Showing 108001 words to 111000 words out of 150281 words

Chapter 37 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3964

tsintar kan shi da kin son ganinta. Har a zuciyar shi bayason ganinta

"Dan Allah Hamma..."

Ta fadi cikin kuka, kai Rayyan yake girgiza mata

"Bana son ji, koma menene, ba zai canza komai ba Layla"

Ya karasa yana juyawa, baisan yana cikin tashin hankali ba saida ya karya kwanar da zata kai shi dakin su yaji kafafuwan shi sun kasa daukar shi, a wajen ya tsugunna ya dafe kirjin shi yana jin kamar zai rabe gida biyu. Bude bakin shi yayi yana fitar da numfashi saboda ta hancin kofofin sun toshe mishi, cikine a jikin Layla. Yaron wani ne yake rayuwa a jikinta, yaron da ba na shi ba. Layla, Laylar shi ake magana a kai ba wata ba. Waye zai musu wannan abin? Waye zai taba mishi ita haka, runtsa idanuwan shi yayi yana kuwa bude su babu shiri saboda kazantar hoton daya hasaso cikin kan shi.

Koma wanene tare da Layla suka ci amanar shi. Abin da yafi tsana a rayuwar shi, ya bude baki ya fada mata yana son ta, Layla da ya dawo da burin fuskantar kowa da sunan soyayyarta ce da dan wani a cikinta. Bangon wajen ya dafa ya samu yana mikewa, so yake ya karasa daki ya kwanta, jiri yake gani a tsugunnen ma. Dakyar ya iya mikewa yana shiga dakin su inda ya samu Bilal a tsaye

"Zuciyata zata fashe Bilal, kirjina ciwo yakeyi"

Rayyan ya fadi, in bai gayawa wani ba da gaske zuciyar shi fashewa takeyi. Bakin shi ba zai iya shiru a gaban Bilal ba, wannan abin ya mishi girma ya dauka shi kadai, so yake a lallashe shi, kamar karamin yaron da yayi mummunar rauni haka yake ji, a hankali Bilal ya juyo yana sauke idanuwan shi akan Rayyan da yake fitar da numfashi kamar mai ciwon asthma. Shima yana gab da fara fitar da numfashi ta wannan sigar idan wani bai yarda dashi ba, idan bai fadama wani laifin shi bane, saboda shi kowa yake cikin rudani, tashin hankalin zai mishi yawa.

"Hamma..."

Bilal ya kira da wani yanayi a muryar shi da yasa Rayyan kallon shi, abinda yake kan fuskar shi na saka zuciyar Rayyan wani irin dokawa, tun kafin ya bude bakin shi Rayyan yake girgiza mishi kai yana rokon shi, baisan kafafuwan shi sun gaji ba sai da yaji gwiwoyin shi a kasa

"Dan Allah Bilal..."

Ya furta a hankali, na shi kan Bilal yake girgiza ma Rayyan din shima, dole ya fada mishi, idan yai shiru bashi da hope akan Rayyan din zai yafe mishi, idan ya fada musu, idan kowa ya sani wata rana zasu ji rokon gafarar shi

"Ni ne Hamma, cikina ne a jikin Layla"

Kan shi Rayyan ya durkusar kasa sosai yana wani irin maida numfashi, watakila haka ake ji yayin fitar rai, saboda wani abu ke fisgar shi da kalaman Bilal. Dakyar bakin shi ya iya furta

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Yana dagowa ya dafe fuskar shi da hannuwan shi ko inya bude zai farka daga wannan mummunan mafarkin. Bilal ma kasa yayi

"Hamma idan nace kuskure ne zaka yarda?"

Bude fuskar shi Rayyan yayi

"Kuskure? Cikin ne zaka dauka ka dora akan kuskure? Layla fa... Bilal ba wata bace Layla"

Rayyan ya fadi yana kallon Bilal, har lokacin yana son ya san me ma yake ji gabaki daya

"Kuskure n..."

Mikewar da Rayyan yayi na katse ma Bilal maganar daya fara. Hannu ya mike mishi

"Bani mukullin mota..."

Da wani yanayi Bilal yake kallon shi

"Baka iya tuqi ba Hamma, me zakayi da shi?"

Yanda Rayyan din yake kallon shi ya saka shi mikewa

"Ni ya kamata in bar maka dakin"

Ya karasa yana ficewa, ko takalmi babu a kafar shi, komawa Rayyan yayi ya zauna, kan shi ya dora jikin gadon dakin yana jin kamar zai mutu. Kwanan shi biyar yau rabon da ya busa hayaki, saboda yana son ya bari, baima yi tunanin akwai wahala sosai a barin shan tababa sai da yake son bari. Jakar shi da sai lokacin ya sauketa daga kafadar shi ya bude, jikin shi har rawa yake lokacin daya dauko kwalin tabar, a yanda yake jin shi zabi biyu yake da shi, ko tabar ko kwayoyin da yayi ma Bappa alkawarin zai sha su kan ka'ida a kowanne yanayi

"Abu daya zai iya sa ka koma Rayyan, dan Allah ka kula, kaga su da taba ne kawai matsalar ka yanzun"

Ya kan ga Bappa din ya dauki robar maganin na shi yana lekawa, kamar yana son kirga su batare daya fito da su gabaki daya ba, ba zai iya surutun maimaita magana daya ba saiya kyale shi. Shisa yanzun ya zabi tabar, kunnawa yayi kuwa, sai da yaja kara goma amman a banza, banda zafin da kirjin shi ya kara har tari yake kamar sabon shiga a shan sigarin. Ko dan yana kokawa da numfashin shine bai sani ba. Amman ya kasa samun sauki ko yaya. Yanda duk yaso ya hango Layla da Bilal ya kasa, idan wani ne daban zai iya lakaba mishi kowanne sigar laifi.

Zai iya cewa tursasa Layla yayi, zai iya cewa ya bata wani abune ta sha. Zai iya cewa komai, amman Bilal ba zaiyi abu daya daga cikin duka tunanin shi ba, gabaki daya Bilal bashi da wani dalili da zai iya tunawa nayin abinda yayi. Shisa baiga dalilin da zai saurari komai ba, iya abinda yaji ya ishe shi har karshen rayuwar shi. Kirjin shi zafi yake kamar ana hura wuta a ciki. Shisa ya sulale ya kwanta, babu abinda yake mishi yawo sai Bilal da Layla da ya kasa haskowa saboda tabbas zuciyar shi tarwatsewa zatayi. Mutum biyun da yafi yarda dasu akan kowa, mutum biyu da suka fi kowa kusanci a rayuwar shi.

Bilal yana fita a bakin kofa ya zauna, hawaye yake nema ko zai samu sauki amman ya rasa su yau

"Kaina kamar zai bude nake ji"

Muryar Jabir ta daki kunnuwan Bilal din, gefen shi ya samu shima ya zauna. Kowa da abinda yake ji, kowa da abinda yake tunani. Yanayi ne da babu wanda zai iya lallashin wani

"Na kasa yarda Hamma Rayyan zai mana haka, zuciyata ta kasa yarda..."

Numfashi Bilal yaja yana saukewa

"Bashi bane ba, ni ne"

Murmushi mai kunar rai Jabir yayi

"Idan kace kaine sai kake tunanin abin zai mana saukin dauka? Ka daina dan Allah Hamma, kabari muji da abu daya"

Jabir ya karasa yana mikewa, gara ko ruwa yaje ya dauka ya sha, koya watsama jikin shi. Koma me da zai dan saukaka mishi abinda yake ji, bin shi da kallo Bilal yayi, wato babu wanda yake son sauraren shi, haka girman yardar da sukayi mishi yake daman? Haka suke ganin ba zai taba cin amanar su ba. Kamar an dora dutse a kirjin shi haka yaji. Kafafuwan shi ya kara ja yana hade su da kirjin nashi ko zai ji dama-dama. Kan shi ya dora a jikin gwiwar shi yana sauke numfashi a hankali.

*

Zaune Ayya take akan kafet, sai yanzun komai yake tabata, yanzun girman abin yake yawo a kwanyarta. Layla da Rayyan, kaddarar su mai girma ce haka ashe? Duk yanda taso ta shiga tsakanin su alkalami ya gama rubutun shi akan su, sai kawai tunanin farraqun da tayi musu ya fado mata. Zuciyarta na wani irin tsalle ta koma cikin makoshinta, daman ance wani rabon har kisa yakeyi. Ko nasu ne yazo a haka? Raba sun da tayine da rabo a tsakanin su shisa ya kullu ta wannan gurbatanciyyar hanyar da take jin gara mata auren, komin yanda zuciyarta bata so zata koyi jure ganin su a tare kamar yanda take ganin Mami da Abbu.

Batason laifin ya zagayo ya dawo kanta, bataso saboda hakan na sakata jin kamar an tsomata a ruwan kankara. Zuciyarta ta tsinke daga inda take a kulle lokacin da taga Abbu a kasa, dan tana jin yanda zuciyar ke mata barazanar daina bugawa a mintunan da Abbu yayi bai tashi ba, yaran da take karewa da kominta, yaran da take jin zata iya komai dan nisanta su da juna, sune hanya irin wannan ta hada har suna neman kashe mata mijin da take so fiye da su, mijin da take kauna fiye da yanda take son kanta.

Yanzun ma kallon shi takeyi, yanda yake durkushe kan gwiwoyin shi yana sharar kwalla, zuciyarta kamar zata fito waje

"Dan Allah Ahmadi kayi hakuri, kar wani ciwon ya shigeka lokaci daya, bansan ya zanyi ba... Kayi hakuri dan Allah, komai zai zo da sauki"

Take fadi tana kokarin tarbe nata hawayen, tasan mijinta, ta san shi din mai rauni ne akan lamurran duniya. Sau nawa ita take nakuda amman take samun karfin halin bashi hakuri duk idan ciwo ya kwanta mata, kuka riris haka Ahmadi yakeyi duk idan ta fara nakuda, balle takan yi mai dogon zangon da sai an fara fidda rai da ita. Yana da raunin da batasan ya zata misalta a fahimta ba, shisa tasan da wahala ya iya daukar wannan kaddarar salin alin. Bata su Rayyan ko Layla takeyi ba yanzun, ta mijinta takeyi, ta tunanin halin da yake ciki da wanda zai shiga anan gaba.

Watakila da batayi katsalandan a cikin al'amarin ba da haka bata faru. Akwai abinda ya girmi tsanar da tayiwa Mami, akwai abinda zai iya tabata fiye da kaddarar da ta hada Mami da Abbu waje daya. Yanzun take gani, abubuwa ne masu tarin yawa suke mata yawo, lokuttan da tayi kokarin shiga hurumin da ba nata ba, canza lamurran da bata da iko a kan su. Zuciyarta da tsoro take bugawa, da kokwanto mai girman gaske kan makomar ayyukanta, kan inda kaddarar da tayi komai dan ta canza take son ta kai ta

"Idan mutuwa ta daukeni yanzun fa Maimuna? Ni ya zanyi? Me zan fadi akan amanar da ban rike da kyau ba? Ke da kanki kin gano mun matsala a rikon da nayiwa Layla, Allah da yake ganin komai fa?"

Sai Ayya taji kamar da ita yake, kamar ya watsa mata ruwan gishiri a ciwukan ta haka taji. Idan ita tata mutuwar ta dauketa kafin ta mike fa? Ya zatayi ita? Me zata fada akan katsalandan da tayi ma kaddara? Wanne hujjoji zata labe a bayan su? Hawayen da suka zubo mata masu zafi ne na gaske.

"Ba kai bane baka da abin fadi, nice. Wallahi nice ban da abinda zance, ya zan kalli yan uwana? Me zance musu ya faru?"

Mami da ta samu bakin magana tayi jero tambayoyin wani sabon tashin hankalin yana dirar mata, tunda suka shigo dakin ta jujjuya maganganun da Ayya ta fada mata. Idan tace ga dalili daya da ya saka ta barin Layla komawa Zaria zatayi karya. Bata san ya akayi ta yarda ta koma ba, a wannan halin ma ba zata iya dorawa kaddara ba, ba kuma ta son yin amfani da kalmar sakaci da take ta mata yawo. Gani tayi kamar akan tarbiyar duka yaran tana iya yinta. Yaune take gane baka taba yin iya yinka a tarbiya, saboda ba abu bane na lokaci daya, ba kuma abu bane iri daya.

Tarbiyar jiya takan banbanta da ta yau, saboda a duk rana halaye kan canza, yanayi mai girma ko karami, bakon yanayi kan samu wajen zama da dan adam. Shisa tarbiya zata zamana yau da kullum. In kayi jiya, yau ma ka kara, saika hada da addu'ar samun karfin yin fiye da ta yau a goben da zaka samu aronta.

"Nayi iya yi na"

Da iyaye da yawa kan fadi ba uzuri bane ba, ba kuma lallai ya zama hujja ba a gaban Allah, su yaran amana ne. Mutum ma ya baka amana kaci ya kake karewa, balle Allah da kan shi da ya zabeka a cikin mutane da dama ya baka amanar yara, ya baka aron lokaci, lafiya, da wadatar kula da su. Soyayyar Layla ta rufe mata ido

"Rikon maraya da wahala"

Shine kalaman da mutane kan furta a duk lokacin da tarbiyar marayun da suka dauki amanar kula dasu ta sami matsala. Kusan shine hujjar da suke kafawa, har wanda basa rike da maraya ma suna hasaso wahalar da take cikin rikon maraya. Yau ta canza mata tunani gabaki daya, babu wani riko na yaro da yake da sauki, babu kuma wani kalar yaro da baya bukatar tarbiya. Maraya ko mai iyaye, musamman maraya da tausayin rashin iyaye kan saka iyayen rikon sakaci kan tarbiyar shi. Bata san me yasa duk wannan tunanin yazo mata a kurarren lokaci ba, babu wanda zai mata uzuri kamar yanda ta kasa yiwa kanta yanzun

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ta furta a fili wani kukan na kwace mata. Ayya ma duk yanda take saka hannu tana share hawayenta basu daina zuba ba. Na Abbu sun tsaya daga idanuwan shi, a zuciyar shi suke zuba da ciwo na gaske, da kuma tunanin ta inda zai fara bullowa abinda yake faruwa dan bai sani ba, yaran shine karfin zuciyar shi, sune kuma raunin shi.

*

Iyaye
Iyayen riko
Jinjina da lokuttan da baccin ku baya tsawaita saboda tunanin tashin hankalin da yake tare da amanar da take karkashin kulawar ku
Fatan alkhairi da tarin sadaukarwar ku
Addu'ar karfin gwiwar ci gaba da kular da kuke
Ta yau tafi ta jiya
Ta gobe ta dara ta
Kuna kokari mun sani
Idan bamu yaba yau ba zamu yaba gobe, kar tunanin rashin jin dadin mu na kankanin lokaci ya rufe idanuwan ku da hango gaba
Rabbi ya tayaku, Ubangijin da ya baku amana ya tayaku rike ta.
Amin thumma amin

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Dec 30, 2020.

26

Ba idanuwan shi ba, har fuskar shi a kumbure take, yayi kuka har wani yaji-yaji idanuwan shi sukeyi. Duka sallolin shi yau a gida yayi su, abinda ya manta ranar karshe da yayi. Ko bashi da lafiya saiya fita masallaci, ruwa kam banda yanzun da Yaya Ayuba ya tsare shi bai shiga cikin shi ba. Duk yanda Ayya tayi fama da shi kuwa, kai kawai ya dinga girgiza mata, da yake tasan halin shi, ta kuma san bashida wani abokin shawara a wannan yanayin daya wuce Yaya Ayuba shisa ta kira mishi shi, dan tana tunanin ko bai san damuwar su ba, zai ma Abbun fada yasa shi yaci wani abu kar ciwo ya hadar mishi biyu.

Fuskar Yaya Ayuba yake kallo dan tun da ya gama magana Yaya Ayuban yayi shiru baice komai ba. Ji yake kamar Abbu ya watsa mishi ruwan kankara, ya rasa mamaki zaiyi, bacin rai ko tashin hankali. Saboda maganar yake ji tana amsawa a cikin kunnuwan shi har yanzun

"Layla ciki gareta, cikin Rayyan"

Lokutta da dama har ran shi yana mantawa Layla da Bilal ba daga jikin Abbu suka fito ba. Shisa maganar ta dake shi ba kadan ba, tana tuna mishi da cewar Layla yar amana ce a hannun Abbu, yar riko ce, marainiya gaba da baya. Baisan wacce irin kwamacala bace wannan da yanda zasu fara bullowa lamarin.

"Kayi shiru..."

Abbu ya fadi zuciyar shi na tafasa

"Hmm"

Yaya Ayuba ya iya furtawa yana sake gyara zaman shi, sosai maganar ke yawata mishi, amman duk yanda ta kai cikin kan shi sai yaji wani irin tashin hankali ya tsirga mishi

"Nayi shiru ne ina so kace mun abinda naji ba dai-dai bane Ahmadi"

Numfashi mai nauyi Abbu ya sauke, shima tun dazun yake jira, tunda ya dawo dakin shi yake so wani ya same shi yace mishi komai daya faru wasa ne, an gwada shine kawai kuma anga yanda yaran shine raunin shi, amman shiru. Duk dakika da zai wuce saiya kara tabbatar mishi da cewa komai da ya faru da gaske ne.

"Ban san ya zanyi ba, wallahi ban sani ba"

Cewar Abbu, Yaya Ayuba na jinjina mishi kai

"Zubar da cikin ba mafita bane ba"

Wani bugawa zuciyar Abbu tayi, aiko mafita ne ma bai hango za ayi wannan danyen aikin da shi ba, zunuban zasuyi mishi yawa. Laifukan zasuyi mishi nauyin dauka matuqa, yana jin kuma da muryar da Yaya Ayuba yayi magana, bamai kwari bace ba, kamar yana son Abbu ya duba yiwuwar lamarin ne. Kuma hakanne a zuciyar Yaya Ayuba, so yake ya duba in zai yiwu a zubar da cikin, zai saukaka musu abubuwa da yawa, musamman maganganu da surutun mutane idan zancen ya fita, amman a fuskar Abbu yaga yanda babu wannan tsarin a cikin jerin mashalar da yake nema.

"Ina tsoron fitar maganar nan Ahmadi, wallahi ina tsoron ta, mutane zasu fadi komai, zasuyi surutai kala-kala... Ba akan Layla kawai zasu dora ayar tambaya ba, gabaki daya Martabar ahalin Dikko sai ta sami tangarda..."

Kai Abbu ya dafe da duka hannayen shi, a tarihin ahalin su gabaki daya, makamancin wannan bai taba faruwa ba. Ya fahimci tsoron Yaya Ayuba, sai dai maganar mutane mai wucewa ce, tunda gabaki daya rayuwar ma ba mai dorewa bace ba, komai zaizo karshe wata rana. Surutun zai taba zuciyar shine idan akayi shi akan Layla, idan aka dora ayar tambaya kan rikon da suke mata, sosai zuciyar shi take ciwo yanzun da tunanin hakan. Mutane zasu ce bai riketa da kyau ba, zasu ce yayi sakaci da tarbiyar ta, Ayya ma bata fito fili tace haka ba, amman ta fada mishi akwai raunin shi a cikin abinda ya faru.

Idan duk tarin kaunar da take mishi bai hanata fadin abinda ta fada ba, bashi da tabbas akan abinda mutanen da suke jiran kuskuren shi zasu fada, cike da matsananci tsoro Abbu yake kallon Yaya Ayuba

"Ya zanyi? Me zanyi?"

Dan jim Yaya Ayuba yayi, a cikin abin duka baiga wani zabi mai sauki ba, in dai cikin yana nan basu da tabbas akan tsayawar maganar a tsakanin su kawai. Amman yanzun bayason fadin wani abu da zai kara firgici da fargabar dan uwan nashi, shisa ya zabi fadin

"Shi Rayyan din ya kamata ya aure ta"

Kai Abbu ya jinjina cikin aminta da maganar da Yaya Ayuba yayi. Wayar shi da take kan kujera ya dauka yana kiran Ayya

"Ki kira Rayyan sai kuzo tare"

Ya fadi tana dagawa, bai jira amsarta ba ya kashe. Mami ma kiranta yayi yace ta taho da Layla

"Gara su san da maganar"

Ya fadi yana kallon Yaya Ayuba da baice komai ba, bayason ya tuna ma Abbu ko da za'ayi auren sai bayan ta haihu dole. Sosai yake kara jinjina lamarin. Ayya ce ta fara shigowa dakin da sallama, duk da gefe ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login