Showing 117001 words to 120000 words out of 142761 words

Chapter 40 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

domin tafiya bai k'arasa kai wa k'ofa ba sai ga Papa ya shigo, da sauri ya wani zaro ido yana kallonsa cike da jin mamakin ganin sa yake magana.

"Papa mai kuma kake yi a nan? Ta ya ma har kai ka san cewar Prof yana asibiti.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi.?" "Masoyi karka yi fishi sosai haka sabo da zan sanar da kai duka gaskiyar." Nan ya shiga sanar da shi komai sannan yaci gaba yana cewa. "Rabin raina *Adeel* yana matuqar buqatar taimako sosai shi yasa na taimake sa." "Papa ni zan iya yin komai sabo da *Adeel* Mum ko kuma Kaka amma wannan a kan Prof ne, shi sam bai cancanci tausayawar mu ba sam bai kamata ka taimake sa ba. A k'alla ya kamata kayi magana da ni kafin ka yanke hukunci, sabo da bai kamata ka shiga wannan ba sabo da Prof mutum ne mai hatsari sosai. Sannan kuma yana cutar da mutanan da suke da kusanci da shi, shi mugun mutum ne dan haka bai kamata ka taimake sa ba hakan sam bai dace ba."

Cike da fishin zuciya *Adeel* ya dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa cikin tsawa, har yana ďaga murya cike da k'unci bak'in ciki tare da tarin damuwa yake magana. "Ya isa haka Barrister cin zarafin ya isa haka ba kuma zan lamunta ba, koma dai miye ya aikata shi ďin mahaifina ne kuma kuskuran sa bai hana ni sansa ba. Kai sam baka san waye Dady na ba shi yasa kake muzantasa haka, kuskuran sa ďaya daka sani bai isa ya tabbatar maka da cewa shi mutumen banza bane, ko wane bawa yana aikata kuskure to amma mai ya saka kai ka tsani Dady sosai? To hakan ya isa ya kamata ka dena ko kuma dai kai kaga a salin b'acin raina." Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai, *Adnan* yayi wani gajeran murmushi na bak'in ciki sannan ya fara magana.

*"Adeel* ni sam ba zan ga laifin ka ba sabo da kai baka san a salin gaskiyar waye mahaifin ka ba, sabo ya rai neka ne cikin k'arya yana yawan fad'a maka cewar yana sanka, amma kuma gaskiyar ita ce bai tab'a sanka ba, amma zaka fahimci hakan a lokacin da ka san gaskiyar waye mahaifin ka." Ya mai da kallonsa ga fuskar Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zamu iya tafiya yanzu.?" "Rabin raina kamar dai kana cikin fishi sosai? Wannan yanayin sam bai dace da kai ba domin kuwa zai iya cutar da kai sosai, da kuma lafiyar ka hakan kuma barazana ce a garemu, sannan kuma na tabbata Mamie ba zata tab'a yafemin ba to dan Allah ka dena cutar da kanka haka please." "Papa ni kawai na damu ne a kanka, sabo da ba zanso Prof ya cutar da kai ba to kawai ka fita daga rayuwar sa dan Allah." Papa yayi shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya amsa shi.

"Kayi hak'uri ďana sabo da ba zan iya fita rayuwarsa ba, ko da ma kuwa a ce zai cutar da ni sosai kamar yanda kake tunani, sabo da ba zan iya barin sa ba to kayi hak'uri a kan hakan." "Papa wai mai kake fad'a ne haka waye shi ďin a gareka da ba zaka iya barin sa ba.?" Yayi shiru kad'an tare da jan numfashi sannan ya amsa shi. "Rabin raina shi ďin Kawun ka ne sabo da shi ďin Yayana ne, wanda na jima sosai ina nai ma bayan wasu tsayin shekaru jiya na koma had'uwa da shi. Shi yasa ba zan iya rabu da shi ba ina fatan zaka fahimce ni sannan kuma ba zaka yi fishi da ni ba dan Allah." Wani irin kallo dukansu suke masa mai cike da jin mamakin abin daya fad'a, cike da k'uncin abin daya fad'a *Adnan* yake magana. "A'a hakan sam ba gaskiya bane sam bai kamata hakan ta kasance ba, ni sam na kasa yarda cewa wai shi ďin Yayanka ne, Papa ta ya a kai ka iya gane sa cikin sauri haka? Papa wannan fa yana buqatar nazari to karka yi saurin amincewa da shi, sabo da zai iya cutar da kai sosai please."

"Masoyina gane Yayana yana da matuqar sauk'i sosai a gareni kamar dai kai d'ana, duk da cewar hakan ta faru tin muna yara amma kuma ba zai yi iya goge tabon sa ba, sannan kuma jinin mu ba zai canja ba kamar yanda bai iya sauya a salin sunan sa ba. Tabon dana gani a gefen kafad'ar sa da kuma jini na da a ka sanya masa ya isa ya tabbatar da gaskiyar, shi ďin Yayana ne sunan sa Prof Abas Muh'd ni kuma Adam Muh'd, dukanmu iyayenmu ďaya kai da *Adeel* ahali ďaya ne to kawai kuyi farin ciki." Motsin da suka ji ne yasa su kai kallonsu garesa cikin hanzari *Adeel* da Papa sun isa inda yake, *Adnan* kuwa ya rufe su da ido hakama Mum ita kallonsu take. Wacce kuma har yanzu bata furta komai ba sun shiga yi masa sannu ya amsa tare da tambayar *Adeel* waye Papa, yayi shiru yana nazari jin yayi shiru ne yasa Papa magana.

"Am da fari sunana Adam Muh'd K'ank'ara kuma ni ne mahaifin *Adnan* abokin *Adeel.* Yaya ina fatan ka gane k'anin naka.?" "A'a sabo da ni bani da k'ani to zaka iya tafiya kawai ka bar nan ka ji ko." "A'a Yaya dan Allah karka fad'i haka ni na san cewar ka gane ni to mai yasa ba zaka amince da ni ba.?" "Na ce ka tafi to kawai ka tafi ka bar ka ji ko." "A'a Yayana ni ba zan tafi ba sabo da." "Malan ya isa haka na fad'a maka cewar bani da wani k'ani to kawai ka tafi, k'ila kuma gaskiyar ka ne a baya ina da k'ani amma shi wannan k'anin nawa, ya mutu ne a rana d'aya da mahaifiyar sa dalilin da yasa na rayu ni kad'ai kenan. To dan haka kai ba zaka tab'a kasancewa k'ani na ba, to yanzu zaka iya tafiya sannan kuma karka k'ara nuna min wannan fuskar taka, daga k'arshe kuma ka fad'a wa yaronka ya fita daga rayuwar d'ana."

Cike da fishin zuciya *Adnan* ya k'arasa gurin su yana cewa. "Kai waye da zaka yi magana da Papa haka? Shi mutum ne wanda yake da daraja da kuma kima a gurin mutane, ba kamar kai ba shi yazo gurin ka cikin qauna da soyayya amma kuma kai, sai kake k'oqarin fusata shi to fa ka sani idan har ka bari ya fusata, to fa ni da kai na zan hukunta ka dan haka ka ki yaye ka ji ko." "Adam irin tarbiyar daka bawa yaronka kenan? Amma banyi mamaki ba sabo da kai ma irin tarbiyar daka samu kenan, shi yasa yaronka shi ma ya tashi haka to ba zan bar irin wannan ya kasance tare da yarona ba. Dan haka ka fad'a masa cewar ya rabu da yarona, sannan kuma kai karka k'ara nuna min wannan fuskar taka na har abada."

"Yaya zaka iya hukunta ni ta duk yanda kake so, duk da cewar bai aikata maka wani zunubi ba, amma sam ba zan baka damar da zaka ci zarafin yarona ba. D'ana a gareni tamkar zinari ne azurfa koma na kira shi da lu'ulu'u, babu wani abin da nake so fiye da ďana sabo da shi ne rayuwata gaba d'aya. D'ana shi ne komai nawa a salin farin ciki na zan iya yin komai sabo da shi, ina matuqar qaunar ka sosai Yayana amma bai kai kamar yarona ba. Yanzu kana cikin fishi sosai zamu tafi wani lokacin zamu dawo." Ya mai da kallonsa ga *Adeel* yaci gaba da magana. *"Adeel* ka kula da shi sosai kai ma ka kula da kanka ka ji ko."

Ya jinjina masa ka tare da furta to ya mai da kallonsa ga fuskar *Adnan* tare da fad'ar sunan sa. "Mu tafi rabin raina dan Allah." Ya jinjina ka cike da fishin zuciya yake magana. "Papa wallahi tallahi idan wannan mutumen ya k'ara fad'ar wani abu a kanka, to zan manta cewar shi d'in Yayanka ne na hukunta sa, ta duk yanda naga dama ba kuma tare da nayi dana sanin hakan ba." Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai.

Papa ya shiga rarrashin sa yayi hugging d'in sa yana sunbatarsa, tare da furta masa dad'ad'an lafuzza masu kwantar da hankali, ya ja hanun sa sun nufi hanyar fita domin tafiya, *Adnan* ya sauke kallonsa ga fuskar *Adeel* tare da fad'ar sunan sa. *"Adeel* ka kula da Mum sosai sannan kuma ka tabbatar Dadyn ka bai cutar da ita ba, koma mai zai faru to ka tabbatar ta kasance lafiya ka ji ko." Yana kai k'arshen maganar sa ya juya yayi tafiyarsa, da sauri Papa ya fita ya bisa a baya yana fad'ar sunan sa, su Mum sun bisu da kallo har suka b'ace...............







*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/10, 10:43 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 48*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Monday 07/03/2022*

*Time 11:18pm*

*Typing................*


Bayan tafiyar su *Adeel* ya maida kallonsa ga fuskar Mum ,lokaci ďaya suka yi ido biyu da juna kasancewar ita ma kallonsa take, sun samu shiru na jim kad'an sannan Mum ta fara magana. *"Adeel* karka bari wannan abin da ya faru yasa kayi tunanin, rabuwa da *Adnan* ko kayi cin zarafin sa ko wani abu daban. Abin duba a nan shi ne waye a salin mak'iyin nasa, shi abokin fad'an nasa tamkar maciji ne yana iya cutar da kowa, musamman ma mutanan da suke tare da shi. Kai kariga da kasan komai a game da mugun halinsa, to ya kamata ka bud'e idanuwanka da kyau domin ka karb'i gaskiya, *Adnan* yaron kirki ne sosai sannan kuma yana qaunar mu sosai. Balantana kuma yanzu kuma da gaskiyar ta fita da cewar, ku biyun ahali ďaya ne hakan yayi matuqar yi min dad'i sosai. To kawai kayi abin daya dace ka ji ko, yanzu lokaci ya tafi sosai zuwa yanzu ya kamata kayi kalaci, to mu tafi domin kaci abinci sabo da ba zan iya jure zama a nan ba, kuma sam ba zan jure jin kalmar a'a daga bakinka ba kawai mu tafi dan Allah."

Kallonta kawai yake sai daga bisani sannan ya jinjina mata ka, a lamar to ya kuma ci gaba da magana. "Mum shin ba zai yu naci abincin tare da Dady ba.?" "A'a ďana ban shirya hakan ba na kai kawai nayi. Ba kuma zan iya ba shi yaci ba to mu tafi dan Allah." "Amma Mum." *"Adeel* kawai kayi shiru mu tafi." Ya jinjina mata ka a lamar to tare da mai da kallonsa ga Prof tare da fad'ar sunan sa. "Dady zan tafi amma ba zan jima ba zan dawo gareka insha Allah." "Na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka ka kula da kanka sosai, sannan kuma ka kula da Mummyn ka sosai sabo da tana cikin fishi sosai, wani lokacin zan samu nayi magana da ita sai ka dawo." Ya jinjina masa ka a lamar to sun juya sun fita Prof ya bisu da kallo har suka b'ace, sun fito sun samu wani guri daban sun zauna *Adeel* ya anbaci sunan Mum yana cewa. "Mum na san cewar kina matuqar yin fishi da Dady sosai, amma kuma zuwa yanzu ya kamata ki sauki daga wannan dokin fishin, ko dan wannan yanayin da Dady yake Mum ko fa sannu baki yi masa ba, sannan kuma yanzu kin hana shi abinci Mum dan Allah karki zama kamar shi please."

*"Adeel* da a ce na kasance kamar shi to da nayi k'oqarin cutar da shi kamar yanda ya min, amma kuma banyi hakan ba rabin raina bayan cutar da mahaifin ka ya min, sai na ji bani da wani babban mak'iyi a cikin wannan fiye da shi. To sam bana jin cewar zan iya taimaka masa da komai kayi hak'uri." "Shikenan Mum ina fatan zuwan rana ko lokacin da zaki yafe wa Dady na." *"Adeel* har yanzu shi Dadyn ka bai buqaci dana yafe masa ba, hakan yana nufin cewar bai shirya nai man afuwata da gafarata ba. Wannan yana nufin cewar bai yi nadamar duk wani abin daya aikata min ba, to dan haka ba buqatar ka damu sosai a kansa ka ji ko yanzu kaci abinci."

Ya jinjina mata ka tare da furta mata to, nan kuwa ta fara ba shi abinci bayan sun k'aras ta tashi ta tafi, *Adeel* ya mata rakiya sai da ta tafi sannan ya juya ya koma gurin Dadyn sa. Ya shiga ciki ya same sa kamar dai yanda ya barsa ya isa inda yake ya zauna tare da fad'ar sunan sa. "Dady duk da cewar kai ne wanda ya raine ni amma kuma ka gagara sanar da ni gaskiyar waye kai, kana da k'ani amma baka tab'a sanar da ni ba mai yasa? Dady k'ila a baya Papa ya tab'a aikata maka wani laifi amma kuma hakan bai dakatar da shi daga sanka ba. Yayi komai domin ganin ka samu lafiya har ma jinin sa ya baka, sannan ya biya maka duka kud'ad'en asibiti, kuma yayi hakan cikin nuna qauna da soyayya amma kuma kai mai kayi? Dady sam bai kamata ka dakatar da Papa zuwa gareka ba sabo da shi ďin d'an uwa na gari ne a gareka. Dady naro e ka daka amince da Papa a matsayin ďan uwa na gari a gareka dama *Adnan* dan Allah." Prof yayi shiru na jim kad'an sannan ya amsa shi. *"Adeel* abin sam ba shi da sauki kamar yanda kake tunani, ďana wannan mutumen da yake kiran kansa da k'anina, shi da mahaifiyar sa sunyi matuqar cutar da ni sosai, sam na kasa manta irin abin da suka aikata min shi yasa ba zan iya amincewa da shi ba kayi hak'uri." "Amma Dady." "A'a ďana kawai kayi hak'uri dan Allah."

Ya jinjina masa ka a lamar to daga bisani yaci gaba da magana. "Dady lokaci ya tafi sosai ya kamata kaci abinci, yanzu fad'a min mai zaka ci na kawo ma.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, "na gode sosai d'ana Allah ya ma albarka kawai ka kawon samosa abin da nafi so." "Shikenan Dady yanzu zan tafi na kawo." Ya jinjina masa ka yana murmushi shi ma abin da yake yi kenan. Ya juya ya fita domin kawo masa abin daya buqata daga garesa wato samosa, ba jimawa sosai ya dawo wanda kuma shi ne da kansa yake ba shi yana ci har ya k'arasa. Tin da jimawa ya gama fahimtar cewa yaron nasa sam baya cikin kyakkyawan yanayi, yana k'oqarin shiga mota Papa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. "Masoyi sam baka cikin kyakkyawan yanayi to ina ga sam bai kamata kayi tuk'i a haka ba, to ni zan tafi tare da kai kuma ba zan amince da jin kalmar a'a ba dan Allah." Ya jinjina masa ka tare da furta masa to, ya rufe motar sa ya juya ya shiga motar Papa sun nufi gida. Ganin yanda yanayin sa yake ta canjawa yasa Papa ya koma gefen hanya yayi parking, yasa hanunsa aljihu ya ciro maganin sa tare da d'aukar bowar ruwa, ya mai da kallonsa ga fuskar yaronsa tare da fad'ar sunan sa. "Masoyi ka sha maganin ka sabo da akwai buqatar ka huta dan Allah." Ba gardama ya karb'i maganin daga hanunsa ya sha cikin tautasa murya yake magana.

"Na gode sosai Papa da irin yanda kake kulawa da ni sosai, ko yaushe kana nuna min qauna sosai tare da nuna min soyayya, duk da cewar na girma sosai amma kuma har yanzu kana nuna min cikakkiyar kulawa sosai, kamar sanda nake yaro gaskiya kai uba na gari ne a gareni, ina godiya sosai da samun ka ina qaunarka sosai fiye da yanda nake sanka I love you so much Papa." Magana yake cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai, ba kuka yake ba amma kuma idanuwansa kwalla suke zubar wa mai tsananin zafi da k'una sosai. kuma zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, cike da qaunar sa ya janyo sa zuwa jikin sa tare dayi masa kyakkyawar runguma sosai yana sunbatarsa.

"Rabin raina kai ďana ne to lalle ya zama dole a gareni dana baka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login