Showing 75001 words to 78000 words out of 142761 words

Chapter 26 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

k'una sosai. Baba ba wani farin cikin da za a samu idan har a kayi auran *Afnan* da Auwal, ka duba kaga yanda take barazanar kashe kanta k'ila a yanzu zamu iya dakatar da ita, to amma idan a kayi auran waye wannan wanda zai yi yunk'urin dakatar da ita.?"

"Baba ya kamata muyi nazari sosai a kan wannan kawai muyi abin da zai saka yaranmu yin alfahari damu, ina nufin mu aurar dasu ga juna domin sai idan sun rayu ne kawai zamu yi farin ciki. Baba k'ila kai kana da yara biyu koma fiye da haka, *Abban Adnan da Abban Afnan* dukansu yara biyu ne dasu, amma kuma ni d'a d'aya kawai nake da shi kamar dai Abba na ni kawai ya aifa. Hakama Abbu qanwata kawai ya aifa ina nufin *Ummu Adyan,* Baba ni ba zan iya jure ganin yarona yana cutar da kansa ba, shi ya damu sosai a game da abokinsa dama *Afnan* idan wani abu ya faru dasu biyun, to ba zan iya dakatar da yarona ba hakan zai cutar da ahalinmu sosai sabo da shi ne farin cikin mu gaba d'aya. Baba kai ne kawai wanda yake da ikon daidai ta komai a nan to naro e ka da kabar *Adnan da Afnan* su yi aure please." Nan kuwa dukansu suka shiga ba shi magana inda kuma daga bisani, suka yi nasaran amincewar sa hakan yayi matuqar saka su farin ciki sosai. Cike da d'auki Appa yake sanar da *Adyan* abin da yake faruwa kasancewar da hausa suke magana, a zahirin gaskiya yayi matuqar farin ciki sosai wanda har sai da yayi wa Baba godiya, ya mai da kallonsa ga Appa tare da fad'ar sunan sa.

"Appa wannan bai k'are ba da akwai wani abin kuma." "D'ana ka fad'a min miye wannan ni zan daidai ta komai insha Allah to fad'a min miye.?" Ya jinjina masa ka a lamar to ya juya da kallonsa ga *Alishart* wacce har zuwa wannan lokacin idanuwanta basu dena zubar da kwalla ba, murmushinsa ya k'aru sosai ya dawo da kallonsa ga fuskar Appa, lokaci d'aya suka yi ido biyu da juna kasancewar shi ma kallonsa yake yana murmushi. "Masoyi shin a game da sirika ta ne? Fad'a min wani abu shin kai ka shirya wa auran ta a yanzu.?" "Eh Appa amma ina san naji ko ita ma ta shirya wa hakan." "Shikenan ka tafi kayi magana da ita." Ya jinjina masa ka ya juya ya nufi gurin *Alishart* Appa kuma ya koma gurin su Abbu. "Ahmad mai yake faruwa a can gurin.?" "Abbu shi ya fad'a min cewar zai yi magana da sirika ta." Ya fad'a yana dariya su Abba kuma murmushi suke sosai ya isa gurin *Alishart* ya zauna, sai wani kallonta yake ya d'ora hanun sa a kan nata ya d'an shafa tare da murzawa ya sunbaceta a gefen fuska.

"Ke k'uncin ya isa haka sabo da su biyun zasu yi aure to kawai muyi farin ciki, to yanzu ina san zan tambiye ki wani abu *Alishart* shin kina sona kuma zaki aure ni gaskiyar zaki fad'a.?" Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar sa take fitar da wani lallausan murmushi sosai, abin birgewa ga wanda ya gani ita kuwa sai wani kallonsa take yayin da take jin yana birgeta sosai, sun jima sosai a haka suna kallon juna sannan daga bisani ta amsa shi. "Eh *Yaya Adyan* ni ina sanka sosai sannan kuma zan aure ka nayi alkawari insha Allah." Cike da d'auki yayi hugging d'in ta yana sunbatarta hakan ya tabbatar wa da Appa cewar yayi nasara. Yayi wani kyakkyawan murmushi sosai tare da fad'ar sunan Abban sa. "Abba ni fa ina tunanin cewa d'aurin aure biyu zamu yi a gobe, sabo da yarona ya shirya zama muji na gari a gurin sirika ta. *Abban Adnan* ina fatan kai ma zaka amince da hakan.?" Yayi murmushi sosai sannan ya amsa shi, *"Abban Adyan* idan har su biyun sun amince da junansu to ni kawai nawa fatan alkhairi ne da addu'a. *Abban Adyan* amma kuma har yanzu *Alishart* yarinya ce shekarun ta sha biyar ne kawai, sannan kuma secondry ne kawai da ita ina ga yayi wuri da nayi mata aure yanzu. To zamu iya barin wannan zuwa wani lokaci idan ta k'ara girma da hankali fatan ka fahimce ni.?" Kamar daga sama yaji muryar *Adyan* ya amsa shi.

"Papa ni ba zan cutar da ita ba hasalima idan a ka d'aura auran to a nan zan barta, taci gaba da karatu ni kawai ina san ta zama tawa dalilin da yasa nake san a yi auran yanzu, Papa dan Allah karka dakatar da faruwar hakan please." Ya jinjina masa ka yana murmushi, "shikenan yarona na amince da auran ka da *Alishart* Allah ya sanya alkhairi Amin." Cike da d'auki yayi hugging d'in Papa har da sunbatarsa yana yi masa godiya dukansu gurin suna farin ciki sosai, nan kuwa suka shiga zan auran inda a ka saka kud'in sadaki dama komai Abba ya ba da umurnin a bada sanarwa ta yanda zata kai ga kunnan kowa. Bayan wani lokaci su Abbu suka yi sallama dasu Papa suka tafi, ai kuwa cikin k'ank'anin lokaci labarin auran *Adyan da Alishart Adnan da Afnan* ya kai inda ma ba a yi tunani ba. Auwal na cikin tafiya Sadiq ya kira layin sa bama tare da sun gaisa ba yake magana, "Auwal shin gaske ne abin da naji a na fad'a.?" "A kan me kake magana fad'a min mai yake faruwa.?"

"Auwal karka fad'a min cewar baka san abin da yake faruwa ba.?" "Sadiq shin idan na sani zan tambiye ka ne kawai ka sanar da ni abin da yake faruwa.?" "Auwal to fa ni naji labarin cewa za a yi auran *Adnan da Afnan* a gobe." "Sadiq wannan k'arya ne amma dukansu biyun suna asibiti basu da lafiya wannan ce gaskiyar." "Auwal gaskiya bana jin cewar wannan k'arya ne, sai dai idan kai ne baka san gaskiyar ba sabo da zancan yayi yawa a gari, musamman a kan social media sannan kuma Minister of information ne wanda ya bada sanarwa. Sabo da tare za a yi auran dana jikan Mr President kuma jikan Governor kaduna wato *Adyan da Alishart qanwar Adnan."* "A'a Sadiq hakan sam ba zai yu ba sabo da ni ne kawai wanda zai kasance mujin *Afnan,* to kama dena wannan zancan banzan ka ji ko zamu yi magana an jima." Ya a jiye wayar tare da juya mota ya nufi asibiti domin samun tabbaci a kan abin da Sadiq ya sanar da shi. Ba jimawa da tafiyar su Appa Anwar ya dawo asibiti wanda zuwan sa yayi daidai dana Auwal, cike da firgici rud'ani tare da tashin hankali yake tambayar su Baba gaskiyar abin da yake faruwa. Ai kuwa nan suka sanar da shi komai ya shiga firgici sosai, yayin da farin ciki yake ta shigar Anwar wanda har ya gagara fad'ar komai. "Amma Kaka ta ya hakan zata kasance? Sam bai kamata a yi man haka ba sabo da ina san *Afnan* sosai, to dan Allah karku dakatar da aure na da *Afnan* dan Allah." Kafin wani ya amsa shi Anwar ya anbaci sunan sa.

"Auwal tin da jimawa ya kamata a ce an yi hakan amma yanzun ma lokaci bai k'ure ba, sabo dasu biyun zasu yi aure abin dana jima ina fata hakan yayi kyau sosai." "Anwar shin ko zaka dena wannan shirmen naka ka sani ko da mai zai faru to ni ne, kawai wanda zai kasance mujin *Afnan* wannan ce gaskiyar." "Shikenan kayi koma miye amma kuma ba zaka yi nasara ba." Ai kuwa nan suka shiga gardama a tsakanin su wanda sai dasu Abba suka shiga tsakanin su, Baba ya shiga rarrashin Auwal tare da ba shi magana ba shi da wani za'bi dole ya d'auki kaddara, bayan wani lokaci su Kaka suka tashi suka fita zuwa gida domin ci gaba da shirin biki. Ya rage saura su Ummu da yamma lis *Afnan* ta farka daga dogon suman da tayi, sannu a hankali take bud'e idanuwanta har suka bud'e su Ummu sun shiga yi mata sannu, kallonsu kawai take ba tare data amsa su ba cikin wata 'yar murya take magana.

"Ummu ina Besty na fad'a wani abu shin da akwai abin daya faru da shi.?" "A'a ba abin daya faru da shi kawai dai har yanzu bai farka ba, amma an fad'a mana cewar yana samun sauki sosai, sannan kuma Baba ya amince da auran ki da *Adnan* hakama za a yi auran *Adyan da Alishart* duk a gobe." Lokaci d'aya farin ciki ya shigeta sosai wanda har ta gagara fad'ar komai, "gaskiya ina farin ciki sosai yanzu zan tafi na duba jikin Besty na, to dan Allah karki dakatar da ni please." *"Afnan* jikin ki bai gama warware ba ki jira jinin da a kasa maki ya k'are tukun kin ji ko." "Ummu ni qlau nake zan iya tafiya to dan Allah karki dakatar da ni please." Ta jinjina mata ka a lamar to ita da kanta ta cire jinin da a kasa mata Ummu ta rik'a ta sun fita zuwa ďakin da *Adnan* yake............




*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[1/28, 8:58 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 31*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Thursday 27/01/2022*

*Time 12:44pm*

*Typing...............*


Sun shiga d'akin sun samu *Alishart* zaune daga gefen sa, ta shiga yi musu sannu da zuwa tare da yiwa *Afnan* sannu ya jiki, ta amsa da Alhamdulallah ta sauke kallon ta ga fuskar *Adnan.* Ta zauna kusa da shi kusa sosai sai wani kallonsa take kallo sosai, ta shafi fuskarsa zuwa kansa tare da sunbatarsa tana furta Allah ya baka lafiya. Su Abbu sun isa gida Ummi sai sannu da zuwa take musu cike da d'aukin ganin su, bayan sun gaisa Appa ya shiga sanar da ita zancan auran *Adyan da Alishart* cike da d'auki take magana. *"Adyan* ka ce ka fara shirin kawo mana kishiya Aunty shin ke kin amince da hakan kuwa.?" "A'a ta ya ma ni zan yarda da hakan a'a kawai dai zamu ba shi wata 'yar k'aramar dama ce, kafin nan kuma zamu san abin da zamu shirya a kai." "Shikenan Aunty ni ina tare dake." Magana suke cikin kyakkyawan yanayi su Abba sun shiga dariyar su, haka suka shiga sanar da 'yan uwa da abokan arziki yayin da labarin ya zaga ko ina, na sassan k'asa ko ina zai zancan a ke a gari yayin da manyan mutane suka fara shirin tafiya d'aurin aure. Zaune kawai take yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da ita sosai, "ta ya zan iya sanar da *Abban Adnan* irin k'uncin da yake a tare da ni yanzu? Shi sam ya gagara fahimta na gaba d'aya yak'i saurara na, hakan yasa ya yanke min hukuncin da bai dace da ni ba sam bai kamata ya hukunta ni har haka ba. Wannan ciwon yafi komai zafi sosai sannan kuma da matuqar k'una sosai, ya kamata a ce ina tare da yarona sabo da zan iya taimaka masa da wani abu, ya Ubangiji ka bawa yarona lafiya sannan ka bawa Mujina damar da zai dena fishi da ni Allahumma Amin."

Da dare dukansu suna tare a nan ďakin da *Adnan* yake, lokaci d'aya suka ji a na buga masu k'ofa *Alishart* wacce ta tafi ta bud'e k'ofar. Ta samu *Adyan* tsaye a bakin k'ofa lokaci ďaya suka sakarwa juna murmushi, murmushi suke sosai wanda har suka gagara furta wa juna komai, sai daga bisani sannan ta furta masa kalmar shigo ciki ya amsa da to yana murmushi. ya fara gaisawa da kowa da yake gurin sannan ya qarasa gurin *Adnan* sai wani kallonsa yake, ya shafi fuskarsa zuwa kansa sannan ya mai da kallonsa ga Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zan iya ganin file ďin *Adnan* da akwai abin da nake san na duba ne.?" Ya amsa shi da to ya tashi ya fita ba jimawa ya dawo tare da wata nurse, wacce kuma ita ce take ri e da file ta fara yin magana da *Adyan* sannan ta ba shi file ďin ta juya ta fita. Shi kuwa ya shiga duba file ďin cike da firgici da rud'ani yake magana da zuciyarsa. *"Adnan* yana da irin rashin lafiya na shi yasa hakan ta faru da shi, wannan sam bai yi ba amma zan kula da shi sosai shi abokina ne to zanyi komai sabo da shi." Ya mai da kallonsa ga Papa tare da fad'ar sunan sa. "Papa shin ko zan iya had'uwa da likitan daya duba *Adnan.?"* Ya amsa da eh ya tashi sun nufi office ďin Dr Habib wanda a can ne, *Adyan* yayi magana da Dr Habib a game da rashin lafiyar *Adnan* ya kuwa sanar da shi komai.

*Adyan* ya d'auki abin rubutu da takarda yayi rubutu ya bawa Dr Habib yana cewa, "Dr Habib ina buqatar duka wad'an nan abubuwan a yanzu." Yayi wani gajeran murmushi sannan ya amsa shi. *"Adyan* gaskiyar ita ce bamu da irin wad'an nan magungunan da alluran, sai dai ku tafi babban kantin siyar da magani a can ne kawai zaku samu." Cike da jin mamakin abin daya fad'a *Adyan* yake amsa shi. "Mai yasa ba za a samu a nan ba.?" "sabo da wanda muke da shi a nan ya k'are amma za a kawo zuwa jibi insha Allah." Ya jinjina masa ka tare da furta ok ya tashi sun fita sun dawo d'akin da *Adnan* yake, wanda kuma Anwar ne wanda ya tafi ya siyo maganin da allura bai d'auki wani lokaci ba ya dawo, *Adyan* yayi masa duk wani abin daya dace ya jima sosai a nan tare da *Alishart* suna magana sannan daga bisani ya tafi. Haka dai dukansu suka tafi suka bar Papa wanda zai kwana da shi, bayan dawowar *Alishart* Mamie ta shiga tambayar ta jikin *Adnan* ta amsa da cewar yana samun sauki, tare da sanar da ita duk abin da yake faruwa Mamie taci ka da mamaki sosai kasancewar Papa bai sanar da ita komai ba.

Duk da irin yanayin da take ciki amma tayi farin ciki sosai, *Alishart* ta fara had'a lipton tea ta sha sannan ta shiga ciki domin ta kwanta, Mamie ma tashi tayi ta nufi bedroom domin ta kwanta yayin da tunani yayi yawa a tare da ita, washe gari bayan ta qarasa shirin ta tsab ta fito ta gaisa da Mamie sannan ta d'auki abincin *Adnan* ta nufi asibiti. Tin bayan ta idar da azkar ta gaisa da Ummu ta tashi ta nufi d'akin da *Adnan* yake, domin duba jikin sa Papa ne wanda ya bud'e k'ofar ta shiga ciki ta fara gaisawa da shi, sannan ta shiga tambayar jikin *Adnan* ya amsa ta da Alhamdulallah yana samun sauki. Ta k'arasa inda yake ta zauna daga gefen sa sai wani kallonsa take kallo sosai, ta nisa sosai tare da jan numfashi yayin da take magana da zuciyarta. "Besty ina fatan ka samu lafiya cikin sauri ta yanda mu biyun zamu kasance a tare, yau ne a ke auran mu amma kuma har yanzu baka cikin kyakkyawan yanayi, zuwa yanzu ya kamata ka dawo haiyacinka ya Ubangiji ka tashi kafad'ar Mujina ka ba shi lafiya Amin."

Magana take cikin wani irin yanayi mara dad'i yayin da idanuwan ta suke zubar da kwalla, mai tsananin zafi da k'una sosai lokaci d'aya ta samu kanta da shafar fuskarsa tare da sunbatarsa, tana mai furta masa kalmar ina sanka sosai Besty Papa sai wani kallonta yake yana murmushi. "Karki damu 'yata mujin ki zai samu lafiya insha Allah to kawai kiyi farin ciki kinji ko." Ta jinjina masa ka tana murmushi mai tare da nuna jin kunya suna haka sai ga Ummu ta shigo, ta gaisa da Papa tare da tambayar sa jikin *Adnan* ya amsa ta da Alhamdulallah yana samun sauki. "Am *Ummu Afnan* idan bakya wani abu ina san ki kula da *Adnan,* ni zan tafi gida nayi shirin tafiya d'aurin aure." "Eh zaka iya tafiya ni zan kula da dukansu." Ya amsa da to tare dayi mata godiya ta amsa da ba komai, suna haka sai ga *Alishart* ta shigo ta fara da a jiye kayan abincin dake hanun ta, sannan ta gaisa dasu Ummu tare da yiwa *Afnan* ya jiki ta amsa da Alhamdulallah, ba jimawa Papa ya tafi bayan tafiyar sa Abba ya shigo ya d'an jima a nan, sannan ya tashi domin tafiya *Alishart* ta dakatar da shi tare da fad'ar sunan Ummu.

"Ummu ya kamata ki tafi gida ki samu ki huta gajiya ni zan kula dasu sosai, to dan Allah karki ce a'a kawai ki tafi dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login