Showing 144001 words to 147000 words out of 150281 words
Bilal
"Ba kwanaki ba, ba satika ba, Bilal ba wata daya ba. Shekaru, shekaru fa... Shekaru zaka dora akan kalmar hakuri?"
Bayan hannun shi Bilal ya saka yana murza idanuwan shi kafin ya dan daga kafadun shi cikin alamar helplessness, bai san me zai fada ba, baisan ya zaice ba. Abu daya ya sani, har cikin motar Lagos ya shiga, har zama yayi ya kasa, bai zaice ga dalili guda daya ba, amman nisan awannin da suke tsakanin Kano da Lagos ne sukayi mishi yawa, nisa yake so yayi da gida, nisa yake so yayi da kowa saboda laifn shi da yake ji yafi karfin yafuwa. Nisa yaso yayi musu ko zai rage musu zafin laifin da yayi, amman ba nisa mai yawan wannan ba.
Yana bukatar ya bude idanuwan shi a duk lokacin da bacci ya dauke shi da sanin cewa suna kusa da shi duk da yayi musu nisa, ko kudin shi bai tsaya an mayar mishi ba, tunda zasu iya siyarwa da wani kujerar, lokacin ana ta saka kaya, jakar shi kawai ya dauka, daman dayar tana goye a bayan shi. Hotel ya kama, wayar shi kasheta yayi, satin shi biyu a hotel din batare daya fito ko ina ba, jinya yayi ba karama ba ta rashin su, ta nisa da gida, ta tunanin halin da kowa zai shiga. Ranar daya fita kuwa sabon sim ya siya ya saka a wayar shi ya adana wancen.
Yasan kudi zasu kare mishi, dole yana bukatar neman wata hanya ta samun kudi, sana'ar karfi ce karshen abinda zaiyi, ba zai karya ba in ba dole ta kama mishi ba ba zai iya ba. Bai saba wahala ba, baima san wani abu wahala ba tun tashin shi. Su Abbu sun tabbatar da hakan, unguwannin da ko da wasa bai tabajin su Ayya na kaiwa ziyara ba nan ya fara nufa yana shiga duk wata private school da yaci karo da ita, bai boye musu cewa shi din bashi da takardu ba, amman yayi karatu har zuwa shekarar shi ta karshe, ya dai ce musu matsala ce ta saka shi ajiyewa dole, fiye da makarantu biyar sun so rike shi, musamman bayan sunyi mishi gwaji, amman sai suka so yin amfani da wannan damar ta cewa ba shi da takardu wajen biyan shi kudin da basu taka kara sun karya ba, haka yaci gaba da yawo wajen sati daya, kafin ya samu wata makaranta a cikin rijiyar lemo can wajen layin masallacin espa.
Da yake shugaban makarantar musulmi ne, mutum mai matuqar kirki da sanin ya kamata. Har kara ma Bilal din kudi yayi daga baya ganin yana da sani ta bangaren addini, makarantar kuma boko ce hade da islamiyya, sai yake koyarwa a duka bangarorin biyu. Anan cikin rijiyar lemon ya samu karamin gida daki biyu ya kama. Watan daya duba account balance din shi yaje cire kudi yaga sun karu sosai, daga farko ya dauka ko wani yayi kuskuren tura mishi kudi, tunda layin da yake ganin alert yana kasa, amman yakan duba ta email din shi. Hakan yayi, yaga Rayyan ne
"Hamma, nauyin zai mun yawa....dan Allah Hamma"
Shine kalaman da ya dinga furtawa yana maimaitawa, yayi nisa da sune dan su sami sauki, ba dan ya kara dora musu wata wahala ba. Sai dai ba zaiyi karya ba, kudin suna taimaka mishi sosai da sosai. Ba zaice ya nemi wani abu ya rasa ba, iya cikin shi da abinda ba za'a rasa ba, kudin ya ishe shi har ma yayi mishi yawa. Watanni shidda ya dauka cir kafin mafarkan kowa na gidan ya fara damun shi, rana daya ya wayi gari yaji kewar su ta danne mishi kirji, numfashin kirki ma baya iyawa, shisa ya dauki sim din shi ya saka a wayar, hankalin shi rabi da rabine ko da yaje wajen aiki, ba zai manta uzurin rashin lafiya daya bayar ba ya kama hanyar gida, a hanya ya tsaya ya siyi kati ya saka a layin
"Watakila ko dan babu kudi shisa sako ko daya bai shigo ba"
Ya fadi a zuciyar shi, har wajen sha biyun dare yana kallon wayar
"Kirana kawai zakuyi, zan dawo gida"
Tunanin da yakeyi kenan a cikin kan shi har wayewar gari inda ya zare layin daga wayar shi, daga lokacin ne kuma ya sami karamar waya ya siya inda ya saka layin a ciki. Daga ranar kuma ya fara kunna wayar daga safiya zuwa karfe biyu na rana, wani lokacin ma yana kwana bai kashe ba, banda yan MTN babu wanda yake kiran shi, ko sako yaji ya shigo sai zuciyar shi ta doka, sai dai idan ya duba yaga ko bankin shi ko MTN din ne dai. Fushi sukeyi, ya san fushi sukeyi da shi shisa basu kira ba, laifin shi ya so wankewa da karin wani laifin na tafiya, amman bai taba cire rai ba, yasan zasu kira shi, komin dadewa zasu kira.
Ba zaice ga yanda yayi shekarun nan batare da su a kusa da shi ba, bai san me ya rike nutsuwar shi har haka ba. Yau din ma kamar kowacce ranar karshen mako, zaune yake bayan ya karya yana marking assignment din yara, sai wasu azuzuwan da test ne yayi musu kasancewar an kusan fara jarabawa yaji karamar wayar shi na ruri, karamin tsaki yaja kawai yana cigaba da abinda yake yi saboda yasan MTN ne, su kadai zasu fara kiran shi kamar suna bin shi bashi. Wutar da aka kawo yasa shi daukar babbar wayar shi da ba wani amfanin kirki yakeyi da ita ba, tunda ya koyi rayuwa babu kafar sada zumunta, abinda bai taba tunanin zai iya yakicewa ba.
Sai dai ya iya karfin halin barin su Rayyan ma, ballantana wani whatsapp, hannu ya mika ya dauki karamar wayar ya duba yaga ko akwai sauran caji tunda ya kwana wajen hudu bai sakata a caji ba, latsawa yayi kawai dan sabo yana shiga yaga missed call din da yasaka shi mikewa babu shiri ganin lambar Rayyan da ko a bacci ya ganta zai ganeta. Mukulli kawai ya dauka yana saka takalma a kafafuwan shi, zai iya tuna ya kulle gidan, amman ko mai mashin daya sauke shi a kofar gidan su, hannu kawai ya saka a aljihun shi yana lalubawa ya kuwa samu dari biyu ya mika mishi, zuciyar shi yake ji a tafukan kafafuwan shi a duk takun da yakeyi, shisa yake jin kafafuwan sun mishi wani irin nauyi na ban mamaki.
Basu kara nauyin ba sai da ya hango Rayyan, wannan karin tsallen da zuciyar shi tayi a ko ina na jikin shi yake jin dokawar ta, shi da kan shi bai gane muryar shi ba lokacin daya kira Rayyan din, yanzun ma da suke tsaye ji yake kamar mafarki, kamar bashi bane tsaye a gaban Rayyan da yaga kamar bai canza ba a shekarun nan, yana nan yanda ya san shi, sai dai akwai wata natsuwa da yake gani a fuskae Rayyan da bai taba sanin yana da ita ba haka.
"Me zance Hamma?"
Wannan karin rashin madafar a muryar Bilal ya fito
"Baku kirani ba. Hamma kirana kawai zakuyi kamar yau..."
Da rashin fahimta Rayyan yake kallon shi, saboda baya gane abinda yake fadi, baya ma gane abinda yake ji balle kuma zantukan Bilal din, wayar shi Bilal ya daga duk da baya tunanin Rayyan yana ganin screen din saboda kankantar wayar
"Baku kira ni ba, kai ma baka kira ni ba, ni din mai laifi ne, ban san ya zan nuna fuskata ba baku neme ni ba Hamma"
Dariya Rayyan yayi mai sauti yana kallon Bilal din sosai, duk shekarun nan jira yake yi su kira shi kafin ya dawo, sau nawa yana daga wayar shi ya danna lambar Bilal din yayi ta kallon ta, saboda yasan koya kira a rufe zaiji ta, kiran ba zai mishi amfanin komai ba sai karin daga mishi burin cewa bai rasa Bilal din ba, daga baya ma daina dannawa yayi saboda yasan an siyarwa da wani daban lambar, balle harya gwada kira wani ya dauka ya tabbatar mishi da yanda ba Bilal kawai ya rasa ba har lambar wayar shi ma ta tafi.
"Ta ya zamu fara kiran ka idan duka muna tunanin ka rasu?"
Kallon shi Bilal yayi, saboda maganganun shi sun daki kunnuwan shi da wani yanayi mai wahalar misaltawa
"Motar da ka shiga, babu wanda ya fita a motar, da alama kai ka dai ka fita"
Kai Bilal yake girgizawa Rayyan
"Ta ina zamu kira ka Bilal? Ta ya zaka jira kiran da bamu san kana jira ba? Kiran da banda karfin zuciyar yin shi in sake jin wayarka a kashe..."
Kan dai Bilal yake girgiza mishi
"Na shiga motar da kuke tunani, amman ban zauna ba, na kasa yin nisa mai tsayin wannan... Ban zauna ba Hamma"
Bilal yake fadi cikin tashin hankali, yana jin zuciyar shi kamar zata tsaga kirjin shi ta fito da halin da yake hasaso sun shiga, sanin tafiya yayi daban, amman tunanin ya rasu? Tunanin sun rasa shi gabaki daya, baisan ta inda zai fara hasaso tashin hankalin su ba
"Ayya fa?"
Ya tambaya, kallon "Sai yanzun tunanin ta yazo maka? Sai yanzun kake tunanin halin da ta shiga? Me yasa kafin ka tafi bakayi tunanin ta ba?" Rayyan yake yi wa Bilal din. Kafin ya dora wasu tambayoyin akan harshen shi yana jifan Bilal da su
"Me yasa zaka tafi? Nace ba zan yafe maka ba na sani, amman me yasa zaka tafi? Idan baka duba ni ba, me yasa zaka bar Ayya? Me yasa ka tafi Bilal?"
Ba tambayoyin Rayyan bane suka saka hawayen shi zuba, yanayin yanda yayi mishi sune, muryar shi, yanayin da yake kan fuskar shi da cikin idanuwan shi
"Hamma..."
Kai kawai Rayyan ya girgiza mishi yana juyawa, komai ne yake dawo mishi sabo, duk wani ciwo da yake tunanin lokaci ya dishe mishi zafin shine yake budewa yana dawowa sabo fil, kiran duk da Bilal yake mishi baisa ya juya ba. Amman takun tafiyar Bilal din da yake bin shi a baya jinta yake har cikin zuciyar shi. Kan shi tsaye bangaren Ayya ya wuce, bata ma falon sai Huda da tana ganin shi tace
"Hamma, yanzun naga Nur, nace tare kuka zo tayi banza ta kyaleni, ko kallona fa batayi ba ta wuce tana neman Ayya....har..."
Maganar da ta dauke mata ya tabbatar wa da Rayyan din cewa ta ga Bilal ne da yake bayan shi, da sauri ta karasa inda Rayyan yake ta kama hannun shi tana girgiza shi, idanuwanta yana kan Bilal, so take ya juya yaga abinda take gani, ya tabbatar mata da yana ganin Bilal din ba ita kadai bace take ganin fatalwa a cikin dakin su, tasan tsoro, amman bata san firgici ba sai yau, muryarta a wahalace ta fito
"Hamma... Hamma"
Ta ke fadi tana sake girgiza Rayyan daya kama hannuwan ta duka biyun ganin tana shirin shidewa
"Na gan shi, ki kalle ni Huda, na gan shi... It's okay...bake ka dai kike ganin shi ba"
Rayyan yace yana so ta dauke idanuwan ta daga kan Bilal ta kalle shi, amman kai take girgiza mishi hawayen da yake cikin idanuwan ta yana zubowa
"Ayya! Ayya!!"
Take kira cikin firgici tana kokarin kwacewa daga rikon da Rayyan yayi mata, amman yaki sakin ta saboda yanda jikinta yake bari zata iya samun matsala idan ya sake ta
"Ayya!!!"
Huda ta sake kira tana neman taimako daga wajen Ayya
"Huda!"
Rayyan ya kira, wani irin kuka take tana fitar da numfashi dakyar, lokacin da Ayya ta fito a gigice itama saboda bata taba jin Huda ta kirata cikin yanayin da ta kirata yanzun ba, sam bata kai hankalinta kan Bilal da ganin ta ya saka shi dafa bangon da yake kusa da shi saboda yanda yaji gabaki daya gwiwoyin shi sunyi mishi sanyi
"Ayya"
Ya kira, amman labban shine kawai suka iya motsawa, sam sauti ko daya bai fito ba, Ayya kuwa Huda ta kama daga hannun Rayyan
"Me ya faru? Lafiya? Me ya faru?"
Take tambayar Huda din, tana karasa tambayar hadi da kallon Rayyan daya sauke idanuwan shi daga cikin nata
"Ayya..."
Huda ta kira cikin sabon tashin hankali tana juyawa, yanayin da yasa Ayya kallon inda ta kalla, tana ganin Bilal, runtsa idanuwan tayi tana sake bude su hadi da jin kamar wani ya watsa mata ruwan kankara saboda tsikar jikinta da ta mike gabaki daya, wani irin yanayi ne da babu kalaman da zasu misalta shi, dole Huda zata firgice, ta sha hasaso ganin Bilal, ba'a mafarki ba a ido biyu, amman da gaske ne, girman kusanci ba zai taba hanaka tsorata ba idan har zakaci karo da mutumin da kasan mutuwa ta rabaku, saboda wani irin tsoro ne kamar bargo ya nannade daga kafafuwanta har zuwa kanta kafin ya sami wajen zama a cikin zuciyar ta.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 30, 2021.
34
"Ayya..."
Bilal ya kira yana sa ta raba idanuwanta da inda yake tsaye tana kallon Rayyan daya daga mata kai yana tabbatar mata da yaji kiran, ba kunnuwanta bane kawai suka ji cewa Bilal ba tsaye kawai yake a cikin dakin ba, har magana yakeyi. Hankalinta ta sake mayarwa kan shi tana ganin yanda yake takawa yana karasawa inda take kamar wanda yake koyon tafiya, da duk takun da zaiyi da yanda zuciyarta take kara dokawa a cikin kirjinta da wani irin tsoro, sai dai kamar jira kawai yake ya karasa inda take kafafuwan shi su kasa daukar shi dan anan gabanta ya durkushe. Yayi kuka mai yawa bayan da ya tafi, amman baiji kalar kukan da yake tattarowa daga duk wani lungu na zuciyar shi daya taba yin ciwo ba irin yanzun.
Dan wani irin gunji ya saki mai tsuma zuciya yana rike kafafuwan Ayya da itama taji sunyi mata wani sanyi, Huda ta ture gefe, ba tsugunna tayi ba, zama tayi akan kafafuwan ta kamar mai zaman sallah tana kallon Bilal, ya sha bamban da fatalwin da take gani a fina-finai, jikin su baiyi kalar na shi ba, batajin kuma ana iya jiyo hucin numfashin su, a hankali ta daga hannunta da kafin ta kai shi fuskar Bilal ya kama shi da duka nashi biyun. Ko da fatalwa ne shi na danta ne, Bilal ne. Hannun shi na shine, hannu ne daya saba kama nata tun kafin yakai girman haka.
Duk da yanzun girman bai canza yanayin shi ba, zata gane hannun Bilal a cikin dubban hannaye, saboda zai rike nata hannun kamar yanda ya rike shi yanzun, cike da yarda da kaunar shi da batajin wani da bai san zafin da ba zai iya fahimta.
"Bilal"
Ayya ta kira yana daga mata kai kawai saboda kukan da yake yi, abu na farko da duk wata mahaifiya takeyi a lokacin da take ganin hawayen da na ita bace sanadin zubar su shi Ayya tayi, zame hannun daga cikin na Bilal ta kama shi zuwa jikinta duk kuwa da girman shi, kan shi ya dora a jikinta yana sake sakin wani sabon kukan, kukane na kewar ta, na kewar su gabaki daya, kukane na ban hakuri, kukane na abubuwa da yawa. Ba zaice ga lokacin daya dauka a haka ba, amman bai dago ba sai da yaji zuciyar shi ta daina nauyin da take mishi tukunna ya dago yana kallonta, ita yau ta nemi inda hawaye suke ta rasa, da kansu sun san cewa yanayin da take ciki sun girme su.
"Bana cikin motar Ayya, ban shiga ba, bana ciki"
Sune kalaman da suka zo ma Bilal, kallon shi Ayya takeyi, kallon shi take saboda bata taba saka ran sake ganin shi ba, kallon shi takeyi kaunar shi da babu inda taje mata tana tasowa tana kuma shafe duk wani bangarori na zuciyar ta daya hakura da shi, bangarorin da sukayi jinyar rashin shi, hannuwan shi ta kama tana saka fuskarta a ciki hadi da sauke wata irin ajiyar zuciya da ta budewa hawayenta waje, wannan karin ita ta kwantar da kanta a jikin Bilal, kukan ta yana sake fito mishi da sababbin hawaye
"Kaga me kayi ko Bilal? Kaga me tafiyar ka tayi mana?"
Rayyan yake fadi yana kifta idanuwa saboda baya son ya fara kuka, yanajin su duka ba kuka sukeyi ba, idan ya fara ba zaiji lallashi ba
"Daada"
Nur da ta fito ta kira Rayyan din, da gudu take tahowa tana saka zuciyar shi mantawa da komai da yake faruwa saboda yanda take dokawa da tsoron karta fadi, bai sami natsuwa ba sai da yaga ta zagayo ta kama kafafuwan shi kamar ta dade bata gan shi ba, ko daki ya shiga tana wani dakin, idan ya fito haka take barin duk abinda takeyi ta tashi ta rugo ta rike shi kamar yayi wata tafiya mai nisa, sai yaji ta nutsar da shi, ta saka zuciyar shi wani irin sanyi. Ganin ta dago daga jikin shi tana kallon Bilal yasa shi kallon Bilal din shima. Sosai Nur take kallon Bilal kamar ta san shi. Abinda kafin psychology yayi mishi bayanin shi yake ganin tsakanin Ayya da Bilal, tsakaninta da sauran yan gidan shi yake gani tsakanin Nur da Bilal da har lokacin baima kula da ita ba.
Hankalin shi gabaki daya yana kan Ayya da ta dago tana saka hannunta ta goge fuskarta da shi. Shima Bilal tashi fuskar yake gogewa, hakuri yake so ya bata, amman kalaman sunki fitowa. Ko da Nur bata kai haka ba, sam yarinyar batayi qwiya ba, kowa ya dauketa zuwa takeyi, gashi bata tsoron mutane, kawai magana ce batayi sosai
"Yarinyar nan ko dai kurma ce Hamma?"
Layla ta tambaye shi, yayi dariya sosai ranar, har yanzun ko shi kadai ya tuna sai yayi dariya
"Allah da gaske nakeyi fa, ko irin wakar nan ta yara Nur batayi sam, in ba kuka take ba bakajin sautin komai"
Kai kawai ya girgiza saboda dariya da ta hana shi magana, shi yanajin wakar da take magana, ba ko yaushe ba, haka ta dade bata fara magana ba, da ta fara din ma ba sosai ba, duk rashin surutun shi yana iya ba Nur labari har ya gama yanayin fuskarta ne kawai zai nuna tana jin shi, ko in abin amsawa ne ta daga mishi kai. Ko kayan wasa tafi son wanda suke kamar bulalluka tayi ta hadawa, sai kuma puzzle da zata zazzage