Showing 15001 words to 18000 words out of 142761 words
Chapter 6 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt
sosai a kunne na fad'a min har yanzu baka ji ba? Ni ina jin kukan sosai sannan kuma idan na rufe idanuwana ina ganin wasu yara cikin wani mummunan yanayi musamman idan ina barci, ni ban san mai yasa hakan take faruwa da ni ba fad'a min wani abu shin kai har yanzu baka jiyo sautin kukan yaron.?"
Magana take cikin wani irin wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba, shi kuwa sai wani irin kallo yake yi mata kallo sosai cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin data fad'a yake magana. "Aisha amma tin yaushe ne hakan take faruwa da ke.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa shi, "gaskiya ba zan iya tinawa ba sabo da na jima a haka." "Aisha amma mai ya saka baki ta'ba sanar da ni gaskiyar ba.?" "Kayi hak'uri sabo da wani lokacin ko da zanji irin hakan to kai baka gida shi yasa ban iya sanar da kai ba." Ya jinjina ka yana cewa, "shikenan zan kula da wannan yanzu ki huta kinji ko ina sanki." Ya fad'a tare da sunbatarta ya d'ora kanta a kan cinyarsa yana wani shafar gashin kanta yayin da yake magana da zuciyarsa.
"Mai hakan yake nufi mai ya saka yaran suke k'oqarin dawowa rayuwar mu? A'a ni sam ba zan bar hakan ta faru ba, ina nufin ba zan ta'ba barin su dawo rayuwar mu ba sabo da ban shirya kar'ban su a matsayin 'ya'yana ba *Adeel* kawai nake buqata, kuma yana tare da ni babu wani dalilin da zai sa ni na buqaci wasu yara kuma, to amma kuma mai ya saka wad'an nan yaran suke bibiyar Aisha mai yasa suke k'oqarin kawo mana qalubale a cikin rayuwarmu? Hakan sam bai dace ba sannan kuma bai kamata a ce su sunyi hakan ba amma zanyi wani abu domin na dakatar da duka wannan. To amma mai ya kamata ni nayi domin dakatar da wad'an nan yaran? Lallai da akwai buqatar su fita daga rayuwar mu gaba d'aya to mai zanyi kenan.?" Haka ya shiga nazari da tinanin abin da ya kamata yayi domin twin's su fita daga rayuwar su, duk da cewar basa tare dasu kuma rayuwar Ummar su suke amma kuma ya damu sosai, to zamu iya kiran wannan da rashin so ko kuma mu kira shi da k'iyayya to Allah ya kyauta Amin.
kwance yake yayin da d'ora *Adyan* a kan k'irjin sa ya runguma shi sosai jikin sa, sannu a hankali take turo ofar har ta bud'e ta shiga ciki tayi tsaye jikin ofa sai wani kallonsu take tana murmushi, lokaci d'aya taji suna birgeta ta nufi inda suke sannu a hankali take tafiya tana sand'a tamkar da zata saci wani abu har ta isa inda suke. sannu a hankali take janye hanun Ahmad daga jikin *Adyan* har ta janye tana k'oqarin d'aukan sa Ahmad yayi saurin dakatar da ita ta hanyar ri e hanun ta, ta nisa tare da jan numfashi tana wani girgiza ka sam bata yi tinanin cewar ba barci yake ba ganin yanda idanuwan sa suke a rufe, sannu a hankali yake bud'e idanuwansa har suka bud'e ya sauke kallonsa ga fuskar ta lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna, kasancewar ita ma kallonsa take sun jima a haka suna kallon juna sannan daga bisani suka sauke kallonsu ga yaronsu wato *Adyan.* Sun samu shiru na wani lokaci sannan daga bisani ya mai da kallonsa gareta ya qara da anbatar sunan ta, magana yake cikin sannu a hankali tare da kwantar da murya duk dan sabo da kar ya tashi *Adyan* daga barci..................
*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[12/28/2021, 10:52 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
*THREE BROTHER'S*
ππππππ
πππππ
ππππ
πππ
ππ
π
*Page seven*
β *β GΜΎOΜΎLΜΎDΜΎEΜΎNΜΎ PΜΎEΜΎNΜΎ WΜΎRΜΎIΜΎTΜΎEΜΎRΜΎSΜΎ AΜΎSΜΎSΜΎOΜΎCΜΎIΜΎAΜΎTΜΎIΜΎOΜΎNΜΎ* ββ
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
*wΜΆΜΆΡ Ξ±rΜΆΜΆΡ Π²ΡΞ±rΜΆΜΆΡrΜΆΜΆ'sΜΆΜΆ ΟfΜΆΜΆ sΜΆΜΆΟ gΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ*
*wΜΆΜΆΡ wΜΆΜΆrΜΆΜΆΓtΜΆΜΆΡ Ξ±sΜΆΜΆsΜΆΜΆΓdΜΆΜΆΓΟuΜΆΜΆsΜΆΜΆlΜΆΜΆΡ pΜΆΜΆΡrΜΆΜΆcΜΆΜΆΡΓvΜΆΜΆΡ nΜΆΜΆΟ pΜΆΜΆΞ±ΓnΜΆΜΆ,*
*sΜΆΜΆΟ mΜΆΜΆΞ±gΜΆΜΆΓcΜΆΜΆΞ±lΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ cΜΆΜΆrΜΆΜΆΡΞ±tΜΆΜΆΓvΜΆΜΆΡ gΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆΜΆ* β *,Π²ΡhΜΆΜΆΟlΜΆΜΆdΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ.Ξ± pΜΆΜΆrΜΆΜΆΟdΜΆΜΆuΜΆΜΆcΜΆΜΆtΜΆΜΆ ΟfΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ pΜΆΜΆΡnΜΆ*ΜΆ *,sΜΆΜΆΞ±vΜΆΜΆΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ ΟuΜΆΜΆrΜΆΜΆ wΜΆΜΆΟrΜΆΜΆdΜΆΜΆsΜΆΜΆ, fΜΆΜΆΟrΜΆΜΆ ΓtΜΆΜΆ wΜΆΜΆΓlΜΆΜΆlΜΆΜΆ* *cΜΆΜΆΞ±uΜΆΜΆsΜΆΜΆΡ ΡΟuΜΆΜΆ nΜΆΜΆΟ pΜΆΜΆΞ±ΓnΜΆΜΆ.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ΖUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ΖARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buΖata namu daga farko.
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana Ζara mana Ζarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
*Saturday 25/12/2021*
*Time 08:14pm*
*Typing..............*
"Mai kike k'oqarin yi ne.?" Tayi shiru na jim kad'an sannan ta amsa mashi, "am ni kawai ina da kwad'ayin na rungumi yarona sabo da na jima bana tare da shi." Magana take yayin da take shafar *Adyan* Ahmad ya sauke kallonsa ga yaron yana murmushi sai kuma zuwa wannan lokacin ya amsa mata. "Ki duba yaron da kyau kiga barci yake cikin kyakkyawan yanayi ga a lama yana farin ciki sosai, to ya kamata ki tafi yanzu sabo da ni ba zan baki damar da zaki d'auke sa ba. A maimakon haka kamata yayi ki tafi ki shirya zuwa school yanzu." Sai kuma zuwa wannan lokacin ne ya sake mata hanu ita kuwa sai wani kallonsa take kallo sosai. "Yaya Ahmad hakan ba daidai bane ni ina iya k'oqari na domin ganin na daidai ta komai amma kuma kai."
"A'a Ahlam karki manta da yarjejeniyar da take tsakanin mu biyun, wanda kuma ke ce da kanki wadda ta tsara komai ko dai ke kin manta ko a'a kina buqatar ni na tina maki ne.?" Shiru bata yi magana ba jin shirun yayi yawa yasa yaci gaba da magana, "Ahlam a game da *Adyan* kin yarda cewar zai kwana Δaya a tare da ke nima zai kwana Δaya a tare da ni, na yarda da hakan ba tare dana musanta ba ke kin tsara komai kuma na amince da duka tsarin. To amma mai ya saka yanzu kike k'oqarin ganin laifi na? Hakan rashin adalci ne kuma sam bai kamata kiyi hakan ba to yanzu zaki iya tafiya jeki." "Yaya Ahmad ni bawai ina bijirewa yarjejeniyar bane a'a abin shi ne ni kawai na damu ne sosai a kan *Adyan.* Ina matuqar jin kewarsa sosai ina san na runguma shi jikina, Yaya Ahmad zuwa yanzu ni uwa ce to sam ba zai zama laifi ba idan har ni na nuna kulawa ta a kan yarona, to ya kamata ka fahimci wannan domin ka iya yi man adalci zan tafi kamar dai yanda ka buqata amma ya kamata na shirya yaron yanzu, lokaci ya tafi sam bana san mu makara zuwa school."
Magana take cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya fad'ar sa ba. Tana kai k'arshen maganar ta ta juya tayi tafiyarta ba tare data jira taji mai zai fad'a ba, ya bita da kallo har ta fice ya dawo da kallonsa ga *Adyan* wanda kuma har zuwa wannan lokacin barci yake, ya shafi kansa zuwa bayan sa cikin tautasa murya yake magana. "Rabin raina lokaci ya tafi sosai zuwa yanzu ya kamata a ce mun shirya zuwa school, amma kuma ga shi kai har zuwa yanzu barci kake to ta ya kuma ni zan shirya ka a haka. Ya kamata nayi wani abu wanda zai tashe ka ba kuma tare da hakan ya cutar da kai ba to mai ya kamata nayi kenan.?" Ya shiga nazari da tinanin mai zai yi ya tashi zaune tare da rungumasa sai wani kallonsa yake yana murmushi, lokaci d'aya kuma ya shiga sunbatarsa yana yi masa cakulkul, nan kuwa ya bud'e idanuwansa yana dariya Ahmad kuwa murmushi yake mai tare da ar dariya.
Ya tashi tare da d'aukan sa sun nufi toilet duk abin da yake a kan idanuwan Ahlam tana kallonsu ta window. Ganin ya shiga toilet yasa ita ma ta nufi bedroom domin ta shirya ba jimawa sosai Ahmad ya fita d'auke da *Adyan* ya fara shirya *Adyan* sannan ya shirya. Hakama a can gurin Ahlam bayan ta fito wanka ta shirya cikin wata kyakkyawar shiga ta doguwar riga shigar ta amsheta sosai, ta fito wanda fitowarta tayi daidai data Ahmad d'auke yake da *Adyan* cike da d'auki ta isa inda suke tana anbatar sunan *Adyan.* Shi kuwa sai wani zillo yake mata yana dariya ta kai hanun ta domin amsar sa, kamar ba zai bata shi ba mai ya gani kuma ya bata shi ta kar'be sa tana yi masa wasa shi kuwa sai dariya yake su kuwa murmushi suke sosai mai tare da ar dariya.
Sun nufi tebur domin yin break past bayan sun qarasa Ahlam ta ba *Adyan* madara sannan suka fita zuwa school, haka dai suka ci gaba da baiwa yaron kyakkyawar kulawa sosai bayan wata goma da tafiyar su, Ahmad ya sanar da duka ahalin cewar Ahlam ta aihu ta aifi yaro mai suna *Adyan.* Su Umma sunyi matuqar farin ciki sosai sunyi ta k'oqarin tafiya amma su Ahlam suka dakatar dasu, sam basu da wani za'bi dole suka fasa a can kuma sunci gaba da baiwa *Adyan* kulawa sosai. Haka yake ko a gurin su Asma'u *Adnan* yana cikin kyakkyawar rayuwa yana kuma samun cikakkiyar kulawa a gurin su sosai, kamar dai *Adeel* yana samun kulawa sosai daga gurin iyayen sa musamman ma Prof wanda ya ba shi gaba d'aya soyayyar sa, shi ne abin da yafi so fiye da komai a rayuwar sa barin ma daya kasance yana da rashin lafiya irin ta Maman sa, kamar dai *Adnan da Adyan* bayan shekaru uku har zuwa wannan lokacin Aisha na fama da yanayin firgici na jin kukan yara tare da mafarki dasu, abin har kamar zai ta'ba ta yanayin ta yana matuqar d'aga hankalin Prof sosai da Umma.
Wani dare tana cikin barci wani matsanancin ciwan mara ya tashe ta, sai wani juyi take tana murkususu a zahirin gaskiya tana jin ciwo sosai, nan ta shiga tashin Prof ya tashi cike da firgici yake tambayar ta lafiya. "Subhanalillah Aisha mai yake faruwa da ke ne haka.?" Cikin wata irin murya ta rashin lafiya take magana. "Prof mara ta take wani irin ciwo sosai ina jin kamar ba zan iya jure zafin ba." "Kai Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un wannan wace irin masifa ce haka yaushe kika daga daga asibiti jinta yanzu kuma mara, ga kuma wannan mummunan yanayin da yake tare dake gaskiya abin da yawa wai shege da hauka, yanzu dare yayi sosai to kiyi hak'uri da safe sai mu tafi asibiti kinji." Sam bata iya amsa shi ba sai dai ta jinjina masa ka a lamar to yaci gaba dayi mata sannu daga bisani kuma ya koma barci. Lokaci d'aya kuma yanayin ta ya soma canja wa inda ta fara jiyo sautin kukan yara kamar ko yaushe, ta toshe kunnan ta tana fad'in, "a'a." wannan kalmar ce kawai take anbatar Prof ya tashi sai wani kallonta yake cike da rashin tausayi ya tashi ya fita Δakin ya nufi wani bedroom domin ya kwanta.
Wanda ita ba ma ta san fitar sa ba kasancewar fuskarta na a sunkuye, Ya shiga bedroom yayi zaune jikin gado yana wani jan tsaki yana furta kalmar. "Wannan wace irin masifa ce haka mai na aikata da a ke hukunta ni ta wannan hanyar? Ina san Aisha sosai amma kuma zuwa wannan lokacin na fara k'osawa da wannan yanayin nata. Wanda har ban san tsayin wane lokaci zai d'auka a tare da ita ba, hakan yana matuqar cutar da ni sosai lallai ya kamata nayi wani abu tin kafin yanayin ta yafi haka muni." Ya jima zaune a nan sannan daga bisani ya kwanta yaci gaba da barci abinsa. Washe gari bayan ya qarasa shirin sa ya fito ya nufi d'akin Aisha ya same ta kwance sai wani juyi take ga a lama bata da lafiya, daga gefe kuma ga *Adeel* nan a zaune yana kuka da sauri Prof ya qarasa ciki tare da isa gurin *Adeel* yana fad'ar sunan sa. *"Adeel* mai yake faruwa da kai fad'a min mai ya saka kake kuka.?" "Dady ni ina jin yunwa Mama bata bani abinci ba." Magana yake yana kuka Prof ya shiga rarrashin sa cike da qaunar sa yake magana. "Kayi hak'uri yarona yau Maman ka sam bata cikin kyakkyawan yanayi shi yasa bata baka abinci ba, amma Dady yana nan kuma tare da kai to zaka samu duk abin da kake so yanzu ni zan shirya maka break past."
Magana yake masa cikin soyayya sai wani lalla'basa yake tamkar kwai yayin da yake rungume da shi, ya mai da kallonsa ga Aisha wadda har zuwa wannan lokacin abu d'aya take shi ne juyi sai wani a zabar ciwo mara take ji a tare da ita. Ya shiga yi mata sannu kallonsa kawai tayi ba tare data furta masa komai ba, ya tashi tare da riqa hanun *Adeel* sun fita zuwa kicin domin girka break past. Ya had'a musu shayi da wainar kwai ya shirya komai a tebur ya juya sun koma gurin Aisha, ya same ta kamar yanda ya barta har zuwa wannan lokacin bata cikin kyakkyawan yanayi cike da jin tausayin ya isa inda take yana fad'ar sunan ta. "Aisha har yanzu marar bata saki ba? Subhanalillah kinga yanzu mu tafi muyi break past sai mu tafi asibiti kinji ko." Cikin wata ar murya irin ta rashin lafiya take magana. "A'a Prof kawai ka tafi da *Adeel* kuyi break past sabo da ni ba zan iya cin komai ba a yanzu."
Zai yi magana ta dakatar da shi ta hanyar girgiza masa ka a lamar a'a, ya jinjina mata ka sannan ya tashi tare da d'aukan *Adeel* sun fice zuwa gurin break past. Basu d'auki wani lokaci ba suka kammala ya shiga ciki ya rik'o Aisha sun fita zuwa asibiti, sun isa asibiti an shiga da ita ciki domin a duba ta *Adeel* ya anbaci sunan Prof yana cewa. "Dady mai ya saka Mama take kuka.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi, "rabin raina tana kuka ne sabo da bata da lafiya amma karka wani damu sabo da zata samu lafiya ka ji ko." Ya amsa shi da to nan Prof ya shiga kiran layin Umma ba jimawa ta d'aga, bayan sun gaisa ya sanar da ita cewar yana asibiti tare da Aisha.
"Subhanalillah mai kuma ya faru da ita.?" "Ciwon mara ne yake damunta, sai kuma wannan firgicin da yake a tare da ita." "Ho! Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un Allah ya bata tafiya gani nan tafe yanzu." Ya amsa da to ya fara sanar da ita asibitin da suke sannan daga bisani suka yi sallama. Doctor's sun jima sosai a tare da ita sannan suka fito cikin hanzari Prof ya shiga tambayar su jikin ta, "Dr Salim to ya jikin na ta.?" "Prof har yanzu muna kanta karka wani damu zata samu lafiya insha Allah yanzu ka tafi ka kawo wannan." ya miqa masa wata takarda ya kar'bi takardar tare da d'aukan *Adeel* ya fice Dr salim kuma ya nufi office. Bayan wani lokaci Prof ya dawo kai tsaye office d'in Dr Salim ya nufa ya kai masa abin daya buqata a siyo, ya kar'bi kayan sun fito tare Dr Salim ya nufi d'akin da Aisha take Prof ma binsa yayi a baya ya tsaya a gefen ofa.
Ba jimawa sai ga Umma nan kuwa ta shiga tambayar Prof jikin Aisha, "tana ciki suna duba ta." "ina fatan ta samu sauki cikin sauri Allah ya bata tafiya." Ya amsa da Amin bayan wani tsayin lokaci da suka d'auka a tare da ita sosai sun fito, su Dr Anisa sun fice zuwa office Dr Salim kuma ya tsaya domin yayi magana da Prof, da sauri Prof ya isa garesa domin jin lafiyar matarsa ya ja hanun sa sun koma gefe cikin kasa-kasa da murya tare da kwantar da ita yake magana. "Dr Salim kana fa tsorata ni da wannan shirun naka dan Allah ka sanar da ni abin da yake faruwa da matata.?" Ya girgiza tare da sauke a jiyar zuciya sannan ya amsa shi. "Prof gaskiyar ita ce Madam sam bata cikin kyakkyawan yanayi sannan kuma tana cikin damuwa sosai, Prof k'ila Madam tana yawan shiga firgici unci da kuma 'bacin rai a ko yaushe, hakan yana k'oqarin ta'ba ta sosai ta hanyar gusar mata da tinanin ta. Prof ka san cewar ita d'in tana da rauni a zuciya wannan yasa ba a san tana unci ko wani abin da zai gajiyar da ita sosai, Prof Madam tana matuqar buqatar kulawa sosai to ya kamata kayi hakan domin ka taimaka mata ta fita daga hatsari."
Wani irin kallo Prof yake yi masa mai cike da firgici rud'ani tare da tashin hankalin abin daya ji yana fad'a, cike da unci bak'in ciki firgici rud'ani da kuma tashin hankali yake magana. "Dr Salim wai mai kake fad'a ne haka a kan matata? Sam bai kamata hakan ta faru da ita ba a'a ni sam ba zan bar wani mummunan abu ya faru da ita ba. Dr Salim dan Allah kayi koma miye domin matata ta samu lafiya lallai ya kamata wannan mummunan yanayin ya barta to kayi komai sabo da ta samu lafiya ka ji ko." "Shikenan zanyi iya abin da zan iya ina fatan ta samu lafiya sosai." Ya jinjina masa ka da kuma haka suka rabu Dr Salim ya nufi office Δin sa Prof da Umma