Showing 105001 words to 108000 words out of 150281 words

Chapter 36 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3971

garin habba, sai Ayat as shifa da zai karanta kullum. Sosai ya tsinci kan shi da yiwa Baba godiya, bai barsu sun tafi ba sai da suka ci abincin dare tare da shi, yanda yake ta musu hira na saka Rayyan jin wani iri.

Saboda shine karo na farko da ya zauna da wani babba suna cin abinci. Ko Yaya Ayuba basu taba yin wannan da shi ba, da suka koma gida ma ya kalli Bappa da nufin yi mishi godiyar da baisan ta inda zai fara ba katse shi yayi

"Karka cemun ka gode, get better, shine godiya da zakayi mun, nasan depression Rayyan, na san duhun da yake cikin shi. Kayi kokari dan Allah, sai muje asibiti daga baya kan kwayoyin nan, yanzun ka fito daga duhun da kake ciki"

Kai ya jinjina, ranar kuwa yayi amfani da duka ruwan zam-zam din biyu kamar yanda Baba yace tunda a hanya suka tsaya suka siyi garin Habba din me kyau. Baiji komai ba saida ya kwanta, kamar ana zare mishi rai haka ya dinga ji, jikin shi ya dauki zafi sai kace yana cikin gidan biredi. Zuwa karfe sha daya na dare ya fara galabaita da tuqar amai da take taso mishi, aman daya dinga kwarawa kamar zai fitar da kayan cikin shi. Haka suka kwana, Bappa yaki yin bacci saboda yanata fama da Rayyan suje asibiti amman yaki. Da safe kasa fita masallaci yayi, sai a gida suka tsaya Bappa yaja musu sallah. Har wajen tara yana jin gabaki daya jikin shi ko karfin kirki babu.

Da Bappa ya taba shi ture mishi hannu yayi

"Rayyan kaji jikin ka kuwa? Tsaf zan soya kwai akan goshin ka, ka tashi muje asibiti"

Banza yayi ya kyale shi, amman halin da yake ciki yasa Bappa ya kira Baba yana fada mishi

"Alhamdulillah, abinda nake tunani ne ya tabbata, ka barshi, aman shine saukin shi. Yaci gaba da sha, har Allah ya taimaka ya fitar da abinda yayi karfi a jikin shi"

Cike da tsoro Bappa yace

"Sihiri ne ko Baba?"

Murmushi kawai Baba yayi ta dayan bangaren

"Allah ya bashi lafiya. Allah ya kare mana imanin mu ya nisanta mu da dukkan abin ki"

Numfashi Bappa ya sauke, yana amsawa da

"Amin"

Kafin yayiwa Baba sallamar. Kwanakin da suka biyo bayan ranar ba masu sauki bane ba, dan duk yanda Rayyan din yaki saida Bappa ya kira likita cikin gida aka daura mishi karin ruwa. Kamar ana zuko wani abu a cikin jijiyoyin da suke jikin shi suna hade da zuciyar shi haka yake ji. Bai taba ciwo irin wannan ba, cikin kwanaki bakwai kamar bashi ba, duk ya fita hayyacin shi, wajen aiki ma randa yaje ca sukayi ya koma ya kara hutawa na sati daya sannan. Yayi wata irin ramewa. Baba sai da ya kara aiko mishi da wasu robobin biyu, yace karya daina sha saiya sha sau biyu yaga baiyi amai a cikin kwanakin ba tukunna.

Ba abinda ya dinga bama Rayyan mamaki sai baccin da yake kusan kwana ya wuni yanayi, saiya alakanta hakan da rashin karfin da bashi da shi. Amman a cikin sati na biyu ranar ya tashi da safe yaji shi kamar yana lilo saman iska, kan shi wasai, sai kace an kwashe wani datti daya jima yana taruwa a cikin kan nashi haka yake ji. Da sukayi waya da Layla dariya yaga yanayi, zuciyar shi na dokawa da wani bakon yanayi da bai taba sani ba, kwana wajen hudu yana tashi a tsorace, saboda gani yake kamar yanayin ba mai zama bane ba.

Sam baiwa Bappa gaddama ba sukaje asibiti, wasu magungunan aka dora shi a kai. Yana sha kuma, yana samun bacci, ashe haka baccin dare yake tattare da Rahma, duk da ba duka daren bane tunda ya samu sauki, amman zaiyi bacci wajen sha biyu har safe, sai yake jin shi duk wani sakayau. Ga Bappa baya barin shi ya zauna shi kadai, kullum suna yawon zaga gari, har gidan ball yake jan shi suje kallo, duk da yakan dawo da ciwon kai. Yanzun yake sanin halayen shi akwai wanda basu da alaka da komai, sam bayason mutane, wannan halin shine. Baba bai daina aiko mishi da robobin zam zam ba, a cewar Baba har yanzun yana bukatar su.

Saboda hutun rashin lafiya da suka bashi shisa basu zo Kano ba, sai yau, Bappa ya sauke shi ya wuce, yanata sauri shisa bai karaso da shi ba, yace zaiyi zuwa na musamman idan ya tashi. Da wata irin kewar Layla da Bilal din ya sauka garin Kano, da ita kuma ya shigo gidan har yake tsaye inda yake yana juya kasancewa waje daya da Abbu batare da yaji kamar iskar wajen tayi mishi kadan ba. Yana kuma jin zuciyar shi sakat

"Ka fada musu cikin jikin Layla ba naka bane ba"

Muryar Ayya ta katse mishi tunanin da yakeyi tana dawo da hankalin shi kanta cike da son fahimtar inda zancen ta ya dosa...

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Dec 26, 2020.

25

Maganganun Ayya ne suke mishi yawo, kafin ya zare hannun shi daga cikin nata, yana kallon Layla da jin an kira sunan shi ya sakata bude fuskarta, idanuwanta har sun kumbura saboda kukan da takeyi. Tana jin su, bata san kalar tunanin da ya kamata tayi ba, duniyar duka take ji ta hade mata waje daya. Ta rasa da wanne zata fara, tashin hankalin abinda yake faruwa da ita karon kanta, halin da su Mami suke ciki, Abbu da take ganin ba zuciyar shi kawai ta taba ba, harda Martabar shi, ko kuwa Rayyan da take ji suna lakabama laifin da ba nashi ba?

Ko yanzun da yazo yake kallon ta, yake neman amsa a cikin idanuwanta, a hankali take ganin yanda komai yake shirin canzawa a tsakanin su. Duk a cikin abinda yake faruwa shi tafi ji, shi tafi tunani, in zai rike hannunta, ya kasance da ita, hargitsin zai mata sauki, amman tana ganin yanda wasu katangu suke fara ginuwa a tsakanin su, wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata, tana runtsa idanuwanta ta bude su a kan Rayyan. Dan kallon ta yakeyi, wannan karin ta cikin idanuwanta yake son tabbatar da gaskiyar abinda kunnuwan shi suka jiye mishi kafin yasan matsayin kalaman a zuciyar shi, kamar ciki yaji ance tana da shi, kamar ji yayi ana kiran cikin da yake jikinta da nashi.

"Hamma..."

Labbanta suka motsa, muryarta sam bata fito ba, amman shi yajita a cikin kan shi, yaji ta a cikin zuciyar shi inda wani abu yake bubbudewa da ciwo na gaske

"Rayyan..."

Yaji muryar Ayya da take kallon shi cikin tashin hankali, saboda shirun shi yana nufin abubuwa da dama, shirun shi yana nufin daukar laifin da ake so a makala mishi, bata san lokacin da ta kama hannun shi tana jijjigashi ba

"Kana da matsala kala-kala tun tasowar ka. Rayyan ka bude bakin ka kace mun ba kayi ba, ka fada kowa yaji wannan matsalar ba taka bace ba"

Wani abu yake ji tokare da makoshin shi, amman baisan ta yanda zaiyi ya hadiye shi ba, bakin shi ya kafe kamar ya kwana biyu bai sha ruwa ba. Baisan yanda akayi jikin shi baya rawa ba, saboda gabaki daya zuciyar shi jijjiga takeyi tana rarrabuwa sashi-sashi.

"Ciki aka ce... Rayyan ciki. Ciki ake magana a kai ba abu na wasa ba"

Ayya ta karasa muryarta na karyewa, idanuwanta sun fara cikowa da hawaye saboda tashin hankali. Dan daya fito daga cikinta ba zaiyi wannan barnar ba

"Rayyan"

Ta kira cike da roko wannan karin, hawayenta na zubowa, kallonta yayi cikin ido, abinda yakan dade baiyi ba, kafin ya kama hannunta da yake damke da nashi ya sauke. Kan Layla ya sake sauke idanuwan shi da suke cike da tarin tambayoyin da baisan ta inda zai fara yi mata su ba, guda daya yake so tayi duk yanda zatayi ta amsa mishi duk da bai furta a fili ba, da dukkan muryar zuciyar shi yake tambayar

"Ciki gare ki? Cikine a jikin shi?"

Bata san ya akayi ba, amman ta fahimci neman tabbaci Rayyan yakeyi, kai ta dan daga mishi a hankali, wasu hawaye na zubo mata. Hawayen da suka hana ta fara ganin wani yanayi da bata da kalmar fassara shi cikin idanuwan Rayyan din, kafin ya dauke idanuwan shi daga cikin nata. Numfashi yake fitarwa a hankali a hankali saboda yanda yake ji kamar baya shiga inda ya kamata, kamar yau akwai abubuwan da suke cunkushe mishi hanyar shiga da ficen iska. Juyawa yayi da nufin barin wajen ko zai samu maganar ta natsa mishi da kyau, ko zai tattara hankalin shi wajen gane girman da maganar take da shi, karfin da yake tare da maganganun da yake barazana da dan zaman lafiyar daya fara samu a duniyar shi.

"Rayyan..."

Wannan karin muryar Abbu ta tsayar da shi cak, tana kuma saka shi juyowa ya kalli Abbu din ido cikin ido

"Ka ce baka taba mun amana ta ba, ka bude bakin ka kayi mun magana"

Wani numfashi Rayyan yaja a wahalce, bashi bane ba, ko zai taba Layla, ba zai taba zama ta wannan fannin ba. Ko kwayoyi yasha ba zai taba ta haka ba. Saboda tunanin abinda yake faruwa yanzun, saboda yanda mutanen da suka fi komai muhimmanci a rayuwarta ne zasu fara dora ayar tambaya akan ta, kafin mutanen da basu taba bada gudummuwar komai wajen tarbiya, ci, sha da sutturarta ba su fara zagayawa da maganganu kala-kala akanta, akan Martabar gidan su. Shisa bayason mutane, wannan halin shine, ko kadan baya son su. Mutanen da yake so basu da yawa, saboda matsalolin da suke tattare da mutane yawa gare su.

"Bani bane Abbu"

Ya furta kalaman cikin kan shi, dama ta farko daya samu tsaye a gaban Abbu, yayi magana da shi kamar yanda kowanne da yake magana da mahaifin shi tazo mishi a haggunce. Martabar Layla zata fi karuwa idan suna tunanin cikin jikinta nashi ne, ba za'a fara mata dukan da yaga ana yiwa wata a film din Hausa da Bilal yake kallo wani lokaci ba, kan sai ta fadi uban cikin da yake jikinta. Idan sun karbi abin, tashin hankalin su ya sauka zasuji a bakin Layla, shikam yanzun ba zasuji komai banda shiru ba. Numfashin daya sauke mai nauyine, kafin yakai hannu yana dan murza goshin shi, kan shi kamar zai tarwatse haka yake jin shi.

"Rayyan rokon ka nakeyi..."

Cewar Abbu, kirjin shi zafi yakeyi, zuciyar shi ciwo takeyi har ko ina na jikin shi yana amsawa. Gara ace wani ne a waje, wanda zai iya shari'a dashi daga filin duniya har zuwa na lahira inda ba zai taba yafe mishi wannan laifin ba. Idan ya zaman Rayyan ne baisan yanda zaiyi ba, bai sani ba kam. Amman tabbas komai zai iya faruwa

"Idan kaci gaba dayin shiru zan dauka da gaske laifin naka ne"

Shirun dai Rayyan ya sakeyi, yana sadda kan shi kasa, kirjin shi Abbu ya dafe, ya dauka hawaye sun mishi kaura a shekarun shi, sai yanzun da yake jin taruwar su a cikin idanuwan shi

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ya furta yana dafe fuskar shi da duka hannuwan shi, wani irin numfashi yake ja yana fitarwa kafin ya bude fuskar shi ya kalli Rayyan da yake tsaye a gaban shi, daga yanzun zuwa wani lokaci da bai hango shi nan kusa ba idan yana ganin Rayyan din zai mishi baki, sosai yake danna zuciyar shi da kalaman da take son furtawa

"Ka fitar mun daga gida Rayyan, ka tafi kawai"

Ba Rayyan bane kawai ya dago da kai yana kallon Abbu, hatta da Mami sai da ta dago. Ayya ma kallon shi takeyi tana son jin ya sake furta kalaman ko zata yarda da taji su daga farko, Rayyan daya fara magana ne ya sata kallon shi

"Ka nuna mun wani uban, Abbu a yanzun nan idan ka nuna mun wani uban ko jakar da take kafadata ba zan sauke ba, zan fita in bar maka gidan ka, zanyi nisa da gidan ka, zanyi nisan da ko nemana kayi ba zaka ganni ba..."

Numfashi Abbu ya sauke yana kallon kasa, kafin ya sake dagowa, baisan lokacin da ya daga hannu ya dauke Rayyan da mari ba, karar na amsawa a ko ina na wajen kafin Bilal ya motsa kafafuwan shi yana karasawa ya shiga tsakanin Abbu da Rayyan din, dan harya sake daga hannu zai kara dauke Rayyan da yake kallon shi ido cikin ido har lokacin da mari

"Abbu... Dan Allah Abbu"

Bilal ya fadi a wahalce, wani nishin wahala na kwace mishi, tunda suka fara magana yake so kasar wajen ta bude ya fada ciki ta rufe da shi, rufewa na har abada ko zai gujema fuskantar kowa da kowa. Amman yaki faruwa, tunda suka kira sunan Rayyan komai ya karasa kwance mishi, kalaman Abbu suke mishi yawo har lokacin, babu tunanin komai a ran shi sai na yanda idan mutuwa ba tazo mishi ba, tabbas karshen zaman shi tare da su yazo. Idan Abbu yace Rayyan ya fita yabar mishi gida a haka, tabbas shi zai saka a rakashi waje ne.

A tsorace yake, tsoron da ya saka shi tunanin akwai sauki mai girman gaske a tattare da mutuwa, wani tsoron na daban yana kara bugar shi, saboda hango kwanciyar kabarin shi da yake cike da kokwanto da yayi, a da laifukan shi yana jin tsakanin shi da Allah ne, yanajin suna da sauki mai girma saboda Allah Mai Rahma ne. Amman yanzun laifin shi nacin amana ne, kuma bayason fara tunanin makomar masu cin amana. Bayaso sam, gabaki daya jin shi yakeyi a gigice kamar zai shide

"Matsa mun Bilal..."

Abbu yayi maganar da wani yanayi da Bilal bai taba ganin shi a ciki ba, kai Bilal yake girgizawa

"Abbu ni ne, ni ne Abbu"

Ya furta a razane, saboda ba zai tuna ranar karshe daya ga Abbu ya dagama wani daga cikin su hannu ba, amman a idanuwan shi yake ganin inda abun duka a kusa da shi yau zai saka shi ya jibgi Rayyan din, ba zai kara wani laifi ba, bayan cin amana ba zai shiga tsakanin mahaifi da dan shi ba, ba zai iya kara daukar wani tashin hankalin ba, kamar zai fashe da kuka yake kara fadin

"Ni ne Abbu"

Kai Ayya ya dafe, hawaye masu zafi na zubo mata, Mami ta kalla, duk ita ta shigo rayuwar su, ta shigo musu da Layla har suka zo inda suke din nan yanzun. Bilal take kallo da gabaki daya ya rikice, tun tasowar su, ko Rayyan zata daka haka yake shiga tsakani, ko da zata rufe ido taci gaba da kai duka ba zai matsa ba, zai amfani da jikin shi ya kare na Rayyan din yana kuka yana bata hakuri. Akwai tarin lokutta da tasan Rayyan ne yayi laifi amman Bilal din zai dauka. Shine yake faruwa a gaban idanuwanta yau, amman ba zata bar shi ba, ba zata kyale shi daukar wannan laifin ba

"Karya yake, ya saba Ahmadi, ya saba daukar laifin Rayyan"

Ayya ta karasa da wani yanayi, kanta sarawa yake ta kowanne bangare, tana tunanin rashin amfani na Malaman duk da tayita asarar kudinta a kansu, duban su da bugun kasar su ya tashi a banza da suka kasa hango mata wannan tashin hankalin, da basu fada mata ko da bata iya kauce mishi ba tasan yanda zata karbe shi tunda wuri, hawan jinin da bata da shine yake son kamata lokaci daya

"Bilal ka matsa kafin in wanke ka da mari kaima"

Cewar Abbu, jiri yake gani sosai zuwa yanzun, amman so yake Bilal ya matsa ya kara ganin Rayyan

"Abbu wallahi ni ne"

Wani murmushi mai ciwo Abbu yayi

"Karyar ce kake bi da rantsuwa Bilal? So kake in yarda da kai haka?"

Kan shi Bilal ya sadda kasa yana rasa inda zai saka ran shi yaji sauki-sauki. Komai ya cunkushe mishi, yana ganin Abbu ya juya ya fara takawa, sai dai ko taku biyu baiyi ba ya yanke jiki ya fadi. Kan shi sukayi gabaki dayan su cikin karaji banda Rayyan da Layla, shi yana nan tsaye inda yake, yana rasa kalar tunanin da yakeyi ko ya kamata yayi. Layla kuma tashin hankali ne ya sake dirar mata, shikenan ta kashe mutum daya da ya karbeta a lokacin da kowa yakita, mutumin da bai taba sakawa taji maraicin da take tare da shi ba. Kuskure daya ya canza mata komai.

Bilal da Jabir ne suka kama shi suna yin dadin Ayya da shi, dan tunanin asibiti baizo musu ba. Jabir ne yayi tunanin samo ruwa ya shafama Abbu a fuska kafin ya bude idanuwan shi yana kokarin mikewa

"Abbu faduwa kayi fa, ka kwanta dan Allah"

Jabir yayi maganar kamar zai saka kuka, baisan tashin hankali ba duk tsayin rayuwar shi sai yau. Ko abokai ne in ka nemi daga mishi hankali zaka neme shi ka rasa ne. Sam baya zama, shisa abin yake tabashi sosai da sosai.

"Idan na kwanta ba zai canza komai ba Jabir, kabar ni in tashi in fuskanci matsalar nan"

Mikewa Bilal yayi, ba zai iya dauka ba, zuciyar shi ba zata iya dauka ba sam. Ficewa yayi daga dakin zuwa nasu. Rayyan kuwa yana inda suka bar shi, Layla yake kallo har su Mami suka bi bayan su Bilal suna barin su kadai a wajen

"Hamma"

Layla ta kira tana son ya taimaka mata, ko da zai zama lokaci na karshe a tsakanin su, ya taimaka ya fahimce ta, saboda tasan babu wanda zai taba fahimtarta. Yanzun a kan idonta taga rashin yarda a idanuwan kowa kan cewa cikin na Bilal ne, kowa yaki yarda, tana kuma ganin katanagar da Rayyan yake ginawa a tsakanin su, idan ta bude bakinta, idan ta fada musu cikin na Bilal ne duka zasu yarda, dole zasu yarda. Amman idan suka ce ta auri Bilal fa? Tunanin kawai ya girgiza duka ilahirin zuciyarta balle ya kasance ya tabbata, da gaske mutuwa zatayi idan ta rasa Rayyan.

Watakila tana da sauran rabon zama da Rayyan shisa yaki musa cikin jikinta ba nashi bane ba, so take ya bude bakin shi yayi mata magana

"Hamma"

Ta sake kira, dafe kan fuskar shi Rayyan yayi da hannuwan shi duka biyun, yakai mintina biyu a haka kafin ya bude su akanta, a karo na farko yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login