da shi da kuma rayuwarsa gaskiya ba shi da kirki na tsane sa." "Aboki gaskiyar ka ne shi bai kasance uba na gari ga *Adeel* ba sannan kuma ya cutar da shi sosai, amma abin farin cikin shi ne har yanzu yana raye kuma duk da haka yana farin ciki, sabo da Mummy da kuma Kaka sannan kuma muna tare da shi to wannan ma kawai ya isa. To ba buqatar muyi magana a kan Dadyn sa sabo da hakan zai saka mu k'unci ne, kuma hakan sam bai dace damu ba yanzu fad'a min wani abu ina qanwata.?"
"Ta fita tare da Ammie to ina Besty da baby na.?" "Qlau suke suna barci ne." Sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama, *Adnan* ya a jiye laptop d'in sa ya kwanta tare da runguma *Afnan* jikin sa. Washe gari bayan sun qarasa shirin su sun fito sun samu Mamie tana shirya abinci a kan tebur, sun tafi sun gaisa *Afnan* ta anbaci sunan ta tana cewa. "Sannu da aiki Mamie kiyi hak'uri dana kasa taimaka maki a kan wannan sabo da." Mamie ta rufe mata baki tana girgiza ka, "A'a 'yata karki fad'i haka sabo da ba laifin ki bane, lokacin da kike lafiya ke ce kike yin duka wannan dan haka ba buqatar ki ba da hak'uri, kawai dai ki kula min da ango na kin ji ko yanzu ki zauna zan tafi na kira Papa ya fito muyi break past."
Ta zaunar da ita sannan ta juya domin tafiya *Adnan* yayi saurin dakatar da ita, ta hanyar yin hugging d'in ta tare da sunbatarta yayi wani kwance jikin ta, cikin kyakkyawan yanayi yake magana. "Mamie ke kina da kirki sosai kin fi ko wace uwa kirki, ke d'in ta musamman ce kin kuma kasance uwa ta gari a garemu ina sanki sosai ina matuqar qaunar ki sosai." Ta janyo sa ya fito ta gaban ta ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa, "ina qaunarka ďana fiye ma da yanda nake sanka Allah yama albarka matarka dama jikana." Sun amsa da Amin dukansu suna murmushi sannan ta juya ta nufi bedroom d'in Papa, bayan tafiyar ta *Adnan* ya tashi *Afnan* sun nufi d'akin su Umma sun isa k'ofa tare da buga k'ofar. *Adeel* ne wanda ya bud'e musu k'ofa sun shiga ciki ya sauke kallonsa ga Mummy wacce take ta aikin kuka, cike da firgici rud'ani tare da jin tausayin ta sosai ya mai da kallonsa ga *Adeel* tare da fad'ar sunan sa.
*"Adeel* mai yake faruwa da ita mai ya saka take kuka.?" Ya nisa sosai tare da jan numfashi yana girgiza ka sannan ya amsa shi. "Tana jin yunwa ne kuma madara take buqata shi yasa take kuka." "Amma kuma kake zaune a nan kana kallonta? Shin kana jin dad'in sautin kukan ta ne shi yasa ka gagara yin komai.?" Yana kai ar maganar sa ya juya ya fita daga d'akin *Adeel* ya shiga anbatar sunan sa amma bai amsa ba. Ba jimawa ya dawo tare da kofin madara a hanun sa cikin hanzari ya isa inda take ya zauna, nan kuwa ya shiga bata madara ita kuwa sai sha take ta kuwa sha sosai. Bayan ta k'arasa sha ya shiga tambayar Umma maganin ta, ta bud'e jakarta ta d'auko ta ba shi *Afnan* taba shi ruwa, nan kuwa ya shiga bata magani kamar ba zata sha ba kuma daga bisani ta yarda ta sha. Zai tashi tayi saurin ri e hanun sa tare da furta masa a'a tayi kwance tare da yin pillow da k'afarsa, ta wani ri e hanun sa tare da lumshe ido bai fi da mintuna goma ba zuwa sha biyar tayi barci. Suna haka sai ga Mamie ta shigo tare da kayan abinci *Adeel* ya kar'bi kwandon dake hanun ta, tare dayi mata sannu da shigowa ta amsa tana murmushi ta zauna tare da gaisawa da Umma, tare da tambayar ta jikin Mummy ta amsa ta da tana samun sauki, Mamie ta bata abincin data shigo da shi Umma tayi mata godiya murmushi kawai tayi mata, ta mai da kallonta ga *Adnan* tare da furta musu su tafi suyi break past.
Sun amsa ta da to ta tashi ta fita bayan tafiyar ta *Adnan* ya gyarawa Mum kwanciyar ta, ya mai da kallonsa ga *Afnan* tare da fad'ar sunan ta yana cewa. "Besty mu tafi sannan kuma ki fad'a masa cewar ya fito muyi break past.?" "Besty shin wai kai kana fishi da shi ne wanda har ba zaka iya yi masa magana ba.?" "Besty kawai kiyi abin dana ce dan Allah na tabbata zuwa yanzu yaron yana jin yunwa sosai." Ya jinjina masa ka tare da kai kallonta ga *Adeel* kafin ta furta komai yayi mata rigagi ta hanyar fad'ar sunan *Adnan.* "Kayi hak'uri ni kawai ba yanda na iya ne, duk da cewar na damu sosai da yanayin ta dalilin kenan amma na gode sosai da yanda ka kula da ita."
"Ba sabo da kai nayi wannan ba nayi ne a matsayin ďan ta, to kaga sam ba buqatar ka gode min to kawai mu tafi muyi break past, idan mun k'arasa da akwai wani muhimmin gurin da zamu tafi, to ka tabbatar cewa duka takardun ka a shirye suke ni kawai na ji wani iri ne, amma kuma hakan sam baya nufin cewar ina fishi da kai to zaka iya yarda da ni, sannan kuma wani lokacin ina da sauran fishi, amma kuma bana jimawa nake sauka to sai kayi hak'uri da ni ka ji ko to yanzu zamu iya tafiya." *Adeel* yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi. *"Adnan* gaskiyar ita ce ni kamar kai nake wani lokaci ina da saurin fishi amma ina da saurin sauka, zaka iya tambayar Kaka a game da wannan to fa kai ma sai kayi hak'uri da ni." "Waw abin mamaki dukanmu ukun muna da yanayi ďaya kamar dai a fuska muna da kamanni sosai, idan a kazo ta b'angaran abinci kuma dukanmu abu ďaya muke so samosa da madara. sannan kuma yanayin halaiyar mu ďaya hakan yayi kyau sosai, tabbas mu ukun mun dace da kasancewa tare to yanzu ya kamata mu tafi Besty mu tafi." *"Adnan ka ce shi ma *Adyan* hakan yake kamar mu.?" Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan, hakama su Umma da kuma haka suka fita zuwa gurin break past...................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/6, 4:08 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 37*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Friday 04/02/2022*
*Time 12:21am*
*Typing.............*
Bayan sun ƙarasa break past Papa ya fita zuwa office *Adnan* kuma ya d'auki *Adeel* sun fita, kasancewar *Afnan* tana cikin yanayin hutu sabo da laulayin da take. Suna fita kai tsaye gidan Abbu suka nufa wato Governor, sam basu samu wata matsala ko damuwa ba kasancewar security na gidan, sunyi matuƙar sanin sa sosai wanda a tunanin su ma ahali d'aya ne, sun shiga gaishe su suka yi tare da basu girma sosai. Sun k'arasa ciki Ummi ta shiga yi musu sannu da zuwa. Bayan sun gaisa ta yi musu iso zuwa gurin Abbu sun same sa yana amsa waya, bayan ya qarasa suka gaisa *Adnan* ya gabatar da *Adeel* garesa Abbu ya amsa shi. *"Adnan* nayi magana da masoyi to ga wannan offer d'in sa ce ta fara aiki, wannan kuma mukullin gida gana mota laptop, waya, da kuma tap wannan kuma kud'in shan mai. Jabir yana waje zai kai ku gidan motar na can ku duba gidan da kyau, idan akwai wani abin buqata to kawai ka sanar da ni ka ji ko. Sannan kuma da akwai masu aiki wad'an da zasu kula da Mummyn sa." *Adnan* ya shiga yi masa godiya yayin da *Adeel* ya gagara fad'ar komai sai wasu zafafan hawaye da suke bin fuskar sa, Abbu ya shiga girgiza masa ka tare da furta masa a'a hakama *Adnan,* ya jinjina musu sannan yayi wa Abbu godiya sosai yayi murmushi sosai tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* karka gode min kawai dai ka kira ni da Kaka ka ji ko."
"Na gode sosai Kaka." "Karka damu *Adeel* kawai ka kula kuma idan kana buqatar wani abu to kawai ka sanar da ni ka ji ko." Ya jinjina masa ka tare da furta to sun d'an jima a nan tare da shi, sannan daga bisani suka yi masa sallama suka tafi a hanya *Adeel* ya anbaci sunan *Adnan* yana cewa. *"Adnan* gaskiya Kakan yana da kirki sosai kamar Papa, gaskiya kayi dace da kyakkyawan ahali irin yanda kuke san juna, abin yana da birgewa sosai ina yi muku fatan alkhairi sannan kuma ina godiya na gode sosai." *Adnan* yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi. *"Adeel* gaskiyar ita ce Abbu ba a salin Kaka na bane, shi d'in Kakan aboki ne ina nufin *Adyan* Abban Ammie ne, kayi hak'uri da ni ban sanar da kai a salin gaskiyar ba *Adeel* jiya da dare, nayi magana da Doctor kuma na sanar da shi komai a game da kai. To shi ne ya buqaci da Abbu ya baka duka wannan to ina fatan ba zaka yi fishi ba.?" Wani irin kallo yake yi masa mai cike da jin mamakin abin da yake fad'a. *"Adnan* banyi fishi ba amma zanso ka had'a ni da *Adyan* domin nayi masa godiya yanda ya kamata."
*"Adeel* sai dai kawai ka gode masa a waya sabo da baya k'asar nan, shi yana k'asar England ne a can yake da zama tare dasu Appa, shi yasa ba zai yu ka iya ganin sa ba amma zaka iya magana da shi video call a waya ko laptop." "Eh zanyi hakan amma shi ma yayi aure kuwa.?" "Eh a rana d'aya a kayi auran mu kuma qanwata ce ya aura, zaka iya tina ranar da a kayi auran jikan Mr President *Adyan Ahmad Aliyu.?"* *"Adnan* kana nufin *Adyan* shi ne wannan yaron jikan Mr President kuma jikan Governor kaduna? Lallai shi ďin na musamman ne suna da k'arfin iko sosai, babban abin farin cikin shi ne suna da kirki sosai." Ya jinjina masa ka yana murmushi mai had'e da dariya da kuma haka suka isa gidan.
Sun fito Jabir da ma aikatan gidan sun shiga nuna musu ko ina na gidan, a zahirin gaskiya gidan yayi matuqar yi musu kyau sosai sannan kuma ga shi babban gida. Bayan sun qarasa zaga gidan su Jabir suka tafi bayan tafiyar su ne suka nufi gurin mota, wata kyakkyawar mota ce k'iran Toyota tayi matuqar yin kyau sosai, hakama an sanya komai a gidan har ma da kayan sawa na dukansu, bayan wani lokaci suka nufi gida inda suka shiga sanar dasu Mamie abin da yake faruwa. Umma tayi matuqar farin ciki sosai da hakan Mamie ta shiga yi musu fatan alkhairi, sun amsa suna godiya bayan Papa ya dawo da dare *Adnan* yake sanar da shi, yayi farin ciki sosai tare dayi musu fatan alkhairi sun amsa suna yi masa godiya. *Adeel* ya kira layin *Adyan* yayi masa godiya sosai ya kuma ba Umma ita ma tayi masa godiya, murmushi kawai yayi wanda ya hana masa fad'ar komai sai dai ya furta musu ba komai. Washe gari su Papa suka tafi suka duba gidan sun kuma yaba gidan sosai, hakan ya k'ara saka *Adeel* farin ciki sosai bayan kwana biyu suka tare a saban gidan su.
Wata safiyar jumu'a tafiya yake kad'an ya k'arasa office wayar sa ta d'auki ruri, ganin sunan *Adyan* ne yasa shi d'aga kiran kafin ya furta komai ya masa rigagi. "Aboki shin kayi magana da *Adeel* kuwa? Na jima sosai ina kiran layin sa amma baya d'aga wa, na kuma kira campany an fad'a min cewar bai shiga office ba. Aboki gaskiya na damu sosai a kansa sabo da ban san abin da yake faruwa da shi ba, Aboki shin ko zaka iya tafiya gida domin ka duba yanayin sa dan Allah.?" "Eh Aboki to kawai ka kwantar da hankalin ka sabo da yana lafiya jiya har dare muna tare, amma Mum bata cikin kyakkyawan yanayi to ina tsoro in ba jikin ta bane yayi zafi sosai, amma yanzu zan tafi gidan domin ganin abin da yake faruwa zamu yi magana ka ji ko."
Ya amsa da to da kuma haka suka yi sallama *Adnan* ya juya ya nufi gidan su Umma, domin ganin abin da yake faruwa ya isa gidan tare da shiga ciki, kai tsaye d'akin Umma ya nufa ya shiga ciki tare da sallama, cike da firgici ya k'arasa inda suke yana fad'ar sunan *Adeel. "Adeel* mai yake faruwa da ita ne haka mai yasa ba zaka kai ta asibiti ba? Ta ji wa kanta rauni tana buqatar kulawar likita sosai to kawai mu tafi asibiti yanzu." Yana k'oqarin tashin ta Umma ta dakatar da shi ta hanyar girgiza masa ka tana cewa. "A'a *Adnan* kawai ka barta a nan tin daran jiya muka tafi asibiti da ita, amma ba abin da a kayi mata yau da safe muka dawo gida." "Umma wane likita ne ya aikata muku haka ya kamata muyi k'aran sa? Shi sam bai san aikin sa ba ya ma kasa duba ta, wannan yana buqatar hukunci sosai Umma mu zamu canja wani asibitin ne, to dan Allah karku dakatar da ni please to zamu iya tafiya da ita yanzu." *"Adnan* duk ma inda zamu tafi to hakan ba zai canja gaskiyar ba, kawai zasu fad'a mana cewar mu siya mata magani ko kuma mu kai ta England, to bamu da wani zab'i shi yasa ka shigo ka same ta a haka, *Adnan* wannan yanayin nata yana matuqar cutar da ni sosai. Amma kuma ba yanda na iya dole nake hak'ura na gode sosai da kulawar ka."
*"Adeel* ni abokinka ne to zanyi komai a kan ahalinka, ita Mum tamkar Mamie na take to zanyi komai domin ta kuma bana, buqatar wata godiya daga gareka ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to lokaci d'aya suka yi hugging juna yayin da, *Adnan* yake ta aikin rarrashin *Adeel* wanda shi ma kwalla yake zubarwa.
*England.*
Kwance take amma kuma ba barci take ba *Adyan* ya shigo, ya isa inda take ya kwanta tare da janyo ta jikin sa yayi mata wata kyakkyawar runguma sosai, ya qara da sunbatarta fuska zuwa wuya ta fita jikin sa tana k'oqarin tashi ya dakatar da ita. *"Adlishart* wai mai kike yi ne haka mai yasa kike hukunta ni haka? *Adlishart* gaskiya ni ba zan iya d'aukar wannan ba, Masoyiya dan Allah ki dena a zabtar da ni haka ciwan yana da zafi sosai da kuma k'una. Rabin raina dan Allah ki dena cutar da ni haka sabo da ina buqatar buqatar ki sosai." Magana yake cikin wata lallausar murya mai dad'in sauraro yanayin sa kuma kamar zai saki kuka, ita kuwa sai wani kallonsa take kallo sosai cike da shagwa'ba take magana. "Masoyi idan kana san duka wannan ya gushe to kawai ka cika alkawarin ka, ina nufin kawai ka had'a ni da Secret super star sannan kuma ka dena kira na da *Adlishart* sabo da sunan namuji ne."
"Shikenan zanyi hakan zan shirya had'a ki da secret super star, amma kuma ba zan dena kiran ki da *Adlishart* ba sabo da wannan sunana ne na baki. Sunan mu biyun ne na had'a ya ba da hakan na had'a wannan sunan tin baki wuci shekaru biyu ba, masoyiya ni ina matuqar jin dad'in na kira ki da sunan sosai, nima zanyi matuqar farin ciki idan kika kira ni da sunan, *Adlishart* fad'a min shin