Showing 102001 words to 105000 words out of 142761 words
Chapter 35 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
k'unci na, ko damuwa ta rashin lafiya ta kuma ita ce babban qalubale a garesu, su ďin sun raine ni da kyau sannan kuma sun bani duka soyayyar su gaba ďaya. Su ďin suna so na da gaba d'aya rayuwar su amma kuma a haka kake san na yarda da abin da kake fad'a, Aboki ni nan nafi kowa sanin irin yanda iyayena suke qauna ta sosai to wannan kawai ya isa, sabo da ba wani abin da zai canja wannan har abada Papa da Mamie sune kawai iyayena, hakan ba zai canja ba to kama dena fad'ar abin da kake fad'a yanzu, sannan kuma kar kowa ya san da gaskiyar ka ji ko."
"Aboki nima ina jin duk irin abin da kake ji a yanzu, sannan kuma nima ba zan jure rashin a salin iyayena ba ina nufin Appa da Ammie, sabo da sune kawai iyayena wad'an da nake alfahari dasu. Sannan kuma ba zan tab'a barin susan da wannan ba, to ya kamata mu birne wannan sirrin na har abada dan Allah." "Eh Aboki ba wanda zai san da wannan sirrin na har abada, nayi alkawari to kai ma kayi alkawari ka ji ko dan Allah." "Eh nima nayi alkawari ba wanda zai san da wannan sirrin, amma kuma ya zama dole mu gano a salin gaskiyar abin da ya faru damu, shin zaka taimaken a kan hakan please.?" "Eh zanyi nima zan taimaka nayi alkawari insha Allah." Ya jinjina masa ka a lamar to lokaci d'aya kuma suka k'ara yin hugging juna, wanda kuma har zuwa wannan lokacin idanuwansu basu dena zubar da kwalla ba. Mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, bayan wani lokaci suka sake juna daga hugging d'in da suka yi.
Nan kuwa suka shiga tunani da nazarin yanda zasu gudanar da binkicen su, sun jima sosai a nan wanda sai dare sannan suka koma gida, *Adeel* ya shiga tambayar su inda suka tafi da kuma dalilin da yasa basu shiga asibiti ba. *Adnan* ne wanda yake amsa shi yayin da *Adyan* ya gagara furta masa komai. *"Adeel* abin shi ne mun tafi wani muhimmin guri ne sannan kuma mun gaji sosai, to shi yasa muka nai mi wani guri muka huta wannan dalilin ne yasa bamu iya tafiya asibiti ba. To ya jikin Mum fatan tana samun sauki ya Kaka tana lafiya.?" "Kaka tana lafiya amma Mum bata cikin kyakkyawan yanayi ni na damu sosai a kanta, nayi ta k'oqarin kiran *Adyan* yazo ya duba ta amma bai d'aga kira na ba, kai kuma layin ka baya tafiya shi yasa na fara damu sosai a kanku biyun, abin farin cikin kuna cikin k'oshin lafiya na ji dad'in hakan sosai." "Muna godiya sosai *Adeel* kayi hak'uri da ban d'aga kiran ka ba, hakan ya faru ne sabo da na manta waya na a office to ina mai baka hak'uri." "Ba komai d'an uwa amma qlau kuke ka? Na ganku sai a hankali kamar kuna k'unci sosai."
Lokaci d'aya suka kai kallonsu ga juna sun kuma mai da kallonsu garesa, "a'a *Adeel* qlau muke muna lafiya kawai ka yarda da ni." Ya jinjina masa ka a lamar to *Adyan* ya anbaci sunan *Adeel* yana cewa. *"Adeel* na gaji sosai ina san zan shiga ciki na kwanta, Aboki kai ma ya kamata ka huta ka ji ko." Ya jinjina masa ka a lamar to suna k'oqarin tafiya *Adeel* ya dakatar dasu. "Am ni zan koma asibiti kuma a can zan kwana to sai da safe asuba ta gari." *"Adeel* ka kula sosai sannan kuma ka kula da Mum da Kaka, sannan kuma idan akwai buqatar nazo ko Aboki to kawai ka kira ni ka ji ko." "Na gode sosai *Adnan Adyan* ina godiya sosai da kulawa Allah ya saka da alkhairi Amin." Sun amsa shi da Amin ya juya yayi tafiyar sa sun bisa da kallo suna girgiza ka, bayan tafiyar sa sun mai da kallonsu ga juna sun jinjina wa juna ka sannan suka nufi bedroom, tafiya yake wani tamkar mara lafiya cikin hanzari *Afnan* ta tashi zaune tare da fad'ar sunan sa.
"Besty qlau kake kuwa fad'a min mai yake faruwa da kai ne haka.?" Ta k'ara shi sun tafi sun zauna sai tambayar sa take mai yake faruwa da shi. "Ba komai Besty ina lafiya kawai dai na gaji ne shi yasa kika ganni a haka." "Besty yau ka jima sosai a waje shi yasa gajiya tayi ma yawa, to yanzu ka samu ka watsa ruwa sai ka sha magani ka kwanta ka ji ko." Ya amsa ta da to ta taya shi ya cire kayan sa sannan suka nufi ban d'aki, ba jimawa suka fito ta taimaka masa ya shirya sannan ta fita, bayan wani lokaci ta dawo hanun ta ri e da kofin madara nan kuwa ta shiga ba shi madara, ya sha kad'an ya furta mata cewar ya k'oshi ta a jiye kofin madara ta shiga ba shi magani, ya sha tare dayi mata godiya ya sauke kallonsa ga cikin ta tare da shafar cikin yana sunbata. "I LUV U MY Child I Love you so much." Ya fad'a tare da qara sunbatar cikin ita kuwa sai wani kallonsa take tana murmushi, ba jimawa yayi barci ita kuwa ta rufe sa da ido tana kallonsa, ita ma kwanta wa tayi tare da rungumasa jikin sa ba jimawa sosai barci ya d'auke ta.
Haka yake ko a gurin *Adyan* bayan kwana biyu zaune yake office tare da *Adnan,* Umma ta turo k'ofa ta shigo sun shiga yi mata sannu da zuwa, ta amsa da to sun bata guri ta zauna bayan sun gaisa taci gaba da magana. *"Adyan Adnan* dan Allah ko zamu iya magana.?" Lokaci d'aya dukansu suka jinjina mata ka tare da furta mata eh, tayi shiru kad'an sannan taci gaba da magana. *"Adnan* shin da akwai abin da kuke b'oye mana ne? Sabo da kwana biyun na kun canja sannan kuma *Adyan* ya dena duba Aisha gaba d'aya ko kusa da ita kun dena zuwa, *Adnan* shin ku biyun kun samu wani sab'ani da *Adeel?* Ko Mummyn sa ta aikata muku wani abu cikin rashin sani? *Adyan* mu kamar ahali ne to ba zanso naga rashin jituwa tana shiga tsakanin mu ba. To naro e ku dan Allah da girman Allah ku sanar dani abin da yake faruwa a tsakanin ku da *Adeel.?"*
*Adnan* ne wanda ya amsa ta yayin da *Adyan* ya rufe su da ido, kasancewar ba komai ya fahimta ba cikin abin data fad'a cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Kaka abin shi ne mu sam ba wata rashin jituwa da take tsakanin mu da *Adeel,* kawai dai mun damu ne da yanayin Mum sannan kuma muna tinani a kan yaran da take yawan maganar su. Mu muna san mu san ko tana da wasu yaran bayan *Adeel,* Kaka shin ke ce wacce ta karb'i aihuwar Mum.?" Ta girgiza ka tana furta, "a'a sabo da tiyata a kayi mata duk da cewar zata iya aihuwa da kanta, amma Prof ya tilassa a kayi mata tiyata sannan kuma *Addel* ne kawai yaron da a ka ciro mata. Haka kuma yasa a ka cire mata mahaifa ba tare da sanin taba, kawai yayi hakan ne sabo da cikar burin sa na samun d'a d'aya kamar dai yanda yake fata."
Nan kuwa ta shiga sanar dasu komai a game da 'yarta dama rayuwar ta gaba d'aya, *"Adnan* yarinya ta tana da kirki sosai kaddaran ta ce ta canja komai, to ina ga ya kamata ku dena shakka a kanta ku yarda da ni, sabo da ni na sanar daku duka gaskiyar gaba d'aya a game da ita." Cike da mamakin abin data fad'a yake magana. "Kiyi hak'uri Kaka muna masu baki hak'uri dan Allah ki yafe mana." Ta amsa shi da ba komai ta tashi tayi tafiyarta sun bita da kallo har ta fice, bayan tafiyar ta *Adnan* ya mai da kallonsa ga *Adyan* lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi kallonsa yake ya shiga tambayar sa abin da suke magana, *Adnan* ya shiga sanar da shi komai ya kuma ci gaba yana cewa.............................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/12, 10:08 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 42*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Friday 11/02/2022*
*Time 09:25pm*
*Typing..............*
"Aboki hakan yana nufin cewar Mum da Kaka bama su san da labarin mu ba, to ina ga sam ba buqatar muci gaba da cutar dasu, ya kamata mu mai da hankalin mu gurin Mum ta samu lafiya." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana. "Aboki ina matuqar mamakin yanda Prof ya aikata irin wannan mummunan zunubin, ta ya ma har zai yi tunanin cutar da Mum har haka? Da fari ya raba ta da yaranta sannan kuma yasa an cire mata mahaifa, daga bisani kuma ya sake ta ya kuma d'auke *Adeel* daga gareta. Ya tafi ya barta cikin mummunan yanayi na ciwon hauka, duk da cewar yana da damar da zai iya taimakon ta, lallai wannan ya k'ware sosai gurin iya zalunci lallai ya kamata mu had'u da shi. Waye shi mai yasa ya aikata duka wannan.?"
"Aboki ba shi zamu fara had'uwa da shi ba da Dr Salim zamu fara had'uwa, sabo da shi ne wanda zai sanar damu duka gaskiyar cikin sauk'i, idan muka san duka gaskiyar sannan sai mu sam ta yanda zamu fuskanci Prof. Wannan shi ne abin da zamu yi zamu shirya komai ta yanda wani ba zai san gaskiyar ba, to kawai ka kwantar da hankalin ka mubi komai a hankali, yanzu abu mai muhimmanci shi ne Mum ta samu lafiya ta dawo haiyacinta. Sannan kuma mu kula da ita yanda ya kamata mu kasance yara na gari a gareta, shin zaka yi hakan kuwa.?" Yayi shiru na jim kad'an sannan ya jinjina masa ka tare da furta masa eh, shi ma ya jinjina masa ka tare da yin hugging d'in sa. Ai kuwa haka suka d'ora duk wata kulawar su a kan Mum, lokaci d'aya *Adyan* ya fara shirin yi mata aiki an yi shirin komai, bayan kwana biyar a kayi mata aiki ta samu tsayin kwana biyu sannan ta farka.
Wani yammaci zaune suke dukansu a nan d'akin da Mum take, lokaci d'aya ta farka daga dogon barcin da take, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e sai wani kallonsu take, suma haka kallonta suke kallo sosai cikin hanzari Umma ta shiga anbatar sunan ta. "Aisha kin farka to ya jikin ki fatan kina samun sauki sosai.?" Ta jinjina mata ka tare da furta mata, "eh Umma ina lafiya na samu sauk'i sosai to fad'a min wani abu ina yarona? Karki fad'a min cewar Prof bai kawo shi gareni ba Umma fad'a min ina *Adeel.?"* Dukansu kallonta suke ba kuma tare da sun furta mata komai ba.
"Umma ni na san cewar Prof ba zai tab'a barin *Adeel* gareni ba, zai yi komai domin ya d'auke sa daga gareni shi sam ba shi da adalci, ban san har tsayin wane lokaci zai d'auka yana cutar da ni ba. Naso a ce ya bani damar da zan kasance uwa ta gari ga yarona, ta yanda zansa yarona ya zama likita domin ya samu damar da zai kula da kansa sosai, ko kuma dai ya zama lauya ta yanda zai yi yak'i da zama irin su Prof. Amma ko yanzu ni zan tabbatar cewa yarona ya kasance abin da zanyi alfahari da shi sosai insha Allah, wannan alkawari na kuma zan cika alkawari na insha Allah, Umma ni nayi matuqar kewar yarona sosai ina kewar *Adeel* sosai. Sabo da har yanzu shi yaro ne shekarun sa uku kawai to dole yana buqatar wacce zata kula da shi sosai, kamar dai ni ko kuma ke amma kuma Prof ya d'auke sa daga gareni. Shi mugu ne ya cutar da ni sosai to ina tsoron kar ya cutar da yarona, to ya kamata na tafi nayi magana da shi yanzu."
Ta yunk'ura zata tashi da sauri Umma ta dakatar da ita, ta hanyar ri e hanun ta tana girgiza mata ka tare da furta. "A'a 'yata sam bakya buqatar had'uwa da Prof Abas a yanzu, sabo da Ubangiji ya daidai komai a yanzu. Da fari *Adeel* ya dawo garemu yanzu kuma kin samu lafiya, a ta dalilin *Adnan da Adyan* wanda godiya ta ba zata biyasu ba, sunyi komai domin ganin kin samu lafiya kuma Alhamdulallah daga k'arshe sunyi nasara, to ya kamata ki natsu ki kwantar da hankalin ki ta yanda lafiya zata samu damar shigarki kin ji ko." "Umma hankali ba zai tab'a kwanciya ba har sai idan na had'u da yarona, to ya kamata na had'u da Prof domin na karb'i yarona. Har yanzu shi yaro ne to dole yana buqata na sosai a tare da shi to kawai ki barni na tafi dan Allah." "Aisha yaronki yana tare dake sannan kuma shi ďin yana kulawa dake sosai, duk da cewar baya tare dake amma kuma ya rayu da soyayyar ki, shi d'in yaron kirki ne kamar abokan sa wad'an da suka kula dake, Aisha ina farin cikin gabatar maki da yaronki *Adeel* kuma jikana, Aisha wannan shi ne yaronki wanda zan iya kiran sa da na musamman." Aisha ta sauke kallonta ga fuskar *Adeel* wanda shi ma kallonta yake kallo sosai, sun jima a haka sannan ta mai da kallonta ga Umma tare da fad'ar sunan ta.
"Umma nifa a haiyacina nake waye wannan da kike kiran sa da ďana? Shi ďana yaro ne d'an shekaru uku to shi nake buqatar had'uwa da shi ba wannan ba, yanzu kawai ki fad'a min ina ďana *Adeel* yake.?" "Aisha lokaci ya tafi sosai shekaru masu yawa sun shige, 'yata yanzu yaronki ya girma sosai wanda har yake kulawa dake. Aisha shekaru ashirin da biyu kenan da kike magana a kai, yanzu yaronki yana da shekaru ashirin da biyar ne ya dawo garemu bayan wani tsayin lokaci, to kawai kiyi farin ciki sosai 'yata sabo da abubuwa sun fara daidai ta kin ji ko." "Umma wai gaskiyar kike fad'a min kuwa yanzu wannan *Adeel* ya girma haka.?" Ta jinjina mata ka tare da furta mata eh tana murmushi, Aisha ta mai da kallonta ga fuskar *Adeel* lokaci ďaya suka yi ido biyu da juna, kasancewar shi ma kallonta yake kallo sosai yayin da tausayin ta yayi yawan gaske a tare da shi.
Sun jima sosai a haka lokaci d'aya ta fara zubar da kwalla shi ma abin da yake yi kenan, cikin wata 'yar murya take furta masa kalmar zo nan ďana, cike da d'auki ya tashi daga inda yake ya nufi gurin ta har yana gudu, yayin da yake fad'ar sunan ta Mummy na yana isa inda take sun wani rungume juna. Ta rungumasa jikin ta sosai tana sunbatarsa shi kuwa yayi kwance jikin ta yana fad'ar sunan ta, Umma sai kallonsu take tana murmushi hakama su *Adyan* kallonsu suke. *Adyan* ya juya zai fita da sauri *Adnan* ya ri e hanun sa tare da kai kallonsa garesa yana girgiza masa ka a lamar a'a, bayan sun sake juna daga hugging d'in da suka yi Aisha ta shafi fuskarsa tare da sunbatarsa tana furta masa kalmar.
"Kayi hak'uri ďana da lokaci bai bani damar da zan kasance uwa ta gari a gareka ba, ka rayu ba tare daka samu kulawa ta ba ni ban tab'a kasancewa uwa a gareka ba, amma kuma duk da haka kai baka gujeni ba sannan kuma ka kula da ni sosai. Na gode ďana ina matuqar yin alfahari da kai sosai zanyi farin ciki sosai idan ka sanar da ni, cewar kana matsayin likita ko lauya dan Allah karka fad'a min cewar baka yi karatu ba. *Adeel* ba zanso ka rayu kamar yanda ni na rayu ba, na rayu ba tare da nayi karatun boko ba wanda wannan ne abin da ya bawa Dadyn ka damar yaudara ta. A gaba na yake magana da Dr Salim amma sam bana fahimtar abin da suke fad'a, sabo da turanci suke wanda da a ce nayi karatu to da duka wannan bai faru ba, to kayi hak'uri dana kasance a haka na kasa kulawa da kai dan Allah ka yafemin ka ji ko ka gafarce ni."
Da sauri ya rufe mata baki yana girgiza mata ka, cike da qauna da soyayya yake yi mata magana. "A'a Mum wannan sam ba laifin ki bane to sam ba buqatar ki ba da hak'uri, sannan kuma nayi karatu ina matakin degree ne kiyi hak'uri da ban kasance matsayin Doctor ko Barrister ba. Ina mai baki hak'uri a game