Showing 72001 words to 75000 words out of 142761 words
Chapter 25 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
(yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Tuesday 25/01/2022*
*Time 11:53am*
*Typing................*
Sun isa asibiti cikin hanzari Doctor's suka shiga da shi ciki yayin da suka bar Mamie da *Alishart* suna kai kawo. Baifi da mintuna sha biyar ba zuwa ashirin sai ga Papa ya ƙaraso, yanayin daya samu su *Alishart* a ciki ya tabbatar masa da cewar da akwai matsala, cike da firgici da rud'ani yake tambayar Mamie mai yake faruwa. "Kawai shi ya suma ne.?" Cike da firgici yake magana, "mine ta ya a kai ya suma mai ya faru da shi ne shin ke kin barsa ya aikata wanin abin daya gajiyar da shi ne? Haka kawai ba zai suma ba dole wani abu ya faru da shi, karki fad'a min cewar wai ba abin daya faru da shi kawai ki sanar da ni gaskiyar mai ya faru da shi.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi, "ban sani ba ni ina gidan su *Afnan Alishart* ta kira take sanar da ni ba shi da lafiya, na koma gida nayi ta k'oqarin tambayarsa mai yake damunsa, amma sai ya amsa ni da cewar qlau yake daga nan kuma sai ya suma." Papa ya mai da kallonsa ga fuskar *Alishart* tare da fad'ar sunan ta.
*"Alishart* fad'a min mai ya faru da shi kafin rashin lafiya.?" "Papa ni ina shirin fita zuwa gidan su Aunty ya shigo gida kuma ko a lokacin baya cikin kyakkyawan yanayi." "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un ya Allah ka bawa *Adnan* lafiya Allahumma Amin." dukansu sun amsa da Amin bayan wani lokaci da suka d'auka a ciki tare da shi sun fito, cikin hanzari tare da nuna kulawa Papa ya isa garesu yana tambayar su jikin yaronsa. Dr Habib ne yake magana da shi, *"Abban Adnan* kawai ka saman a office kuzo tare da Madam." Sun amsa da to sun bisa a baya sun shiga office d'in bayan sun zauna Dr Habib yaci gaba da magana. *"Abban Adnan* a gaskiya yanayin yaronku yayi tsauri sosai, a kullum kuma a ko yaushe ina yawan fad'a muku cewar yaronku yana matuqar buqatar farin ciki sosai, hakama yaronku yana matuqar buqatar kulawa sosai domin lafiyar sa. Amma sam bakwa kulawa da shi yanda ya dace mai yasa kuke wasa da rayuwar sa har haka, ku fad'a min wani abu shin kuna buqatar ku rasa yaronku ne na har abada.?" Lokaci d'aya dukansu suka furta masa kalmar a'a Papa yaci gaba da magana.
"Doctor dan Allah ka dena fad'ar haka wallahi muna iya k'oqarin mu gurin ganin *Adnan* yayi farin ciki sosai. Sannan kuma muna matuqar ba shi kulawa sosai munyi matuqar damuwa da shi sosai, amma a 'yan kwana biyun nan na dena gane masa kamar dai shi yana 'boye mana wani abu a game da shi, Doctor dan Allah ka sanar da ni a salin gaskiyar abin da yake faruwa da yarona.?" Yayi shiru yana wani jinjina ka sannan daga bisani ya fara magana. *"Abban Adnan* gaskiya naji mamaki sosai daka fad'a min cewar kuna kulawa da *Adnan* sosai, sabo a binkicen da muka yi masa mun fahimci cewar yana tare da k'uncin mai matuqar girman gaske sosai, wannan ciwon da yake da shi a k'arkashin zuciyar sa yana k'ara girma sosai, wanda idan ya jima a haka ko k'uncin sa yafi haka to zuciyar sa zata buga ko ta fashe. Wanda kuma a wannan lokacin ni sai dai kawai na baku hak'uri sabo da kuwa yaronku ba zai rayu ba." "A'a hakan ba zata faru da yarona ba ni ba zan ta'ba barin hakan ta faru da shi ba, to ya kamata nayi wani abu domin na dakatar auran sabo da ba zan jure rasa ďana ba." Ta tashi da sauri har tana gudu ta fita office ďin Papa shi ma tashi yayi ya bita a baya cike da jin mamakin abin data fad'a. Dr Habib ya bisu da kallo yana girgiza ka Mamie na k'oqarin shiga d'akin da *Adnan* yake, Papa yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta.
A can gurin *Afnan* kuwa ta dawo gida cikin wani irin mummunan yanayi mara kyau, yayin da take kuka amma zuwa wannan lokacin kukan zuci take yayin da idanuwanta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai ta samu parlour cike da jama'a, sai jiran dawowar ta suke domin fara shagalin sanya ta lalle. Kai tsaye d'akin ta ta nufa ba tare data furta wa kowa komai ba, su kuwa sun shiga fad'ar sunan sa yayin da wasun su suke kiran ta da Amarya. Cike da k'unci ta shige d'akin ta tare da rufe k'ofar cike da firgici Ummu ta shiga buga mata k'ofa tare da fad'ar sunan ta, amma hakan sam bai sanya ta bud'e k'ofar ba sai tunani take da nazarin abin da *Adnan* ya fad'a mata. "A'a ni sam ba zan bar wani mummunan abu ya faru da Besty na ba, to lallai ya zama dole da nayi wani abu domin na dakatar da auran nan. Sam ban damu da duk abin da zai faru ba idan har zan kasance tare da abin da nafi qauna, ina san Besty sosai ina matuqar masifar qaunar sa sosai to ya zama dole nayi koma miye domin na same sa."
Tana kai k'arshen maganar ta ta juya ta nufi hanyar fita ta bud'e k'ofar ta fito, ta samu su Ummu tsaye a gefen k'ofa ba wanda tayi wa magana sai ma juya da tayi domin fita, da sauri Hajiya ta ri e hanun ta tare da fad'ar sunan ta. *"Afnan* wai mai kike yi ne haka? Tin d'azu muke nan zaune muna jiran dawowar ki, domin fara shagalin shafa maki lalle kin shigo ba tare da kinyi wa kowa magana ba. Muna ta k'oqarin ganin kinyi magana amma baki amsa kowa ba yanzu kuma kin fito zaki fita, *Afnan* shin ko zaki iya sanar damu a salin abin da yake faruwa dake.?" Shiru bata yi magana ba sai ma k'oqarin cire hanun ta cikin na Hajiya take domin tafiya, ganin hakan ne yasa Hajiya tace da Hafsat ta shafa mata lalle. Tana k'oqarin shafa mata lalle *Afnan* ta bige hanun ta tare da furta mata kalmar.
"A'a karki yi kuskuran shafa min wannan lallen sabo da ba zan iya cire fatar jiki na ba, to ya kamata dukanku da kuke a nan ku sani na fasa auran Yaya Auwal ni ba zan aure sa ba." wani irin kallo suke yi mata mai cike da jin mamakin ta sosai, *"Afnan* qlau kike kuwa.?" "Eh Aunty Nafisa ina lafiya kawai dai ba zan aure sa ba." Cike da 'bacin rai Hajiya ta kifa mata wani wawan mari ta kuma ci gaba da fad'a da ita. *"Afnan* to bara kiji wallahi tallahi ko zaki mutu sai an yi auran ki da Auwal, wannan umurni ne bawai shawara ba to ya kamata ki yarda da gaskiyar Hafsat ki shafa mata lalle." Da sauri ta fizge hanun ta daga hanun Hajiya ta nufi kicin ba jimawa ta fito, hanun ta ri e da yuk'a dukansu wani irin kallo suke yi mata mai cike da jin mamakin ta, "na rantse duk a kayi kuskure shafa min lalle to fa tabbas sai na kashe kai na, ba kuma zan kashe kai na cikin sauk'i ba tabbas zan a zabtar da kai kafin na mutu kamar haka." Ta rufe idanuwan ta tare da yanka hanayen ta duka biyun jini kuwa sai zuba yake, da sauri Ummu ta nufi inda take tana fad'ar sunan ta tana k'oqarin rik'a ta, tayi saurin dakatar da ita ta hanyar furta mata a'a ta mai da kallonta ga Hajiya taci gaba da magana.
"Hajiya zaki iya duka na idan kina so amma kuma ni na za'bi mutuwa fiye da nayi aure da Yaya Auwal, ni ban ta'ba san shi ba sabo da ni da kuma zuciya ta Besty kawai muke qauna, sannan kuma shi ne kawai wanda zai kasance Mujina na har abada wannan alkawari ne." Tana kai k'arshen maganar ta ta juya ta nufi hanyar fita cikin hanzari Ummu ta anbaci sunan ta. *"Afnan* d'an dakata kina zubar da jini ya kamata mu tafi asibiti yanzu." "A'a Ummu qlau nake Besty na zai kula da ni sosai to sam ba buqatar ki damu kinji ko." Taci gaba da tafiya har ta fice daga parlour ta nufi gurin *Adnan* domin had'uwa da shi. Ta isa gidan tin a gate Habu ya sanar da ita cewar suna asibiti, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali ta fita ta shiga taxy ta nufi asibiti.
*"Ummu Adnan* shin da akwai abin da kike 'boye min gaskiyar zaki fad'a.?" Magana yake cike da k'unci da 'bacin rai cikin firgici rud'ani tare da tsoro da fargaba take magana. "Kayi hak'uri ni bani da wani za'bi ne sabo da ya buqaci da karna sanar da kai, shi ya damu ne sosai a kan auran da *Afnan* zata yi da Auwal, sabo da yana qaunar ta sosai kuma yana buqatar auran ta sosai. A kullum yana cikin kukan rashin ta hakan yana matuqar saka shi k'unci sosai sannan kuma." Papa ya dakatar da ita cikin tsawa tare da d'aga murya, "ya isa haka kiyi shiru mai yasa ke sam ba kiyi tunanin sanar da ni ba? Da a ce ke kin sanar da ni gaskiyar to da nayi komai domin ganin ya samu farin ciki sosai, ni Abban sa to zanyi komai sabo da ya kasance cikin farin ciki to mai yasa ke ba kiyi tinani a kan hakan ba? Sabo da kuskuran ki yanzu yana kwance ba shi da lafiya sosai ke ce wacce take da alhakin duka wannan, ke wace irin uwa ce taya zaki yi k'oqarin cutar da yaronmu har haka? Hak'iqa kin aikata min babban zunubi wanda yake da matuqar girma sosai."
"Wanda har ban san ta yanda ni zan hukunta ki ba shikenan yanzu kawai ki tafi, ki bar nan kuma karki koma dawowa sannan kuma idan har wani mummunan abu ya faru da yarona, to fa ki sani ko ni ban san wane irin hukunci zan yanke maki ba, to kiyi fatan ya samu lafiya ta yanda hukuncin ki zai zo maki da sauk'i sosai to yanzu ki tafi ni zan kula da ďana." "A'a sam bai kamata na tafi ba sabo da yarona yana buqata na a nan, to dan Allah kayi hak'uri ka yafemin please." "Asma'u nace ki tafi to kawai ki tafi kinji ko ki tafi." Bata da wani za'bi wanda wannan dalilin ne yasa ta juya domin tafiya, zuwan *Afnan* ne ya dakatar da ita daga tafiya, tafiya take tana wani rangaji kamar zata fad'i sai wani lumshe ido take yayin da hanayen ta suke ta zubar da jini, da sauri Mamie ta ri e ta tare da rungumata jikin ta sun shiga anbatar sunan ta, yayin da ita kuma sunan *Adnan* take fad'a.
"Papa dan Allah ku yafemin sannan kuma karku yi fishi da ni, sabo da ni Besty yana kwance asibiti yanzu ba jimawa sosai shi ya sanar da ni gaskiyar, Papa gaskiyar ita ce nima ina matuqar masifar qaunar Besty sosai ina sansa sosai. To dan Allah kayi komai domin ka dakatar da aure na da Yaya Auwal sabo da." Tana cikin magana ta suma hankalin su Papa ya dad'a tashi sosai, ya kira nurse sun shiga da ita ciki domin a duba ta bayan wani lokaci Dr Habib ya fito tare da sanar dasu cewar tana buqatar jini. "Shikenan mu tafi a duba nawa idan zai yi." "A'a jinin ka ba zai yi mata ba to ya kamata ka kira wani wanda za a duba." Ya jinjina masa ka a lamar to Dr Habib ya juya ya nufi office Papa ya sauke kallonsa ga Mamie tare da fad'ar sunan ta. "Asma'u kamar dai ni na fad'a maki cewar ki tafi to mai ya saka har yanzu kike tsaye a nan? Kawai ki tafi dan Allah ki bar nan sabo dake ne duka wannan ya faru, ke ce wacce take da alhakin duka wannan to kawai ki tafi." Cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa ta juya ta fice, yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai.
Bayan tafiyar ta Papa ya ciro wayar sa daga aljihu ya shiga kiran layin Abba, ba jimawa ya d'aga Papa ya shiga sanar da shi duk abin da yake faruwa. Abba ya shiga firgici sosai ya amsa shi da ga shi nan tafe sunyi sallama, Abba ya shiga kiran layin Anwar ya sanar da shi komai da Papa ya sanar da shi ya amsa shi dasu had'u asibiti. Ba wani d'aukan lokaci su Abba suka qaraso asibiti sun had'u da Papa cikin hanzari sun nufi office ďin Dr Habib, ya tashi sun nufi d'akin gwaji inda kuma a kayi narasa jinin Anwar yayi daidai da nata, nan a ka shiga d'ibar jinin sa bayan an qarasa an yi duk wani abin da za a yi, daga bisani a ka sanya wa *Afnan* jini Abba ya kira layin Baba dasu Ummu ya sanar dasu abin dake faruwa. Kafin su ankara asibitin ta d'auki taron jama'a sosai.
Misalin k'arfe 12:00pm jirginsu Appa ya sauka Abuja to kaduna, suna fitowa Airport *Adyan* yace da driver su nufi asibiti kasancewar *Alishart* ta sanar da shi komai a waya. Tare suke dasu Kaka wato Abba ko nace Mr President wanda yayo musu rakiya daga Abuja, sun samu su Abbu a nan Airport suna jiran isowar su, sun shiga mota dukansu sun nufi asibiti gurin *Adnan* kamar dai yanda *Adyan* ya buqata..............
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/27, 10:50 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 30*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Wednesday 26/01/2022*
*Time 01:11am*
*Typing.................*
Sun samu rakiyar jama'ar su zan iya kiran sa da runduna sabo da suna da yawa sosai, ga tarin security sun isa asibiti ba wani d'aukan lokaci suka isa d'akin da *Adnan* yake. Cike da mamakin ganin su tamkar a mafarki dukansu sun shiga yi musu sannu da zuwa, sun amsa suna murmushi tare da sake fuska nan kuwa suka shiga gaisawa da juna. Tare da tambayar jikin *Adnan Adyan* ya shiga tambayar Papa abin da yake faruwa da shi, ya sanar da shi duka gaskiyar cike da firgicin abin daya fad'a yake magana. "Papa ni na san dole sai hakan ta faru da shi dalilin da yasa nazo nan kenan, abokina yana san *Afnan* sosai kuma ita ma tana qaunarsa sosai, wanda dukanmu a nan mun san da hakan to ya kamata a ce su biyun sun rayu da juna na har abada. Papa naro e ka karka bari na rasa abokina sabo da shi ďin aboki na gari ne a gareni, shi yasa nake fatan na rayu da shi Appa Kaka dan Allah kuyi k'oqarin daidai komai, domin idan wani abu ya faru da *Adnan* to fa nima." Da sauri Appa da Ammie suka rufe masa baki tare da furta masa a'a, hakama su Abbu abin da suke fad'a kenan har suna had'a baki.
"Karka fad'i komai ďana komai zai yi daidai insha Allah *Adnan* zai samu lafiya, hakama zai kasance muji ga abar qaunarsa wato *Afnan* insha Allah." "Da gaske.?" Appa ya jinjina masa ka a lamar eh shi ma ya jinjina masa ka yana murmushi, ya juya ya nufi gurin *Adnan* wanda yake kwance bama ya san inda yake ba, bayan tafiyar sa Appa ya sauke kallonsa ga fuskar Kaka wato Baba tare da isa inda yake, ya zauna gefen sa daga k'asa ya kama hanayen sa tare da fad'ar sunan sa. "Baba naro e ka daka bar wad'an nan masoyan biyu su rayu a tare, domin kaddaran su ta nuna cewa idan basu rayu a tare ba to fa zasu mutu a tare. Baba gaskiyar ita ce mu zamu yi farin ciki kawai ne idan har yaranmu suna farin ciki, sannan kuma ba zamu iya jure ganin su a cikin k'unci ba. Baba na tabbata ba wasu iyayen da zasu so ganin yaransu a cikin irin wannan mummunan yanayin, abin yana da matuqar zafi sannan kuma da