Showing 75001 words to 78000 words out of 150281 words
dai ka kula da kan ka dan Allah. Ni duk ka tsoratani..."
Numfashi Rayyan ya sauke yana juyawa kawai. Maganganun shine suka yawaita a lokaci daya yau. Shisa suka tsorata Bilal din, sai juyawa su yake a ran shi. Yana jin kamar wani abu mai girma na shirin faruwa da su yau din nan. Shima ta shi zuciyar bugawa takeyi, ruwan daya gani a roba shiya dauka ya kwance yana kafa kai ya shanye, na karshen na sauka bakin shi da wani dandano daya kasa ganewa. Anan ya tsaya yana mayar da numfashi, wayar shi ya zaro daga aljihu ya ajiye akan tebir din, wani irin sama-sama yake jin shi, banda yanayin Rayyan babu abinda yake gani
"Allah ya sauke ka lafiya Hamma"
Ya furta jin zuciyar shi bata daina rawa ba. Agogon hannun shi ya kwance, kamar zazzabi yake son yi, da wahalar gaske gabaki dayan yau ya iya zuwa makaranta. Kayan jikin shi ya rage yana barin gajeran wando, shima wandon anan ya cire shi yana zare kafafuwan shi ya tsallake tunda Rayyan din da zai fada ya ajiye wando a kasa baya nan. Ya kama riga ya cire yaji kamar jiri zai dibe shi, babu shiri ya zauna a gefen gadon batare daya juya ba balle yaga Layla, kan shi ya dafe cikin hannuwan shi biyu. Da gaske duniyar shi ce take wasan kura da shi. Ya gwada mikewa yafi sau biyar yana kasawa saboda yanda jiri yake dibar shi, babu shiri ya kwanta ko zai samu sauki. Daga nan ba zai ce ga iya lokacin daya dauka baisan abinda yake faruwa a duniyar ba.
Kamar a mafarki haka Layla ta bude idanuwanta tana ganin komai na rabe mata biyu
"Hamma..."
Ta kira a cikin kanta ganin Bilal din a kwance a gefenta, sai taga tazarar da take tsakanin su tayi mata nisa, ga yanda jikinta duka yai nauyi sanda taja shi tana matsawa sosai kusa da shi
"Hamma"
Ta sake kira tana jin ashe gara da tazo, ashe Rayyan bai tafi ba, watakila kuma daya daga cikin mafarkan da ta sabane na shi, saboda yanayin ta ya nuna haka, tana jinta kamar tana yawo a gajimare, hannunta ta dago tana dorawa akan fuskar shi, fuskar da take mata kyau a kowanne yanayi, duk da duhun dakin ya hana mata ganin shi sosai, sai tarin kasumbar da yake fuskar shi. Kamar yanda take jinta a mafarki hakama ya kasance a wajen Bilal, dumi yaji ta inda bai taba zato ba, dumi yake ji akan kirjin shi da wasu sassa na jikin shi inda Layla ta kwanto, sai kan fuskar shi da sam baisan meye a kai ba, har saida ya kai na shi hannun yana kama nata cikin na shi.
Ya sha ganin hannuwanta, ya sha hasaso yanda zasu kasance a cikin na shi, amman yau daya jisu a cikin nashin, a duniyar da yake suna dayane yazo mishi
"Aisha"
Ya furta iya kan shi yana kara rikota a jikin shi, yanajin yanda bugun zuciyar shi ya karu har cikin idanuwan shi da suke a rufe, yanda ta biye shi na kara tabbatar da mafarkin da yakeyi. A cikin su babu wanda ya dawo hayyacin shi har sai da Layla taji abinda yake faruwa ya girmi duniyar da take tunani ta mafarki ce, ya kuma girmi duniyar da take ciki gabaki dayanta, a dai-dai lokacin da Bilal ya rabata da Martabar da bata san haka take ba a duk lokuttan da Mami take kira mata ita sai yau da tashin hankalin rabuwa da ita ya wujijjigata yana fisgota daga duniyar da ta fada zuwa ta mutane, lokacin da ta bude idanuwanta tana son saka duk wani karfi da zata iya tattarowa ta ture Bilal din.
Tashin hankali yayi kadan a yanayin da take ciki, saboda taji muryar shi a kunnenta da wani irin yanayi yana furta
"Aisha... Aisha"
Muryar da yanayin bai hanata gane waye ba, sunan daya kira na sake tabbatar da firgicinta, azabar da take ratsa ruhinta ta girmi mafarki tabbas da ta fassara abinda yake faruwa din da mummunar mafarki, kuka da ihu take son tattarowa daga wani loko da tashin hankalinta yake faruwa, dakyar ta samu ta iya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
A matuqar wahalce tana jan numfashin da ta fitar da sauran natsuwar daya rage mata kafin azaba da tashin hankali su sake rabata da hankalinta...
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Dec 9, 2020
18
Da wani irin ciwon kai ya sauka, ga alamun zazzabi yanaji. Ya kira wayar Layla yafi sau goma bata daga ba. A ranaku da ba irin na yau ba, kira daya idan yai mata bata daga ba shikenan. Ya san in tazo zata kira shi. Amman yau din wani irin tsoro yake ji da bai san dalilin shi ba, tsoron ma bai kara yawa ba sai da ya kira Bilal shima bai daga ba. Bilal da ko karatu yake sai ya mishi magana zai ajiye waya ya natsar da hankalin shi waje daya. Idan jarabawa akeyi ma, kamar yaro haka zai ce
"Ban wayar nan Bilal..."
Zai saka a key ya ajiye yana fadin
"Na ajiye Allah kuwa Hamma"
Sanin halin shi yake saka Rayyan din kin yarda, sako na shigowa zai sake dauka, shisa yakan mike ya dauki wayar ya ajiye a gefen shi
"Kayi abinda yafi danna wayar muhimmanci"
Yakan fada mishi, ya rasa dadin me suke ji shi da Layla kan danne-dannen wayar nan. Ji yake kamar ya tsaya a hanya ya samu wata motar da zata juya da shi Zaria saboda rashin natsuwar da yake tare da ita.
"Allah Ka san halin da nake ciki, Ka san damuwa ta, Ka san zuciyata ba zata iya daukar wani abin ba. Allah Ka sa lafiyar su"
Shine abinda yake fadi yana maimaitawa, duk inda network zai dawo mishi sai ya gwada lambar Bilal da ta Layla, amman duka tana shiga basa dauka ne. Yana sauka a tashar ya tsaya ya kira Bappa da bugu daya ya daga yana sallamar da bai jira Rayyan din ya amsa ba ya dora da
"Har ka karaso ne? Ka jirani a tashar in zo yanzun"
Rayyan din dan dakuna fuska yayi, saboda Bappa nayi kamar sun san juna, kamar sun saba ba yau bane farkon maganar su
"Eh, ok tam"
Rayyan ya iya cewa yana sauke wayar daga kunnen shi, fita yayi daga tashar zuwa bakin titi. Anan yayi tsaye, masu mashin da napep na ta mishi magana, harya kawo iya wuya, ga shi gari yayi duhu tunda sai bayan Magriba suka sauka.
"Alhaji tafiya ne?"
Wani mai mashin ya fadi a karo na biyu, kamar bai ga ya girgizawa mutane wajen hudu kai cikin alamar a'a ba.
"Sai ka daukeni ka dorani, me yasa dole sai kun sa mutane magana ne?"
Jinjina kai mai mashin din yayi
"Allah ya baka hakuri, daga tambaya"
Wani irin kallo Rayyan ya watsa mishi, dai-dai lokacin da wata mota baqa, kirar Honda Accord DC V6 ta tsaya a gaban shi. Gilashin aka sauke daga bangaren da yake, kafin aka kunna fitilar cikin motar haske na gaurayewa
"Rayyan?"
Bappa ya fadi daga cikin motar, Rayyan din na jinjina mishi kai
"Muje..."
Cewar Bappa, hannu Rayyan yasa yana bude murfin motar ya shiga, batare da yace komai ba ya rufe. Bappa ma baice mishi komai ba yaja motar, hankalin shi sam ba'a kan titi yake ba, shi dai yana garin Bauchi, zaune a cikin motar Bappa da sai kamshi takeyi. Amman hankali da natsuwar shi suna garin Zaria. Baisan anyi parking ba sai da Bappa yace mishi
"Mun zo"
Budewa yayi yana fita, in da duk Bappa ya sa kafar shi nan Rayyan yake mayarwa, ko sunan Hotel din bai duba ba, daga yanayin shi bayan sun shiga ya dan gane ko ina ne, ciki suke shiga sosai har suka karasa daki mai lamba 19, inda Bappa ya zaro mukulli daga aljihun shi yana bude dakin. Da sallama ya shiga, Rayyan na biye da shi, ya mayar da dakin ya rufe, akwai haske gauraye da dakin, babba ne da tanqamemen gado sai tv da take ta aiki, amman babu magana, anyi kasa da ita. Har da kujera doguwa a cikin dakin. Yayi kyau sosai da sosai. Ko ina a gyare tsaf, da alama zaiyi tsada
"Na san ka kwaso gajiya, ga sallah kuma da wahala kun tsaya..."
Bappa ya fadi yana saka Rayyan kallon shi, dogone dan da wahala idan bai mafi Rayyan din tsayi ba, sai dai shi siririne, da kasumba a fuskar shi, akwai abin sallah a goshin shi, wata natsuwa Rayyan yake gani a tattare da Bappa, duk da kananun kayane a jikin shi yayiwa Rayyan din kwarjini. Mutanen da suke mishi kwarjini basu da yawa, duk izzar da kake tare da ita kuwa. Da hannu Bappa ya nuna mishi bandaki
"Ga toilet din nan"
Jakar da take rataye a kafadar shi Rayyan ya sauke akan kujera, bandakin ya karasa yana zira takalman da suke ajiye a bakin kofa ya shiga sosai yana rufewa. Har ruwa ya watsa, sannan ya daura alwala. Sanda ya fito sai yake jin shi ya samu yar natsuwa. Sai kan shi da yake ciwo kamar ganga ake bugawa a ciki. Baiga Bappa ba a dakin ya dai shimfida mishi darduma, sun tsaya sukayi azahar inda akaci abinci, shi banda nutri-milk da biscuit babu abinda ya sakawa cikin shi, shima dan yana bukatar wani dan karfi ko ya yake kafin zullumi ya saka shi faduwa.
Sallolin shi yayi a nutse yana zaro wayar shi ya duba, ganin lokacin isha'i yayi ya saka shi gabatar da ita. Zaune yake akan kafet din yau ya rasa kalar addu'ar daya kamata yayi bayan rokon Allah da yasa daga Bilal har Layla lafiyar su kalau. Lambar Layla ya sake kira
"Dan Allah ki daga"
Ya fadi a hankali, amman bata daga din ba, haka Bilal. Rasa abinda yake mishi dadi yayi a duniya, saboda zuwa yanzun ya aminta da zuciyar shi, tabbas wani abu ya faru, babu yanda za'ayi yayi tafiya haka ace ko sau daya Bilal bai neme shi ba. Lakca zai tafi yayi yamma, in har bai fada mishi zaiyi yamma ba ya dinga kira kenan har sai ya mishi text cewar yana aji
"Wai ni karamin yaro ne Bilal?"
Ya taba tambayar shi wani lokaci da yayi mishi kira goma akan shidda tayi ina ya tsaya bai koma gida ba
"Ni dai ka dinga fadamun in ka san zaka biya wani waje"
Bilal din ya amsa cike da damuwa a muryar shi, amman yau ya tafi wani waje mai nisa haka ace ko sau daya Bilal bai neme shi ba, da gaske ba lafiya ba, wani abu ya faru, ko da shi ko Layla. Saboda tunanin Rayyan din sam bai kai gida ba, kallon wayar shi yake kamar yana so ta taimaka mishi da wata maslaha. Amman shiru
"Ayya..."
Zuciyar shi ta ambata, a karo na farko a tsayin rayuwar shi da yaji yana son ya kirata da kan shi, yana kuma bukatar taimakonta, watakila ita tayi magana da Bilal a tsayin ranar. Ko Bilal baiyi magana da kowa ba, tabbas zaiyi da Ayya, lambarta ya lalubo ya kira, zuciyar shi banda dokawa babu abinda takeyi mishi, tana dagawa bai jira ta gama sallamar ba yace
"Ayya kinyi magana da Bilal?"
Dan jim da tayi ya sa Rayyan din kiran
"Ayya"
Yana jin numfashin da ta sauke
"Rayyan?"
Ta kira sunan shi kamar tana shakkun cewa da gaske ya kirata, da gaske tana magana da shi
"Kunyi magana? Bilal..."
Ya sake maimaitawa
"Ina ta kira bai dauka ba, tun da safe da yace mun ya kaika ta sha, yace yana da lakca da safen da, amman ba za'ayi ba zaije gida ya kwanta yayi bacci, har yanzun bai kirani ba, na kira shi yafi sau hamsin bai daga ba. Na kasa samun natsuwa"
Runtsa idanuwan shi Rayyan yayi yanajin kamar bangwayen dakin na hadewa da shi a ciki saboda wani irin tsoro daya taso mishi
"Kai ma bai neme ka ba?"
Ayya ta tambaya da wani irin yanayi a muryarta, kai Rayyan yake girgiza mata, tashin hankali bakon abune a wajen shi, ya san kunci, ya san rashin natsuwa, yasan bacin rai, har tsoro ya sani saboda yana jin shi idan ya ga mage, yana kuma jin shi duk idan ya sauke idanuwan shi akan Layla, ya san abubuwa da dama, tashin hankali bakon shine, musamman mai hade da firgici irin wannan. Kafin wasu dakika ya fara kokawa da numfashin shi
"Rayyan!"
Yaji muryar Ayya kamar a wata duniya kafin wani haske ya gilma ta cikin idanuwan shi yana saka shi runtsa su ya sake budewa, ji yake kamar an kama kafafuwan shi an sadda kan shi kasa ana jijjiga shi, idan wani abu ya sami Layla, baisan ya zaiyi ba, amman bai kara sanin asalin firgici ba sai da yai tunanin wani abu ya sami Bilal
"Gabana sai faduwa yake tun safe"
Ya tuna maganar Bilal jiya da daddare
"Kayi addu'a"
Ya amsa shi, yana kallon yanda ya danyi jim kamar mai nazarin wani abu sai kuma yaci gaba da danna wayar da yakeyi, sai yau din yaga kamar akwai rama a cikin idanuwan Bilal din da baigani ba sai yanzun yake tunawa
"Ka kwantar da hankalin ka, watakila ko ya ajiye wayar wani waje bai ganta ba, ka san Bilal"
Wani irin numfashi Rayyan ya sauke
"Ni da ke mun san Bilal baya ajiye abu ya rasa in da ya ajiye Ayya"
Cewar Rayyan yana sauke wayar daga kunnen shi ya kashe kiran, a gefe ya ajiyeta yana dafe kan shi da hannuwa biyu, tabbas da ace zai sami motar da zata juya Zaria ba zai kwana a garin nan ba yau, bashi da wata natsuwa idan bai sami Bilal ba. Bappa ne ya shigo da leda a hannun shi yanayin sallamar da Rayyan ya amsa ya dora da
"Zan iya samun motar da zata koma Zaria yau?"
Da mamaki Bappa ya kalle shi
"Da daren nan? Amman ka san hanyar ba aminci gareta ba ko? Kuma me yasa kake tambayar motar Zaria"
Cike da damuwa Rayyan yace
"Zan koma ne"
Sai da Bappa ya karasa ya ajiye ledar hannun shi ya zauna sannan ya fuskanci Rayyan sosai
"Lafiya dai ko?"
Bai san me yasa yaji kamar zai iya yadda da Bappa ba, bayan shi din baya yarda da mutane. Amman yana cikin damuwa kalar da bai taba sani ba, taimako yake bukata ko daga wajen waye
"Ina ta kiran kanina baya dagawa"
Kai Bappa ya jinjina
"Watakila baya kusa da wayar, ko kuma ya yarda ba'a kai da tsinta an kashe ba. Ko wani ya dauke, akwai dalilai irin haka"
Kai Rayyan ya girgiza mishi, yau kalamai yake nema da zai misalta abinda yakeji Bappa ya fahimta
"Banda kanina, Bilal ba haka yake ba. Zai kirani ko da wayar wani ne ya fadamun. Yaune na farko da muka yini bamuyi magana da juna ba"
Numfashi Bappa ya sauke
"In shaa Allah komai lafiya. Ka kwantar da hankalin ka, ba kada lambar ko abokin shi haka? Sai ka kira a duba shi?"
Kai Rayyan ya girgiza, a karo na farko yana dana sanin halayen shi, da ace ko lambar mutum daya a cikin gidan nasu yana da ita yau zatayi mishi rana
"Mutum yana da ranar shi Hamma, duk yanda kake tunanin baka bukatar wani bayan ni da Layla ba fata nai maka ba, Allah kar ya nuna maka ranar da zata karyata tunanin ka..."
Ga ranar ta zo yau, ranar da Bilal yayi mishi addu'a karya gani
"Allah bai amshi addu'ar ka ba Bilal"
Rayyan ya fadi a zuciyar shi
"In shaa Allah komai lafiya. Na san zai kira"
Numfashi kawai Rayyan yaja yana mikewa dakyar, kamar abinda ake kira "anxiety attack" ne yake shirin kamashi saboda tashin hankalin da yake ciki. Inda jakar shi take ya karasa ya dauka yana budewa, jikin shi babu inda baya bari sanda ya dauko kwalin sigarin shi, ya dauki kara daya ya saka a baki ya lalubo lighter din saiya tsinci kan shi da juyawa, yau abubuwan da suke baqi a wajen shi yake tayi
"In ba zaka damu ba"
Ya cewa Bappa da yayi dan murmushi yana girgiza mishi kai. Kunna sigarin yayi yana shanyeta cikin yan dakika ya sake kunna wata, sai da ya sha kara biyar, amman jikin shi bai daina kyarmar da yake yi ba. Karshen daya rage ya karasa bakin kofa inda ya hango kwandon shara ya zuba, harda kwalin daya tara toka a ciki. Dawowa yayi yana kara saka hannun shi cikin jakar shi ya laluba, kafin zuciyar shi tayi wata irin dokawa da bata da alaka da su Bilal, ya manta magungunan shi, jiya bai saka a jakar shi ba
"No.. No... Please no"
Yake fadi cikin tashin hankali yana kara dubawa ko watakila bai manta din ba, amman babu su, har kayan ya fito da su yana duddubawa, kafin ya sake mayarwa yana runtsa idanuwan shi, ji yake kamar wani abune a cikin kan shi yau da yake jiran cikar lokaci kafin ya tarwatse. Juyawa yayi ya nufi kan gadon, bai karasa ba yaji muryar Bappa da shaf ya manta yana dakin ta daki kunnuwan shi
"Ka ci abinci sai ka kwanta"
Kai Rayyan yake girgiza mishi yana zama a gefen gadon saboda yanda jikin shi yake bari, sosai yanzun yake bukatar magungunan shi, badan bacci ba, sai dan mugun sabon da jikin shi yayi, jiya bai sha ba in zai tuna, yini biyu kenan bai sha ba, shisa jikin shi yake sanar da shi babu lafiya.
"Kana bukatar ka sa wani abu a cikin ka"
Cewar Bappa da ya bude ledar take away din da yayo musu a cikin hotel din, shinkafa ce dafaduka ta sha nama da kayan hadi, harda hadin salad a gefe. Yana kallon Rayyan din ya sake girgiza mishi kai
"Yunwa da withdrawal effect ba hadi bane me kyau"
Bappa ya karasa maganar yana saukowa kasa kan kafet din dakin ya ja abincin shi daya saka cokali a ciki ya fara ci. Shi din ya karanci Psychology ne a kasar amurka, zai koma yaci gaba, saboda yana son zama abinda ake kira Profiler, akwai graduate degree da zaiyi akan forensic psychology kafin ya fara aiki da hukumar tsaro ta yan sanda da yake a can kasar, yana da kokarin da yasan da wahala idan bai samu ba.
Shi din dan gidan Sheikh Abdullah Bappa ne, sunan kakan shi yaci wato Muhammad sai suke kiran shi da Bappa kamar yanda ake kiran kakan na shi, baban shi