Showing 60001 words to 63000 words out of 142761 words

Chapter 21 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

ganin ta, "Papa ina lafiya ka yarda da ni qlau nake ita kawai taji tsoro ne sabo da ban d'aga kiran ta ba, amma ina lafiya to zaka iya yarda da ni sabo da ni gaskiyar nake fad'a." Ya shafi fuskar sa zuwa kansa tare da sunbatarsa yana fad'ar sunan sa. "Ina fatan haka d'ana yanzu zan tafi sai da safe ka kula sosai *Afnan* kema." "Eh Papa zan kula sosai sannan kuma bayan nayi magana da shi zan kwanta a ďakin *Alishart."* "Hakan yayi kyau 'yata Allah yayi muku albarka." Dukansu sun amsa da Amin ya juya ya fita bayan tafiyar sa *Afnan* ta kai hanun ga *Adnan,* wanda shi ma kallonta yake kallo sosai daga bisani kuma ya tafi ya zauna, ta bisa da kallo hakan kuma ya tabbatar mata da cewar yana tare da damuwa sosai.

Ta nufi inda yake ta zauna sai wani kallonsa take kallo sosai daga bisani kuma ta fara magana. "Besty zaka iya 'boye wa kowa damuwar ka amma banda ni, sabo da nafi kowa sanin ka a wannan duniyar Besty kawai ka sanar da ni gaskiyar miye damuwar? Domin na san ta yanda zan iya taimakon ka." Kallonta kawai yake ita ma haka kallonsa take sun jima a haka suna kallon juna, ba kuma tare da sunji sun gaji ba bayan wani lokaci da suka d'auka a haka sannan daga bisani ya amsa ta. "Ke kinfi kowa sani na kuma kinfi kowa fahimta na kina gane ko wane irin yanayi na, Besty ni kawai na damu ne a kan qanwata yanzu ba jimawa ni na shiga d'akin ta, na samu tana magana da *Adyan* video call Besty abin damuwar shi ne ita tana sanye da rigar barci ne kawai a jikin ta. Besty ni naji wani iri sosai hakan yasa nayi mata fad'a sosai har tayi kuka ban kuma iya rarrashin ta ba, Besty ni kasa gane dalilin da yasa *Adyan* zai aikata haka? Sam bai kamata ya ganta a cikin irin wannan shigar ba, amma kuma shi yayi hakan Besty mai yasa yayi hakan mai yasa zai ga qanwata a cikin wannan shigar.?"

Magana yake cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ita kuwa sai kallonsa take kallo sosai ta shafi kansa zuwa bayan sa tare da sunbatarsa, a ka da kuma gefen fuska shi kuwa dai kallonta kawai yake ba kuma tare daya furta mata komai ba. "Besty amma kana da tabbaci sosai a kan hakan kuwa? Besty zai iya yuwa kai kawai hasashe ne kake, Besty mu kawai muna yarda ne da abin da idanuwan mu suka gani bawai abin da muka ji ba. To Besty ya kamata ka k'ara tinani a kan abin da kake fad'a kafin yanke hukunci, sabo da kana cikin fishi sosai to zaka iya yanke hukuncin da bai dace ba, Besty *Adyan* aboki na gari ne a gareka to ni sam bana tinanin cewar zai iya cutar da kai sosai har haka. Besty to yana da kyau ka k'ara tinani shin da gaske kai ka yarda da abin ka ji kuwa.?"

Yayi shiru sai kallonta kawai yake ita ma haka kallonsa take suna haka suka jiyo wayar *Adnan* na ruri, lokaci d'aya dukansu suka kai kallonsu ga wayar dan ganin wanda yake kira, sun ga sunan *Adyan* ya bai yana a kan wayar sa amma bai d'aga ba ya kira da dama amma kuma bai d'aga ba. "Besty mai ya saka ba zaka amsa shi ba? Ya kamata ka saurare sa dan Allah kaba shi damar da zai wanke kansa a gareka please." Har zuwa wannan lokacin kallonta yake ba kuma tare daya furta mata komai ba, ganin ba zai yi magana bane yasa ta d'aukar wayar sa ta d'auki number *Adyan,* tasa a wayar ta tare da danna kira ba jimawa sosai ya d'aga ta anbaci sunan sa ta kuma ci gaba da magana. *"Adyan* kana magana da *Afnan qawar Adnan."* Da sauri ya amsa ta yana cewa. "Yauwa na gode Allah *Afnan* nayi farin ciki sosai da kika kira, *Afnan* wani abu yana faruwa wanda sam na kasa fahimta, yanzu ne ba jimawa ina magana da *Alishart* sai naji *Adnan* yana mata magana, *Afnan* ni ban san abin daya fad'a mata ba wanda ya saka ta kashe wayar ta. *Afnan* zuwa yanzu layin ta gaba d'aya bai ya tafiya shi kuma bai ya d'aga kira na, *Afnan* ba zan 'boye maki ba ina cikin k'unci sosai sabo da ban san abin da yake faruwa dasu ba, ni na damu sosai a kansu shi yasa ma na fara zuwa garesu gobe ina fatan dukansu suna lafiya."

Daga yanayin yanda yake magana ta fahimci cewar yana tare da damuwa sosai, tayi shiru kad'an tare da jan numfashi sannan daga bisani ta amsa shi. *"Adyan* shin video call ka kira *Alishart.?"* "A'a voice call ne amma mai ya saka kika tambaya.?" "Ba komai kawai dai ni ina san na sani ne." *"Afnan* dan Allah ki sanar da ni wani abu a game da dukansu biyun kafin ni nazo." "Shikenan *Adyan* ni zanyi hakan to ka kula sosai sai da safe." "Na gode sosai *Afnan."* Da kuma haka suka yi sallama ta dawo da kallonta ga *Adnan* kafin ta furta komai ya tashi ya fita, ita ma tashi tayi ta bisa a baya yana fita kai tsaye d'akin *Alishart* ya nufa ita ma haka, sun shiga ciki sun samu har zuwa wannan lokacin kuka take kuma kuka sosai, da sauri suka qarasa inda take suna rarrashin ta bayan wani lokaci *Adnan* ya shiga tambayar ta.

"Qanwata shin video call nazo na samu kina yi da *Adyan.?"* Ta girgiza ka tare da furta a'a yaci gaba yana cewa, "to mai kike yi da laptop a wannan lokacin.?" "Yayana nifa karatu kawai nake yi masa shi yasa nake anfani da laptop, to amma mai ya saka kai kake fishi da ni sosai shin ni na aikata maka wani zunubi ne.?" Cike da k'unci ya dafe ka hanu biyu tare da furta. "Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un mai na aikata ne haka? Ki yafemin qanwata ya kamata nayi magana da *Adyan* yanzu." Ya kar'bi wayar *Afnan* ya shiga kiran layin *Adyan* yana ringing amma bai d'aga ba, ya kira da dama amma bai d'aga ba hakan ya tabbatar wa da *Adnan* cewar ba lafiya. Ya tashi da sauri ya fita dukansu sun bisa a baya wanda kuma d'akin sa ya nufa, sun shiga ciki dukansu da sauri *Adnan* ya d'auki wayar sa, ya shiga kiran layin Appa ba jimawa ya d'aga ba tare da sun gaisa ba *Adnan* ya fara magana.

"Appa ya kamata ka had'u da *Adyan* yanzu sabo da bai ya cikin kyakkyawan yanayi." "Ok na gode sosai *Adnan."* Ya amsa shi da ba komai sunyi sallama, "duka wannan laifi na ne ba zan ta'ba gafarta wa kai na ba idan har wani mummunan abu ya faru da *Adyan.* Da akwai buqatar na hukunta kai na ko na samu wani daban ya hukunta ni ina buqatar hukunci sosai, ni na aikata babban zunubi wanda yake da matuqar girma sosai." "Yayana wai mai yake faruwa ne dan Allah ka sanar da ni please.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa ta, "ba komai qanwata 'yar damuwar kad'an ce dare yayi sosai ya kamata ki tafi ki kwanta kinji sai da safe." Ta amsa shi da to ta juya ta fita bayan tafiyar ta *Afnan* ta qarasa inda yake ta zauna kusa da shi kusa sosai, sai kallonsa take ta d'ora hanun ta a kan nasa tare da saka faratan ta cikin nasa ta d'an matse kad'an, ta yanda ba zai ji zafi ba kallonta kawai yayi ba tare daya furta komai ba.

"Besty dan Allah ka dena hukunta kanka haka sabo da hakan yana cutar da ni sosai, kai ba kayi komai ba kawai kana kare qanwarka ne wannan kuma abin daya dace ne, kiyi magana da *Adyan* na tabbata zai fahimce ka sannan kuma ba zai yi fishi ba." Ya shafi hanun ta da yake cikin nasa tare da sunbata. "Na gode Besty na idan baki to ba zan iya yin komai ba, ke ce gwarin guiwa ta kuma garkuwa ta to ina san kiyi man alkawarin cewa ke ba zaki ta'ba bari na ba na har abada." Ta jinjina masa ka tare da furta masa, "eh nayi alkawari ba zan ta'ba barin ka ba na har abada, zan rayu da kai har k'arshen rayuwata wannan alkawari ne kuma zan cika alkawari na insha Allah. Besty ni gaba d'aya gaskiyar nake fad'a ma to zaka iya yarda da ni." "Na gode sosai Besty." Ya fad'a tare da sunbatarta tayi murmushi sosai tare da janyo sa jikin ta, tare da sunbatarsa yayin da take magana da zuciyarta. "Besty ina matuqar qaunar ka sosai kamar yanda kai ma kake, ina fatan zuwan ranar da zaka sanar da ni gaskiyar cewa kana so na, zanyi farin ciki sosai da zuwan wannan ranar ina qaunarka sosai." Ta kai kallonta garesa ta ga idanuwansa rufe ga a lama yayi barci, murmushin ta ya qaru ta shafi fuskarsa zuwa kansa tare da sunbatarsa, ta wani qara saka shi jikin ta tare da rufe idanuwan ta ba jimawa ita ma barci ya d'auke ta............





*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/21, 3:52 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 25*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Wednesday 19/01/2022*

*Time 10:34pm*

*Typing............*

Kiran salla ne ya tashe shi daga barci ya sauke kallonsa ga fuskar *Afnan* wacce take barci a zaune, wani irin kallo yake yi mata kallo sosai ya tashi zaune, wanda kuma har zuwa wannan lokacin kallonta yake kuma kallo sosai. Ya shafi fuskarta zuwa gashin kanta lokaci d'aya kuma ya samu kansa da sunbatarta, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e, tayi tozali da fuskar shi, lokaci d'aya ta saki wani kyakkyawan murmushi sosai. Shi kuwa dai har zuwa wannan lokacin kallonta kawai yake kallo sosai, ba kuma tare daya furta mata komai ba ita ma haka kallonsa take cikin kwantar da murya take magana. "Barka da asuba Besty na fatan ka tashi cikin k'oshin lafiya babu sauran wani k'unci.?" "Mai ya saka kika yi haka ta ya zaki kwana a zaune yayin da kike rungume da ni? Besty hakan sam ba adalci bane kuma sam bai kamata ke ki aikata min hakan ba, gaskiya naji wani iri sosai sannan kuma naji ba dad'i, amma kuma duk da haka ina godiya sosai na gode da kulawar ki a kai na na gode sosai."

"Besty dan Allah ko zaka dena wannan yawan godiyar haka please? Domin ni a shirye nake da nayi komai sabo da kai musamman wanda zai saka ka farin ciki sosai, lokaci ya tafi sosai an fara ik'ama ya kamata ka tafi masallaci yanzu." Tana cikin magana suka ji Papa yana buga musu k'ofa tare da fad'ar sunan *Adnan,* da sauri ya rufe mata baki tare dayi mata a lamar tayi shiru, ta jinjina masa ka tana murmushi jin Papa yana ta buga k'ofar tare da fad'ar sunan sa yasa shi amsa wa. "Naam Papa na tashi zan shiga toilet nayi alwala ne." "Hakan yayi kyau to ka saman a parlour." Ya amsa shi da to Papa ya juya ya nufi parlour ta sunbaci hanun sa da yake kan bakinta, yayi murmushi sosai mai tare da 'yar dariya sannan ya tashi ya shiga toilet, ba jimawa sosai ya fito ya fita zuwa masallaci ita ma tashi tayi ta shiga toilet tayi alwala ta fito ta fara salla.

Bayan ta idar tayi azkar sannan ta tashi ta nufi bedroom d'in *Alishart,* hakan tasa ko da *Adnan* ya dawo bai same ta a d'akin sa ba, ya nufi gado ya kwanta tare da d'aukar wayar sa ya shiga kiran layin Appa, wayar ta jima tana ruri kamar zata tsinke sannan ya d'aga kiran bayan sun gaisa *Adnan* yaci gaba da magana. "Appa *Adyan* fa fatan ba abin daya faru da shi.?" "Eh na isa gurin sa a kan lokaci na samu na ba shi magani sai yayi barci, har zuwa wannan lokacin barci yake na gode sosai da kulawa, ko yaushe kana kare shi daga shiga hatsari kai aboki na gari ne sosai, nayi farin ciki sosai daka shiga rayuwar sa Allah ya ma albarka." "Ba komai Appa ka dena yi mun godiya ni zanci gaba da kare *Adyan* daga shiga hatsari iya rayuwa ta, sabo da shi ba kawai abokina bane a'a ina jinsa tamkar d'an uwa na jini ina qaunarsa sosai wannan ce gaskiyar." *"Adnan* kai kana da kirki sosai Allah yayi albarka na gode sosai." Ya amsa shi da Amin da kuma haka suka yi sallama nan kuwa ya shiga kiran layin *Afnan* ringing biyu ta d'aga.

"Mai ya saka kika tafi.?" "Ba komai Besty kawai dai ina san na shirya ne ka san muna da shiga kotu k'arfe goma, to ya kamata ka shirya yanzu sabo da akwai gunda zamu fara tafiya kafin shiga kotu." "Eh Besty ban manta ba kawai dai ina san na k'ara yi maki godiya ne na gode sosai da kulawa Allah ya bar zumunci ya kuma bar qauna da kuma tare Allahumma Amin ya hayyu ya kayyum." "Ko zaka dena wannan yawan godiyar? Lokaci na tafiya ka tashi ka fara shirin ka karmu makara ka ji ko." Ya amsa ta yana murmushi tamkar da yana a gaban ta da kuma haka suka yi sallama. Ya tashi ya nufi toilet domin yayi wanka ba jimawa ya fito ya fara shirin sa, ya shirya tsab ya d'auki wayar sa ya kama aikin chart haka yake ko a gurin *Afnan.* Tayi shirin ta tsab wanda kuma sai lokacin ne ta fito ta nufi gida, tana k'oqarin fita Mamie ta dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. *"Afnan* ki jira muyi break past mana dan Allah." Ta jinjina mata ka a lamar to ta qarasa inda take tare da gaishe ta, ta kuma ta ya ta sun shirya abinci a tare ba jimawa su Papa suka fito sun fara gaisawa sannan suka nufi tebur, sunyi break past cikin kyakkyawan yanayi bayan sun qarasa *Afnan* ta tashi ta nufi gida. Tare ta fita da *Adnan* sun shiga gidan sun samu su Ummu suna break past, sun gaisa dasu *Afnan* ta nufi d'akin ta domin ta canja kayan jikin ta, ba jimawa ta fito *Adnan* ya tashi sun fice.

*England.*

Zaune suke suna fira cikin raha wasa da dariya sai ga *Adyan* ya fito cikin sauri, har kamar zai fad'i da sauri dukansu suka shiga fad'ar sunan sa tare da tambayar sa. *"Adyan* ka tafi a hankali mana, ina ma zaka tafi ne kake wannan uban sauri haka.?" "Appa yau ina da kallon wasa ne to kuma an kusa a fara wasan shi yasa nake sauri sosai, sabo da ba zanso a fara wasan bana gurin ba shikenan ni zan tafi sai na dawo." *"Adyan* kana san wasan tsere sosai amma kuma hakan babban qalubale ne ga lafiyar ka, to ina fatan ba zaka manta da wannan ba? Ta yanda ba zaka yi kuskuran shiga wasan ba." Yayi shiru na jim kad'an sannan ya jinjina masa ka a lamar eh, *"Adyan* to yanzu ina san kayi man alkawari ni da Ammie cewar kai ba zaka yi ko wane wasa wanda yake da hatsari ba." Yayi shiru na wani tsayin lokaci sannan daga bisani ya amsa shi. "Appa kawai dai ku yarda da ni sosai na muku alkawarin zan iya kulawa da kai na sosai, sannan kuma ba zanyi abin da zai saka rayuwa ta a cikin hatsari ba ni zan kasance lafiya." *"Adyan* mu kawai mun damu ne a kanka da kuma lafiyar ka, shi yasa muke dakatar da kai duk wani abin da yake da hatsari to kayi hak'uri a kan hakan." "Appa Ammie kuyi hak'uri ku yafe man a kan komai dan Allah." *"Adyan* mai kuma kake fad'a ne haka? Kai yaron kirki sosai to ba buqatar ka fad'i haka ka ji ko."

Ya jinjina masa ka a lamar to dukansu sun rungumi juna tare da sunbatarsa sannan ya tashi ya fita, tafiya kawai yake amma sam bai ya cikin kyakkyawan yanayi yayin da tinani iri daban-daban yayi yawan gaske a tare da shi sosai, da kuma haka ya isa gurin wasan a nan cikin mota yayi duk wani shirin sa kamar dai yanda yasa ba. Sannan ya fito ya nufi gurin wasan wanda zuwa wannan lokacin har an fara gudanar da wasan, da sauri ya qarasa gurin har yana gudu ya hau nasa mashin ya bisu a baya, lokaci d'aya gurin ya d'auki ihu tare da anbatar sunan sa *Adlishart* shi ne sunan da a kafi fad'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login