Showing 135001 words to 138000 words out of 142761 words
Chapter 46 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
tashi zuwa wani guri daban, ba jimawa ta dawo tare dasu *Afnan Adnan* ya shiga yi musu sannu da zuwa, sun amsa suna murmushi mai had'e da dariya bayan sun gaisa Mum ta shiga tambayar, *Afnan* jikin ta ta amsa da cewar tana samun sauki sosai, ba jimawa sai ga Papa ya fito wanda fitowarsa tayi daidai da shigowar Prof. Nan kuwa Papa ya shiga yi masa sannu da zuwa, ya amsa cikin kyakkyawan yanayi sun tafi sun zauna sun gaisa gaba d'aya, Prof ya sauke kallonsa ga fuskar Mum wacce ita kuma wani guri daban take kallo, lokaci ďaya kuma ta tashi tare da furta musu kalmar sai an jima.
Da sauri Prof ya dakatar da ita ta hanyar fad'ar sunan ta. "A'a *Ummu Adeel* sam bai kamata ki tafi yanzu ba dan Allah." Ba tare data kalli ko kusa da inda yake ba take magana. "Mai yasa zanci gaba da zama a nan bayan kuma ina da buqatar na tafi.?" "Na san cewar zaki tafi ne sabo da ina nan amma bawai sabo da kina da buk'atar tafiya ba, *Ummu Adeel* dan Allah karki ci gaba da hukunta ni haka, eh na san cewar ni na cutar dake da yawa sosai, amma kuma hakan sam baya nufin cewar ba zaki yafemin ba. Na tabbata kin ji dalilin da yasa na aikata maki duka wannan, Aisha na amince da cewar na yaudareki sosai amma kuma hakan bai hana ni sanki ba, bai zama dole daki yarda da ni ba amma Ubangiji shi yafi mu sanin gaskiyar. Aisha dan Allah ki yafemin ki gafarce ni a kan duk wani zunubin dana aikata maki please." "Wai da gaske kana san na yafe maka to shikenan zanyi hakan amma a bisa wani sharad'i." Cike da d'auki yake tambayarta miye sharad'in, tayi shiru kad'an sannan ta ci gaba da magana.
"Prof sharad'in shi ne ka dawo da baya shekaru ashirin da biyar da suka wuce, ta yanda zan samu damar kasancewa uwa ta gari ga sauran yarana daka kashe. Sannan kuma ka kasance uba na gari ga duka yaranmu, kuma muji na gari a gareni siriki na gari a gurin Umma na, ta yanda komai zai wuce a guri na zuciyata da kuma rayuwata gaba ďaya. Idan kuma ba zaka iya yin hakan ba to karka k'ara furta min komai na har abada." "Aisha da a ce ni zan iya yin hakan to da tin da jimawa nayi hakan, amma ba zan iya dawo da baya ba ke ma kin san da haka, to dan Allah karki yi min hukuncin da bai zan iya d'auka ba. A game da yaran kuma nima naso a ce sun rayu, domin na nai mi afuwarsu gafararsu da kuma yafiyarsu, ba lallai ki yarda da ni ba amma nima ina matuqar bak'in cikin abin dana aikata. Musamman cutar da yaran da nayi wannan shi ne babba kuma mummunan zunubin dana aikata a rayuwata, kuma na tabbata wannan k'uncin shi ne abin da zai zamo silar mutuwa ta, amma kafin nan zanso a ce kin yafe min ta yanda zan samu kyakkyawar gobe, Aisha dan Allah da girman Allah kiyi hak'uri ki yafemin please."
"Prof k'ila dai wani lokaci amma ba yanzu ba sabo da." "A'a Aisha dan Allah ki dena a zabtar da ni haka domin." Cikin sauri *Adnan* ya dakatar da shi. "Malan ya isa haka ta ce a'a to mai yasa kake san ka matsa mata ne? Karka yi k'oqarin tursasata ga abin da bata da ra'ayi da shi, ta ce wani lokaci to kawai ka jira ko kuma dai ka k'ure hak'urin ta, ta yanda ba zata yi tunanin yafe maka ba to karka bar hakan ta faru da kai domin." "Barrister ko zaka iya yin shiru haka dan Allah? Sabo da sam baka taimakawa to ina ga kawai mu bar wannan a tsaninsu please." *"Adeel* to mai kake san na fad'a ne shin kana san na goyi bayan ta yafe masa ne? A'a sabo da bai cancanci yafiyarta ba cikin sauk'i, zata iya yafe masa amma ba cikin sauk'i haka ba. Sabo da akwai buqatar ta hukunta shi a kan duk wani zunubi nasa, to ka da ka hana ta yin abin daya dace kawai sabo da yana mahaifin ka, domin ita tana yin abin daya dace ne kuma kai ma kanka kasan da haka."
"Barrister amma kuma hakan sam ba zai canja gaskiyar ba, shi ya tab'a zama mujin ta sannan kuma har yanzu shi ne uban yaranta, ko da a ce suna raye ko a kasin haka Barrister bawai ina cewa Dady bai aikata kuskure ba, a'a ni kawai ina ganin ya kamata duka wannan ya wuce mu kuma amince da gaskiyar, Dady ya cutar da ita sosai ya kuma amince da hakan sannan kuma ya nai mi afuwarta gafaranta da kuma yafiyarta. Hakama dukanmu a nan mun ga nadamar abin daya aikata a tare da shi sosai, ni d'in nan nafi kowa sanin waye Dady na da kuma yanda yake, sabo da da shi ne nayi gaba ďaya rayuwata Barrister Dady na yana tare da nadama sosai. Kuma ya jima sosai a cikin ta a kullum kuma a ko yaushe, ba abin da yake sai tunanin yanda zai samu yafiyar Mum. Yayin da damuwa tayi matuqar yi masa yawa sosai, wani lokacin ma kwalla yake zubarwa to ya kamata ku kyautata masa zato, Mum ba zan ce ki yafe masa ba sabo da na san kina yin abin daya dace, Dady ka jira kamar yanda ta fad'a insha Allah lokaci zai zo wanda Mum zata yafe maka."
"Nima ina fatan haka ďana *Adnan* dan Allah ka fad'a min mai ya saka kake tare da tsanata sosai? Ni dai ban san na aikata maka wani kuskure ba amma kuma kai baka tab'a sona ba, *Adnan* ni Uncle ďin ka ne to ya kamata ka koyi yanda zaka girmama ni. Na san cewar kai ka damu sosai a kan Aisha amma hakan baya baka damar da zaka rik'a fishi da ni sosai, dukanmu ahali ďaya ne to ya kamata muso juna a gurin mahaifin ka na koyi wannan. To dan Allah ka dena cutar da ni sosai haka please." "Mum ni zan shiga ciki mun gode sosai da ziyara, *Adeel* ka kula da ita sosai ina gaida Kaka." Ya yunk'ura zai tashi Papa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar fad'ar sunan sa. "Rabin raina shin ko zamu iya yin magana yanzu dan Allah.?" Ya jinjina masa ka tare da furta eh Papa yaci gaba da magana.
"Masoyi dan Allah ko zaka dena fishi da Yayana kuma Kawunka dan Allah.?" "Shikenan Papa daga yanzu zan kasance d'a na gari a garesa, idan har yayi alkawarin kasancewa Kawu na gari a gareni zanyi hakan kawai sabo da kai, ina sanka Papa ina matuqar masifar qaunarka sosai." Magana yake cikin wani irin yanayi yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai Papa ya tashi daga inda yake ya koma kusa da shi ya zauna kusa sosai. Ya fara da share masa kwalla tare da sunbatarsa sannan ya fara magana. "Nima ina qaunarka sosai d'ana fiye da komai dana mallaka, kai abin da nafi so fiye da komai na gode sosai da samun ka ďana." lokaci d'aya suka yi hugging juna su Mum sai wani kallonsu suke, Mamie ta tashi daga gurin zaman ta ta nufi inda suke, yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai. "Masoyi wannan rungumar ahali ce to sam bai kamata ka bar Mamie a gefe ba, ko da yake wannan lafin Papa ne to banyi fishi ba rungumar ahali."
Sun k'ara runguma juna sosai suna murmushi mai had'e da dariya sosai, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna daga hugging d'in da suka yi, wanda kuma har zuwa wannan lokacin su Prof kallonsu suke yayin da suke jin suna birgesu sosai, parlour yayi jim kad'an ba mai magana a cikin su Papa ne wanda ya kau da shirun gurin, inda ya shiga rarrashin Mum tare da bata magana a kan ta yafe wa Prof abin daya aikata mata. A zahirin gaskiya tana matuqar jin nauyin Papa sosai, wanda wannan dalilin ne yasa ta amsa shi da to sam bata da wani zab'i, wanda dole ta furta wa Prof cewa ta yafe masa yayi matuqar farin ciki sosai da hakan, ya shiga yiwa Papa godiya dama ita Mum farin ciki gurin *Adeel* sam ba zai fad'u ba. Sai dai na ce yana farin ciki sosai yayin da *Adnan* ya gagara fad'ar komai, bayan wani lokaci su Mum suka tafi Prof kuwa sai dare sosai ya tafi.
Bayan kwana biyu *Adeel* yake yiwa Mum ta yin komawa gidan Prof tayi jim kad'an sannan ta amsa shi. *"Adeel* cewar na yafe wa Dadyn ka baya nufin zan koma kasancewa a tare da shi, a wannan rayuwar idan da akwai wani abin dana tsana to Prof ne, auran sa da nayi shi ne babban kuskurena a rayuwa ko a wancan lokacin mugunyar kaddara ce ta had'a ni aure da shi. To sam ba zanso wannan mummunan kaddarar ta k'ara kasancewa tare da ni ba, kayi hak'uri ďana sabo da ba zan tab'a komawa a gurin mahaifin ka ba, ni da shi mun riga da mun rabu rabuwa kuma ta har abada wannan ce gaskiyar, to ya kamata ka amince da ita ka ji ko." "Amma Mum." "A'a *Adeel* kawai ka amince da gaskiyar sabo da ba abin da zai canja ta ka ji ko dan Allah." Ya jinjina mata ka yayin da idanuwan sa suke zubar da kwalla mai tsananin zafi da k'una sosai. Ta shiga share masa kwalla tana rarrashin sa tare da ba shi magana, ta yanda zai iya fahimtar ta ba shi da wani zab'i wannan yasa dole ya hak'ura da buk'atar sa.
Wani yammaci su uku ne kawai a parlour Abba ya sauke kallonsa ga fuskar Umma tare da fad'ar sunan ta. "Asiya ni kuwa zanso na san abin da yasa Aisha bata san ta koma gidan Prof? Shin shi d'in ya ta'ba yunk'urin cutar da ita ne ina san na san gaskiyar gaba ďaya.?" "Eh haka ne shi ďin ya cutar da ita sosai." Nan kuwa ta shiga sanar dasu komai daya faru cike da jin mamakin abin data fad'a Abba yake magana. "Mine shi wane irin uba ne da har zai yi tunanin cutar da yaransa haka? Duk da cewar yaransa ne amma da akwai buqatar na hukunta shi, sabo da kuskuran sa ne yaran suka mutu to ya kamata duniyar ta san wane irin uba ne shi, tabbas ni sai na hukunta shi a bisa mummunan zunubin sa." "A'a Yaya dan Allah karka yi naro e ka ka da ka aikata masa komai dan Allah." "Asiya duk da irin girman zunubin daya aikata kuma kina nuna tausayawar ki a kansa mai yasa.?"
"Yaya bawai sabo da shi nake wannan ba a'a sabo da yaran ne, sabo da ba zanso yanayin ya cutar dasu ba." "Asiya a kan wad'an da yara kike magana.?" Shiru bata yi magana ba, "Asiya ki amsa ni a kan wad'an da yara kike magana.?" "Yaya to ai yaran sun rayu kuma suna cikin kyakkyawar rayuwa sosai. Sannan su ne wad'an da suka yi k'aryan cewa sun mutu, sabo da basa san kowa ya san gaskiyar musamman iyayen da suka rayu dasu, wanda wannan dalilin ne yasa suke fad'ar cewar sun mutu wannan ce gaskiyar." Cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana. "To ta ya suka bar gidan marayun.?" "Basu ne suka bar gidan ba mutanan da suka fara d'aukan rik'onsu suka rabosu da gidan, su kuma sun rasa yaran a nan hanyar katsina ta hanyar yi musu fashi tare da sace yaran, to a lokacin ne yaran suka rabu amma abin farin cikin shi ne, dukansu sun samu iyaye na gari kuma abin alfahari sosai."
Cike da firgici da rud'ani Abbu ya mai da kallonsa ga fuskar Abba tare da fad'ar sunan sa. "Yaya bayanin ta yana nufin cewar." Da sauri Umma ta dakatar da shi ta hanyar furta masa kalmar. "Eh hasashen ka gaskiya ne to ba buqatar sai ka fad'i sunan sa, sabo da bai kamata wani ya san da wannan ba kuma sam banso kusan gaskiyar ba, amma ba yanda na iya ne sabo da ya zame dole to dan Allah da girman Allah, karku sanar da kowa wannan sirrin musamman su Ahmad sabo da hakan zai yi matuqar cutar dasu sosai, dama shi yaron fatan kun fahimci abin da nake fad'a.?" "Ke kina da kirki sosai sannan kuma kina matuqar qaunar ahalinki sosai, duk da cewar kun san a salin gaskiyar amma baku tab'a nuna wa ba kawai kun bar abin a zuciyarku, gaskiya nayi matuqar farin ciki da hakan sosai, dama ba wanda ya san gaskiyar ko a baya balantana kuma yanzu, da muka san a salin gaskiyar gaba ďaya karki wani damu Asiya sabo da ba wanda zai san wannan." Nan ya shiga sanar da ita komai a game da *Adyan* ya kuma ci gaba da magana.
*"Adyan* tamkar rayuwarmu yake to zamu yi komai sabo da shi, yanzu fad'a mana waye d'ayan yaron kuma yana ina.?" Tayi shiru kad'an sannan ta amsa shi da cewa *Adnan,* cike da jin mamakin abin data fad'a yake magana. "Asiya wai kina magana a kan *Adnan* yaron San Adam Muh'd.?" Ta jinjina masa ka tare da sanar da shi komai Abba yaci gaba da magana. "Ni naga yanda San Adam yake matuqar qaunar yaronsa sosai, zai yi matuqar wahala ka ji ya kira sa a salin sunan sa sai dai masoyi ko rabin rai, gaskiya shi uba na gari ne a gurin yaransa nayi farin ciki sosai daya kasance tare da *Adnan.* Sannan kuma mutum mai matuqar girma da daraja irin San Adam Muh'd bai kamata ya san gaskiyar ba, sam ba zamu cutar da shi ta wannan hanyar ba, abin farin cikin shi ne dukanmu ahali ďaya ne to wannan ma kawai ya isa."
Sun jima sosai suna tattaunawa a game da zancan, daga bisani suka tsayu a kan ba wanda zai san gaskiyar, bayan kwana biyu a safiyar litinin ce *Afnan* ta tashi da ciwon nak'uda, cikin hanzari tare da nuna kulawa su Mamie suka d'auke ta zuwa asibiti. Tare suka tafi dasu Anwar bayan sun isa asibiti ne Mamie ta sanar dasu Papa, kasancewar sun fita zuwa office cikin hanzari suka nufi asibiti, ganin ta jima tana abu ďaya yasa *Adnan* kiran layin *Adyan* ya sanar da shi, ya amsa shi da ga shi nan tafe sunyi sallama bai fi da mintuna ashirin ba sai ga *Adyan,* wanda tare yake da *Aliahart* dasu Appa Ammie ta shiga ciki dan ganin abin da yake faruwa. Ta kuwa same ta cikin yanayi na ban tausayi sosai, nan kuwa ta shiga taimaka mata dan ganin ta aihu lafiya, ba jimawa sai gasu Mum kasancewar *Adnan* ya sanar da ita a waya, bai fi da mintuna goma ba sai ga Prof wanda shi kuma Papa ya sanar da shi.
Duka ahalin suna nan har dasu Mama jin yanda a ke zancan cewa *Afnan* ta wahala, yayi matuqar tsorata *Alishart* sosai lokaci ďaya duk ta shiga firgici sosai, kafin su ankara wani zazza'bi mai zafi ya rufe ta wanda yazo mata tare da ciwon mara mai tsanani sosai. cikin hanzari *Adyan* da Appa sunyi kanta lokaci ďaya kuma jini ya fara yi mata zuba, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya gani yake magana. "A'a sam bai kamata hakan ta faru da ita ba bai kamata ta shiga cikin wannan yanayin ba, Appa kai ka riga da kasan komai a game da ita to ya kamata a yi mata C. S. Yanzu cikin gaugawa sosai."
"Eh ďana nima abin da nake qoqarin fad'a kenan, yanzu mu fara kai ta ciki sannan sai mu shirya komai." Ya amsa shi da to Appa yasa nurse sun d'auke ta zuwa ďakin tiyata, ya fara magana da shugaban asibitin sannan suka fara shirin yi mata C. S. Wanda kuma Prof ne ya bata jini ba jimawa sosai a ka fara yi mata C. S ba jimawa sosai da shiga da ita tiyata, sai ga Ammie ta fito tana yi musu kyakkyawan albishir na cewar ta aifi twin's duka maza, duk da cewar ta aihu lafiya amma basa wata murna sosai ta shiga tambayar su abin da yake faruwa. Sun sanar da ita da sauri ta juya ta nufi d'akin tiyata domin ganin abin da yake tafiya, ta same su sun kusa k'arasa aikin su ita ma ta saka nata gudunmuwa, bayan wani lokaci ta koma fitowa tana mai yi musu albishir na cewar an ciro mata twin's mace da namuji..................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/23, 6:22 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*THREE BROTHER'S*
👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑
*Page 55*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu