Showing 87001 words to 90000 words out of 142761 words

Chapter 30 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

da shi sannan ta zauna tare da fad'ar sunan sa.

*"Adeel* dan Allah ka sanar da ni gaskiyar abin da yake faruwa da kai.?" Yayi shiru kad'an sannan ya shiga sanar da ita komai magana yake cikin k'unci sosai yayin da yake kuka. "karka yi kuka ďana komai zai yi daidai to kawai ka jure ka kuma jajirce ka ji ko zo nan." Ya jinjina mata ka a lamar to ya k'ara matsawa kusa da ita kamar dai yanda ta buqata, ta rungumasa jikin sa tana d'an buga bayan sa bayan wasu 'yan mintuna ya tashi ya fita, ba tare daya san inda ya nufa ba tafiya kawai yake damuwarsa tana k'ara girma sosai. Hakan yasa yanayin sa ya fara canja wa sai wani rangaji yake tamkar zai fad'i, yasa hanun sa ya ri e k'irji yayin da yake furta kalmar wash abin damuwar shi ne a tsakiyar titi yake, motoci sai hon suke yi masa domin ya kauce wa hanya amma ina zuwa wannan lokacin ya fara fita haiyacinsa. Tin daga nesa ya hange sa wanda kuma ya gama fahimtar cewa sam baya cikin kyakkyawan yanayi, ganin yanda yake tsakanin motoci wad'an da kuma cikin sauri suke yasa shi koma wa gefen hanya yayi parking.

Ya fito mota ya nufi gurin sa da sauri har yana gudu cikin hanzari ya janyo sa jikin sa har suka fad'i, *Adnan* ya tashi tare da kai kallonsa garesa ya shiga fad'a da shi fad'a sosai. "Shin ka haukace da kake k'oqarin kashe kanka ko dai kai ka sha wani abin ne.?" "Dan Allah ka taimaki Mummy na." Yana fad'ar haka ya suma cike da firgici *Adnan* ya shiga jijjigasa yana furta masa kalmar, ka tashi amma bansa cike da rud'ani yasa wani ya taimaka masa sun sa shi mota ya nufi asibiti da shi. suna isa a ka shiga da shi ciki domin a duba bayan wani lokaci Doctor ya fito, *Adnan* ya shiga tambayar sa jikin sa yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "Am abin shi ne yana tare da tarin damuwa sosai to a yanzu yana matuqar buqatar hutu sosai, to ya kamata ya huta sannan kuma ka kula da shi sosai." Ya jinjina masa ka a lamar to bayan likitan ya tafi shi kuma ya shiga gurin *Adeel,* ya zauna gefe da shi sai wani kallonsa yake kallo sosai yayin da yake magana da zuciyarsa.

"Waye shi mai yasa yake cikin damuwa har haka? Mai ya yake faruwa da Mummyn sa sannan kuma mai ya saka yake san ya kashe kansa? Tabbas wani mummunan abu yana faruwa da shi ina fatan ya samu lafiya cikin sauri, domin na samu damar da zan iya taimaka masa da wani abu. Ya Ubangiji ka kare Mummyn sa ka hana wani mummunan abu ya faru da ita Amin." Bayan wani lokaci ya farka cikin firgici sosai yayin da bakin sa yake fad'ar sunan Mummyn sa. Yana k'oqarin tashi *Adnan* yayi saurin dakatar da shi ta hanyar ri e hanun sa tare da furta masa. "A'a ya isa ka dakata dan Allah likita ya fad'a min cewar kana buqatar hutu sosai, to ya kamata ka huta ka ji ko dan Allah." "A'a sam ba zan iya zama a nan ba sabo da Mummy na da Kaka ta dukansu suna buqata na sosai, to ya kamata na tafi na gode sosai daka taimaken." "Wai da gaske kana san ka rayu sannan kuma ka damu sosai a kan ahalinka? To amma mai ya saka kake k'oqarin kashe kanka idan har gaskiyar kake fad'a." Cike da jin mamakin abin daya fad'a yake magana.

"Wai mai kake fad'a ne haka taya ma kai zaka fad'i haka? Ni sam ba zan ta'ba aikata irin wannan mummunan zunubin ba, sabo da Mummy na da Kaka ta suna buqata na sosai to ya kamata na tafi yanzu." "Shikenan ni zan sauke ka gida sannan kuma zanso ka sanar da ni da abin da zan iya taimaka maka.?" "Na gode hakan ma ya isa kai kana da kirki sosai, bayan nan kuma ni sunana *Adeel Abas* kai fa ko zaka iya fad'a min sunan ka.?" Wani irin kallo *Adnan* yake yi masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, cike da d'auki yayi hugging d'in sa yayin da yake fad'ar sunan sa. *"Adeel* wai kai ne haka mai yake faruwa da kai ne? Shin ka gane ni kuwa abokin ka tin na yarinta *Adnan Adam* shin ka tina ni kuwa.?" Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake sa daga rungumar da yayi masa, sun fuskanci juna wani irin kallo *Adeel* yake yi masa cike da d'auki yake magana.

*"Adnan* wai kai ne a nan? Lokaci ya tafi sosai shekaru goma sha biyar kenan sai yau muka k'ara had'uwa. Gaskiya nayi matuqar farin cikin sake had'uwa da kai ina abokin ka? Ina nufin *Adyan* ina fatan zuwa yanzu ya samu cikakkiyar lafiya sosai.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "abokina yana lafiya yanzu yana kulawa da kansa sosai, *Adeel* amma na ji mamaki sosai da na ji kayi magana a kan kulawa da Mummyn ka, wanda kuma a baya kai ka fad'a min cewar Mummyn ka bata raye *Adeel* amma qlau kake kuwa.?" "Eh *Adnan* qlau nake kawai dai a wancan lokacin ban san a salin gaskiyar bane, Dady na ya b'oye gaba d'aya gaskiyar gareni shi ya min k'arya, a game da Mummy na bai fi watan ni hud'u da ni na san gaskiyar ba. *Adnan* Mummy na bata cikin kyakkyawan yanayi ga shi kuma ni na kasa yin komai, duk da cewa abin yana matuqar cutar da ni sosai *Adnan* ya kai ko magani na gagara siya mata, duk da irin yanayin ta *Adnan* hakan yana da zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una."

Nan kuwa ya shiga sanar da shi komai magana yake yayin da yake kuka kuma kuka sosai, cike da jin tausayin sa yake magana yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla. *"Adeel* gaskiya ka bani tausayi sosai dama duka ahalin gaba d'aya, *Adeel* ni zan kula da wannan idan ka amince zan d'auke ku zuwa kaduna, a can zan baku gidan da zaku zauna sannan zaka samu aiki kuma Mummy zata samu kulawa sosai. *Adeel* dan Allah karka ce a'a ka barni nayi wannan please." *"Adnan* gaskiya bai kamata kayi duka wannan ba, sabo da wannan d'awainiya ta ne to ba zan d'ora maka nauyin ba na gode da kulawa."

*"Adeel* wannan shi ne abin aboki na gari yake yiwa abokin sa, abokai na gari ko yaushe suna taimaka wa junan su ba kuma tare da sunji sun gaji ba. To daga wannan lokacin zasu iya kiran kansu da ahali *Adeel* kaddaran had'uwa da kai ne, yasa ni zuwa nan garin d'aurin auran wani abokin aikin mu, to na ro e ka dan Allah da girman Allah ka da ka dakatar da ni daga taimaka wa please." Ya jinjina masa ka tare da furta kalmar na gode sosai yayin da yake kuka. *Adnan* ya shiga rarrashin sa yana ba shi magana bayan wani lokaci ya k'ara hutawa suka samu sallamar likita, sun tashi sun nufi gida sun fara da siyan magani sannan suka isa gida, *Adeel* ya gabatar da *Adnan* gurin Umma tare da sanar da ita komai daya fad'a masa. Umma ta shiga yi masa godiya ya amsa ta da ba komai bayan sun gaisa *Adeel* yayi masa nuni da Mummyn sa, ya kai kallonsa gareta tare da tashi ya nufi inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai, sai wani kallonta yake kallo sosai yayin da tausayin ta ya cika zuciyarsa.

Ya sauke kallonsa ga rubobin ruwan da suke rungume jikin ta, ya nisa tare da jan numfashi yana girgiza ka ya mai da kallonsa ga *Adeel* kafin ya furta komai yayi masa rigagi. *"Adnan* abin shi ne tana kiran wad'an nan rubobin da yaranta sam bata rabuwa dasu." *"Adeel* shin tana da wasu yaran ne bayan kai.?" "A'a ni kawai ne d'an ta wannan kawai rashin lafiyar ta ne tazo a haka." *Adnan* ya jinjina masa ka tare da furta Allah ya bata tafiya, da dare suna cikin fira wayar sa ta d'auki ruri yayi murmushi sosai sannan ya amsa kiran. "Aboki barka fatan kana lafiya ina qanwata fatan tana tafiya.?" "Muna lafiya Aboki ta ya *Afnan* da kuma ďana fatan suna lafiya.?" "Dukanmu muna lafiya aboki ina da kyakkyawan labari a gareka." "Ina farin ciki da duk abin da zaka fad'a min." "Aboki ina tare da *Adeel."* "Waw kyakkyawan labari aboki yaushe ku biyun kuka had'u.?"

"Yau ne kuma har yanzu mu biyun muna tare." "Aboki shin ko zaka iya had'a ni da shi dan Allah.?" "Ya amsa da eh ya bawa *Adeel* waya tare da fad'a masa wanda yake kallayi ya amsa tare da yin sallama. *"Adeel* barka shekaru goma sha biyar kenan ya d'auke ni ina fatan had'uwa da kai, *Adeel* ni na gode maka sosai a bisa taimakon rayuwata da kayi, na gode sosai kuma nan ba jimawa zanzo domin na had'u da kai na tabbata dukanmu zamu yi farin ciki da hakan." *"Adyan* gaskiyar ita ce *Adnan* ne wanda ya taimake ka, ni kawai na kasance a tare da kai ne har zuwa lokacin daya dawo gareka, shi ďin yana da kirki sosai haka kai ma kana da kirki sosai ni ďin na ji dad'in had'uwa daku." Haka suka ji gaba da magana na tsayin wani lokaci sannan daga bisani kuma suka yi sallama.

Washe gari sunka shirya tsab sun fara da kai wa Malan mukullin gida, sun d'auki duk wani abu mai muhimmanci sannan suka koma hanyar kaduna. Misalin k'arfe 03:30pm suka isa garin kaduna Mamie ta shiga yi musu sannu da zuwa, sun amsa Mamie ta kawo musu ruwa da juice mai sanyi *Adnan* ya shiga yi mata sannu. Ta shafi kansa zuwa fuskarsa ta k'ara da sunbatarsa tana furta masa, "rabin raina ba buqatar ka gode min sabo da ina yin abin daya dace ne, nayi kewarka sosai fatan kana cikin k'oshin lafiya.?" "Qlau nake Mamie sannan nima nayi matuqar yin kewarku sosai ina Papa da Besty.?" "Papa bai jima da fita ba Besty kuma tana barci, ka san mai gidan nawa baya san wahala da yawa zaka iya tafiya ka duba su."

Ya jinjina ka yana murmushi *Adeel* ya anbaci sunan sa tare da tambayar sa. *"Adnan* shin kayi aure ne sannan kuma kana da yaro? To amma mai ya saka baka sanar da ni ba.?" "Kayi hak'uri *Adeel* bawai na b'oye maka bane kawai na bari ne sai munzo sai na gabatar da duka ahalin gareku, sannan kuma shi yaron naka har yanzu yana ciki bai fito ba, cikin wata biyu ne kawai zaka had'u dasu ba jimawa insha Allah." Ya jinjina masa ka yana murmushi mai tare da dariya hakama Mamie da Umma murmushi suke, bayan wani lokaci suka tashi Mamie ta kai Umma da Mummy masauki, hakama *Adnan ya tafi da Adeel* masauki daga bisani kuma ya nufi d'akin sa, domin had'uwa da kyawawan furannin sa wato Besty da kuma Babyn sa......................






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/4, 7:23 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 36*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Wednesday 02/02/2022*

*Time 11:47pm*

*Typing................*


Sannu a hankali yake tura k'ofar har ta bud'e, ya shiga ciki tare da rufe k'ofar ya sauke kallonsa gareta, sannu a hankali yake tafiya har ya isa inda take ya zauna kusa da ita kusa sosai. Sai wani kallonta yake ya kai hanun sa ya shafi cikin ta tare da sunbatarta yana furta. "I love you my child i love you so much." Yaci gaba da shafar cikin yana sunbatarta sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, ta sauke kallonta garesa wanda shi kuma cikin ta yake kallo. Ta kai hanun ta tana shafar kansa tare da fad'ar sunan sa ya d'ago fuskarsa, sun fuskanci juna lokaci d'aya suka sakarwa juna murmushi mai tare da 'yar dariya. Ya tashi ya koma kusa da ita ya kwanta tare da rungumata jikin sa, sai wani sunbatarta yake ita kuwa tayi kwance jikin sa tamkar wacce za a mai da ciki a aife. "Besty nayi kewarki sosai da kuma Babyn mu Papa da kuma Mamie, dukanku ina tare da kewarku sosai abin farin cikin shi ne kuna lafiya, to yanzu fad'a min wani abu shin ke kin kula da Babyn mu sosai kuwa.?" "Eh Besty nayi hakan sannan Papa da Mamie suma sun taimaka sosai, gaskiya nima nayi matuqar yin kewarka sosai ina sanka Besty."

"Nima ina qaunarki sosai amma kin ji abinci kuwa sabo da ba zanso yunwa ta cutar da Babyn ba.?" "Kayi hak'uri ban samu naci abinci ba sabo da bana san naci duk da cewar ina jin yunwa sosai." "Besty yanayin zai iya cutar da lafiyar Babyn yanzu ki fad'a min duk abin da kike so, ni kuma zan tafi na kawo maki nayi alkawari insha Allah." "Shikenan tin jiya nake da kwad'ayin naci awara to yanzu ka tafi ka kawo min." "Eh zan tafi kuma zan dawo da ita insha Allah bara na tafi yanzu." "Na gode Mujina am yauwa karna manta ina su *Adeel* fatan suna lafiya.?" "Eh qlau suke dukansu an kai su masauki." "Hakan yayi kyau to yanzu zaka iya tafiya." Ta fad'a tana murmushi shi ma haka murmushi yake sosai ya k'ara sunbatarta, sannan ya tashi ya fita ita kuwa ta bisa da kallo tana murmushi har ya fice.

Yana fitowa kai tsaye d'akin da *Adeel* yake ya nufa ya buga masa k'ofa daga ciki ya amsa da shigo, ya tura k'ofar ya shiga ya same sa zaune bakin gado ya k'arasa inda yake ya zauna. *"Adeel* kayi hak'uri dana dame ka abin shi ne idan kana buqatar wani abu, to zaka iya sanar da Mamie na sabo da ni zan fita Besty tana buqatar taci awara, ka san yanayin mata masu ciki kamar k'ananan yara suke amma wata rana zaka fahimci hakan. To ni zan tafi ka kula sosai sai na dawo." *"Adnan* zan tafi tare da kai dan Allah." *"Adeel* ya kamata ka huta ka ji ko." "A'a *Adnan* qlau nake to dan Allah karka dakatar da ni please." "Shikenan zamu iya tafiya." Ya amsa da to sun tashi sun fice zuwa nai man awara ya fara sanar da Mamie, dama su Umma sannan suka tafi sun d'an jima a waje sannan suka dawo, abin farin cikin shi ne sunyi nasaran samun awara sun shigo ciki sun samu dukansu a parlour.

*Adnan* ya fara zuwa kicin ya d'auko pilet sannan ya isa inda take ya juye mata sannan ya fara bata a baki tana ci, su Mamie sai kallonsu suke suna murmushi Mummy ta tashi daga inda take ta nufi gurin su *Afnan,* ta zauna tare da furta musu kalmar nima zanci Umma zata yi magana ya dakatar da ita yana girgiza mata ka, nan kuwa ita ma ya shiga bata a baki hakan kuma yayi matuqar yi masa dad'i sosai a ransa da ma zuciyarsa. Su Umma sai kallonsu suke Mamie sai murmushi yake yana sanya wa yaronta albarka, *Adeel* ya anbaci sunan sa tare da furta masa kalmar kayi hak'uri, *Adnan* ya girgiza masa ka tare da furta masa ba komai yana murmushi. Da dare Papa ya dawo gida bayan sun gaisa *Adnan* ya gabatar da shi a gurin su Umma, sabo da shi ya riga daya san labarin su a gurin yaronsa *Adeel* ya shiga yi masa godiya, ya amsa shi da ba komai yana murmushi Mamie ta shirya musu abinci a tebur sannan ta shiga ciki gurin Papa.

Bayan sunci abinci su Umma sun shiga ciki domin su kwanta, hakama *Adeel* bayan tafiyar su *Adnan da Afnan* tashi suka yi suka fita zuwa gidan Abba, sun kuwa samu dukansu a tare Amal ta shiga d'auki tana yi musu sannu da zuwa. Sun amsa ta suna dariya sun gaisa dasu Anwar sannan suka ci gaba da fira cikin raha wasa da dariya, sun jima sosai a nan suna fira sannan daga bisani suka yi sallama dasu suka nufi gida. Sun samu su Papa suna k'oqarin shiga ciki sunyi sallama da juna sun shige, suna shiga ciki kai tsaye gurin wanka suka shiga ba jimawa suka fito, sunyi shirin kwanciya suka kwanta ba jimawa *Afnan* tayi barci. Ya shafi fuskarta tare da sunbatarta yana murmushi ya kai hanun sa, ya d'auki laptop ďin sa ya shiga kiran layin *Adyan* ba jimawa ya d'aga suka fara magana. "Aboki barka idan kana da lokaci ina san zamu magana yanzu a game da *Adeel* ne." "Eh zamu iya fara wa yanzu ina sauraran ka." Ya amsa shi da to nan kuwa ya shiga sanar da shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login