Showing 1 words to 3000 words out of 170049 words

Chapter 1 - SARKI SAMEER BOOK 3 by yaya Azeema.txt

29 Nov 2025

7195

[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*BARKAN MU DA SHIGOWA SARKI SAMEER KASHI NA UKU, WANDA NAKE FATAN ALLAH YABANI IKON KAMMALA SHI LAFIYA KUMA NAKE FATAN YAKASANCE NA ƘARSHE,*  

*_Typing........✍️✍️_*

_____Bata ƙarasa ba yakai mata wata uwar shaƙa awuya yana ta fitar da numfashi idonsa sun kaɗa sunyi ja yama kasa magana ya shaƙeta kawai, ita kuma tana ta faman kakari zatayi amai tana ƙoƙarin ƙwatar kanta, amma ina ƙarfin su ba ɗaya ba, bai sake taba saida yaga ta daina numfashi sannan yasake ta, tafi luuuu ta faɗi a ƙasa mataciyyyya........✍️✍️

___cike da ɓacin rai zuciyar sa kamar zata fito waje ya tsugunna agaban ta tare da kara hannun sa akan hancinta yaji bata numfashi miƙewa yayi tsaye yana yarfa hannun yana neman mafita can wata dabara ta faɗo masa tunkan mutane su riskesa aciki gwara yayi takansa ta yanda babu wanda zai tuhumesa, da sauri ya cicciɓeta ya ɗorata aka faɗarsa ya nufi bedroom ɗinta akan gado ya shinfiɗeta sannan ya fito daga ɗakin cikin hanzarin har yana tuntuɓe wajen tafiya, cak yaja ya tsaya tare da daskarewa agurin jinsa da ganin sa da numfashin sa suka fara yi masa barazanar ɗaukewa subar gangar jikinsa, ba komai bane ya haddasa masa wannan ɗaukewar ta wucin gadi face tozali da yayi da Meer tsaye da waya a hannun sa alamar video yake ɗaukar sa,

A hankali Meer ya shiga takawa zuwa inda ya ƙame agun, Saida yaje ɗab dashi sannan ya tsaya agabansa yana kallon ƙwayar idon sa da suka canza kala zuwa na tashin hankali,

Videon ya kunna masa tare da nuna masa shi, videon tunda ga loƙacin da matar ta fito tana tafa hannun ne har loƙacin datake faɗa masa maganganun da loƙacin da ya tashi ya shaƙeta harta dena numfashi sannan ya sake ta ta faɗi a ƙasa, tundaga farko dai har zuwa ƙarshe, babu abun da bai fito ba daga wayar,

Yana kaiwa ƙarshe Meer ya kashe wayar tare da sakata a aljihu yana binsa da kallo tundaga sama har ƙasa,Saida yagana ƙare masa kallo sannan yace finally ko ba ace komai ba duk wanda yaga videon zai samu amsar sa dan haka yanzu sai ka jira hukunci biyu baya ga wancen da ake zarginka da shi yanzu kuma ka ƙara da kisan kai gaskiya ka burgeni da ka iya aikata haka kaiɗin ka kasance me fuska biyu kana nuna kai babu abun da kasani kai na Allah ashe kaine ƙungurumin munafikin to maza ina sauraron ka faɗa min ta yanda akai kuka koreta daga gidan kuma ka gaya min waye da waye yake da hannu aciki kafaɗa min tun muna shaida juna kafin inyi maka yaren da zakagane kuma magana ta bazu taje kunnen kowa, kuma da kanka nake son kaje ka faɗawa mutane kisan kan da kayi da hannun ka ka kashe matar ka,

Buɗar bakin Waziri sai kawai ya kwashe da dariya kamar zararre haka yadinga tiƙar dariyar sa saida yayi me isarsa sai kuma yaƙara haɗe rai tare da canza fuska, ta koma ba wani alamun tsoro atattare dashi ya shiga zagaya Meer yana karkaɗa kai sannan ya dawo gabansa yace "Wow! wow!! wow!! lalle ɗan ƙaramin zaki ya girma yaro ƙwazon ka ya matuƙar burgeni saidai fa ka makaro kai atunanin ka wannan abun da ka ɗauka kasamu hujja akaina kenan hhhhhh abun ma abun dariya kasani tun loƙacin da ka ajiye wayar na ganka kai ka isa kamin wayo masu iya magana sukan ce abun da babba ya hango yaro ko ya taka dutsen dala bazai hango ba, kaina ba irin naka bane nayi wasa da ƙwaƙwalwarkane ta hanyar ƙara toshe maka lissafi,

Dakatawa yayi da maganar sai kuma ya ƙara fashewa da dariya, yace "nafi ƙarfin kakanka bare kuma uban ka hartakai ga kai ƙaramin yen yen kai harka isa kasa kani a fargaba baka isa naji tsoron kaba, yaushe kazo duniyar yaushe aka haifeka bari ingaya maka tun ranar da kukazo kallo ɗaya nayi maka nagama karantar ka kuma nasan dole zaka zo gurina, kaɗanyi ƙoƙari wajen ganoni da wuri harka fara tuhuma ta to tuhumar ka gaskiya ce ina da hannu tsudum tsudum acikin lamarin nan duk da nima ina da uban gidana, labarin da nabaka duk ƙaryane sannan hasashen ka yayi daidai, fulani bata da masaniya akai ƙwarai kuwa da ita muke aiki wajen aiwatar da koman mu ni da kaina naje nasa akayi duk abun da akayi ta amince aka saka mata cikin ƙarya da masaniyar mu ɗanta da ta ɗauko yazo gidan nan ita kanta bata sani ba, kai ƙarewa ma tana haihuwa mu muka juyar mata da mahaifa ta yanda baza ta taɓa haihuwa ba ita kuma munyi iya ƙoƙarin mahaifar tata taƙi juyuwa shiyasa muka shirya muka fitar da ita daga cikin gidan daga ita har ƴaƴan nata, tundaga kan ubanka har kan ƙanin ubanka, saboda ba maso ɗaya daga cikin jinin Muhammad yayi mulki agidan nan munfiso masarautar tazama mara gata da galihu ai ta mugunta acikin ta shiyasa muka ɗora wani daban daga waje wannan duk shirin mune, bana jin tsoron ka shiyasa nagaya maka duk wannan batun kuma ko ka faɗawa wasu babu me yarda dakai ko sauraron kama baza ayi ba indai ba ƙwaƙwarar hujja zaka samu ba ta fatar bakidai baka isa anyar da dakai ba, hmmm yaro man kaza baka san waye niba shiyasa kayi gigin shigowa gonata shawara da zan baka shine kayi gaggawar zare hannuka akan binciken nan dakake shirin yi abun da zaifi maka sauƙi ma shine da zaku tattara inaku inaku kubar masarautar nan gaba ɗayan ku hakan sai yafi muku sauƙi dan bazaku taɓa yin nasara akan mu ba kuma mulki bazai taɓa dawo wa hannun kuba na rantse da Allah jinin Muhammad bazai taɓa mulkar garin nan ba, ɗaya bayan ɗaya sai mun ƙara ɓatar daku ɓatan da har abada kuma bazaku sake dawowa ba da ƙafafun ku zaku bar cikin gidan nan gaba ɗayan ku,

Tunda yafara magana Meer yake binsa da kallo ko kaɗan akalaman sa babu wanda ya tsoratar dashi saima zugasa da yayi zai ƙara sake datse damtse wajen yin nasara akansu shi a tunanin sa bazai kamu ba shiyasa ya zauna ta zube masa abun dake cikin sa wannan kwa babban ganganci ne sai ya nuna masa zamani ya canza duk ƙarfin kansa zai nuna masa nasa ya ninka nasa sau ɗari shima akaran kansa bazai tona masa asiri yanzu ba sai yafara sanya masa tsoran sa sai ya haddasa masa tsoro da furgici sai yasa daidai da second ɗata tunanin sa yake cike da tashin hankali daga yau yagama farin ciki arayuwar sa ta ruwan sanyi zai ladaftar dashi yabashi kashi,

Gyara tsayiwar sa yayi sannan shima ya ɗora da cewa, lalle ne tsohon banza kayi ƙoƙari naji duka baya nanka kamar yanda kace saida ƙwaƙwarar hujja za akama ka to ina mai tabbatar maka nan bada jimawa ba zan samo ta kuma wannan videon da na ɗauka dole shima hujja ce taya zaka kare kanka dashi idan mutane suka gani,

Waziri yayi wani irin murmushi irin yaro kenan kana wasa dani sannan shima ya gyara tsayiyuwa yace "wannan videon da kanka zaka gogesa domin baida wani amfani agurin ka bare kuma gurin wasu wannan abun da ka ɗauka, ka ɗauka kamar film kagani domin shirine bawai gaskiya ba kaɗan na nuna maka daga cikin juyar da kai dazanyi ta hanyoyi da dama, Kai atunanin ka zan kashe matata da kaina wannan ai ganganci ne to wannan kaɗan kagani gaba ɗayan mu kanmu a haɗe yake aduk loƙacin da abu yafaru da ɗaya atake wani zai kawo masa taimako ta wata hanyar daban, da bamuyi haka ba yanda ka ajiye mana waya anan da zamu ɗora da wata maganar ne daban ta yanda zaka samu hujja amma sai muka ankare da shirin da kayi sai mukayi maka wasan kwaikwayo, Ni matata bata mutu ba kuma ba shaƙar mutuwa nayi mata ba, shiru tayi sannan ya ɗan ɗaga murya yace "Indota"

Yana faɗa kuwa saiga matar da yakai ɗaki ta fito tana sakin wani shu'umin murmushi tare da taku ɗaiɗai har ta ƙaraso gurin Meer tace yaro ya kaga shirin namu Allah sarki har kaban tausayi aradun Allah, nima dai shawara ta agareka shine ka cire hannun ka aciki in bahaka ba zaka saka kanka cikin tashin hankali a kowace rana sai munsan yaka cikin tashin hankali, tagget ɗin na farko akan zamu fara da mahaifiyar ka sai kuma mahaifinka sai kuma mtsww kodan ma bashi da amfani gaya maka sauran kawaidai sai ka kasance cikin shiri da basu kariya idan zaka iya duk wanda yaci tuwo damu miya ya shamu, zamu barka cikin hayyacin ka tayanda zamu fi jin daɗin tarwatsa maka ƙwaƙwalwar ka, tayanda ko ance ga mulki ka hau da bakinka zaka ce bakaso dan nasan idan muka tsaya wasa kaine sarki saidai bazamu taɓa barin hakan ta faru ba, wannan alƙawarin ƙungiya ne, kamar yanda ya faɗa maka sai mun ƙara tarwatsaku ɗaya bayan ɗaya sai munsa kunyi nadamar dawowa sai kungwammace dama kun ƙaraci rayuwar ku a inda kuke sai kunji dama baku san su waye muba, sanin mu masifa ne, loƙacin da take wannan maganar waziri kuma yabar wajen ya shige ɗaki bai daɗe ba kuma ya fito, hannu wansa abaya yana jinjina kai,

Meer da taƙaici da mamakin kalaman ta suka isheshi tana cikin maganar cike da ɓacin rai jijiyoyin wuyan sa har sunyi raɗau raɗau dasu idanun sa sunfara canza kala, tana cikin maganar baisan loƙacin da ta kwashe ta da wani irin rikitaccen mari ba tare da kai mata shaƙa awuyan ta ya haɗata da jikin bango, jikin sa duk sai rawa yake tunda yaji sun ambatar masa iyaye hankalin sa yafara gushewa idanun sa suna neman su ƙafe saboda wani tsabar taƙaici da baƙin ciki da yake jin suna taso masa daga ƙasan zuciyar sa ji yake idan baikashe taba agunnan hankalin sa bazai taɓa kwantawa ba, yana cikin shaƙar tata, Waziri yafara ƙoƙarin jansa ta baya amma ko gezau baiyi ba, wani sirinji ya zaro daga cikin aljihun sa taf yake da ruwa aciki ko ruwan meye Allah masani, Meer bai ankara dashi ba sai jin saukar allaura yayi agefen wuyan sa take kansa ya fara juya masa tun yaba gani har ganinsa ya ɗauke, a hankali ya shiga sakar mata wuyan saboda jikin sama gaba ɗaya ya saki, suna kallon sa har yafara tafiya zai faɗi saima matsawa da Waziri yayi dan kar ya faɗo kansa a haka har yakai ga ƙasa ya faɗi agun,

Numfashi ta shiga saukewa na wahala dan ba ƙaramin shaƙa yayi mata ba, ruwa Waziri ya ɗauko mata ya bata ta shiga sha da sauri da sauri saida ta shanye suka sannan ta jefar da robar tana ɗan shafa wuyan ta, Ta kalli Waziri tace Allah kuwa yaron nan baida hankali ƙarfi kamar na doki da bakayi sauri ba ai sai ya kashe ni kaji kuwa zafin da naji dan har na fara jin ƙamshin lahira,

Ɗan dariya Waziri yayi yace ke ai daga ganin zubin shi kinsan bazaiyi imani ba idan ya riƙe mutum yanzu dai ai munyi maganin ɗan iska, yau yaga samu yaga rashi, ta kalle sa cike da rashin fahimtar magananr sa tace "bangane ba yaga nema yaga rashi,

Jinjina mata kai yayi yace"ƙwarai kuwa yaga samu yaga rashi dan kwa yana tashi babu abun da zai iya tunawa mugama gaya masa komai kuma mungoge masa sanin wannan allurar da nayi masa ai ta mantau ce ta idan ya tashi sai tambayi abun da ya kawosa nan ke ina taƙaice miki ma saidai mukai shi makwancin sa dan bazai iya komawa da ƙafar saba,

Ɗan zaro ido tayi tace kana nufin zaiyi losing memory ɗinsa ne gaba ɗaya,

"A'a ba haka nake nufi ba ina nufin ba kawaidai zai manta abun awa biyu da yafaru dashi na baya, zai cigaba da harkar gabansa zaima manta da abun da yakawo sa gaba ɗaya bare kuma ya tuna abun da muka gaya masa ko ɗaya bazai tuna ba.........✍️✍️


*Plsss ayi malej da wannan wallahi yau bamu samu wuta ba,*
[15/11, 10:50 pm] #yaya Azeema#: 💅SARKI  SAMEER💅
                      (DA ZAFI ZAFI)
                             By
                  ❤️xeemat...love❤️
   
              *BOOK* 3️⃣

*Ga mai buƙatar littafin sarki Sameer tundaga book 1 har zuwa book 3 zai biya 400 kacal akwai 1&2 completed, zukuturo da kuɗinku ta wannan asusun 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank, ko kuma wannan 0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida jaiz bank, sai kuturo da shaidar biyan ta wannan number ɗin 08124226526*

           *_Typing........✍️✍️_*

_____A'a ba haka nake nufi ba ina nufin ba kawaidai zai manta abun awa biyu da yafaru dashi na baya, zai cigaba da harkar gabansa zaima manta da abun da yakawo sa gaba ɗaya bare kuma ya tuna abun da muka gaya masa ko ɗaya bazai tuna ba.........,

Wata iriyar shu'umar dariya ta saki harda tafawa tace "shiyasa nake ƙara sonka na wajena aikin ka na kyau, yanzu meye plan ɗinmu na gaba, dan naga alamar yaron nan da zafin sa yake bazai raga mana ba dole mu fara kawar dashi, kar muje muna kallon ruwa ƙwaɗo yayi mana ƙafa,

Kallon ta yayi yace kar ki damu dashi a rana ɗaya zanyi maganin sa in yasan wata ai baisan wata ba, daga yanzu duk wani motsin mu zai kasance akan idon mu zan zuba masa idanuwa akansa duk inda zai shiga za a kawo min rahoton sa daga zarar naga zaiyi min hauka zan nuna masa na fisa iyawa, kedai kibar komai a hannu na dan wannan ba wani babban abu bane da zaifi ƙarfin na kar kisanar da kowa a ƙungiya, bare labari ya riske shi nasan zaifi ɗauka da zafi magana har takai ƙarshe, a zo afara tsari ba nutsuwa, gwara abi komai a hankali asannu komai zai dawo normal labarin zai ƙara shuɗewa kamar da za a manta dasu kamar yanda aka yi abaya,

Ah daman ni wazan gayawa, ai yaron nan fa yaban tsoro wallahi bakaji shaƙar da yayi min ba nifa ina tunanin ma anya ba ya tare da aljanu masu ƙarfi ajikin sa,

Waziri ya ɗanyi murmushi irin nasu na manya yace "ke bakiga zubin saba daman ai kinsan ya riƙe mutum bazai ji da daɗi ba, yanzu dai duk ba wannan ba ɗauko min wayata inkira Ab........, Shiru yayi da maganar yana kallon wajen ƙofa sannan ya maida kallon sa ga matar tasa yace "kamar motsin mutum nake ji fa yayi maganar yana kallon ta da kyau,

Ɗan maƙale kafaɗa tayi tace anya kuwa gaskiya bana tunanin akwai wani ni banji motsin komai ba amma dai bari induba ingani tafaɗa tana ƙarasa miƙewa tsaye,

Tana tashi sai wayar sa ta ɗauki ruru hakan yasa ta dakata da niyar zuwa wajen ƙofar ta nufi inda wayar sa take, tana ɗaukowa tace kaji ɗan halak ana maganar sa saiga kiransa, ƙarasawa tayi wajen sa tare da miƙa masa wayar, Ya amsa yana ƙara faɗaɗa murmushin fuskar sa yana karɓar wayar sai sukaji ƙarar waya ƙes kamar an ɗauki hoto da sauri ya ƙara maida kallon sa ga bakin ƙofar, Sai kuma yaƙara kallon ta kamar ɗazu yace "kinji abun da naji yanzu taɓe baki tayi tace haba kaidai wallahi kana neman kazama ma tsoraci ba wani abu da naji kasan ance marar gaskiya ko a ruwa gumi yake shiyasa abubuwa suka fara yi maka gizau amma dai bari dai in duba maka kaga zahir saika daina tsorata haba sai kace bakaiba kana neman ka canza da tsoro,

Ɗan murmushi yayi tare da amsa wayar yana jinjina kai dan ya yarda da maganar ta ta,

Ita kuma ta nufi bakin ƙofar tana ƙara tsokanar sa da matsora ci tana dariya.......,

_______Cikin zaro ido cike da tsoro da fargaba tayi baya zata faɗi  tana shirin fashewa da kuka, Azeema dake gefen ta tayi saurin toshe mata baki tare da janta baya da sauri suka bar gurin ƙofar gudun kar asirin su ya tonu,

suna fitowa waje Ameesaha ta fashe da kuka ta rungume Azeema, Azeema da itama jurewa kawai take tayi saurin  kamo hannun ta suka bar gurin gaba ɗaya basu nufi inda mutane suke ba can bayan wani waje suka nufa gurin da ba mutane a wajen,

Saida suka je sannan Azeema ta zaunar da ita akan wani ɗan tudu ta dafa kafaɗar ta tace besty plsss dan Allah kiyi shiru ki nutsu miyi magana, kada wannan maganar ta sa kifita daga cikin hayya cin yakamata ki aro jarumta kisaka wa kanki bafa mutuwa yayi ba,

Cikin kuka Ameesaha tace "besty bazan iyaba waɗannan mutanen sunfi ƙarfi na kinfa ji me sukace sai sun tarwatsa rayuwar mu shin me muka tsare musu gwanda ma kawai inje ingaya musu mubar gidan nan nidaman hankalina bai kwanta ba acikin gidanan idan bamu barmusu gidan ba kashe mu zasuyi mumu duka gashi yanzu sun fara takan dadda ta wataƙil ma yanzu sun kashe ta tana faɗar haka taƙara fashe wa da kuka tana faɗawa kanta,

Riƙeta Azeema tayi tace "kidaina faɗar haka in sha Allah ma dadda bata mutu ba tana nan da ranta zata dawo ku cigaba da rayuwa kuma acikin gidan nan kisa Allah aranki babu abun da suka isa suyi muku wanda Allah bai muku ba, abun da nakeso dake shine kiyi shiru, nifa banma ga abun tada hankali sosai ba tunda idan suna ganin shi baida shaida mu ai muna da ita kama ta yayi ma ki godewa Allah da Allah ya kawo mu akan loƙaci kisan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login