Showing 78001 words to 81000 words out of 142761 words

Chapter 27 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

Allah." *Afnan* ta jinjina mata ka hakama Abba ta amsa su da to sun tafi tare da Abba, suna ta shirin tafiya d'aurin aure ganin lokaci ya tafi Appa ya sauke kallonsa ga Ammie tare da fad'ar sunan ta. "Ahlam *Adyan* fa ya kammala shirin sa kuwa.?" "Gaskiya bana tunanin hakan amma zan tafi na duba shi yanzu." Ya jinjina mata ka a lamar to ta tashi ta nufi bedroom d'in da *Adyan* yake, ta shiga d'akin tana fad'ar sunan sa ta yi rashin sa'a baya nan ta duba shi har toilet, amma dai kuma bata yi nasaran ganin sa ba cike da firgici ta fito tana fad'ar sunan sa. Cikin hanzari Ahmad ya fito sun isa ga juna ya shiga tambayar mai yake faruwa, "Yaya Ahmad *Adyan* baya nan na duba shi sosai amma ban gansa ba, Yaya Ahmad ni ina jin tsoro sosai sabo da ban san inda shi ďin ya tafi ba." "A'a bai kamata ki ji tsoro ba sabo da ba abin da zai faru da shi, yanzu mu tafi gurin Abba da Abbu ina fatan ya kasance tare da ďaya daga cikin su mu tafi." Ta amsa da to sun nufi part ďin Abba sun same su zaune a parlour, cikin hanzari sun shiga tambayar su *Adyan.*

"Ahmad mai kake fad'a ne haka ina *Adyan* ďin yake.?" "Abba ban sani ba baya ďakin sa to nayi tunanin ko yana tare daku ne." "A'a bai zo nan ba amma zan kira Al'ameen na ji ko suna tare." Sun amsa shi da to nan kuwa ya shiga kiran layin Abbu ba jimawa ya d'aga, Abba ya shiga tambayar sa *Adyan* ya amsa shi da basa tare, Abba ya sanar da shi baya gida Abbu ya amsa shi da ga shi nan tafe sunyi sallama, da sauri Ahmad ya juya ya fita har yana gudu su Abba ma tashi su kayi suka fita, dan ganin inda zai tafi sun fito sun same sa yana tambayar security yaronsa, Jabir ya sanar da shi cewar ya fita tare da Jibrin. "Kawai ka bani shi a waya." Ya amsa shi da to nan kuwa ya shiga kiran layin Jibrin ba jimawa ya d'aga ya bawa Ahmad wayar ya amsa yana cewa. "Kana magana da Ahmad ne fad'a min ina ďana *Adyan* yake.?" "Ranka shid'ad'e shi ya buqaci dana kai shi asibiti ne, sannan kuma yana cikin k'oshin lafiya na tabbata a kan hakan to zaka iya yarda da ni."

"Shikenan na gode." Da kuma haka suka yi sallama ya bawa Jabir wayar sa, tare da sanar dasu Abba abin da yake faruwa sunyi murmushi sannan suka juya suka koma ciki. Sunci gaba da shirin su bayan wani lokaci suka nufi gurin d'aurin aure, bayan wani lokaci daya d'auka a kwance ya farka, sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e, sai wani kallon kansa yake dama inda yake, lokaci d'aya suka shiga anbatar sunan sa tare da yi masa ya jiki, kallonsu kawai yake ba tare daya amsa ba ya sauke kallonsa ga fuskar *Afnan* sannan ya fara magana. "Mai kuma kike nan ya kamata ki tafi yau ne a ke bikin saka ki lalle to mai kuma kike yi a nan? Ya kamata ki tafi sabo da a gida suna jiran ki to kawai ki tafi ki bar nan dan Allah." Kuka kawai take yayin da take kuka kuma kuka sosai, cike da k'unci ta tashi domin tafiya da sauri *Alishart* ta dakatar da ita ta mai da kallonta ga Yayanta tana cewa...............




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/3, 4:31 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 32*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Friday 28/01/2022*

*Time 05:37pm*

*Typing...............*


"Yaya wai mai kake aikata wa ne haka? Sam bai kamata kayi wa Aunty haka ba godiya ya kamata kayi mata, a maimakon wannan fad'an da kake yi mata cikin tsawa Yana." "Ya isa *Alishart* to kawai kiyi shiru kina san nai mata godiya ne sabo da k'oqarin da take ba bari na? Ko a'a zanyi mata godiya ne sabo da ta za'bi kasancewa tare da Yaya Auwal a maimakon ni? Ko zanyi mata godiya ne sabo da farin cikin da nake ciki a yanzu duk a dalilin ta? *Alishart* ita ta za'bi Yaya Auwal a kai na duk da cewar ta san gaskiyar, wanda kuma hakan ne ya tabbatar mani da cewar ita bata ta'ba sona ba. Shi yasa ta za'bi Yaya Auwal a matsayin muji ta yanda zai d'auke ta gaba d'aya daga gareni, *Alishart* wannan rashin adalci ne sannan kuma hakan yana yi min zafi sosai." Magana yake cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa sosai, ba kuka yake ba amma kuma kwalla ce take bin fuskar sa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo. *Alishart* ta tashi daga inda take ta nufi gurin sa ta zauna kusa da shi kusa sosai, tare da kama hanayen sa ta fara da share masa kwalla sannan daga bisani ta fara magana.

"Wannan ba gaskiya bane Yayana kawai dai rashin fahimta ne, ita Aunty sam ba haka take ba sannan kuma ita ba zata ta'ba cutar da kai ta wannan hanyar ba. Yayana Aunty tana qaunar ka sosai sannan kuma a shirye take data yi komai sabo da kai, ita har sai da tayi barazanar kashe kanta kawai sabo data same ka, har sai data kusa rasa ranta duka sabo da kai." Nan kuwa ta shiga sanar da shi komai yayi matuqar mamakin abin data fad'a. "Yayana zuwa yanzu ku biyun muji da mata ne to ya kamata ka kula da matar ka sosai, sabo da tana buqatar ka sosai sannan kuma kiyi farin ciki dan Allah." "Qanwata wai gaskiya kike fad'a min kuwa shin ni na ji ko sosai kuwa? *Alishart* wai da gaske ni da Besty zamu kasance muji da mata.?" Ya jinjina masa ka a lamar eh cike da d'auki ya kai kallonsa ga *Afnan,* wacce take tsaye gefen k'ofa lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take, sun jima a haka sannan daga bisani ya anbaci sunan ta.

"Besty ki yafemin sannan kuma kiyi hak'uri ki dawo gareni please." Cike da d'auki ta nufi gurin sa da sauri har tana gudu, tana isa garesa sunyi hugging juna sun jima a haka sannan daga bisani suka sake juna, sai wani kallon juna suke kallo sosai yaci gaba da magana. "Besty da a ce ke kin yi nasaran kashe kanki to da ba zan ta'ba gafarta maki ba na har abada, sannan kuma zanci gaba da hukunta kai na har zuwa lokacin da nima zan mutu, Besty ina sanki sosai shi yasa sam ba zan juri rashin ki ba, dalilin da yasa nake kwance a nan kenan na gode da kika zab'e ni a matsayin, a matsayin mujin ki wanda zaki k'arasa duka rayuwar ki da shi na gode sosai Besty na." Kallonsa kawai take yayin da take wasa da fuskar sa cikin kyakkyawan yanayi take magana. "Besty kai ne rayuwata ruhina dama zuciyata to ba zan rayu ba idan har narasa ka, shi yasa na za'bi mutuwa fiye da aure na da Yaya Auwal. Abin farin cikin shi ne daga k'arshe munyi nasara kaddaran mu ta amince mana, da mu rayu da juna na har abada zuwa yanzu mu biyun muji da mata ne abin gwanin dad'i sosai." Ya jinjina mata ka yana furta.

"Eh da dad'i sosai am Besty kiyi hak'uri sannan kuma ki yafemin a kan abin da ni na aikata maki, Besty ni kawai na kasa jurewa ne ganin wani yana k'oqarin raba mu, Besty gaskiyar ita ce ni ina ban saba da rashin ki ba shi yasa ba zan iya jure rashin ki, to dalilin da yasa ni na aikata maki hakan kenan to ina fatan zaki y dan Allah." Da sauri ta rufe masa baki tana girgiza masa ka yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai, wanda kuma wannan dalilin ne ya hana mata fad'ar komai shi ma abin da yake yi kenan. Cike da shauk'i sun k'ara yin hugging juna *Alishart* dai sai kallonsu take tana murmushi, bugun k'ofar da suka ji ne yasa su sake juna daga hugging d'in da suka yi, *Alishart* ta tafi domin ta bud'e k'ofar ta bud'e ba tare data tambaya waye ba, ta samu *Adyan* tsaye bakin k'ofa sun tari juna da wani kyakkyawan murmushi, sai wani kallon juna suke sosai lokaci d'aya kuma ya samu kansa da yin hugging d'in ta, tare da sunbatarta ya kuma ci gaba da furta mata kalmar yana qaunar ta. Ita kuwa sai kallonsa kawai take tana murmushi ba tare data furta masa komai ba, bayan wani lokaci ya sake ta daga hugging d'in da yayi mata sannan suka shiga ciki.

Cike da d'aukin ganin juna suke anbatar sunayen juna har suna had'a baki, *Adyan* ya isa inda yake cike da qauna da soyayya sun gunrume juna har da wani rufe ido, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna sai wani kallon juna suke, yayin da kwalla take bin fuskar su wacce kuma zamu iya cewa ta farin ciki ce. *"Adnan* bayan shekara goma sha biyar yau mun sake had'uwa da juna, gaskiya ina matuqar farin ciki sosai to ya jikin ka fatan kana samun sauki sosai.?" "Eh aboki ina samun sauki sosai kuma duka sabo da kai ne, *Adyan* na gode sosai daka ceci soyayya ta abin da ni na gagara yi. Na gode sosai sannan kuma ina yi ma fatan alkhairi a kan auran ka da qanwata, amma *Adyan* hakan bai yi kusa ba? Am ina nufin ita d'in har yanzu yarinya ce shekarun ta sha biyar ne, to ba zata iya d'aukan d'awainiyar ba ga shi kuma kun riga da kunyi aure kawai sai dai nai muku fatan alkhairi."

"Karka wani damu aboki sabo da ita ďin a nan zata zauna tayi karatu, bayan ko wane hutu zanzo na tafi da ita yanzun ma bayan bikin Ameer zamu tafi tare da ita insha Allah. To ba buqatar ka damu sabo da zan kula da ita sosai kamar rayuwata, ni kawai ina san ta zama tawa shi yasa na buqaci auran ta yanzu." "Kai kana da kirki sosai aboki na gode a kan komai." "Ba buqatar kayi godiya yanzu fad'a min wani abu shin ka samu wani labari a game da *Adeel.?"* "A'a amma ina fatan ya bai yana a garemu nan kusa kuma kusa sosai." "Nima wannan ne fatana." Ya mai da kallonsa ga *Afnan* sun gaisa ya mata fatan alkhairi, ta amsa tare dayi masa godiya shi ma tayi masa fatan alkhairi, ya amsa yana murmushi sannan daga bisani ya shiga duba *Adnan.* Abin farin cikin shi ne yana samun sauki sosai sunci gaba da fira, daga bisani kuma *Adnan* ya shiga tambayar *Alishart* Mamie bata da wani za'bi, wanda wannan dalilin ne yasa ta sanar da shi gaskiyar abin daya faru. Hakan yayi matuqar saka shi k'unci sosai ya kar'bi wayar ta ya shiga kiran layin Mamie ba jimawa ta d'aga. "Hellow *Alishart* shin komai qlau yake a nan.?" Shiru bai amsa ba taci gaba da magana.

*"Alishart* ki amsa ni komai qlau ya jikin ďana yake shin yana samun sauki kuwa dan Allah kiyi magana.?" Cikin wata 'yar murya yake furta mata kalmar kiyi hak'uri cikin hanzari ta anbaci sunan sa. *"Adnan* ya jikin ka kayi hak'uri da ban samu na kula da kai ba, amma ina fatan ka samu lafiya cikin sauri domin ka dawo gida, ta yanda zan kula da kai sosai nayi matuqar kewarka yarona to fad'a min ya jikin ka.?" "Zan samu lafiya ne kawai idan ina tare dake, sabo dake ce kawai wacce zata iya kulawa da ni sosai, Mamie ina jin yunwa sosai amma kuma zanci abinci ne kawai idan ke kika bani a baki. To ina fatan zaki yi min wannan alfarmar dan Allah ko kuma ni ba zanci komai." "Eh zanzo ďana kawai ka jira zuwa na yanzu." Hakan ya saka shi farin ciki ba jimawa suka yi sallama *Adyan* ya anbaci sunan *Alishart* yana cewa, *"Alishart* bani wayar ki zan kira Ameer yazo ya d'aukan mu tafi, nima ina jin yunwa to ya kamata na tafi nayi break past ba jimawa zan dawo insha Allah."

*"Yaya Adyan* akwai abinci a nan ni zan had'a maka break past." *"Alishart* abin shi ne ina da nawa abincin wanda nake kira da na musamman." "Wannan wane irin abinci ne wanda ya zama na musamman a gareka.?" Murmushin sa ya k'aru sosai ya anbaci sunan samosa da madara, cike da mamakin abin daya fad'a take magana da shi. *"Yaya Adyan* gaskiya ku biyun kuna da abin mamaki sosai, bayan kamannin da kike da juna ra'ayin kuma iri ďaya ne wannan abincin da kake magana, shi ne abincin da Yayana yafi so yana matuqar san abincin sosai." *"Alishart* wai gaskiyar kike fad'a kuwa.?" Ta jinjina masa ka a lamar eh ya mai da kallonsa ga *Adnan* shi ma ya jinjina masa ka a lamar eh. Murmushin sa ya k'aru sosai ya mai da kallonsa ga *Alishart* tare da fad'ar sunan ta.

*"Alishart* hakan ne yake nuna k'arfin abotar mu ina farin ciki da hakan sosai." Suna haka suka ji a na buga masu k'ofa ko a wannan karon *Alishart* wacce ta tafi ta bud'e k'ofar, ta ta samu Abba da Papa a k'ofa ta shiga yi musu sannu da zuwa sun dawo tare. Bayan sun gaisa Papa ya shiga tambayar *Adnan* yayi break past, "a'a Papa ina jiran zuwan Mamie ne domin ta ciyar da ni da hanayen ta." "To amma ka sanar da ita hakan.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh, "shikenan zanyi magana da ita a waya." Ya ciro wayar sa ya shiga kiran ta ba jimawa ta d'aga ba tare da sun gaisa ba yake magana. "Shin kin shirya zuwa asibiti ko a'a.?" "Am dama ina jiran izinin tafiya ne daga gareka." "Yaron yana jin yanzu sosai to kizo da sauri kinji ko." Ta amsa shi da to suna k'arasa waya ta tashi ta nufi asibiti.

Ba wani d'aukan lokaci sai ga Mamie cike da d'auki tayi hugging d'in yaronta tana sunbatarsa, daga bisani kuma ta fara ba shi samosa k'amshin ya daki hancin *Adyan,* ya wani lumshe ido tare da jan numfashi ya qara da furta. "Waw k'amshin da dad'i sosai zanso cin wannan sosai." Mamie tayi kiran sa ya tafi nan kuwa ta shiga basu gaba ďaya har da *Afnan.* Hakan yayi matuqar yiwa dukansu dad'i sosai musamman *Adnan,* bayan wani lokaci sai gasu Amar abokan aikin su *Afnan* ganin hakan ne yasa su Papa suka tafi, har da Mamie ita ma tafiya tayi su kuma sunci gaba da fira irin ta abokai, *Adnan* ya gabatar da *Adyan* garesu haka kuma *Adyan* yaci gaba da kulawa da shi, har ya samu sauki ya samu kwana biyar asibiti sannan ya samu sallama.

Bayan kwana biyu suka fara hidimar biki tare da *Adyan* a kayi komai da Amaryar sa, an yi komai an gama Amarya *Afnan* ta tare da Angon ta *Adnan.* A nan gidan Papa ta tare yayin da *Adyan* yake ta sintirin zuwa gurin *Alishart,* wani lokaci ya kan d'auke ta zuwa gidan Abbu, bayan wani lokaci a ka fara hidimar auran Ameer wata biyu da auran su *Adnan* wata rana............





*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[2/3, 4:36 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 33*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login