Showing 33001 words to 36000 words out of 150281 words
shine Bilal ya samu gurbin karatu a jami'ar, idan suna tare da Rayyan din acan zaifi dadewa baizo gida ba.
Tana kara gayawa kanta harda rashin Bilal a kusa dashi yasa ya kasa zama waje daya. To Bilal din ya fada mata cewa sunayen farko ya fito babu nashi a ciki, idan Allah ya taimaka sai jeri na biyu da suke tsammani a cikin satin tukunna. Da yake sunyi hutun islamiyya duk suna gida ranar, yaran nata ne suka rage mata tunani, dan suna zaune sunata hira harda Bilal, sai dariya suke. Daga bakin kofa ma zaka iya jiyo rakadin su, Rayyan ya shiga da sallama, yana saka wani irin shiru biyo bayan amsa sallamar tashi da sukayi, kamar basu bane suke ta hira yan dakika da suka wuce.
Kamar yanda baisan taya zai fara hira dasu ba, haka suma basu san abinda ya kamata suyi a gaban shi ba. Duk kuwa tarin kaunar da suke mishi, kowa gudun yin kwakkwaran motsi yakeyi kar su bashi dalilin da zaisa ya juya, dan yana tsaye yaki karasawa
"Ka shigo mana to, kayi tsaye kamar dan sanda"
Cewar Bilal, yana saka har Zubaida bin shi da kallo, dan Bilal ne kadai yake da kwarin gwiwar yi ma Rayyan din magana haka, ita ma sai tayi sa'a yake gaishe da ita. Yana iya wucewa ta wuce, zata kuma yi karya idan tace hakan baya bakanta mata rai sosai. Tana shekararta ta karshe a jami'ar Bayero inda take karantar Mass Communication. Mijin da zata aura a makarantar suka hadu lokacin tana shekararta ta biyu, yanzun kuma yana aiki da gidan jaridar Rana. Dan kusan duk bangaren karatun su daya da ita, kawai shi din journalist ne. Wani lokacin har mamaki Zubaida takeyi na yanda ko kadan Rayyan bai damu da su ba.
Tasan kowa abin nacin ran shi, ba dai sa tattaunawa ne, aikam karasawa Rayyan din yayi ya zauna kan hannun kujerar da Bilal yake, a hankali Bilal din yaci gaba da jansu da hira har kowa ya saki jiki, amman da ido Rayyan yake binsu, yau dai yayi kokari tunda har saida aka kira sallar Magriba tukunna duk suka tashi. Ayya taji dadin shigar tashi, ta manta ranar karshe daya zauna ya hada mintina sha biyar cikakku a cikin dakin nata. Duka abinda basu sani ba shine maganar da Bilal yayi mishi
"Kai kasan ko na zauna ni bansan me zance ba, ku bakwa gajiya da surutu"
Rayyan ya fada a takura
"Ko bakace komai ba idan ka zauna Ayya zataji dadi, saboda Allah ko tausayinta bakaji? Uwa uwa ce (Batul Mamman) Rayyan. Ace sai dai Ayya tazo inda kake, kai ba zakaje ka gaisheta ba idan ba yunwa ce ta koraka ba... Babu wanda zai fada maka baka kyautawa, nima dana fada maka ba lallai ka saurara ba, tunda kai babu wanda ya isa ya saka a hanya"
Bai amsa Bilal din ba harya fice daga dakin. Da rana ya aiki Layla ta siyo mishi batirin tocila din shi da yake amfani da ita a makaranta, yasan zai iya siya idan yaje, kawai yana son dalilin da zai ganta ne, tunda yasan washegari zai koma makaranta, duk ranar aiken rashin dalili yake kirkira yana mata, sanyinta ne yake mishi wani iri, kamar ba Layla ba yau, harar da takan watsa mishi duk idan tagaji ba taso ta fada mishi tana kuma tunanin baya ganinta yau babu.
Sosai ya dinga sakata kananun abubuwa amman sai yaganta da sanyi-sanyi, shisa da ta kawo mishi battery din yace
"Menene? Me yake damun ki?"
Kallon shi tayi da idanuwanta, itama ba zatace ga asalin abinda yake damunta ba, kamar zatayi zazzabi take ji, ga wani irin ciwo da takeji kasan cikinta nayi, inya tsira mata har cikin bayanta da cinyoyinta da suka rike takeji
"Kawai bana jin dadine"
Ta furta a sanyaye
"Shine baki fadamun ba?"
Cikin ido ta sake kallon shi, yanajin dadin ganin masifar da take cike da idanuwan nata
"Yanzun nake ganin Layla"
Ya furta a ran shi
"Idan na fada maka zai hanaka aikena ne?"
Numfashi ya sauke, a ranaku da ba yau ba zai bige bakinta, amman a kasan maganar da tayi yana ganin da gaske bata da lafiya.
"Kai me yake damun ka?"
Ta tambaya saboda yanda ya tattare girar shi yau ya wuce misali, da alama akwai abinda yake ran shi, kafadu yadan daga mata
"'Hamma..."
Ta kira a kagauce, inda yasan yanda takeji zai fada mata in yayi niyya koya sallameta taje ta kwanta
"Ki barni ni dalla can. Bilal ne wai ina zama a dakin Ayya"
Dariya tadan yi
"To ka zauna mana, abune me kyau ai"
Da alamun neman taimako ya kalleta wannan karin
"Labari sukeyi in sun zauna. Bansan me zance ba"
Numfashi ta sauke
"Ka zauna kawai, ko baka ce komai ba ka zauna"
Dan jim yayi kafin ya jinjina kai a hankali
"In tafi shikenan?"
Kallonta yayi, tayi rau-rau da idanuwa
"Allah Hamma cikina na ciwo"
Kallon nata dai yaci gaba dayi, a hankali ta dan daga kafarta da ta gaji da tsayuwa tana sake ajiyeta, ta daga dayar ma, yana kallon ta, so takeyi ta tafi
"Hamma mana"
Layla ta sake fadi kamar zatayi kuka
"Haka kawai duk inda nayi kina bina, yaune zaki dameni da kina son tafiya?"
Azabar ciwo ta fara damunta, da gaske yau batasan kalar ciwon nan daya addabeta ba. Ganin da yayi idanuwanta na tara hawaye yasa shi fadin
"Ki kwanta in kinje, kowa ya aike ki kice nace ki kwanta. Idan na hadu dake saina dakeki"
Juyawa tayi kawai ta fice. Bilal da Layla suka saka shi zuwa dakin Ayya ya zauna yau. Suna kuma dawowa sallar Magriba ba bai koma ba. Nan daki yayi zaman shi, har akayi isha'i ya sake fita, da suka dawo Bilal ne yaje ya dauko musu abinci a bangaren Ayya ya dawo, sukaci, zanen da Bilal din yaga yanayi yasa shi ficewa ya koma dakin Ayya, dan yasan ko maganar duniya zaiyi Bilal din bashi da lokacin shi. Sanda ya dawo ma kwanciya yayi yana barin shi kan takarda. Alamar bacci ma Rayyan bayaji, abinda yake kanshi yake son fitarwa, abinda yayi sati manne a kwakwalwar shi.
Hoton Layla, ba wasu kaya bane a jikinta ranar, uniform din islamiyya ne da hijabin take ruwan kasa mai cizawa, tana tsaye nesa da gida kadan ita da Farida, da littafi a hannun Farida din da alama suna duba wani abune, gefen fuskarta kawai yagani, sai yayi mishi kyau sosai, yanayin ta a hakan, da ta kare mishi idanuwanta. Tun ranar hoton yake manne a cikin kanshi, kamar yana son ya fito da shi fili kafin ya bace, ya kyale shine da nufin idanuwanta su tarwatsa mishi hoton, sai dai a satin ta saka idanuwan shi cikin nata yafi a kirga, amman tana barin wajen sai hoton ya dawo mishi, shisa yau yake son fito da shi, yana da tabbacin ba zai gamu a ranar ba, amman zak fito da taswirar, sai yayi sauran aikin ko idan ya koma ne. Ko ba komai zai sami abinyi kafin kewarta ta danne shi.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Nov 17, 2020
09
Shi sam baiga dalilin da Haris zaice tare zasu koma makaranta ba. Ya fahimci zumudin da Bilal yakeyi, duk da baiji shi ba sam a tafiyar farko da zaiyi. Yanzun ne yake jin dadi da Bilal din zai kasance makaranta daya da shi. Amman yana da tabbacin surutun da zasu dingayi shi da Haris kafin su sauka Zaria kan shi yayi ciwo. Shisa ya zabi yau din a matsayin ranar da zai koma, kawai saboda Haris yace zaiyi gaba, amman ya nace ya zauna jiran shi.
Yau ma tunda ya tashi yake jan jiki, duk da hakan na da alaka da hankalin shi gabaki daya da yake kan Layla. Sam baiji motsin ta ba, ya dade a bakin kofa da safe yana ganin shige da ficen yaran gidan har suka tafi makaranta, amman bai ganta ba, yaso ya tambayi wani ko jikin ne yasa bata fito ba, amman gaisuwar da suka dinga mishi ce tasa bakin shi yin nauyi saboda surutun har ya fara hawar mishi kai. Haka ya gaji ya koma, ga kasa da baisan waya shigo da ita dakin ba, sai da ya kara sharewa sau biyu tukunna yaji ya taka tsakar dakin da ya sha tayal ya mishi dai-dai.
"Kai fa muke jira... Kana ganin har biyu ta wuce, dare kake so muyi?"
Bilal ya fadi yana shigowa dakin, kafafuwan shi Rayyan ya bi da kallo
"Kai ka shigo da kasa, ban san sau nawa zance ka dinga cire takalminka a bakin kofa ba, har takalmi na siyo na yawo a daki, amman baka amfani da naka"
Numfashi Bilal ya sauke, yana zare takalman daga kafar shi, ya saka hannu ya dauka yana fitar dasu bakin kofa, kwana biyu da Rayyan din baya nan wannan ka'idojin na shi duk ya manta su, karasawa yayi ya zauna gefen gado
"Yanzun ba zaka wanke hannun ka ba, ka taba takalmi haka zaka kama kofi, yasa na daina hada kofuna da kai"
Numfashi mai nauyi Bilal yaja yana fitar wa
"Hamma ka sama mun lafiya, hannun ka ne ko nawa? Maganar da ake so kayi ba ita zakayi ba, sai kace bakin ka ya gaji da magana, amman baya taba gajiyawa kan tsegumi"
Duk surutun shi sama-sama Rayyan din yake ji, hankalin shi yayi nisa wajen tunanin ina da ina takalman Bilal din suka taka, wacce kazantar ya kwaso da su ya kuma saka hannu ya damuka, wannan matsalar shi ce kamar yanda ya fada, amman Rayyan din bayason yaje ya taba mishi wani abu da wannan hannun nashi daya dauki takalma. Ya dauka surutu da mutane ne abinda yafi tsana a zamantakewa, sai da ya fara girma yagane kazanta ce abinda yafi tsana, tsantsanin da yake da shi ba karami bane ba.
Lokutta da dama baka raba shi da karance-karance kan kwayoyin cutukan da suke rayuwa da mutane a mu'amalar yau da kullum. Yana son lafiyar shi, yana bala'in ririta lafiyar shi, tana jerin abu na farko da yake roka a dukkan addu'ar shi, shisa yake kara taka tsantsan idan ya tsare da iyawar shi, Allah saiya taimake shi. Dan ya kula mutane basu da wani buri daya wuce su ja mishi amai da gudawa. Haka shekaranjiya da suka dawo daga masallaci Bilal ya siyi wani rake, kuma har yake mishi tayi, tun suna hanya ya fara gabza kamar bashi da hankali.
"Ka tashi dan Allah ka shirya mu tafi"
Bilal din ya fadi yaba dorawa da
"Hamma..."
Ganin da yayi kamar Rayyan din baya jin shi, sai lokacin ya kalle shi
"Meye? Karka dameni, kuyi gaba da Hamma Haris mana, dole sai kun tafi dani?"
Ya karasa maganar yana mikewa, shi ya gama shiryawa, Layla ce baigani ba
"Ni na gama shiryawa, ka tashi..."
Rayyan ya furta kamar an mishi dole, mikewar yayi, kafin yai wani motsi Haris ya daga labulen dakin tare da yin sallama, idanuwan shi ya tsayar kan Bilal dan yasan ko Rayyan yayi wa magana kai tsaye ba lallai ya amsa shi ba
"Kun gama? Yamma nayi"
Kai Bilal ya daga mishi
"Yanzun zan kiraka daman"
Rayyan kuma Haris din yake kallo, muryar shi can kasan makoshi yace
"Hamma..."
Daga Haris din har Bilal kallon shi sukayi a tare, fuskokin su dauke da mamaki
"Layla fa?"
Ya furta har lokacin muryar shi daga kasan makoshi ta fito, kamar maganar na mishi wahalar gaske
"Bata da lafiya, ko makaranta bata je ba, tana ta amai jiya da dare, sai da sukaje asibiti da...."
Daga kan kalmar bata da lafiya bayajin wani abu ya kara zuwa kwakwalwar shi, zantukan duk da Haris yakeyi iya kunnuwan shi suka tsaya lokacin daya fara takawa, wuce Haris din da yayi a bakin kofa ya katse mishi maganar da yakeyi, takalma ya zira. A tsayin rayuwar shi ba zai iya tuna ranar karshe da ya taka bangaren Mami ba, ko Layla zai kira daga bakin kofa yake tsayawa ya kwala mata kira, idan bata nan Mami kan fito ko ta aiko a fada mishi bata nan, idan ita ta fito da kanta ta fadi juyawa yakeyi. Itama kamar tasan ba karamin taimako tayi mishi na saukakewa kanta yi mishi magana, haduwa hamsin in zasuyi zai matsa ta wuce ne, fuskarta ma baya kallo balle tasa ran zai gaisheta.
Inda sabo ta saba, a yaran dakin Ayya daga Khalifa sai Bilal ne suke gaishe da ita ko da yaushe, amman sauran sai randa suka ga dama, idan tayi musu magana dai suna amsawa, kuma babu wanda zatace ya taba mata rashin kunya. Amman ta kula ba ita kadai bace, kowane Rayyan baya kulawa, shisa bata taba kullatar shi ba. Amman yau babu wani tunani ya shiga dakin yana fadin
"Layla..."
Mami da take kitchen tana wanke-wanke sai da taji gabanta ya fadi, dan yau sai taji kamar a cikin dakinta Rayyan yayi magana, hakan ya sata tsame hannuwanta daga cikin ruwa tana fitowa, ganin shi tayi a tsaye, yau ya sauke idanuwan shi akan fuskarta
"Mami ina Layla?"
Ya furta, yana kara mata mamakin da takeyi, kafin ta iya cewa
"Tana dakinta"
Dan yau ikon Allah take gani muraran, bata taba jin sunanta a bakin shi ba, ta manta ranar karshe daya kalli fuskarta yayi magana da ita. Balle kuma ace ya taka dakin ta, amman yau Rayyan ne da kafafuwan shi a cikin dakinta, lallai kam abin babba ne. Shikam harya fara takawa yayi tunanin baisan inda dakin nata yake ba, juyowa yayi, Mami da tasan tambayar da zaiyi ta daga hannunta tana nuna mishi, baice komai ba ya nufi dakin.
"Allah Kai Ka san dai-dai..."
Mami ta furta a hankali tana komawa cikin kitchen dan karasa wanke-wanken ta. Tana barin Rayyan daya taka har kofar dakin da Mami ta nuna mishi yana Kwankwasawa
"Layla!"
Ya kira yana saka Layla da tun da ta farka cikin dare, magungunan da aka bata a asibiti suka saketa ta rasa abinda yake mata dadi a duniyar gabaki daya. A islamiyya ta sha cin karo da darussan da sukayi magana akan al'ada, menene ita al'adar da hukunce-hukuncen ta a tsari na addinin musulunci. Kuma tun da suke aji biyu a sakandire ta kanji wasu a ajin suna zancen. Sai dai babu wanda taji yana labarin ana shan irin wahalar da take sha tun jiya, mararta take ji tamkar wani ya saka shebir a ciki yana kwashe duk wani abu da bai mishi ba.
Ko numfashi dakyar take iya fitar da shi, bayanta da cinyoyinta a rike su. Har suna sakata tunanin ko jijiyoyin duk dayane suka fara daga bayan nata zuwa cikin cinyoyinta. Ciwo ne da bata taba sanin irin shi ba. Dan ita kabarta da zazzabi, shima sai Mami tayi da gaske zata zauna waje daya. Bata taba wata rashin lafiya da ta kwantar da ita waje daya haka ba. Tana juye-juye ne taji muryar Rayyan, dan kara dakuna fuska tayi dan a tunanin ta cikin kanta ne, dan ko dazun tayi tunanin harya wuce makaranta.
"Layla!!"
Ya kara fadi yana doka kofar fiye da sau daya kamar yanda yayi da farko, bata san lokacin da ta sauko daga kan gadon tana karasawa inda kofa take ba, kama hannun tayi ta murza tana bude mishi
"Hamma..."
Ta fadi cike da mamaki, da gaske shine
"Me ya same ki?"
Rayyan ya furta da damuwa kwance a fuskar shi, yanayin da ya dirar mishi da bakunta tunda ba sabawa yayi ba, idanuwanta ta sauke cikin nashi
"Ki daina kallona!"
Yai maganar a tsawace yana sakata sadda kanta kasa, idanuwanta na fara tara hawaye, nashi idanuwan Rayyan ya lumshe yana bude su a kanta, dai-dai lokacin da mararta tai wata irin murdawa, sai da ta rike kofar tana kiran sunan Allah, ba ita kadai ta rikice ba, hatta shi Rayyan din yanayinta ya ruda shi
"Wai me yake damun ki? Me asibiti suka ce yana damun ki? Kin sha magani?"
Kai kawai ta iya daga mishi, ganin dakyar take a tsaye yasa Rayyan din kama hannunta da yake jikin kofar yana janta suka shiga cikin dakin. Komawa tayi kan gado ta kwanta, yanda duk zata misalta ciwon da take ji ta kasa, ko idanuwanta ta kasa budewa tunda ta kwanta. Tana jin Rayyan ya mika hannu yana daukar mayafin da takan rufa da shi in taji sanyi, duk da ba bargo bane, zanin gadone babba, warware shi yayi yana budewa ya rufa mata. Kafin ya samu wajen zama kan durowar da take gefen gadon. Kallon yanda lokaci zuwa lokaci Layla takan kara runtsa idanuwanta alamun tana cikin azabar ciwo yakeyi.
Jin yanayin yake har cikin ran shi, shi bai taba ganin tayi rashin lafiya haka ba tun tasowar su. Yana nan zaune yana kallon yanayin ta Mami tayi sallamar daya amsa batare daya dauke idanuwan shi daga kan Layla ba
"Me yake damun ta wai? Ko za'a koma asibiti"
Murmushi Mami tayi
"Ai da sauki, an bata magunguna kuma ta sha"
Kai Rayyan yake girgizawa tunda Mami ta fara magana, yana dago kai ya kalleta
"Layla ce Mami. Bata rashin lafiya irin haka... Kinsan bata rashin lafiya irin haka"
Ya karasa maganar da wani yanayi a muryar shi. Kamar baisan yanda zai fadi kalaman ta fahimce shi bane. Itama Mami batasan yanda zata fara gaya mishi ciwon da Layla takeyi bana asibiti bane ba, yanda zai fahimci asibiti sunyi iya nasu kokarin, zai wuce nan da wasu yan kwanaki.
"Nasani, zataji sauki karka damu..."
Kai kawai ya jinjina, tana ganin yanda bai yarda da maganganun ta ba, ya dai mayar da hankalin shi kan Layla ne yana kara gyara zama. Sake ficewa Mami tayi daga dakin, anan tabar Rayyan zaune, sosai ya nutsar da hankalin shi akan Layla, har sai da yaga yanayin ta ya canza da alamar bacci ya dauketa. Amman ko motsi tayi sai gaban shi ya fadi, gabaki daya komai yake ji baya mishi dadi. Kamar daga sama yaji ana fadin
"Hamma kai muke..."
Hannun shi ya daga guda daya yana dakatar da Bilal, dayan hannun yakai bakin shi da furta
"Shhh..."
Kafin ya mike tsam yana fitowa wajen dakin, ya dan koma ciki yana fisgo Bilal da ya shiga suka fito, muryar shi can kasa yace
"Meye?"
Kallon shi Bilal yake da mamaki
"Ban gane meye ba, kasan kai muke jira har la'asar tayi ko?"
Numfashi ya sauke, gabaki daya ba yajin yana da natsuwar wata tafiya yau
"Ni kam sai gobe"
Baki Bilal ya bude yana kallon shi, so yake yaga ko