Showing 129001 words to 132000 words out of 142761 words

Chapter 44 - THREE BROTHERS Complete Novels By Bil-Fauzee U-Adyan.txt

komai, tare da had'in guiwar Abokinsa shi yasa wallahi nayi matuqar tsanar su sosai. Gashi kuma suna barazanar d'auke ďana daga gareni, to zan tabbatar da cewa wannan burin nasu bai cika ba to yanzu zaka iya tafiya, sannan kuma ka fad'a wa Maman cewar har yanzu ina raye, kuma cikin k'oshin lafiya duk da cewar ban samu kulawarta ba, to kawai ka tafi ka bar nan dan Allah......................






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/18, 11:13 PM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*THREE BROTHER'S*

👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑
👑

*Page 52*

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/


*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*


Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk littafin da kike buƙata namu daga farko.



Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa a wajen rubutu mai yawa.



*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Tuesday 15/03/2022*

*Time 05:51pm*

*Typing................*


"Yaya shi Ɗana ba kamar yanda kake tunani bane, hakama *Dr Adyan* shi ma yaron kirki ne sosai, to duk kan su ukun sun dace da kasancewa abokan juna. K'ila dai kuskuren daka aikata ne yasa ubangiji yake hukunta ka ta haka, Yaya ko acan baya ni ban tab'a yi maka k'arya ba, to ba kuma zan fara a yanzu ba ni gaskiyar nake fad'a ma, Mama ta jima da mutuwa kuma kai ne wanda yake da alhakin mutuwar ta. To ka gode Allah da yasa ita ďin ta kasance uwa ta gari a gare mu, sabo da ta yafe maka duk wani zunubin daka aikata mata kafin ta mutu. Yaya shin wai kai kama yi tunani a kan yanda na kasance bayan mutuwar ta, sabo da a lokacin ina yaro d'an shekaru biyar kawai, nayi k'unci sosai na kuma shiga matsanancin hali sosai. Godiya mai tarin yawa ga Kawu Bala mutumen daya kasance uba na gari a gareni."

Nan kuwa ya shiga sanar da shi yanda ya rayu bayan mutuwar Maman su. "Yaya duk da irin yanayin dana tsinci kai na amma hakan bai hana ni sanka ba, sannan kuma ban cire tsammanin cewa wata rana zamu k'ara had'uwa. Ko yaushe ina tare da k'uncin rashin ka ina jin cewar kamar na rasa wani jigo a tare da ni, ina jin cewar ban cika ba sabo da bana tare da kai, sabo da kai ne kawai ahalin da nake da shi kuma ina qaunarka sosai, amma kuma kai baka tab'a tunani a kai na ba hasalima tsanata kawai ce a tare da kai. Ni nayi iya k'oqari na domin na zama k'ani na gari a gareka, amma kuma kai baka tab'a tunanin zama Yaya na gari a gareni ni ba, amma kuma duk da haka ina nuna ma qauna da soyayya, Yaya naro e ka daka da ka ta da duka wannan ka amince da ni a matsayin k'anin ka please." Magana yake cike da k'unci yayin da damuwa tayi yawan gaske a tare da shi sosai. Prof kuwa sai wani kallonsa yake kallo sosai jikin sa gaba ďaya ya mutu, da jin irin abin daya fad'a cikin mutuwar jiki da sanyin murya yake magana. "Adam wai da gaske kake Mama ta mutu.?" Ya jinjina masa ka tare da furta masa kalmar eh.

"Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un na shiga uku na lalace, mai na aikata ne haka ta ya a kai na cutar da Mama na irin wannan mummunan zunubin haka? Ni kawai na ji wani iri ne sosai sannan kuma na ji ba dad'i, a lokacin data yanke hukuncin kai ni almajiranci ba tare data yi tunani a kai na ba. A kullum kuma a ko yaushe zuciyata tana fad'a min cewar Mama bata sona, wanda wannan dalilin ne yasa na yanke shawaran na tafiya ta, sannan kuma irin yanda take nuna maka qauna da soyayya yana na fara jin tsanar ka a tare da ni. Adam wallahi banso Mama ta mutu ba naso a ce ni da ita mu k'ara had'uwa, amma mummunar kaddara ta ta hana ni damar k'ara kasancewa tare da ita. K'ila gaskiyar yaronka ne ni ďin nan nafi kowa rashin sa'a a cikin wannan duniyar, na cutar da mutane da dama kuma dukansu ahalina ne, da fari Mama na ce wacce na fara cutarwa, sai kuma kai da wasu mutanan daban ga kuma Aisha, ta so ni da duka zuciyarta dama rayuwarta gaba d'aya. Amma kuma ni sai na zab'i dana cutar da ita kuma mafi munin cutarwa sosai, hakama *Adeel* shi ma na saka shi a cikin lamarin kuma yanayin ya cutar da shi sosai, Adam a zahirin gaskiya ni mutumen banza ne wanda ba wanda zai so ya kasance ahalin shi, Adam kawai ka tafi ka barni naci gaba da kasancewa ni kad'ai, ni na cancanci irin wannan mummunan hukuncin ko ma fiye da haka. Wannan shi ne abin daya dace da ni to kawai ka tafi."

"A'a Yaya ni zanci gaba da kasancewa a nan tare da kai, sannan kuma ina farin ciki sosai tare da alfaharin kasancewar ka Yayana. Yaya a rayuwa ko wane mutun yana aikata kuskure, amma mafi alkhairin cikin su shi ne wanda zai gane cewar yayi kuskure sannan ya tuba, Yaya har yanzu k'ofar tuba a bud'e take to zaka iya gyara komai, abin da yafi komai dad'i shi ne ita Mama ta yafe maka sannan kuma ta sanya maka albarka. Haka kuma nima sam bana fishi da kai to na tabbata *Maman Adeel* ita ma zata fahimce ka, sannan kuma zata yafe ma ko dan sabo da yaronku, hakama dai *Adeel* shi ma ba zai jima sosai yana fishi da kai ba. To na tabbata duka wannan k'uncin namu zai kau rayuwa zata k'ara bamu damar da zamu yi farin ciki sosai, sannan kuma daga k'arshe ahalinmu ya cika wannan shi ne abin da yafi komai dad'i, to ka dena k'unci sabo da hakan zai k'ara cutar da lafiyar ka, wanda ni kuma sam ba zanso hakan ba sabo da ina san ka samu lafiya cikin sauri." "Adam kai sam ba zaka tab'a ganewa ba, sabo da ni d'in nan na aikata wa Aisha mummunan zunubi, wanda ba zata iya yafemin ba na har abada kamar dai yanda ta fad'a."

"Yaya har yanzu ita ďin uwar ďanka ce kuma tana san duk abin da yaronta yake so, to na tabbata zata yafe ma idan har *Adeel* ya shiga cikin lamarin." "Adam abin sam ba shi da sauk'i kamar yanda kake tunani, amma zansa ka fahimci gaskiyar wani lokaci to ina fatan kai ma zaka yafemin dan Allah." "Ban tab'a d'aukan ka a matsayin mai laifi ba, to ta ya kuma zanyi fishi da kai a'a ba zan tab'a aikata hakan ba, bana fishi da kai Yayana to kai kuma fa shin har yanzu kana tare da tsanata a zuciyarka.?" Yayi shiru kad'an sannan ya amsa shi. "A'a k'anina bana yi ka yarda da ni ina qaunarka sosai." "Yaya wai da gaske kake.?" "Eh k'anina gaskiyar nake fad'a." Cike da d'auki ya tashi daga inda yake ya tafi kusa da shi ya zauna kusa sosai, sai wani kallonsa yake shi ma haka kallonsa yake sun jima a haka, sannan daga bisani suka yi hugging juna farin cikin su ya k'aru sosai. To zan iya cewa zuwa yanzu komai ya wuce tsakanin Prof da Papa.

Sunyi nasaran isa garin Jigawa lafiya *Amna* ta shiga yi musu sannu da zuwa, kasancewar ita kad'ai ce a parlour bayan sun zauna ta tafi ta kawo musu ruwa da juice mai sanyi, ta koma ta zauna tare da gaishesu cikin ladabi da biyayya, bayan sun qarasa g *Adeel* yaci gaba da magana. *"Amna* ina fatan ba ke kad'ai ba ce Mama da Abba suna nan.?" "Eh suna ciki Maman twin's ce bata cikin kyakkyawan yanayi, ka dai riga da ka san komai a irin wannan ranar ce ta rasa twin's, shi yasa yanayin ta na yau yafi ko wane k'unci da muni sosai. Kamar dai kullum muna tare da kewar twin's sosai, bara na shiga ciki na sanar da Abban twin's zuwan ku, amma sai kunyi hak'uri da yanayin sa balantana kuma Mama." "Karki damu *Amna* zamu kula da wannan insha Allah." Ta jinjina masa ka tana wani gajeran murmushi sannan ta tashi ta nufi d'akin Mama, sun bita da kallo cike da jin mamakin abin data fad'a, ba jimawa sosai sai gata ta dawo tare dasu Mama. Abba ya shiga yi musu sannu da zuwa bayan sun gaisa, *Adeel* ya shiga gabatar dasu Mum da kuma *Adyan* a matsayin Aboki, kasancewar sun ta'ba had'uwa da *Adnan* bayan ya k'arasa *Adnan* yaci gaba da magana.

"Mama kamar dai yanda na fad'a muku a wancan lokacin, na cewar zan sake had'aku da twin's to nayi nasara, Abba har yanzu twin's suna raye kuma cikin kyakkyawar rayuwa, na tabbata zaku yi matuqar farin ciki da ganin su sosai." Cikin hanzari har suna had'a baki suke furta masa kalmar suna ina. "Mama Abba *Amna* a yanzu haka twin's suna tare daku." Cike da jin mamakin abin daya fad'a take magana. *"Adnan* ni sam na gagara fahimtar abin da kake fad'a, dan Allah ka fad'a min ina twin's suke kuma ta ya zan had'u da yarana.?" "Mama yanzu haka da yaronki kike magana ga kuma d'ayan yaronki a nan." Ya nuna *Adyan* wani irin kallo suke yi musu mai cike da jin mamakin su sosai. *"Adnan* wai gaskiyar kake fad'a kai da *Adyan* kune twin's yarana.?" "Eh Mama ni gaskiyar nake fad'a to zaki iya yarda da ni." *"Adnan* to amma mai ya saka a wancan lokacin baka sanar damu gaskiyar ba.?" "Mama sabo da ban samu Aboki bane amma da ni na gano gaskiyar shi ne muka zo gareku, ku yafemin da ban iya sanar daku gaskiyar ba a wancan lokacin, ni kawai na zab'i dana zo nan tare da d'an uwa ta yanda zaku fi farin ciki sosai."

"Karka ba da hak'uri ďana sabo da baka aikata wani zunubi ba, abu mai muhimmanci shi ne har yanzu ku biyun kuna raye kuma cikin kyakkyawar rayuwa. To wannan ma kawai ya isa yanzu kuzo nan ku rungumi iyayenku." Sun tashi sun nufi inda suke cike da d'auki su Abba sunyi hugging d'in su, sai wani sunbatarsu suke sun jima sosai a haka, sannan daga bisani suka sake juna su Umma sai wani kallonsu suke suna murmushi. "Twin's a zahirin gaskiya ba zan iya sanar daku girman farin cikin da muke ciki ba, tin bayan da muka rasa ku bamu k'ara samun wani farin ciki ba. Amma yanzu muna farin ciki sosai godiya ga Allah wanda ya k'ara bamu damar kasancewa tare, Alhamdulallah! Alhamdulallah!! Alhamdulallah!!!." Magana yake cikin kyakkyawan yanayi yayin da farin ciki yake ta shigarsu sosai. Bayan wani gajeran lokaci *Amna* taci gaba da magana. *"Yaya Adnan Yaya Adyan* duk tsawon rayuwata na rayu da burin had'uwa daku, duk da cewar bani da sani daku amma kuma na rayu da soyayyar ku, ko yaushe buri na shi ne ahalinmu ya k'ara cika musamman idan su Mama suna cikin k'unci sosai. *Yaya Adnan* tin a wancan ranar da kazo nan ka kuma kira ni da qanwarka, to tin a wannan ranar ni na fara jin wani irin a tare da kai, naso a ce tin a wancan ranar ka sanar da ni gaskiyar amma ko yanzu ina farin ciki sosai. Sannun ku da dawowa gida muna farin ciki sosai da zuwan ku."

Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi abin birgewa, suma murmushi suke sosai mai had'e da dariya. "Kiyi hak'uri qanwata da ban iya sanar dake gaskiyar ba, a wancan lokacin kawai ina san nazo nan tare da d'ayan Yayanki. To fatan hakan bai saka ki kai fishi da Yayanki ba.?" "A'a Yayana sam ba wani abu makamancin wannan, sannan kuma abin farin cikin shi ne yanzu dukanmu muna tare da juna. Sannan kuma dukanku kuna cikin kyakkyawan yanayi to wannan yafi komai ina qaunarku sosai Yayana."

"Na gode sosai qanwata." Cike da farin ciki tayi hugging d'in dukansu biyun, bayan sun sake juna *Adnan* yaci gaba da magana." "Qanwata dan Allah ki bamu guri zamu yi magana dasu Abba." Ta amsa shi da to ta tashi ta fita zuwa wani guri daban, bayan tafiyar ta *Adnan* ya mai da kallonsa gasu Mama yayi shiru na jim kad'an sannan ya fara magana. "Mama Abba da akwai abin daya kamata na sanar daku." "Rabin raina ka sanar damu koma miye zamu saurare ka.?" Ya jinjina masu ka a lamar to sun samu shiru na wani lokaci, ta daga bisani ya shiga sanar dasu komai a game dasu sam ba abin daya b'oye musu, bayan ya sanar dasu a salin gaskiyar ya kuma ci gaba da magana. "Abba Mama dan Allah bama san wannan sirrin ya fita, munyi matuqar yarda daku sosai wanda wannan dalilin ne yasa muka sanar daku duka gaskiyar. Ku iyaye na gari ne a garemu to shi yasa ba zamu iya b'oye muku gaskiyar ba, to fatan zaku fahimce mu sannan kuma zaku amince da buqatar mu dan Allah.?"

Wani irin kallo suke yi masa mai cike da jin mamakin abin da yake fad'a, cike da k'unci bak'in ciki b'acin rai tare da tarin damuwa take magana. "Shikenan ďana zamu yi kamar yanda ka buqata daga garemu, abin farin cikin shi ne har yanzu muna tare sannan kuma kun amince damu a matsayin iyayenku. To wannan kawai ya isa haka kuma zamu yi komai domin farin cikin yaranmu, mu kawai burin mu shi ne ku ci gaba da kasancewa matsayin 'ya'yanmu na har abada." Magana take cikin wani irin yanayi wanda ban san ta yanda zan iya sanar daku shi ba. Ba kuka take ba amma kuma idanuwanta kwalla suke zubar wa, mai tsananin zafi da k'una sosai zamu iya kiran abin da kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo, lokaci ďaya kuma *Adyan da Adnan* sun shiga share mata kwalla cike da d'auki tayi hugging d'in su tana sunbatarsu, sun jima sosai a haka sannan daga bisani suka sake juna cikin tausasa murya *Adyan* yake magana.

"Mama har yanzu mu yaranki ne sannan kuma na har abada, to domin muci gaba da kasancewa a tare na har abada to akwai abin da zamu yi." "D'ana fad'a min ta ya hakan zata yuwu.?" "Mama hakan kawai zai yu ne idan kun amince zaku tafi tare damu." Kafin ta amsa shi *Adnan* yayi mata rigagi. "Eh Mama eh Abba dan Allah ku amince da hakan please naru e ku dan Allah." Mama ta kai kallonta ga fuskar Abba kafin ta furta komai yayi mata rigagi. "Shikenan Maman twin's zamu yi hakan ta yanda zamu samu damar kasancewa tare da yaranmu ahalinmu ya k'ara cika." "Na gode sosai Abban twin's." "Hakan yayi matuqar yin kyau sosai daga bisani dai ahalinmu zai k'ara cika, Mum Mama da kuma Abba zasu kasance a guri ďaya ta yanda ko yaushe zamu kasance a tare da juna."

Magana yake cike da d'auki farin ciki da murna sosai, dukansu suna farin ciki sosai bayan sun k'ara wannan zancan, *Adnan da Adyan* sun tashi sun nufi gurin *Amna* sun same ta zaune tana danna waya, ga a lama charting take sun tafi inda take sun zauna cike da d'aukin ganin su take magana. "Yayuna Sannunku da shigowa." "Yauwa qanwata kina zaune a nan? Ai kuwa da akwai abin daya kamata muyi magana a kai yanzu." *Adyan* ne yake magana yayin da *Adnan* ya rufe su da ido yana murmushi. "Yayana ka fad'a min koma miye.?" "Am qanwata abin shi ne zaki b'oye wannan sirrin na cewar mu 'yan uwan juna ne, sabo da fitar da wannan sirrin zai iya cutar da iyayenmu ina nufin iyayen rik'onmu. Sun kasance iyaye na gari a garemu sannan kuma basu tab'a yunk'urin cutar damu ba, ko yaushe suna nuna mana qauna da soyayya tare da cikakkiyar kulawa sosai, sun bamu duka soyayyar su shi yasa ba zamu iya cutar dasu ta wannan hanyar ba, qanwata ke ma zaki fahimci hakan a lokacin da kika had'u da dukansu, to ina fatan kin fahimci abin da nake nufi.?"

"Eh Yayana na fahimta sannan kuma ina tare da hukuncin ku, nayi alkawari ba wanda zai ji wannan insha Allah to zaku iya yarda da ni." Magana take cikin kyakkyawan yanayi yayin da fuskar ta take fitar da wani lallausan murmushi sosai. Suma abin da suke yi kenan bayan wani lokaci suka tashi suka fita zuwa babban parlour, ba jimawa dukansu suka tashi suka nufi tebur domin suci abinci. Bayan sun k'arasa sunci gaba da fira misalin k'arfe 03:00pm su Mum suka kama hanyar tafiya gida, bayan kwana biyu su *Adnan* suka dawo suka tafi dasu Abba, wanda kuma a nan gidan su Mum suka zauna da part ďin su wani yammaci................................






*BY. B. U. A. CE. Wannan al'qalamina ne.*
[3/21, 6:37 AM] Bil-Fauzee U-Adyan: 👑👑👑👑👑👑
👑👑👑👑👑
👑👑👑👑
👑👑👑
👑👑

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login