Showing 123001 words to 126000 words out of 150281 words

Chapter 42 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3987

inda muke yanzun ko zan samu sauki. Ayya ina zan kai laifin nan?"

Rayyan ya tambaya yana kallon cikin idanuwanta

"Ya zan fara rayuwa a duk rana da sanin nayi sanadin mutuwar Bilal?"

Ya karasa maganar wasu hawaye na cika misji idanuwa. Numfashi me nauyi ya sauke yana sake kallon Ayya da ta sadda kanta kasa, bata son ganin shi, ya kashe mata yaro dole taqi son ganin shi, shima baya son ganin kan shi yanzun nan. Juyawa yayi yana ficewa daga dakin, sai dai baisan inda ya kamata ya nufa ba, bakin kofar dakin su ya tsaya yana tsintar kan shi da kasa shiga. Abu daya zai gani na Bilal abinda yake ji yana gab da ballewa a tare da shi zai balle, tsaye yake yana maida numfashi yana kuma son ganin hawayen da suke cikin idanuwan shi basu zuba ba. Kirjin shi ya dan dafe yana murza inda yake ciwo kamar zai rabe biyu.

"Hamma..."

Yaji muryar Layla da ta saka shi juyawa, kamar tsayuwar wahala take mata shisa ta dafa bango. Ta dade bakin kofa ko zata ga giccin Mami kafin ta samu ta fito, tana jin numfashin da Rayyan din yake fitarwa ta cikin wayar cikin yanayin daya daga mata hankali, gashi tanata magana shiru kafin kiran ya yanke. Zuciyarta ta kasa hakuri, wata irin soyayyar shi ce take dawainiya da ita, tunanin halin da yake ciki, tsantsar ciwon zuciyar da taji a cikin muryar shi ya hade yana sakata kasa hakuri sai ta gan shi, ko na dakika biyune ta leqa taga yana nan dai zata samu sauki. Sai da ta fara takowa taji kamar tana yawo saman iska.

Shikuma kallonta yakeyi, idanuwanta na saka shi jin wani iri, amman ya kasa daina kallon su, saboda a cikin su yake ganin tarin rudani a shimfide, kafin ya samu ya kalli duka fuskarta da har zanen kashin kuncinta ya fito kamar wadda ta dade tana jinya, tayi zuru zuru ta fita hayyacinta. Tana cikin firgicin da yake jin duka shine silar shi

"Layla"

Ya kira da wani yanayi mai wahala

Idanuwanta cike taf da hawaye tana jan numfashin da ta fitar da shi tare da hawayen ta da suka zuba, dayan hannunta ta saka ta share su, tana kallon yanda fuskar shi take cike da gashi, kayan jikin shi sunyi daudar da bata taba ganin shi da ita ba, shi kan shi ya mata wani irin cuku-cuku. Ko takalma babu a kafafuwan shi, Rayyan da ko a daki baya yawo babu takalmi ko safa, Rayyan da ta san zai iya wanka hudu a rana, shine yau a firgice haka. Hannunta ta kai tana dafe cikinta da taji kamar ya kulle, yanayin da ya saka Rayyan bin cikin nata da kallo.

Akwai yaron Bilal a cikin nata, a jikinta yana rayuwa, kwai daya da Bilal yake da rabon samu a duniya. Kwan da zaizo ta hanyar da kowa yake gudu saboda shi

"Ki yafe mun Layla"

Yayi maganar yana sadda kan shi kasa, wasu hawayen ne masu zafi suka zubo mata, bata san me yasa yake rokon ta yafe mishi ba. Bayan ita din ya kamata ta roki ya yafe mata. Jin tayi shiru ya saka shi sauke idanuwan shi cikin nata, yana jin yanda bata kyauta mishi ba

"Ban hana ki zama a gidan mu idan bana nan ba? Me yasa kika zauna?"

Kafadu ta dan daga mishi, bata da bakin magana bata da wani bayanin da zatayi mishi

"Baki kyauta mun ba, kin sani ko?"

Da ta taimaka mishi bata zauna ba, da ya gujema abubuwa da yawa. Duk da kukanta na kara mishi zafin da zuciyar shi takeyi. Amman yana bukatar raba laifin da wani. Numfashi ya sauke ya juya da nufin shiga daki

"Hamma..."

Ta kira shi, juyowa Rayyan yayi, kuka yake so yayi har sai inda hawayen shi suka tsaya. Amman bayason yi a gabanta. Baya son kowa ya lallashe shi. Idan ya gama duk zai roke su da su yafe mishi, sai ya kara yawaita addu'o'in shi akan Bilal ko zasu isa wanke girman abinda yayi mishi idan suka tsaya a gaban Allah.

"Idan na kira ka daga, dan Allah kayi mun kowanne hukunci karka rabani da kai, abubuwan da suka rage mun basu da yawa"

Kai kawai ya iya daga mata yana shigewa daki. Wani irin numfashi ta sauke mai nauyin gaske tana samu ta koma bangaren su tana wucewa daki. Wannan karin waje ta samu ta zauna, kafafuwanta taja ta hade su da kirjinta, sai taji bata iya fitar da numfashi sosai, kamar ta matse cikin nata da yawa, babu shiri ta sauke kafafuwan nata, kafin wani irin tashin hankali ya dirar mata, cikine a jikinta da gaske, da duk ranar da zata wuce da yanda cikin zai cigaba da fitowa. A hankali take jin yanda ba rabuwa da Rayyan bane matsalarta ta farko, yanda zata fara rayuwa da cikin da in ya tako duniya bata da amsar bashi, cikin da Bilal baya nan ballantana ya tayata yi mishi bayani

"Na shiga uku"

Ta furta a hankali tana fashewa da kuka, komai nata ya canza, rayuwarta, makaranta, watakila tabarta kenan har abada, idan haihuwa tayi ta ina zata fara yawo da yaro cikin mutane, me zata ce musu idan sun tambayeta? Ya Mami zata fara shiga dangi, wacce tambaya kowa zai jefe ta da ita? Watakila kowa ya fara tunanin Mami bata riketa da kyau ba, su Abbu basu riketa da kyau ba saboda ita din ba yarsu bace ba. Duk yanzun ne ta samu damar yin wannan tunanin da yake kara daga hankalinta, kasa ta kwanta kan tayal din dakin da sanyin shi ke kara mata zazzabin da ya sake saukar mata, kuka takeyi marar sauti, kukan da bata hango ranar da zata daina shi ba.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 7, 2020

29

Tayi kuka fiye da wanda tayi na rasuwar Bilal, kukan da bata tabayin kalar shi a tsayin zaman duniyarta ba. Saboda akwai banbanci a kuka na rashi, akwai kuma banbanci a kukan sanin cewa kaine da laifi a wannan rashin, kuka ne tayi na dana sani kan abubuwa da dama. Yanda duk zata so raba nata laifin da Dije da kuma Gwaggo da suka dorata akan bin Malamai ta kasa, sosai take so ta boye bayan ko da kuruciya ce dan samun sauki. Amman da hankalin ta lokacin, ko da kuwa da shekaru za ayi amfani wajen auna hakan, balle kuma zaman gidan miji da kuma yawan yara.

Ba abokai nagari da zatayi shawara da su bane ta rasa a lokacin, da ta dora kacokan laifin akan su Hajiya Dije. Tana zagaye da yan uwanta da suke matukar kaunarta. Yan uwan da ta gujewa saboda suna gaya mata gaskiyar da bataji. Sai ta dinga ganin kamar babu kaunar nan da tayi tunanin akwaita a tsakanin su. Da sun fada mata abinda take son ji kamar yanda su Gwaggo suka dingayi. Yanzun ne da hankalinta ya dawo jikinta take tunani kala-kala. Ko da asiri Mami tayi ta aure Abbu ba zai zama dalilin da itama zata ce ta fara shiga Malamai ba, wannan ba uzuri bane ba sam.

Balle da idanuwanta bata shaida hakan ba, Gwaggo ta fara kawo mata wannan tunanin. Kuma ta hau ta zauna saboda yayi dai-dai da abinda take son ji. Akwai tarin son zuciya a abinda tayi. Yanzun tunanin cutar da Haris ko da yaya ne sai da ya sa kanta sarawa saboda tarin kaunar da takeyi mishi. A baya idanuwanta ya rufe da soyayyar da taga Abbu yana nuna mishi, tana manta lokacin tata kuruciyar da girma, da kuma yanda kaf kowa yake maganar kusancin da take da shi da nata baban. Bata kuma duba kalar kusancin da take da shi da Bilal ba, da yanda duka yaranta sukan ce tafi son Bilal akan su.

Tunani ne kala-kala yake mata yawo yanzun. Son zuciya ya kaita ya barota, abinda taso da dan wani sai Allah ya juya shi kan nata yaron, ko ma tace nata yaran. Tana ta takamar tana kula da abinda yake faruwa da su, sai ta kasa fahimtar a baudadden halayya irin na Rayyan akwai tarin abubuwan da yake fuskanta. Balle kuma ta kalli Bilal da kullum take dorawa nauyin kula da Rayyan din. Sai ta maida hankalinta wajen raba abinda kaddara ta rigada ta gama rubutawa, a karo na babu adadi tayi kokarin cutar da Layla. Da yake kaddara na biye da su sai gata da cikin Bilal ta hanyar da Ayya zatayi komai da zata iya dan kaucema faruwar hakan.

Yanzun da take wannan tunanin sai abin ya kara tsoratata, saboda tana jin yanda cikin jikin Layla ne kwai daya da Bilal yake da rabon samu a duniya. Kwan da bata damu da hanyar da ya samun ba in dai zai taka duniya ta rike shi a cikin hannuwanta. Har cikin zuciyarta take jin son abinda yake cikin Layla din. A gefe daya kuma tana tunanin da idanuwan da zata kalli Rayyan yanzun. Zata so ta fada mishi da ita ya kamata ya raba laifin da yake jin ya mishi nauyi. Amman hakan ma ba mafita bane a hargitsin da yake ciki. Idan ta gaya mishi zata kara rikita shi, amman tana bukatar yafiyar shi, duk da take mahaifiyar shi wannan hakkine mai girman gaske.

Balle kuma yanzun ta kula da Rayyan din ya samu lafiya. Saboda kalar kusancin da yake tsakanin su a yan kwanakin nan, ba zata kara jefa shi cikin hargitsi ba. Zata fara da dai-dai ta tsakanin ta da Ubangijin ta da farko, sauran zasu fi zuwar mata da sauki, zata roki Allah da ya saka sauran lamurran zuwa mata cikin sauki. Tana nan zaune a daki taji an kwankwasa, sai da ta share hawayenta sannan ta amsa, ta dauka ma Rukayya ce, sai taga Rayyan ne, yanda ya fara sauko rabin fuskar shi yana sakata runtsa idanuwan ta kafin ta sake bude su akan shi, dan yayi mata kamar Bilal, manya kayane a jikin shi farare kal sai hula ruwan omo mai cizawa.

"Ayya yanzun zan wuce, Bappa ya karaso"

Numfashi ta sauke tana kallon shi

"Har kana da natsuwar komawa?"

Tayi tambayar a sanyaye, kafadu Rayyan ya dan daga mata. Idan ma bashi da natsuwar komawa ba zai zauna ya jirata ba. Tunda bashi da tabbacin ranar zuwanta ko zata zo din. Komawar shi yafi mishi, ko bakomai zai samu abin yi banda zama cikin dakin su yana duba hanya kamar zai ga shigowar Bilal kowanne lokaci.

"Zai ragemun tunani, idan na koma din"

Kai ta jinjina mishi, wani irin yanayi take ji a zuciyarta da ba zai misaltu ba

"Kayi wa Abbun ka sallama?"

A hankali ya girgiza mata kai, ya shiga dakin Abbun ya samu harya fita. Yana yawan shiga yanzun, saboda yana rage mishi zafin da yake ji a zuciyar shi, ba wai suna hira bane ba. Yanzun ya san rashin son surutu halin shine, kawai yanajin dadin yanda yake iya zama waje daya da Abbu din batare da yaji iskar dakin tayi mishi kadan ba. Idan labarai Abbu yake kallo zasu kalla tare, har sai ya gaji da zaman sannan yake tashi yayiwa Abbu sallama ya koma nasu dakin. Jiyama a dakin Abbu suka ci abincin dare tare, abinda bai tabayi ba a iya yanda zai iya tunawa.

Yaji dadin abin saboda shine abu na farko da ya saka a cikin shi duk tsayin jiya. Yana daki yana kukan da ya kasa tsayawarwa sai da ya tsaya da kan shi. Ya fadama Abbu cewa yau zai tafi, amman basuyi sallama ba yau din

"Ya tafi sanda na shiga. Zan kira shi a waya..."

Ya furta a hankali yana juyawa

"Allah ya tsare ya bada sa'a. Ka kula da kanka"

Hannun kofar da yake rike da ita ya murza sosai, addu'ar Ayya na nutsar da wani abu cikin kan shi, sai da ya hadiye yawi sannan ya amsa da

"Amin thumma amin"

Harya bude kofar yana shirin fita ta kira sunan shi, dan juyawa yayi

"Idan na kiraka ka daga Rayyan"

Kai ya jinjina mata yana ficewa, duk da wani abu a tare da shi na fada mishi ya bata hakuri, da duk lokuttan da ta kira shi yana kallo bai daga ba, ba laifin shi bane ba, a lokacin yanajin magana da ita takura ne, shisa yakan zabi yaki dagawa. Amman abinda yake saka shi kuka yanzun ya kula bashi da wahala. Shisa ya zabi yin shiru, hakurin da zai bata zaiyi shi ta hanyar kiran wayarta kafin ita ta kira shi. Da wannan tunanin ya fice daga dakin, yana nufar dakin Mami da ya dade a tsaye bakin kofa yana tunanin shiga.

Wani numfashi yaja mai nauyi yana fitarwa kafin ya shiga dakin da sallama yana cire takalman shi daga bakin kofa ganin Mami zaune a falon, amsawa tayi tana dorawa da

"Rayyan..."

Bata hadu da shi ba tun ranar rasuwar Bilal, bata ma fita ba saboda dalilai kala-kala, daya daga cikin babban kunya da nauyin Rayyan din kan yanda ta yanke mishi hukunci batare da ta tsaya taji bakin shi ba. Ga shi duniyar duka bata mata dadi a kwanakin, bata da lafiya amman ba zatace ga guri daya da yake mata ciwo ba. A cikin zaman makokin Bilal bata da natsuwar kirki, mutuwar bata daketa ba sai bayan an watse sadakar ukku, saboda zuciyarta bata da natsuwa kar Layla ta gifta cikin danginsu wani ya kula da cikin da take dauke da shi. Nasihar duk da Abbu yayi mata ta kasa natsuwa.

Batajin akwai wanda zai taba gane halin da take ciki. Ita kadai tasan abinda take ji. Shisa Layla din ma ta kasa samu ta zauna suyi wata magana. Tana hango yanda ba rayuwar yarinyar bace kawai ta canza harda tata. Da ace tana da mahaifa ko daya da suka rage da taji sauki, zataje wajen su ko kuka tayi su fada mata magana mai sanyi, su karfafa mata gwiwar daukar kaddarar da ta sameta. Amman babu, maraicinta bai taba tsaya mata irin na yanzun ba, saboda Ahmadi na bata dukkan kulawa. Bata da bakin da zata amsa tambayoyin mutane, kunnuwanta da zuciyarta basu da karfin jure ma maganganun su.

"Mami"

Rayyan ya kira cikin sigar gaisuwa yana karasawa cikin dakin sosai. Kallon mamaki take bin shi da shi, sai take ganin kamar akwai abinda ya canza a tare da shi da bashida alaka da mutuwar Bilal. Kujera ya samu ya zauna yana sauke numfashi a hankali, jin shirun yayi yawa yasa Mami fadin

"Abinda ya faru... Kayi hakuri, na yanke maka hukunci da sauri"

Murmushi mai ciwo Rayyan yayi

"Baya nufin bani da laifi, ina da laifi mai yawa Mami... Kiyi hakuri"

Idanuwanta taji sun cika da hawaye, shi baizo dan wani abu ba sai dan Layla. Ba Ayya bace kawai tayi tunani akan cikin da yake jikin Layla, har shi dinma, Bilal bai bar mishi wani abu da zai dinga tunawa da shi ba, ko da hotone yana bukata, suna da hotuna da yawa tare da Bilal, dan shi din baya gajiya da daga camera din wayar shi. Wani lokacin ma yana harar shi haka zai dauke su yana dariya, da zai samu duka wannan hotunan da yaji dadi, ko su zai dinga dubawa, yana bukatar wani abu banda kayan sakawa na Bilal. Cikin da yake jikin Layla ne abu mai girma na Bilal da zai dinga dubawa.

A daren jiya bayan rokarwa Bilal gafara da kuma Rahmar Allah harda cikin jikin Layla ya hada. Sosai yake jin son kan da yayi a cikin hakan, saboda yaga Layla, yaga yanda ta koma. Ba karamin kalubale yake hangoma rayuwarta a tare da cikin ba. Amman babu yanda zaiyi, bai isa ya hana zuciyar shi son ganin abinda zata haifo ba. Jinin Bilal ne, yaro ko yarinyar Bilal ce, yana son gani, shine kwai kwara daya na Bilal. Duk da zuciyar shi ta kasa hasko mishi Bilal din da Layla, cikin ya manne a wani waje cikin zuciyar shi, shisa yazo ya bama Mami hakuri, baice ita dole sai taso cikin ba, amman karta tsangwama wa Layla, tana cikin wani hali da alama.

"Dan Allah kiyi hakuri Mami, bansan ya kike ji ba. Amman naga Layla... Duka abin ya fara tabata kafin mu ya taba mu, kiyi mata fada, ki zageta idan hakan zaisa ki samu sauki, amman dan Allah kiyi hakuri, ki yafe mata. Ki yafe ma Bilal, nima ki yafe mun... Duka mu din masu laifi ne"

Hawayen da take rikewa ne suka zubo mata, tunda take bata taba jin Rayyan yayi magana mai tsayin wadda yayi ba yanzun. Ba kalaman shi bane suka sakata kuka, yanayin yanda yayi maganar ne, sai da ta goge hawayen sannan ta iya amsa shi da

"Allah ya yafe mana gabaki daya"

Mikewa Rayyan yayi, ganin yanda take ta share hawaye shisa bai iya sake cewa komai ba ya fice daga dakin. Ya so ya ga Layla, amman bai da karfin zuciyar cewa Mami tayi mata magana. Zai kirata a waye idan ya tashi. Yana fita daga dakin mikewa Mami tayi tana share wasu sababbin hawayen da suke zubo mata. Sannan ta iya nufar dakin Layla da ta tura, a zaune ta sameta a kasa, ta dora kanta saman gado, karasawa Mami tayi tana zama gefen gadon, sai da ta zauna, Layla taji gadon ya motsa sannan ta san ta shigo.

Nata hawayen da suke zuba ta goge da sauri, muryarta a dishe tace

"Mami..."

Wani irin kukane ya kwacewa Mami da yasa Layla matsawa tana dora kanta a jikin Mami din, itama kukan takeyi

"Dan Allah Mami ki yafe mun, ba zan sake ba. Dan Allah Mami, ban san ina zan saka raina ba, ina jin tsoro Mami...sosai ina jin tsoro"

Layla take fadi tana wani irin kuka

"Shikenan ko Mami? Babu wanda zai sake ganina da mutunci, kowa zai ce mun yar iska... Wallahi Mami ni ba yar iska bace, ki yarda dani, ban san me ya faru ba, kuskurena daya na dauka, nice naje gidan su Hamma, da banje ba, kuskure daya nayi Mami, amman kowa ba zai jini ba, kowa ba zai mun uzuri ba ko? Kema bakya sona yanzun, na san kin daina sona, Abbu ma haka, na muku laifi, Mami za'a zageku saboda ni..."

Hannu Mami ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login