Showing 6001 words to 9000 words out of 150281 words
numfashi karkiyi kusa dani..."
Murmushi mai ciwo Maryama tayi, wani bangare na zuciyarta takeji a gajiye da halayyar Maimunar
"Duk yanda bakyason ganina Ahmadi ya hadamu..."
Ido a bude Maimuna take kallonta
"Magana zaki fadamun? Dakina zaki shigo ki fadamun magana?"
Wani murmushin Maryama ta sakeyi da yasa Maimuna takeji kamar ta dauketa da mari, kafin ta kai hannu a cikin ta tana shafawa, haka kawai yau sai takejin tana son bakantawa Maimuna rai ko yayane
"In Allah ya yarda na dan yan watanni da nawa a hannuna"
Tana karasa maganar ta juya da shirin fita daga dakin, tanajin tsakin da Maimuna taja a fili
"Aikin banza aikin wofi, sai kin haifo ukku a tare zan san dai-dai kikejin kanki dani a cikin gidan nan"
Labulen Maryama ta daga tana ficewa daga dakin, Rayyan da yayi shiru a jikinta ta mayar kan bayanta tana daukar zani ta goyashi. Zatayi karya idan tace bata girgiza dajin cikine a jikin Maryama ba, duk da bata saka idanuwa akan lamurranta, ko yawu bataga ta tsartar ba. Ta rasa dalilin da yasa maganar take daga mata hankali haka, nan gefen gado ta zauna duniyar nayi mata shiru. Yara uku ba wasa bane, ko da ukkun Maryama ta ajiye a gidan Ahmadi ba masu shekaru kamar nata ba, tunda ko yanzun tana morar yaran nata da dauke mun wannan, mikon mun wancen. Amman batason kwan Ahmadi a cikin wata macen, batason ya daga idanuwan shi ya kalli wasu yara a cikin gidan nan banda nata.
Malamin Khadi ma ba haka ya buga mata kasa ba
"Ki kwantar da hankalinki, ba wani dadewa zatayi a gidan ba tunda ba wai son gaskiya Ahmadi yake mata ba, kuma yanzun haka sati mai zuwa aljanun da Malam ya aika can kasar Masar zasu dawo da hadin turaren da zai karya sihirin"
An kuma kawo mata turaren da ta yarfe gadonta da shi Ahmadi ya kwanta, duk wani magani da aka bata tayi amfani dashi tayi, amman ko ran girkinta Ahmadi ya leqa Maryama idan tayi magana saiya nuna rashin jin dadin shi
"Kema ina zuwa dubaki ranar nata girkin, me yasa abin magana baya miki wahala?"
Haka yace mata kwana uku da suka wuce, ganin washegari Maryaman zata karbi girki, kuma ya yini zir baya gidan, ta dauka ba zai kwasar mata mintina cikin lokacinta da sunan duba Maryama ba.
"Namiji kenan..."
Maimuna ta tsinci kanta da furtawa, ashe ciki Maryama take dashi amman ko da wasa Ahmadi bai furta mata zancen ba, sai yayi shiru abin shi, watakila da bataji a bakin Maryama ba sai ya nuna kanshine zata gani. Ahmadin ta da komai ya danganci rayuwar shi itace ta farkon sanin shi, da ita yakan shawarta sanar da Yaya Ayuba ko Nasiru wani lokacin. Rana daya wata ta shigo tsakiyar su da hakan
"Allah ya kwashe miki albarka Maryama"
Ta sake furtawa hawaye cike taf da idanuwanta, duk mazan duniya ta rasa wa zata kyalla idanuwa a kan shi sai Ahmadi.
**
Da yake yau girkin Maimuna ne, kai tsaye dakinta Ahmadi ya wuce bayan ya dawo sallar Isha'i. Ya siyo kankana, da kan shi ya tashi ya fita zuwa kitchen ya dauko faranti da wuka ya dawo ya zauna
"Ina Khalifa da Zubaida? Ba dai sunyi bacci ba"
Kai Maimuna ta girgiza mishi
"Yau ma gidan Yaya zasu kwana kenan"
Ahmadi ya furta da murmushi a fuskar shi kafin Maimuna ta sami damar fada mishi, yanajin dadin kusancin da makotakar su da Yayan shi ta wanzar tsakanin yaran su. Shi kanshi ma yanzun ma sai sukai karfe tara a waje da Yaya Ayuban suna hirar su wasu lokuttan. Hakan ba karamin dadi yake mishi ba, a lokuttan da Maimuna ta hada mishi zafi sai yaji zuciyar shi ta sanyaya idan sunyi hira da Yayan. Duk da bayason rage mutuncinta a idanuwan dan uwan nashi, shisa ko da wasa bai taba gwada fadar laifinta ba ballantana ya nemi shawara.
Duk fadan da zasuyi, sukan shirya, kuma yana yafe mata ko da bata nemi hakan ba, son da yake mata mai girmane. Yana gudun kar ya fadama Yaya Ayuba wani laifin Maimuna din, shi yazo ya yafe mata, Yaya Ayuban na kallonta da abin, sam ba zaiji dadi ba. Kankanar ya raba gida uku, ya dauki kashi daya ya saka a ledar, yanda yake jin wata irin gajiya jar a kasusuwan jikin shi yau zaiso ace zai iya baiwa Maimuna kankanar dan ta mikawa Maryama. Amman mitarta zatayi karshe harda rashin kunyar da ta koyi yi mishi tace ba zata kai ba. Shisa ya mike da kan shi yana kuwa cin sa'a Maryaman ta fito rike da buta a hannunta, murmushin nan nata tayi mishi
"Maryama..."
Ya furta cike da jin dadin ganinta, yana mika mata kankanar da ta ajiye butar hannunta tana dan tsugunna ta saka hannuwa biyu ta karba cike da girmamawa
"Allah ya saka da alkhairi. Sannu da kokari"
Murmushin shi Ahmadi ya kara fadadawa
"Ya zazzabin? Yayi sauki ko?"
Ya tambaya kamar dawowar shi bai dubata ba, kulawar shi daban take.Kai ta daga mishi cike da jin nauyi, tunda taga har wannan watan bata ga al'adarta ba, ta tabbatar da zarginta na cewa ciki take dauke dashi, ba wani canji takeji a jikinta ba, banda yawan kwadayin abinci mai manja, sai zazzabi da takan kwana dashi wani lokacin, amman lafiya kalau take jinta, wasu amaye amaye ko tashin zuciya duk Allah bai daura mata ba. Tana taso ta fadama Ahmadi zargin da takeyi amman nauyin hakan takeji sosai, banda yau da kishi yasa tayi ma Maimuna burga da cikin, ita kadai tasan da abinta.
"Sai da safe, kisha maganin da na siyo indai kinji ya dawo, da safe sai mu fita a dubaki asibitin wajen aikin mu"
Kai ta iya jinjina mishi
"Allah ya hutar da gajiya"
Ta furta tana juyawa daki, labule kawai ta daga ta ajiye ledar kankanar ta dawo ta dauki buta, kasala takeji yau sosai, dan tun taliyarta data dafa da manja ce da tayi saura taci da daren nan. Kan kunnenta aka kira isha'i tana kwance tana juye-juye a daki sai yanzun Allah yai mata fitowa. Alwala ta daura ta koma daki abinta. Ahmadi ma dakin Maimuna ya koma, yana karbar Rayyan daya saka babban yatsan shi a baki yana ta tsotsa
"Gaka da alamomin hakuri amman sai rikici ko?"
Ahmadi yai maganar kamar yaron zai fahimci me yake cewa, Maimuna da ta sakko kasan itama ta dauki wuka tana karasa gyara kankanar daya yanka, ta dauka tana mika mishi, hannun shi ya duba saboda yayi gaishe-gaishe da mutane
"Ban wanko hannu ba"
Dan kara matsawa tayi tana fara zare kwallayen jikin kankanar ta mika saitin bakin shi daya bude ta saka mishi a ciki, taunawa yayi yana jinjina kai
"Wai... Daman yace mun me kyau ce wallahi, dana sani kwallo biyu na siyo..."
Kallon shi Maimuna takeyi
"Da zaki? Naga batai ja ba sosai"
Ta karasa tana sakawa a bakinta itama, sake gyara wata tayi tana kara ba Ahmadi
"Aikam da zaki..."
Cewar Maimuna, kafin Rayyan daya fara mutsilniya a jikin Ahmadi yana kwakkwabe fuska yasata furta
"Wallahi karka dagamun hankali, na rasa inda ka kwaso rigima"
Dariya Ahmadi yayi
"Me kake nufi?"
Ta furta tana kallon shi, kai yake girgiza mata yana kawo bakin shi ganin ta gyara kankanar da ke hannunta, a nata bakin ta lunkuma
"Ka wanko hannuwanka ka sha da kanka, so kake kace ni ya biyo da alama"
Dariya yake sosai, dariyar da ta kwana biyu bata gani ba, gyara Rayyan yayi yana amfani da dayan hannun shi ya riko nata da take kokarin kwacewa tana dariya. Yayi kewar wannan rahar a tsakanin su, yayi kewar matar shi, kallonta yake da wani yanayi a fuskar shi
"Nayi kewar ki"
Cikin idanuwan shi ta kalla, ita kadai ce macen da take iya hada idanuwa dashi kai tsaye haka, har maza kance yana musu kwarjini, ko Maryama bata iya kallon shi haka. Maimuna kance
"Kai din nawa ne, nawa ne ni kadai Ahmadi"
Kuma ya yarda shi din nata ne, duk da bai kasance nata ita kadai ba kamar yanda taso, amman natan ne
"Kaji ka, abinda muna tare a gida daya ko da yaushe, me yasa kake magana kamar ka dade baka ganni ba?"
Numfashi mai nauyi ya sauke
"Dan Allah mu daina fada, ki daina mun rigima, mu koma zaman mu kamar da"
Murmushi tayi kawai, murmushin da yake ganin kamar yana da wata manufa data wuce nishadi. Haka suka kasance daren kamar satin amarcin su, har wajen biyun dare, da Maimuna lafe a jikin shi suna bacci. Da yake shi bamai nauyin bacci bane, kwakkwaran motsi ma yakan ji, cikin baccin yake jin kakarin aman da ya sashi bude idanuwa yana saurarawa, sosai yake jin ana kakarin, yaso zame Maimuna a hankali ba sai ta tashi ba dan ya fita ya duba, amman itama din ba nauyin baccin gareta ba
"Ina zaka je?"
Ta furta muryarta cike da bacci tana murza idanuwa
"Kamar Maryama ke amai, bakiji bane ba?"
Ya amsa kasa-kasa saboda dare, tsaki Maimuna taja
"Munafuncine kawai, dan Allah ka koma ka kwanta"
Da mamaki yake kokarin ganin idanuwanta saboda duhun da yake dakin. Rigar shi da yake tunanin tana ajiye wani waje kan gadon yake lalube har ya samota, kokarin sakawa yake a jikin shi Maimuna ta tashi zaune
"Fitar zakayi kenan?"
Ta bukata a harzuqe, hakafa kwanaki ta fito tana wannan kakare-kakaren, Ahmadi ya kwana zarya yana fita dubata. Shine yau daga dawowar shi dakinta zata sake bullo da wannan sanaben
"Kasan dai yau kwanana ne ko? Halin matane baka sani ba Ahmadi? Munafuncine ba wani abu ba"
Kai kawai ya girgiza yana sauka daga kan gadon
"Bari in dubata...."
Itama saukowa tayi, zuwa lokacin idanuwanta sun saba da duhun tana dan ganin shi, aikuwa hannu yaji ta riko mishi
"Babu inda zakaje fa, kanajin ma kamar ta koma daki. Wannan ai shiga hakki ne"
Fisge hannun shi Ahmadi yayi
"Me yake damunki ne wai? Ina tausayinki ya tafi? Ko ta tafi daki bazan duba yarinyar mutane bayan naji sarai amai tayi ba? Kinga Maimuna ki fita idona kafin in saba miki"
Ya karasa yana fara tafiya zuwa hanyar kofa, yanajin ta biyo shi, baibi takanta ba ya fice daga dakin, hasken farin wata ya haske tsakar gidan, ko takalma bai saka ba ya nufi bangaren Maryama, yana shiga ya sameta a zaune da fitilar kwai a dakin
"Maryama? Jikin ne?"
Kai ta girgiza mishi
"Aa wallahi. Amai ne kawai, inajin kankanar dana sha na kwanta ce ta juya mun ciki"
Kuma da gasken take, dan karatun littafin tarihin Annabi (SAW) Kamalalle takeyi bacci ya dauketa anan kasa inda ta saka filo, kawai farkawa tayi tana zufa, kafin taji wani amai ya taso mata, dakyar takai tsakar gida. Duk wani abu da yai saura a cikin nata kuwa saida ta fitar dashi, kuma garas take jinta banda yar galabaita da tayi. Ahmadi bai yarda da ita ba, tsugunnawa yayi yana saka hannu ya taba wuyanta ko da zazzabi, amman lafiya kalau yaji jikinta
"Sannu..."
Murmushi Maryama tayi
"Yawwa... Kaje ka kwanta, kaga da safe zaka fita, gara ka huce gajiya"
Kallonta yakeyi yana son tabbatar da lafiyarta
"Babu wani abu da yake miki ciwo dai ko?"
Kai ta jinjina mishi
"Kin tabbata? Ki fadamun dan Allah"
Murmushi takeyi sosai
"Allah babu inda yake mun ciwo...dan Allah kaje ka kwanta"
Numfashi Ahmadi ya sauke
"Shikenan, Allah ya kara lafiya, idan da wani abin dai kizo ki tasoni kinji ko? Allah ya tashe mu lafiya..."
Kai Maryama ta jinjina mishi, tana kara ganin dalilin da yasa kaf dangi kowa yakejin daman yar shi ce a gidan Ahmadi, ba zata gaji da godewa Allah da wannan damar da ta samu ba, har zai fita ya kara juyowa
"Ko in miko miki ruwa?"
Kai ta girgiza mishi tana nuna kwanon sha da yake a rufe
"Kagan shi nan na dibo fa tun dazun..."
Sannun dai ya sake yi mata kafin ya fita, ya gyara mata labulen dakyau saboda sauro. Kafin ya wuce inda ya samu Maimuna a bakin kofar dakinta tsaye
"Idan cin amana dai kasa a gaba babu inda zai kaika wallahi"
Ta karasa maganar ranta na suya, sai takejin kamar kamshin turaren da Maryama kan hayaqa a zuwan turaren wuta a jikin shi. Watakila wata sa'ar Malamin ta ya bata na fito da Ahmadi tsakiyar dare ta goga mishi wannan shu'umin turaren
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Dan girman Allah Maimuna ki saka ma ranki salama"
Ahmadi yai maganar cike da gajiya, yana mamakin kishi irin nata, wani lokacin yana jin daman ya hakura sun rayuwa su kadai kamar yanda taso, daya kaucewa duk wannan rigingimun
"Ta ina zan fara sakama raina salama bayan baka bani wannan zabin ba? Bance maka munafunci bane, kawai bata kaunar ganin na kebance dakai saita tsiri wani abin da zaka ha'ince ni"
Rabata yazo yi, gara ya wuce ya kwanta, inya tsaya biye mata zaiyi. Kamar ba ita bace tagama mishi alkawarin zasu zauna lafiya dazun nan. Amman sai ta tare kofar, wani irin kishine turnuke da zuciyarta, kamshin turaren Maryama da hancinta yake jiye mata sai take ganin kamar wani abin sukayi a yan mintina daya dauka a dakin nata da sukai mata nisan awanni, tare mishi hanya tayi
"Ka koma dakin nata mana, ka koma inda ka fito Ahmadi tunda haka kake so tun daga farko"
Ta karasa maganar wani irin kuka na kwace mata, yana da nashi dakin, kudine da sun shigo hannun shi akwai hidimar da zaiyi dasu, bai karasa bangaren ba, kuma duk da haka akwai wani dakin da zai iya zuwa ya kwanta a bangaren Maimuna, dakuna uku yayi mata, harda dakin girki, bangaren Maryama dakuna biyu itama da na girki, har lokacin akwai tankamemen fili da katanga kawai yaja mishi, banda filin tsakar gida, wannan sai a hankali zai dinga gine kayan shi tunda ba sauri yake yi ba. Hannun ta ya kama ya cire daga kofar yana shigewa cikin dakin da ta bishi.
"Wallahi Allah zai kamaka idan baka mana adalci"
Runtsa idanuwan shi yayi yana bude su hadi da sauke numfashi, kukan da takeyi na kara taba zuciyar shi
"Kamshin turarenta kakeyi fa, Ahmadi kamshin turarenta kakeyi ranar girkina. Wanne irin rashin adalcine wannan? Ko cikin da take dashi ne yasa kake wannan rawar kafar?"
Juyowa Ahmadi yayi yana kallon Maimunar da mamaki
"Ciki kuma?"
Hawaye ne suka kara tsiyayo mata
"Kana nufin kace mun baka sani ba?"
Mamaki yake kan mamaki
"Maryaman ce take da ciki?"
Ya kara tambaya, kai kawai Maimuna ta jinjina tana rabashi ta wuce kan gado ta kwanta. Ya dade a wajen yana jinjina maganar, ko dan ita Maimuna macece shisa ta gane Maryama na da ciki. Har ran shi kuma yaji dadi, yanzun yake fahimtar kwadayin manjan da ake ta mishi abinci da shi kwana biyu. Murmushi kawai yayi yana karasawa kan gadon. Kukan da Maimuna takeyi na kara dagula mishi lissafi, matsawa yayi daf da ita yana rikota jikin shi, tun tana kwacewa harta hakura
"Kamshin ta fa kakeyi"
Ta sake fadi tana zame jikinta, mikewa zaune yayi ya cire rigar ya cillar a kasa, yana kara komawa kan gadon ya rikota
"Kiyi hakuri Maimuna..."
Kuka takeyi sosai, ya rasa kalar kishin nan nata, abin kuma yafi karfin shi, addu'a yake mata na samun salama, amman kamar tunzura abin yake karayi. Ya jima yana lallashinta
"Karka kara zuwa wajenta in kama dakina"
Amsata yayi da to, dan a zauna lafiya, da duk wasu sharudda da taketa kafa mishi, sannan tadan ji nutsuwa, ko rubutun data diga mishi a ruwa dazun ya fara aiki, na kokarin kwato shi daga hannun Maryama ne, Allah ya fara taimakonta da alamu, zatayiwa Khadi maganar wannan turaren na Maryama dan bata yarda dashi ba. Da zata iya ma da kanta zata tambayi Ahmadi taje gidan Khadi din suje wajen Malam tare, amman tsoro takeji, ta gwada sau daya, ta kasa karasawa, sai take ganin kamar wani zai ganta, kamar za'aje a fadawa Ahmadi inda taje. Tafi gane duk yan kudaden da zata samu ta ba Khadi din, duk wani abu da za'a karbo mata a karbo. Da wannan tunanin a ranta bacci yayi awon gaba da ita.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:06 PM - 111: Nov 1, 2020
3
1986 Kano.
Yaron da yake rike a hannunta take kallo, yaran da duka satin shi biyar a duniya, wasu hawaye masu dumi na tarar mata cikin idanuwa. Amman zuwa yau tasan cewa kukan nan babu wani amfani da zai musu, kukan ba zai dawo mata da kaninta ba, ba zai canza kaddarar yaron da yake hannunta ta Maraici a satika biyu bayan haihuwar shi ba. Ba zatace tashin hankali bakonta bane ba, tasan shi a lokacin da ta raya Yayya, ta kuma san shi a lokacin da Ahmadi ya hadata da Maryama da ta zame mata Karfen kafa (Rufaida Omar). Tana kuma cikin shi har yanzun da Maryama ta ajiye kwai a cikin gidan Ahmadi, dan duk lokacin da zata ga giccinta ko kukan yaran nata Haris, sai taji wani abu ya tsirga mata.
Kwance take a daki tun bayan da tayi sallar asuba satika biyu kenan da suka wuce, haka kawai jikinta yai wani irin sanyi, ba shida alaka kuma da fadan da sukayi da Ahmadi tasani, kishinta a duk ranar da yake dakin Maryama daban da abinda takeji yanzun. Ko daya shigo ya dubata ma da safe inda yake bata kalla ba, ballantana ta amsa dukkan tambayoyin da yakeyi mata. Tana jin shi harya fice, dakyar ta iya tashi ta watsa ruwa, Rayyan ma tayi mishi wankan. Gobe ko jibi take da niyyar yaye shi, a karo na farko da har zatayi yaye batare da wani cikin ba.
Zatayi karya idan tace abin baya damunta, bata da kowa da yake fahimtar ta duk dangi, daga Gwaggo Bare sai Khadi. Yayyanta mata da suke ciki daya data gwada fada musu damuwar ta zancen su kusan kala dayane
"Kiyi hakuri da kaddarar ki Maimuna, kowa da kika gani ba son kishiyar nan yakeyi ba, ki cire wasu zarge-zarge daga ranki tunda mijin ki na son ki"
Shisa ta koyi kame bakinta a gabansu, son da suke ikirarin Ahmadi nayi matane dalilin komai, sunki fahimtar soyayyar nan tashi da yake matace yake rabawa da Maryama. Soyayyar da aka ga yana mata ce ta tsone idanuwan su Maryama harta shigo mata gidan miji. Yanzun kuma soyayyar da suka kasa nasarar dakushewa gabaki daya a zuciyar shice dalilin da take zargin suna son hana mata cigaba da ajiye yara a gidan Ahmadi. Ko da ta tambaye shi tana so taje gidan Gwaggo Bare a lokacin bai hanata ba, tana