Showing 39001 words to 42000 words out of 150281 words

Chapter 14 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3982

kuwa gabaki daya lamarin ne yake sanyaya jikin shi, yaran nashine yake ganin kamar sunyi kankanta, kamar ma basu da hankalin hango kaddarar da take bibiyar su.

Rayyan ne kaddarar su
Rayyan ne suke tunanin zai zama tushen komai.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 22, 2020

10

BAYAN SHEKARA UKU

Ita kadai tasan cikin kalar fargaba da tashin hankalin da take a shekarun nan. Yanda duk taso ta nisanta kanta da Hajiya Dije ko dan gudun suje inda za'a binciko mata abinda zai daga mata hankali sai ta kasa, Rayyan na bata tsoro, yanda yake manne da Layla duk idan ya dawo makaranta yana karya mata zuciya. Musamman yanzun da take ganin suna kara girma, yaranta na wani irin girma da har mamakin shi takeyi. Ita ce harta aurar da Khalifa da Zubaida. Kuma duk lokacin da zata sami Ahmadi da maganar takan ga gajiyawa a fuskar shi, kamar ya gaji da yanda ta kasa daukar ido ta saka akan Rayyan din da Layla kamar yanda yayi

"Ya kike so inyi? Ko akan dukan da yakeyi mata nayi magana tsini ne kawai bakina baiyi ba. Kinsan halin Rayyan, abinda ya ga dama shi yakeyi"

Ahmadin yace mata wani lokacin, ita ko dukan bata so, batason wani abu na hada danta da Layla. Batason ganin shi a bangaren Mami sam-sam. Rayyan din ya kara mata tsanar matar kamar zata hadiyi zuciya haka takeji duk idan taga giccinta. Yau da kanta ta shiga kitchen, har Rukayya na mata tsegumi

"Ayya saboda su Hamma zasu dawo shisa kika ce ke zakiyi girki..."

Dariya kawai tayi, wannan karin sun dade, watansu na hudu kenan rabon su da gida. Duk da ta wani fannin dadewar tayi mata dadi bana wasa ba. Hakan na nufin aikin da Malam Ma'azu kwano kamar yanda Hajiya Dije ta kira shi yaci. Daman tace a borno yayo karatun allo, a haka idan ka ganshi zaka raina shi, sai dai aiki yake kamar babu gobe. Tashin farko dubu goma Ayya ta ajiye mishi na bugun kasa, inda yace ta saka tafin hannunta kan wani rairayi da yake cikin falankin katako. Batayi musu ba ta saka, duk da tasan zancen gizo ba zai wuce na koki ba, ba nan bane wajen farko da sukaje da Hajiya Dije, kuma duk maganar shige dayace, Layla na rike da kurwar Rayyan, danma yana da dakakkiyar zuciya da sai abinda tace ne zaiyi.

Wannan ma suna shiga ta fara labarta mishi matsalarta akan Rayyan din, kafin yace yasan kasa zata nuna mishi komai, ta saka hannunta akan yashin, suna zaune suna kallon yanda yake rubutu yana sharewa yana sakeyin wani, kafin yayi numfashi mai nauyi yana dago kai ya kalli Ayya

"Yaron ki zai zama shahararren mai kudi, akwai nasarori da suke biye da shi. Shisa abokiyar zamanki ta kasa zaune da tsaye a kan shi. Saboda taje an duba mata yanda kaf gidan ba za'ayi mai arziqin shi ba. Yarinyar da kike magana da ita aka, idan baki tashi tsaye ba duk abinda zai samo a kansu zai kare, ke kanki ga katanga nan naga ana ginawa tsakanin ku"

Wani irin numfashi Ayya taja, tana duban Hajiya Dije, zuciyarta na wata irin dokawa

"Yaushe Maryama zata kyaleni in huta?"

Murmushin "Na fada miki ai" Hajiya Dije tayi mata

"Da nace miki ki dinga nemar wa yaranki ko da tsarine ca kikayi kamar Maryama ba zata iya cutar da su ba. Kin daiji da kunnuwan ki yanzun ai"

Kai Ayya ta jinjina mata, taji kam, ba waje daya ba biyu ba, kuma ta gasgata tunda zuwan karshe da Rayyan din yayi, saboda ta mishi magana akan Layla yasa shi daina shiga bangaren ta gabaki daya har suka koma. Sosai abin ya bata tsoro, ashe katanga ake mata da dan data tsugunna ta haifa, dan daya fito daga cikinta. Rashin imani irin na Maryama ba zai misaltu ba. Aiki Malam Muazu yace za ayi sosai akan Rayyan din

"Gaskiya kudin ki zaiyi yawa, saboda za'a yanka raguna baki da fari guda daya, da zuciyar su za'ayi aikin, sai an hada guda biyu za'a musanya su da ta danki da take rike a wajen su... Aikine babba, zan kuma baki garin maganin da nake so ki tabbata ko yayane shi yaron yaci dan ya karya katangar da take tsakanin ku"

Hakan kuwa akayi, kudaden duk daya bukata ta bashi su. Daman yace zata ga canji, ba karamin dadi take ji ba ganin yanda Rayyan din ya zauna a makaranta har tsayin wata hudu,mutumin da baya iya hada satika hudu batare da yazo Kano kona kwana daya ba. Shisa take shirya girkin nan da kanta. Duka zata hade abincin ta barbade, har Bilal ma yaci dan shima yana bukatar duk wata kariya da zata ba Rayyan. Dan ma shi tana kula da yanda yake janye jikin shi daga bangaren Maryama, ya rage shiga kamar da, hakan ba karamin dadi yake mata ba.

Gabaki daya cikin nishadi take a duka ranar. Saima da taji sallamar Bilal, da murmushi dauke a fuskar shi. Su Rukayya kance basa bambance muryar Bilal da ta Rayyan musamman yanzun da suka zama Samari, sannan idan a fisge ka kalle su zaka iya dauka Bilal ne, sai ya shigo sosai zaka ga Rayyan ne. Kamannin su har Abbu suke ba mamaki, yana kara jinjina karfin dangantaka ta jini, duk da mutane da yawa kan iya yin kamanceceniya batare da alaka ta komai ta hadasu ba.

Sai dai Rayyan yafi Bilal din haske, kuma yanzun ya dan fishi tsayi duk da su duka dogaye ne, Ayya kan cewa Abbu itama ai doguwar ce duk idan yace tsayin shine yaran suka biyo. Yanzun kuma Bilal na tara suma a kan shi, Rayyan kuma yana asketa kasa sosai sosai, kuma ya tara kasumba a fuskar da ta saka shi wani kwarjini na daban, Bilal gemu ne da samarin yanzun suke ajiyewa da har dariya yake baiwa Ayya. Wani lokacin ma fayau zakaga fuskar shi, ya aske komai.

"Ayya..."

Bilal ya furta yana fadada murmushin shi, kafin ya karasa cikin dakin yana zama kan kujera hadi da sauke numfashi

"Yan Zaria"

Ayya ta fadi tana saka Bilal din yin dariya, yayi kewarta matuka

"Harma mun zama yan Zaria kenan Ayya... Ina kowa? Wallahi nayi kewarki da yawa..."

Sosai Ayya take murmushi, tasan yayi kewarta, tunda yana iya kiranta sau biyar ma a rana. Itama idan ta cika awa hudu bata ga kiran shi ba sai ta neme shi. Rayyan ne ma harta saba, a cikin watannin nan hudune da take tunanin aikin Malam ne ya kirata sau biyu, daga gaisuwa yayi shiru, sai tace ta dinga tambayar shi makaranta da lafiyar shi da ya dinga amsa ta dai-dai

"Ayya gaisuwa ce kawai"

Ya fadi a hankali, da yasan yanda taji dadin gaisuwar da ko sau dayane a wata ya kirata. Tunda yai wayar hannu sai a wajen Bilal ta sami lambar shi saboda yanda bai taba gwada kiranta ba. Idan sunyi magana to Bilal ya bashi wayar shi ya gaisheta, shima daga yanayin yanda zai magana tasan a kunne kawai Bilal ya saka mishi wayar batare daya shirya ba

"Duk idanuwanka yayi zuru-zuru"

Dariya mai sauti Bilal yayi

"Jarabawa ce Ayya... Sai kinga Hamma, gara nima tunda komai na samu ina ci"

Numfashi ta sauke, ai baizo ba ballantana ta gan shi. Da kanta ta mike tare da fadin

"Allah yasa an rubuta a sa'a, bari in dauko maka abincin ku..."

Kitchen ta wuce ta dauko mishi kuloli guda biyu da cokula, mikewa Bilal yayi ya amsa yana ficewa daga dakin zuwa dakin su, tunda ya karya kwana ya hango Layla a tsaye, jikinta sanye da wandon jeans ruwan bula da riga ja a jikinta, sai hula, tayi mishi kyau tun ta gefen ta daya hango, yana jin zuciyar shi ta matse a kirjin shi, cikin shekarun nan ya fahimci muhimmanci da Layla take da shi a rayuwar shi. A cikin shekarun ne kuma yayi kokarin janye jikin shi saboda yanda kusancinta da Rayyan yake wahalar da shi.

Suna zaune su biyu zata zo waje, daga nesa zaka ga yanda idanuwanta suke kafe kan Rayyan, lokutta da yawa in ba kuka Rayyan din ya sata ba, sam bata kula da yana waje. Idan Rayyan yana nan idanuwanta a rufe suke daga sauran abubuwan da bashi ba. Ranar da Rayyan ya riko hannunta ji yayi wani abu na budewa a kirjin shi, shisa yanzun yake tashi yana basu waje, yafi mishi kwanciyar hankali, abinda bai gani ba bazai bata mishi rai ba sam.

Wani lokacin idan Rayyan ya kai mata wani dukan har a zuciyar shi yake jin zafin, amman daya kirata zata sake dawowa. Zaka rantse da Allah rashin kirkin da Rayyan yake mata take so. Bashi da inda yake jin sauki-sauki sai wajen Aisha. Yanzun ma daya huta yayi la'asar wajenta zai tafi ko zuciyar shi zatayi sanyi-sanyi. Da ba kulolin abinci bane a hannun shi sam ba zai karasa inda suke ba, ya koyawa kan shi nisanta da Layla, musamman in tana tare da Rayyan haka. Numfashi yaja yana fitarwa, duk wani karfin hali da zai iya ya tattaro yana takawa har inda take tsaye a bakin kofa, kafin yaga Rayyan da yake tattaro shara.

"Hamma Bilal..."

Layla ta fadi cikin sigar gaisuwa batare da ta kalle shi ba

"Layla..."

Ya amsa a sanyaye, yana shirin karawa da tambayar lafiyarta Rayyan ya dago, da bayan hannun shi ya kai ma Layla wani duka da yasa Bilal runtsa idanuwan shi kamar a kan shi hannun zai sauka, ya bude su a hankali yana ganin Layla da ta kauce tana kara turo baki

"Nace bai sharu ba kika tsaya gardama dani... Uban meye wannan?"

Ya karasa maganar yana nuna mata wata kasa da batasan daga inda ya sharota ba, saboda har karkashin gadon dakin nasu sai da ta share, kujerar shi da teburi kuwa daga su tayi ta ajiye a gefe, sif din kayan su har samanta sai da ta taka kujera ta share, haka ta sake takawa ta gogo daga saman zuwan jiki, tasan halin shi, dan yatsa zaisa ya dangwalo yaga ko da kura babu

"Wallahi shara hudu nayi Hamma"

Ta furta a gajiye, Rayyan din najan wani tsaki

"Ba abinda kika iya sai shirme..."

Ya fadi yana saka abin kwashe shara ya tattare kasar ya mika mata, karba tayi tana juyawa, shima cikin dakin ya shiga. Inda Bilal ya rufa mishi baya yana samarwa kulolin da suke hannun shi mazauni a tsakar dakin. Rayyan links din jikin rigar shi yake cirewa, dan manyan kayane a jikin shi, wani yadi ruwan kwai da ya sake fito da hasken fatar shi

"Ayya na tambayar ka"

Bilal ya fadi badan ya tsammaci amsa daga wajen Rayyan din ba, bai bashi amsar ba kuwa ya wuce yana nufar bandaki, dan ruwa kawai yake son watsawa. Tun da safe kafin su taho yace Layla ta bude dakin ta share musu. Yana saka kafar shi yaji kamar ya taka kasa. Wayarta da ta saukaka mishi komai yanzun ya kira

"Baki share dakin nan ba Layla"

Ya furta bayan ta daga, kafin ta amsa shi ya dora da

"Ki zo yanzun"

Gardamar da ta tsaya mishi da rantse-rantse yasa shi cewa ta dauko mishi tsintsiya. Sanda ta kira shi take fada mishi taci jarabawar aji shidda wato WAEC mamaki ya dingayi yanda rayuwar take wani irin sauri.

"Wayar waye wannan din?"

Shine tambayar da yayi mata a madadin tayata murnar cin jarabawar da ta fada mishi tayi

"Wayata ce, Abbu ya bani saboda naci exams dina"

Yanayin muryarta yasa shi gane ta turo bakinta ne take mishi magana

"Saina fasa bakin ki kina mun magana haka"

Shiru tayi, ya kashe wayar daga bangaren shi, kusan kullum sai ta kira shi, yana dagawa kuma gaisuwar shi itace

"Lafiya? Ko maitar ce ta motsa? Me yasa kike kirana?"

Amman ranar duk da bata kira shi ba, haka zai saka wayar a gaba yai ta kallo, ko yana aji wayar na silent, rabin hankalin shi yana kan darasin da ake musu, rabin hankalin shi na kan wayar. Ranar kuma saiya nemi dalilin da zai kirata, ko yace ta duba dakin su taga ko wani takalman shi ruwan kasa suna nan, ko kuma wata takarda da yasan babu ita sam-sam. Kawai yana dai son yaji muryarta ne. Yana fitowa daga wanka ya samu har filattai Bilal ya kawo, sai da ya samu riga da wando marassa nauyi ya saka a jikin shi ya feshe da turare kamar zai fita wani waje. Sai daya zauna yake jin gajiya sosai.

Filattan ya mika hannu ya dauka yana tashi tsaye. Inda ruwan leda yake jingine ya karasa ya fasa yana daukar guda daya. Bandaki ya shiga ya kara dauraye filattan ya dawo ya dauki cokulla suma ya dauraye. Bilal na kallon shi harya gama, da kan shi ya bude kulolin, wake da shinkafa ne, sai miyar kaji da kamshinta ya cika dakin.

"In zuba maka ko saika yi wanka?"

Rayyan ya bukata yana kallon Bilal

"Ka zuba mun"

Kai Rayyan ya girgiza

"Jikin ka baya maka danqo?"

Wani irin kallo Bilal yayi mishi

"Da ruwan sikari nayi wanka da safe? Ko motar sikari muka shigo?"

Murmushi Rayyan yayi da yake wahala kagani a fuskar shi. Amman sam jikin shi baya mishi dadi rana ta fito ta fadi bai cakar da Bilal din ba, bai ga hawaye a fuskar Layla ba, ko basa tare yana son yaji muryarta ta canza ta cikin waya alamar ta kwade shi a cikin tunaninta yafi a kirga

"Daga tambaya?"

Ya fadi yana mayar da hankalin shi kan abincin da yake zubawa a filet

"Akan me jikina zaiyi danqo to?"

Shiru Rayyan din yayi yana kyale shi, yana gama zuba abincin ya mayar da kulolin ya rufe, nashi filet din ya dauka yana gyara zaman shi kan kujera saboda yunwa yakeji ta fitar hankali, ko karin safe baiyi ba. Biscuit ne leda daya a cikin shi duk ranar. Bilal ya riga shi gama cin abincin, yana kallon shi ya wuce bandaki yayo wanka ya fito. Shadda ya saka a jikin shi harda hula, kafin wani lokaci ya fito das da shi. Wata leda Rayyan din yaga Bilal ya bude jakar shi ya zaro

"Na fita..."

Ya furta a hankali yana wucewa ya zira takalman daya fito dasu. Bangaren Ayya ya shiga yana samunta a zaune

"Sai ina haka? Anata baza kamshi"

Dariya yayi a kunyace

"Zan dan fita ne Ayya... Amman kafin Magriba in shaa Allah zan dawo, idan ba inda zakije da motar ki..."

Kafin ya karasa maganar ta katse shi da fadin

"Kaje ka dauki mukullin yana kan gado..."

Murmushin godiya yayi mata yana cire takalman shi ya wuce har can cikin dakin nata ya dauko, ya fito ne tace

"Ka gaishe ta"

Cike da kunya yace

"Ayya..."

Dariya tayi sosai, shima dariyar yayi yana wucewa har wajen motar Ayyar daya bude ya shiga. Saboda ita ya koyi tuqi tunda ta siyi motar da shiya fara sanin zata siyeta dan tare ma sukaje. Sai da ya tsaya yayi la'asar a hanya kafin ya nufi Kinkinau inda gidansu Aisha yake, har harabar gidan aka bude mishi ya shigar da motar yana fitowa, tsaye yayi a wajen ya kira wayarta. Daga inda yake tsaye yana hango ta tana saka hijabinta a bakin kofar da zata hadaka da cikin gidansu, kamar ta kasa jira ta saka daga cikin gida saboda zumudin da takeyi na son ganin shi.

"Allah ji nake kamar na dade banganka ba"

Ta furta bayan sun gaisa, dariyar shi yayi, yana kallon yanda sosai kominta yake mishi kamar Layla, har shigen yanda take magana, yanzun girma yasa yana ganin banbanci sosai a tsakanin su. Saboda tunda yake da Aisha zai kirga ranakun da ya taba ganin kalar kayanta, saboda hijabai take sakawa, hijabanta kuma masu hannune dogaye sosai har suna share titi, inba ranakun da ta saka abaya ba, ya hangi kala kalar kayan nata ta kasa. Layla kuwa hijabi wahala take mata, ranaku dai-daine zaka ganta da hijabi, ko in zataje islamiyya ko kuma tana idar da sallah ta fito daga daki kafin ta cire.

Yana son kalar shigar Aisha, saboda tattare take da mutunci na gaske, yanda Layla take saka kananun kaya ko skirt din da take tafiya dakyar a cikin shi yakan mishi tsaye a rai. Musamman idan yaga fita zatayi a hakan, zaita tunanin tarin mazan da zasu ganta da wannan shigar. Sai yaga har wani haske ke gilmawa ta cikin idanuwan shi saboda kishin da yakan taso mishi. Amman ita ko a jikinta, hannuwa Aisha ta tafa a saitin fuskar shi, tana saka shi ware mata idanuwan shi da sukafi komai yi mata kyau a tattarr da shi

"Tunanin me kakeyi?"

Kafadu yadan daga mata yanayin murmushi

"Kinyi kyau"

Ya furta a madadin tambayar da tayi mishi, kanta ta saddar kasa cikin jin kunyar shi

"Kaima kayi kyau ai"

Kai ya girgiza mata

"Idan banyi kyau bama ke ba zaki gani ba"

Dariya tayi sosai, akwai gaskiya a al'amarin shi, kullum kyau yake mata, tun bata da hankali har yanzun da tayi, soyayyar da take mishi mai girma ce, ba zata taba barinta taga wani aibu a tattare da shi ba. Yau ko da wani ne zai kawo mata zance marar kyau akan Bilal tana da yakinin zuciyarta ba zata taba aminta ba, ita bata ma yarda da yanda Ummi yayarta take cewa Rayyan yafi Bilal dinta kyau. Rayyan da ko fara'a bayayi, Bilal kuwa ko hada idanuwa kukayi zai maka murmushi. Ko kamar da ake cewa sunyi ita bata gani, nesa ba kusa ba Bilal yafi mata Rayyan kyau.

"Son da kike maine Allah. Amman Rayyan yana mun kyau tun muna makaranta"

Ummi ta fadi, haushima taji ta tashi tabar mata wajen. Da aji daya Ummi ta wuce ta, ita tun waccen shekarar ta zana jarabawa, jamb ce bataci ba, kuma ta nace sai ABU zataje. Ita Aisha bata taba tunanin zuwa wata ABU ba, dan duk kawayenta BUK suka nema. Saboda Bilal, dan ta samu damar ganin shi kullum ta biyewa Ummi suka nemi gurbin karatu a ABU din wannan shekarar tunda ita tayi sa'ar cinye jarabawar ta jamb.

"Sanda zan bar Zaria fa lokacin zaki shiga aji uku, haka ni zan dawo gida ki barni da kewar ki"

Cewar Bilal da ta fada mishi inda ta cike

"Zaka gane yanda nake ji duk idan kazo zaka koma"

Dariya yayi sosai

"Ramawa kike sonyi shisa kika zabi Zaria kenan ko?"

Ya tambaya yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login