Showing 66001 words to 69000 words out of 142761 words

Chapter 23 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

kuma yaci gaba da nai man mafia, washe gari bayan ya qarasa shirin ya nufi gurin *Afnan* jin ya kira wayar ta layin ta a kashe, ya shiga gidan tare da shiga ciki bai samu kowa a parlour ba hakan ta ba shi damar shiga d'akin *Afnan.* Ya shiga ciki ya hangeta zaune a tsakiyar gado ta had'e kai da guiwa tana kuka, da sauri ya qarasa inda take yana fad'ar sunan ta ya d'ago fuskarta sai wani kallonta yake kallo sosai, ya shiga share mata kwalla yana rarrashin ta lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin hugging d'in ta, yana sunbatarta ita kuwa tayi kwance jikin sa tamkar wacce za a mai da ciki a aife, sun jima a haka sannan daga bisani ya fara magana.

"Besty dan Allah ki sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa dake please.?" Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa take sanar da shi abin da yake faruwa, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data fad'a yake magana. "Besty wai kinji abin da kike fad'a kuwa? Ta ya ma hakan zata faru to amma ke kin amince da auran kuwa.?" "Besty shi Baba magana d'aya tak yake to ba zan iya canja hakan ba." "Eh gaskiyar ki ne dama ku biyun ahali d'aya ne k'ila shi yasa Kaka yaga ya dace ku biyun kuyi aure, ina yi muku fatan alkhairi tare da kyakkyawan zama bayan kunyi aure. Babbar qawata kuma aminiya ta zata yi aure ta ya kamata nazo na fara shiri na, sabo da ina san nayi shiri na musamman amma kuma zanyi kewarki sosai, sannan kuma hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai amma zan jure fatan alkhairi Besty na, amma ke zaki yi kewata kuwa fad'a min shin zaki yi kewata kuwa.?" Kallonsa kawai take yayin data gagara furta masa komai sai wata soyayyar sa take ji tana qara shigarta, ta ko ina jikin ta shi ma haka kallonta yake wanda shi ma yana cikin yanayi irin nata.

"Hak'iqa zanyi matuqar yin kewarka sosai sabo da ni sam ban saba da rashin ka ba, Besty ni sam bana jin cewar zan iya jure wannan ba sabo da yana da zafi sannan kuma da matuqar k'una sosai. Besty gaskiyar ita ce ni nayi matuqar sabo da kai shi yasa sam bana san na barka sabo da hakan zai yi matuqar cutar da ni sosai." "Besty shin ba zai yu ki dakatar da wannan auran ba? Ina nufin kawai ki fad'a wa Yaya Auwal cewar ke bakya sansa ta hakan ne shi da kansa zai dakatar da auran. Wannan ce kawai damar da kike da ita na kasancewa tare da ni na har abada to kawai kiyi hakan." Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Ita kuwa sai kallonsa take kallo sosai yayin take jin soyayyar sa na k'ara shigarta sosai, jin shirun shirun yayi yawa yasa ya sake daga rungumar da yayi mata ya tashi yayi tafiyar sa, ita kuwa ta bisa da kallo ba tare data dakatar da shi ba ya isa gida kai tsaye d'akin sa ya nufa.

Yayi tsaye jikin bango sai wani kallon photon su yake kallo sosai, ya shafi photon tare da sunbatar fuskar *Afnan* lokaci d'aya ya samu kansa da zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Cike da k'unci ya watsar da kayan da suke kan madubi tare da furta a'a, ihun sa ne yayi sanadin shigo da Mamie cikin d'akin da sauri ta isa inda yake tare da rungumasa jikin ta, ta shiga rarrashin sa tare da anbatar sunan sa ta riqa shi sun tafi sun zauna cike da nuna kulawa take magana da shi. "D'ana mai yake faruwa da kai ne haka dan Allah ka sanar da ni miye damuwar.?" Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake sanar da ita abin da yake faruwa, *"Adnan* shin kai kana san *Afnan* da aure ne.?" "Eh Mamie ina matuqar masifar qaunar ta sosai sannan kuma bana san na rasa ta ga shi kuma zata yi aure da Yaya Auwal. Mamie ni ban san ya zanyi ba rashin Besty zai yi matuqar cutar da ni sosai, amma duk da haka zan jure sannan kuma sam bana san ki sanar da kowa wannan musamman Papa, Mamie ina san kiyi man alkawarin cewa ke ba zaki ta'ba sanar da kowa wannan dan Allah." "Amma ďana hakan zai cutar da ni sosai ni kuma sam ba zanso hakan ba to ya kamata nayi wani abu, sabo da na dakatar da wannan auran sannan kuma na sanar da Abban ka shi ma zai iya taimaka." "A'a Mamie dan Allah karki yi please." Magana yake yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai, kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, ta amsa shi da ba zata sanar da kowa ba ya jinjina mata ka a lamar to ta shiga rarrashin sa tana ba shi magana...............




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/24, 7:49 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 27*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/



*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Saturday 22/01/2022*

*Time 08:51pm*

*Typing.................*


Bayan kwana biyu suna ta shirin tafiya gurin break past sai ga *Adnan* ya shigo, ya zauna sun fara gaisawa san nan ya shiga tambayar *Afnan.* "Abba Besty fa.?" "Tana d'akin ta." "Shikenan zan duba ta a can." Ya tashi ya nufi bedroom d'in *Afnan* sukam da kallo suka bi shi har ya shige, sannan suka juya suka nufi tebur domin yin break past. Ya shiga ciki tare da rufe k'ofar san nan ya juya da kallonsa ga gado, amma bai same ta a nan ba ya fad'a a zuciyarsa, "bata cikin nan to tana wane gurin ina kuma ta shiga ne.?" Ya juya zai fita k'arar da ya ji ne yasa shi juyo da fuskar sa nan kuwa yayi tozali da fuskar *Afnan.* Wacce take tsaye jikin k'ofar toilet d'aure take da towel a jikinta wanda tsayin sa bai fi cinya ba, wani irin kallo yake mata wanda ban san ta yanda zan iya fad'ar sa ba, ita ma haka irin wannan kallon take yi masa wanda ya gagara fahimtar mai take nufi da shi, wani irin kallo suke yiwa juna kallo sosai ba kuma tare da sun gaji da kallon juna ba. Bayan wani lokaci ya juya domin tafiya ba kuma tare da ya furta mata komai ba, yana ƙoƙarin bud'e k'ofa tayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa ya tsaya cak ba tare da ya juya ba ta ci gaba da magana.

"Besty mai ya saka zaka fita ba kuma tare daka furta min komai ba? Faɗa min wani abu shin ni na aikata maka wani zunubi ne gaskiyar zaka fad'a.?" Shiru bai amsa ba yayin da yake jin zuciyarsa tamkar wuta dan zafi, ganin bai jiyo da kallonsa gareta ba ya tabbatar mata da ba zai amsa ba, taci gaba da tafiya har ta isa inda yake ta fito ta gaban sa ya kau da fuskar sa daga gareta. "Besty ka amsa ni shin kai kana fishi da ni ne? To amma wane irin zunubi ne aikata maki dana cancanci irin wannan tsats'tsauran hukuncin daga gareka.?" Shiru har zuwa wannan lokacin bai amsa ta ba. "Besty naro e ka dan Allah ka sanar da ni laifin dana aikata maka please.?" Magana take cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai, ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. Kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, shi ma abin da yake yi kenan kamar ba zai yi magana ba mai ya gani kuma ya amsa ta. "Besty ni bana fishi dake kawai dai zan fita ne domin na baki dama ki shirya, to fatan kin fahimci abin da nake nufi yanzu ki tafi ki shirya idan kin qarasa to ki same ni a gida."

"Mai yasa kake hukunta ni haka shin yau ba zaka ta ya ni shirya wa ba? Besty ba yau bane rana ta farko da kai ka ganni a haka sannan kuma ko yaushe kana ta ya ni shirya wa, kamar dai yanda nake yi idan na same ka a haka to amma mai ya saka yau kake kau da kanka a kai na.?" Magana take yayin da hanayen ta suke shafar fuskarsa zuwa wuyan sa, sam ya kasa jure irin abin da take yi masa wannan yasa ya janye sa daga jikin sa, ya bud'e k'ofa yayi tafiyar sa ba tare daya furta mata komai ba ita kuwa ta bisa da kallo cike da jin mamakin sa sosai. "Mai yasa Besty yake fishi da ni mai ya saka sam baya san ya sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da shi? Yana cikin k'unci sosai amma kuma baya san ya sanar da ni, zanyi komai domin na taimake sa sabo da ya fita cikin wannan mummunan yanayin." Ta tafi ta shirya ta fito ta fara gaisawa da Ummu sannan ta nufi gurin *Adnan,* ta shiga ciki ta samu Mamie tana kwashe kayan abincin daga tebur zuwa kicin, ta nufi inda take tare da gaishe ta bayan sun gaisa ta shiga tambayar *Adnan.*

"Mamie Besty na fa.?" *"Afnan Adnan* ya fita ni nama yi tunanin cewa ku biyun kuna tare." "Ya fita to ina kuma ya tafi kenan.?" "Ban sani ba amma ki kira layin sa sai kuyi magana." "Ta jinjina mata ka a lamar to ta tashi ta fita Mamie ta bita da kallo tana girgiza ka, *Afnan* kuwa ta shiga kiran layin sa amma kuma wayar a kashe take, "Besty wai kana ina haka mai ya saka zaka kashe wayar ka ina fatan ba abin daya faru da kai? Ya Ubangiji ka hana wani mummunan abu ya faru da Besty na Allah ka kare shi a duk inda yake Amin ya hayyu ya kayyum." Ta koma kiran layin Abdallah ba jimawa ya d'aga ta anbaci sunan sa tare da tambayar sa. "Abdallah kana ina.?" "ina office." "Shin kaga Besty na kuwa.?" "Eh yana office amma baya cikin kyakkyawan yanayi." "Na gode sosai sai na shigo." Ya amsa ta da to da kuma haka suka yi sallama, ta shiga mota ta nufi office ta isa office cikin hanzari ta shiga ciki ta samu *Adnan* kwance cikin kujera, ta nufi firij ta d'auko robar ruwa sannan ta nufi gurin da yake ta zauna tare da bud'e jakar ta, ta d'auko maganin sa tare da kai kallonta garesa cikin kwantar da murya take magana.

"Besty tin da ba zaka sanar da ni damuwar ka ba shikenan ba zan matsa maka ba, amma yanzu da akwai buqatar ka sha magani sabo da zai taimaka maka sosai." "Kiyi hak'uri ni kawai nayi mafarki da wannan matar ne shi yasa kika ganni a haka, Besty ni na rasa wacece wannan matar da take zomin ku san ko yaushe a cikin barci na. Yanayin yana da matuqar ban tausayi sosai hakan yana saka wa naji wani iri sosai, Besty ban san komai a game da wannan matar ba amma kuma ni nayi matuqar damuwa sosai a kanta. Besty to ya idan kuma wannan mafarkin nawa gaskiya ne fa mai zai faru da wannan matar kenan.?" Magana yake cike da firgici k'unci da 'bacin rai yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. "Ka dena damuwa Besty wannan kawai mafarki ne kuma mafarki ba gaskiya bane, to ka kwantar da hankalin ka ka ji ko yanzu ka sha magani please."

Ya jinjina mata ka a lamar to nan kuwa ta fara ba shi magani ya kuma sha ba gardama, bayan ya qarasa sha ta d'ora kansa a kan cinyarta tana shafar kansa zuwa bayan sa, ta qara da sunbatarsa ba jimawa sosai barci ya d'auke sa yayin da ita kuma ta rufe shi dana mujiya tana kallonsa. Ya jima sosai yana barci sannan ya farka ta had'a masa madara ya sha, bayan wani lokaci suka tashi suka nufi gida haka dai kwana ki suka riqa shigewa, zuwa yanzu saura kwana biyar auran *Afnan* da Auwal kwance take amma ba barci take ba, waya take da Yayan ta kuma masoyin ta wato *Adyan. "Alishart* fad'a min wani abu shin *Adnan* qlau yake kuwa? A 'yan kwana biyun nan sam bana gane masa shin wani abu yana faruwa da shi ne.?" *"Yaya Adyan* shi ya damu ne sosai sabo da Aunty zata yi aure da Yaya Auwal." Cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana. *"Alishart* wai kina san ki fad'a min cewar *Afnan* zata yi aure da wani daban ba *Adnan* ba.?" Ta amsa shi da eh yaci gaba yana cewa, *"Alishart* amma mai ya saka *Afnan* zata cutar da *Adnan* ta wannan hanyar? Hakan sam ba adalci bane kuma shi bai cancanci hakan daga gareta ba, zanyi magana da shi yanzu zan koma kiran ki an jima." Ta amsa shi da to da kuma haka suka yi sallama nan ya shiga kiran layin *Adnan* wanda sai a karo na uku ya d'aga.

*"Adnan* qlau kake kuwa fad'a min shin ka shirya fad'uwa a soyayyar ka? *Adnan* kana san *Afnan* sosai to ya kamata kayi koma miye domin ka same ta, ni zan taimake ka a kan hakan to ya zama dole ka jajirce a kan soyayyar ka domin kayi narasa. *Adnan* har yanzu kana da damar da zaka kasance muji ga *Afnan* to kawai ka tabbatar kayi hakan ka ji ko." *"Adyan* hakan sam ba shi da sauki kamar yanda kake tunani shi ďin ahalin su ne, Kakan su ďaya kuma shi ne wanda ya bada auran Besty ga Yaya Auwal. To bana jin ni zan iya dakatar da auran amma na sanar da Besty ta dakatar da auran, amma kuma har yanzu banji komai daga gareta ba to ina tunanin ko ita ma ta amince da auran, shi yasa nayi shiru sabo da ba wani abin da zan iya."

*"Adnan* har yanzu kana da damar da zaka ceci soyayyar ka, kawai ka fuskanci *Afnan* ka bai yana soyayyar ka a gareta kasa taji ba zata rayu ba sai da kai. *Adnan* kayi komai domin ka same ta zan shigo domin na ta ya ka wannan yak'in." Sun jima sosai suna magana sannan daga bisani suka yi sallama ai kuwa tin daga wannan ranar, *Adyan* ya fara shirin tafiya gida Nigeria bayan kwana uku jirginsu ya tashi zuwa Nigerian. Tare suke dukansu sun sauka a garin Abuja bayan kwana biyu suka nufi Kaduna, wani yammaci zaune suke a part d'in Anwar sun jima a zaune amma duk da haka ba mai magana a cikin su, *Afnan* ta anbaci sunan sa katin ta furta komai suka ji a na buga masu k'ofa, Amal ce wacce ta tafi ta bud'e k'ofa ta dawo tare da Auwal ya isa gurin Anwar ya zauna. Ya ba shi hanu sun gaisa su Anisa sun gaishe sa *Adnan* ya tashi tare da fad'ar sunan *Afnan.* "Besty zan tafi zamu ci gaba an jima." "Shikenan zaka iya tafiya amma idan ka tafi to karka ta'ba dawo wa gareni, wannan hukunci na kenan kuma ba zan ta'ba canja hakan ba."

Tana kai k'arshen maganar ta ta tashi ta nufi d'akin ta ya anbaci sunan ta amma bata amsa, ya juya zai fita Anwar yayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. *"Adnan* ka same ta a ciki na tabbata komai zai yi daidai insha Allah, am yauwa idan ka shiga ciki to ka tabbatar ka rufe k'ofar daga ciki sabo da wani zai iya takura ku biyun." Ya jinjina masa ka ya juya ya nufi d'akin *Afnan* cike da k'unci Auwal ya anbaci sunan Anwar. "Anwar kai wane irin Yaya ne taya zaka had'a qanwarka da wani daban? Anwar mai kake aikata wa ne gobe ne za a yi bikin saka ta lalle jibi za a d'aura mana aure amma duk da haka kana had'a ta da wani mai yasa.?" Magana yake cike da k'unci sosai Anwar kuwa sai wani kallonsa yake yana murmushi, cike da izza da gadara yake magana da shi. "Kanka a ke ji wai mahaukaci ya fad'a rijiya ni bani da lokacin magana da kai sabo ina da abin yi, domin naga a lamar kai baka da abin yi Anisa tashi mu shiga ciki wannan umurni ne." Bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta tashi suka shiga ciki cike da k'unci shi ma ya juya ya fita.........





*BY. B. U. A.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login