Showing 141001 words to 144000 words out of 150281 words
ta kalle shi, farar riga ce ya saka T-shirt, da alama bai goge jikin shi ba dan fuskar shi da alamun ruwa a jiki har lokacin, kamar damuwa take karanta a shimfide a fuskar shi, yanda yaji idanuwanta na mishi yawo ne yasa ka shi kallon cikin nata idanuwa yana girgiza mata kai
"Wani abune daban Layla, ba ke bace ba"
Saboda zai rantse yana jin sautin tunanin ta cikin kunnuwan shi, idanuwanta da yake ganin hawaye a ciki na saka shi gyara zaman shi ya saka hannuwa yana riko fuskarta
"Na san banda wani abu da zan baka Hamma, ba haka na hango yau ta kasance mana ba..."
Layla ta ke fadi wasu hawaye masu zafi na zubo mata. Kai Rayyan yake girgiza mata, sam bayason inda tunaninta yake so ya dauketa
"Bana so, bana son wannan shirmen tunanin naki. Kin zo mun dake, kin zo mun da Nur, kin bani duk abinda nake so harda abinda banyi zato ba, dan Allah ki bari, karki kara mun damuwa da tunanin nan naki... Raina a bace yake, amman bake bace"
Ya karasa maganar yana matsawa sosai ya sumbaci goshin ta, yana sake sumbatar kuncinta kafin ya riko ta jikin shi yana sauke wani irin numfashi, ya manta yanda kusanci da ita haka yake samar mishi natsuwa, ya manta yanda jinta a jikin shi kawai yake kwantar da duk wata murya da take neman daga mishi hankali, sosai ya kara riketa a jikin shi yana sumbatar duk wani waje da labban shi zasu iya sauka kafin ya sake riketa kamar zai koma jikinta
"Nagode Hamma..."
Layla tace tana dorawa da
"Nagode da ka zamar dani matar ka"
Dariya yayi mai sauti yana sake riketa
"Nagode da kika zama matata, nagode Layla. Ba zan miki alkawarin baki farin ciki ko da yaushe ba, amman In shaa Allah zanyi kokarin ganin kinyi farin ciki koyaya ne a duk ranar da zan samu aronta tare dake, Nagode... Nagode"
Yana jin amsarta ta yanda ta kara shigewa a jikin shi, Ayya tace itace mafarin komai, tace laifin duka nata ne, baisan ko Layla da take jikin shi bane ta sauya tunanin shi, bai san ko dan Ayya din daga jikinta ya fita ba, amman ya kasa dora duka laifin a kanta, ya ga fuskarta, ya ga idanuwanta, ba tun yanzun yasan duka rayuwarta ta ta'allaqa ne wajen ganin ta kare su daga duk wani abu da zata iya ba. Idan da ta hango abinda tayi zai iya tabasu ba zatayi ba, yana ganinta ita da Haris, tana kaunar shi kamar daga jikinta ya fito. Kuskure ne tayi, kowa baifi karfin yayi kuskuren ba, ko da akwai son kai a cikin shi, baice ran shi bai sosu ba, baice ba za'a dauki lokaci ba kafin ya daina jin ciwon abin. Amman zasu kai wajen, kamar yanda shi da Layla suka kawo yau.
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Jan 30, 2021
33
Fitowa tayi daga wanka, idanuwan ta kan Nur suka fara sauka kafin ta saki salati
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Idanuwan shi Rayyan ya daga ya kalleta a kasalance, kamar bai san dalilin yin salatin nata ba, yana kallo ta karaso ta kama Nur tana karewa gashinta da yake tsaye birci-birci duk ya cakude waje daya kallo wani malolon bakin ciki ya taso ya tokare mata wuya. Ita kadai tasan wahalar da tasha daren jiya tayi mata kitson, da kuka da komai, har dukanta sai da tayi, saboda Rayyan din ya kwana asibiti wajen aiki, Aminu Kano bangaren masu matsalar kwakwalwa. Ta san indai ya dawo ba za'ayi ba tunda Nur ba son kitso takeyi ba, ko kibiya ta gani a hannun Layla sai ta saka kuka.
"Kwance mata kayi?"
Ta tambaya, gira Rayyan ya daga
"Me yasa zakiyi mata kitso? Kin matse mata kai dakyar take motsa wuyanta, har gefen kan ya fara yin alamar kurji"
Sakin Nur tayi kawai, idan tayi magana tsaf hawayen takaici zasu biyo baya. A shekaru uku da aurenta da Rayyan ba zata ce bata cikin kwanciyar hankali ba. Amman tunanin da tayi na cewar auren Rayyan shine zai gyara mata komai, idan tana tare da shi babu wani abu da zai dameta ne ya sha bamban. Mutane ne suka nuna mata damuwar ta babu inda zata je, kamar yanda suka koya mata rayuwa da damuwar a kasan zuciyar ta. Ko biki akeyi ko suna idanuwan mutane akan Nur suke fara sauka, Nur suke fara gani, kamar yanzun rayuwar ta gabaki daya ta tattara ne akan yarinyar
"Ita ce wannan ko? Allah sarki"
Sune kalaman da suka fi tsaya mata a kirji suna sakata jin wani irin ciwo na ban mamaki. Ba manta yanda aka sami Nur tayi ba, amman na rana daya tana so ta rufe idanuwan ta, ta bude su ta kalli yarta a matsayin ya, ta kalleta batare da taga tabon da tayi mata ba, tabon da shi kowa yake fara dubawa. Ba son kai zatayi ba, amman Nur tana da kyau, sosai tana da kyau saboda tana kama da Bilal, kamannin da yasa in ba sanin su kayi ba sam ba zaka gane ba daga jikin Rayyan ta fito ba, gashi tana da hasken fata kamar na Rayyan din. Sai dai kyawunta ya kasa dishe munin tabon da yake tare da ita.
Shekarar su daya da aure, Rayyan ya saka ta sake yin jamb ta nemi gurbin karatu a BUK.
"Kina da buri kafin faruwar komai, abubuwa da yawa sun canza miki, bana son ya zamana harda wannan...ki koma makaranta Layla, kiyi karatu, ki fita da sakamakon da kike burin fita, ki nemi aikin da kike fatan samu"
Shine kalaman shi, kalaman da suka bude mata zuciyarta suna dawo mata da burin ta sabo. Ko ba komai makarantar ta rage mata damuwa, yanzun tana shekara ta biyu, ta sha wahala a farkon zango na biyun a shekarar saboda laulayin cikin da yake jikinta, ga kula da Nur, tunda Rayyan yaki yarda a sakata makaranta sai a sabon zangon da za'a shiga, dan ma bakomai take yiwa yarinyar ba saboda Rayyan in dai yana gida fiye da rabi da kwata na lokacin shi yana kan Nur dinne, in ba bacci tayi ba ita Layla bata samun kan shi sam. Duk da haka ta sha wahala, tunda in dai aikin safe yakeyi sai ta dafa mishi abinda zai tafi da shi. Wata ukku na farkon cikin ta wahala sosai, yanzun ne ma ta dan samu saukin laulayin.
Yau da ya kama asabar zasu je gida ne gabaki dayan su. Basu ma tashi da wuri ba, indomie da kwai ta dafa ma Rayyan din da Nur, ita tana da sauran doyar da sukaci da daddare, ita tayi warming taci. Yanzun ma mai ta shafa ta dauki kayanta tana ficewa daga dakin ta kyale su. Sanda ta dawo ta gama shiryawa tsaf
"Ki gyara mata kan, ina takalman ta?"
Ya bukata, inda suke Layla bata kalla ba
"Magana fa nake yi"
Rayyan ya sake fadi da alamar dariya a muryar shi, sarai yasan ta kule, ranta a bace yake. Babu yanda zatayi da shine kawai tunda ya fita rikici, ya kuma fita iya fada. Baisan sau nawa zai gaya mata ta daina ma Nur kitso ba, duka yarinyar yaushe kanta yayi kwarin da za'a kama shi ana mai kitso, ko gashin kirki ma babu, keyar ba komai har yanzun. Kawai salon a saka mata ciwon kai. Ya ce ta dinga shafa mai sai tayi mata kalba ta saka mata hula, kan da za'a rufe in ba rigima ba meye nayi mishi kitso. Sanin Layla ba kula su zatayi ba yasa ya mike yana daukar Nur din, da kan shi ya karasa in da kayanta suke ya samo wata farar hula mai duwatsu a jiki ya saka mata, takalman ma shi ya dauko mata.
A shekarun natsuwar da bai taba sanin akwaita ba ita ya samu da auren Layla, rayuwar su bata cike da farin ciki ko da yaushe, suna da nasu matsalolin, amman babu rana daya da zaice baiyi dariya daga dukkan zuciyar shi ba, iya wannan yakan isa ya kori koma menene yayi ma farin cikin shi kutse a ranar, balle kuma Nur da yake jin ita din duka rayuwar shi ce. Akan ta yake jin damuwar da a fuskar Abbu kawai yakan ganta, damuwa ce da iyaye suke ji a lokuttan da yaran su basu da lafiya, a lokuttan da zasu ji kukan yaran nasu batare da sanin me yake damun su ba.
Ko faduwa tayi yaga jini duk wani abu da yake kwance a tare da shi saiya ta shi. Yana son Layla, daga baya yasan soyayyar su Ayya, amman son da yake yiwa Nur daban ne, bai san ko dan ita yake gani tana rage mishi kewar Bilal ba, ko rike ta yayi yakan ji wani kusanci da Bilal na ban mamaki. Bai san lokacin da ya daina duba hanyar dawowar Bilal ba, rana daya ya tashi yaji zuciyar shi tayi wani sanyi da yake tare da hakuri, sanyin da yazo mishi da daukar kaddara. Yayi kuka dai ranar, sosai yayi kuka a jikin Layla, kukan da bai bari zuciyar shi tayi mishi ba saboda yana saka ran dawowar Bilal din.
Abinda ya zame mishi jiki shine tura kudi a account din Bilal, duk da yana da wani bankin da yake ajiya, duk yanda yaso ya daina saiya kasa, daga safiyar da aka biya albashi zuwa yamma sai ya kasa samun natsuwa idan bai tura ba, a lokutta irin ranar yakan ji daman ace yaga gawar Bilal, da ya dibi kasa ya zuba a kabarin shi, da tuni ya aminta da rashin shi. Amman har abada akwai bangaren shi da ba zai taba daina jin kamar Bilal din yana da rai ba.
"Layla ki kira mun Bilya a wayata, ki saka mun a speaker..."
Rayyan ya fadi yana gyarawa Nur madaurin takalmin ta
"Mota na mun wata kara tun jiya, mutuwa tayi jiya fa a hanya, dakyar ma ta tashi, in munje gida sai yazo ya dauka"
Wayar tashi Layla ta dauko can karshen gado
"Yaushe screen dinka ya kara fashewa?"
Ta bukata
"Nur ta fado da ita shekaranjiya"
Kai kawai Layla ta girgiza, idan tace ya daina bata wayar shi ba zaiji ba. Tunda yana da kudin sake screen. Tana jin dadin yanda bako da yaushe soyayyar yarinyar take rufe mishi ido ba. Kusan tama fi tsoron shi duk da baya dukanta, yana mata ihun da ba ita ba har Layla sai ta tsorata.
"Na ga karamar wayar ka, bayan gado ta fada...mantawa nayi tun jiya... Na saka ta caji tana falo..."
Layla ta fadi tana duba contacts din shi, amsa ta yayi hakan yasa ta daga kai ta kalle shi, da yake suna ne ta fara rubutawa ta saka "Bil..." bata karasa ba sai ta kira lambar farko data fito, ta amsa Rayyan ta mayar da hankalin ta kan screen din, zuciyarta na wata irin dokawa. Jikinta har rawa yake lokacin da ta kashe kiran ganin lambar Bilal, wajen kiran ta shiga ta goge kar Rayyan ma ya gani. Kafin ta kira mishi Bilya din, sai da ta fara ringing sannan ta karasa ta mikawa Rayyan din. Mayafin ta, jaka da sauran tarkacen da zasu bukata ta dauka suka fice daga gidan.
Sosai suka bata lokaci akan hanya saboda Rayyan yayi kwana ya tsaya siyawa Nur mangoron da tunda ta hango shi ta cikin motar take zillo tana dukan gilashin kamar zata fita ta dauka
"Daada...ina so, ina so"
Take fadi tana sake maimaitawa
"Dan ubanki sai kin fasa mun kunne ne?"
Cewar Layla tana juyawa ta harari Nur din da take sake ziro kai tana kiran
"Daada"
Kamar yanda take cewa Rayyan, duk yanda Layla taso ta gyara mata ya koma "Daddy" taki. Harta hakura ta kyaleta.
"Da ni nace ka tsaya a siya mangoro babu surutun da ba zakayi mun ba"
Layla ta fadi cikin sigar mitar da Rayyan bai ko kulata ba. Bayan motar ya ajiyewa Nur ledar yana fadin
"Karki taba sai munje gidan Ayya sai a wanke a yanka"
Kai ta daga mishi tana murmushin jin dadi. Da suka karasa ma, Rayyan bai shigar da motar ba tunda Bilya zai zo ya dauka. Anan kofar gida ya ajiye ta, shi ya fara fita ya bude bayan ya taimakawa Nur yana sauko da ita, ledar mangoron ya dauka, kiciniyar da zata fara yi da shi yasa ya sakar mata yana kallon ta, ganin zata fadi yasa shi karba ya zare guda daya a ciki ya bata ta rungume shi kamar ta rike jariri. Dariya yayi kawai yana rufe motar. Tare suka shiga gidan, Nur na rugawa da gudu ta nufi bangaren Ayya, shi baima karasa ba yaga Bilya na kiran shi, dagawa yayi yana sakawa a kunnen shi
"Gani a kofar gida yallabai"
Batare da Rayyan ya amsa ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana juyawa. A can gefe ya hango Bilya da yana ganin shi ya fara takowa, sake gaisawa sukayi Rayyan ya mika mishi mukullin motar, yana fada mishi abinda yaji tana yi
"Dan Allah ka duba min kafin anjima in dai ba wata matsala bace babba"
Rayyan ya fadi, saboda gabaki daya satin da zai kama aikin dare gare shi, yafi jin dadi ace da motar shi, gashi yasan halin Bilya, ya iya gyara ga ba ha'inci, amman akwai shiririta.
"In shaa Allah zan kiraka dana duba"
Sallama suka yi, ya tsaya duba text din MTN da suka cire mishi har naira dari na wani caller tune da bai san lokacin da ya shiga tsarin ba. Karamin tsaki yaja kawai, yana tura musu sakon da zai bashi damar fita daga tsarin, matsalar shi da su kenan. Sai su fara cire maka kudin da babu dalili. Sakon Bappa ya amsa ta manhajar WhatsApp, shima Allah ya kama shi, addu'ar Baba taci, sosai yaso ya sake gudu yabar kasar, yanzun gashi nan da matar shi harda yaro daya. Sai dai yaki garin Kano sam, a Kaduna yayi zaman shi, in dai ya shigo sai dai ziyara, zumunci mai karfi ne a tsakanin su, duk da Rayyan ba zai kira matar Bappan da Layla kawaye ba.
Sukan gaisa dai idan sun shigo gari da Bappa din, da ta haihu kuma Layla taje ranar suna ta dawo washegari. Iya wannan din ya ishi su biyun, dan suna zumunci babu inda ya zamana dole matan su ma suyi. Juyawa Rayyan yayi bayan ya saka wayar a aljihun shi, ya kama kofar gidan zai tura kenan yaji kamar iska ta dibo mishi muryar da take cikin kan shi ta fito da ita waje tana dukan kunnuwan shi da muryar
"Hamma..."
Sai da ya runtsa idanuwan shi kafin ya bude su yana tura kofar
"Hamma..."
Aka sake kiran shi cikin muryar da wannan karin ba kunnuwan shi kawai ta daka ba, har da zuciyar shi. Idanuwan shi ya sake runtsawa a hankali ya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Saboda ya bawa shekara wajen biyu baya rabon daya shiga cikin wannan yanayin, ba zai koma ba, ba zai koma lokuttan da yake jin kamar takun tafiyar Bilal da baisan yana da sauti ba sai bayan ya rasa shi, ba zai koma lokacin da yake neman fuskar Bilal a cikin duk wani taro da zai gani, a masallacin juma'a, har a wajen jana'iza idan ya samu halarta. Lokuttan da muryoyin mutane da yawa a cikin gidan su take mishi kama da ta Bilal, lokuttan da zai iya rantsewa ba'a cikin kan shi kawai yakan ji muryar Bilal ba. Yana da yarinya yanzun, yana da Nur, zaiyi duk wani kokarin ganin bai rabu da nutsuwar da yake tare da ita ba koya ne.
Saboda tana bukatar shi da duka wata natsuwa da yake da ita. Ba yanzun ba kawai, har lokuttan da zasu zo a gaba, lokuttan da ko tunanin su yayi sai kirjin shi ya dauki zafi, tana bukatar tsayayyen uba da zata rugo wajen shi da dukkan tambayoyin da mutane zasu saka tayi mishi, ba zai bari rashin Bilal ya raunana shi ba. Kafar shi ya daga ya saka guda daya a cikin gidan yaji an dafa mishi kafada
"Hamma"
Wannan karin da rauni muryar ta fito tana tsinka abubuwan da Rayyan bai san suna hade a jikin shi ba, kafin zuciyar shi ta fara dokawa cikin sautin da yake ji har cikin kunnuwan shi, a hankali ya juyo yana fara sauke idanuwan shi kan fuskar Bilal, yawu yake tattarawa yana so ya hadiye ko zai jika makoshin shi da yake ji a bushe, ya bude bakin shi yafi sau biyar yana mayar da shi ya rufe
"Hamma ni ne"
Bilal ya sake fadi, Rayyan bai yarda ba, ko yaushe zai iya farkawa, wani zai iya zuwa ya tashe shi abinda yake faruwa ya zamana mafarki. Hannun shi ya daga yana kaiwa fuskar Bilal ya taba, ba zai tuna ko ya yanayin Bilal yake a duk mafarkan shi ba, sake taba fuskar yayi, wannan karin samu yayi ya gyara tsayuwar shi ya saka duka hannuwan shi biyu yana taba fuskar Bilal din yana son tabbatar da cewa shine a tsaye a gaban shi ba mafarki yake yi ba
"Ni ne, ni ne Hamma"
Bilal ya sake fadi muryar shi na karyewa sosai, wani irin numfashi Rayyan yaja yana sauke shi hadi dayin dariya mai sauti, dariyar da ta saka yaji idanuwan shi sun cika taf da hawaye, dariya ce da babu wani nishadi a tare da ita, wani abu yake so ya fadi amman ya kasa
"Kace wani abu Hamma... Dan Allah kayi magana"
Dariyar Rayyan ya sake yi, yana kai hannuwa ya share kwallar da yake ji a cikin idanuwan shi, juyawa kawai yayi ya tura kofar wannan karin yana shigewa cikin gidan, yana jin Bilal na bin bayan shi, juyawa yayi ya daga mishi hannu cikin alamar da take nuna ya daina bin shi, kafin ya sake juyawa yaci gaba da tafiya, ko hanya baya gani sosai saboda idanuwan shi da suke cike taf da hawaye. Sake juyowa yayi wannan karin duka hannayen shi biyu ya saka ya hankade Bilal din
"Hamma"
Bilal ya kira yana dafe kirjin shi inda Rayyan din ya hankade yana dorawa da
"Kayi hakuri..."
Na shi idanuwan cike da hawaye shima, sai da Rayyan ya dan duqa saboda yanda yake jin numfashin shi kamar baya kaiwa kirjin shi, kafin ya mike tsaye sosai yana kallon