Showing 78001 words to 81000 words out of 150281 words
sanannen Malami ne, duk kuwa da tarin arziqin da suke da shi. Suna da dattako, ana kuma ganin girman su a garin Kano, da wahala ka kira sunan Baban shi ace an samu mutane biyar a waje babu wanda ya san shi ko yaji labarin shi. Tun da ya dauko Rayyan yaga alamun damuwa a tare da shi, karantar shi yake tayi har zuwa yanzun.
Yanayin dabi'un shi, yanda jikin shi yake kyarma da idanuwan shi da sukayi wani irin haske duk kuwa da doguwar hanyar daya sha yasa Bappa gane cewa yana ta'ammali da miyagun kwayoyi. Watakila shima Rayyan kamar sauran mutane ne masu fama da depression, daga shan magungunan da zasu taimaka sai su dinga kara daya akan ka'idar da likita ya rubuta, a hankali a haka sai abin ya zame maka shaye-shaye batare da ka kula ba. Ka kara wa kanka matsala da kanka. Rayyan kuwa shiru yayi yana tauna maganganun da Bappa yayi kafin ya kwanta yana juyawa, Bappa bai san shi ba, dan ya gane daya daga cikin matsalar shi baya nufin ya gane gabaki daya.
Amman jikin shi kyarma yake, makoshin shi yakeji kamar an zuba yashi saboda bushewar da yayi, harshen shi babu miyau ko daya a ciki. Numfashi Bappa ya sauke yana mikewa, Rayyan baiga me yakeyi ba saboda ya rufe idanuwan shi har sai da ya karaso in da yake kwance yana fadin
"Ungo"
Bude idanuwa yayi, yaga robar ruwa sai irin maganin shi guda biyu a dayan hannun Bappa, jikin shi na kara sabon bari ya mike yana karbar maganin ya watsa a cikin bakin shi hadi da lumshe idanuwan shi, kafin ya sake bude su yana karbar robar ruwan ya kora
"Ka kara mun guda biyu"
Kai Bappa ya girgiza mishi
"Zai rikeka zuwa safe"
Ya fadi yana wucewa ya koma inda ya tashi, abincin shi yaci gaba daci, Rayyan kuwa ya kai mintina talatin kafin maganin ya fara nutsar da shi, rawar jikin da yake ya bari, ya sake gwada kiran su Bilal amman shiru. Wannan karin Bappa da yake kwance akan kujerar cikin dakin yana danna waya ya kalla, a saman damuwar shi tunanin waye Bappa ya darsar mishi, haka kawai ya tsinci kan shi da son sanin waye Bappa?
*
Sama-sama yake jin shi, iskar da yake shaka da fitarwa ma kamar an daureta da zaruruwa haka take shiga kofofin hancin shi. Jin shi yake kamar a cikin wani mugun mafarki da zai farka daga shi ko yaushe. Sai dai kamar ya farka kusan awa daya da ta wuce ko fiye da haka, babu agogo a hannun shi balle ya duba lokaci, ba shi da natsuwar kiyastawa kuma. Amman tabbas ya farka daga abinda ya tabbata ba mafarki bane ba, dumin jikinta ya fara tabbatar mishi da ba mafarki yake ba, kafin ya kara ware idanuwan shi akan fuskarta, wani irin mikewa yayi yana hankadeta gefe tare da fadin
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
A matuqar razane, kan shi ya kalla da yanayinta itama kafin komai ya dawo mishi, ba Aisha bace ba, Layla ce, Layla ce. Wata murya a cikin kan shi take fadi tana maimaitawa. A matuqar gigice ya suturta kan shi, baisan abinda ya kamata yayi ba banda kokarin ganin ta tashi, dabarar ya shafa mata ruwa bata zo mishi ba, haka yaci gaba da jijjigata a gigice har Allah ya dawo mata da hankalinta ta bude idanuwanta akan shi
"Layla ki tashi, dan Allah ki tashi ki karyata mun abin nan, ki ce mun karya ne, ki ce mun ko a mummunan mafarki ba zai faru ba..."
Bilal din yake fadi a gigice, yana girgiza ta, sai da ta kama hannun shi ta ture, jinta take kamar tana yawo a saman gajimare, dakyar taja jikinta tana mikewa, numfashi dakyar take fitarwa lokacin da ta kama skirt dinta tana saukewa, idan tace ga abinda take ji karyane, a fadin duniya babu wasu kalamai a cikin kowanne yare da zasu taba yiwa halin da take cikin adalci wajen fassara shi. Kafafuwanta ta sauko daga kan gadon, tana mikewa taji wani irin abu ya tsirga mata, amman bata da lokacin ririta kowanne ciwone yake taso mata, dakin kawai take son bari
"Layla..."
Bilal ya kira, amman bata kula shi ba, dankwalinta ta dauka tana daurawa. Ta dauki jakarta da mayafi
"Layla..."
Ya sake kira ganin tana shirin nufar kofa a halin da take ciki. Shirun tashin hankalinta yake karanta da yake kara bugun zuciyar shi. Bashi da karfin motsawa balle ya hanata ficewa daga dakin. Tun fitarta bai motsa daga inda yake ba, sai yanzun daya samu yaja jikin shi yana dora kan shi a jikin katifar, idanuwan shi ya lumshe kamar hakan komai daya faru yake jira ya dawo mishi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ya furta daga wani lungu na zuciyar shi jikin shi na wani irin bari
"Me zan cewa Abbu? Me zan cewa Abbu..."
Yake fadi kamar wanda ya sami tabin hankali, har lokacin so yake ya tuna lokacin da Layla ta shigo dakin, so yake ya tuna yanda akayi ta hau kan gadon shi, yanda akayi wannan kaddarar ta same su, ko tabin hankali ya fara bai sani ba, tunda ance in kana hauka baka sanin abinda yake faruwa. Saboda in ba hauka yake ba babu yanda za ayi ace wani abu ya faru a tsakanin shi da wata mace daban da igiyar aure bata kulla su ba, balle kuma Layla. Yana da yakinin ko mazinaci ne shi ba zai bi Layla ba, yana mata son da ba zai yarda su kasance a irin wannan yanayin ba.
Hannun shi daya dora kan katifa yaji kamar ya taba wata lema-lema, ba shiri ya dago kan shi yana kallon wajen da hannun shi, abinda yagani na kara gudun zuciyar shi, baisan yanda ciwon bugun zuciya yake ba, amman tabbas yana gab da kama shi, saboda abinda yake gani na kara tabbatar da ko ciwon hauka yake, to tabbas a cikin wannan ciwon ya kasance tare da Layla. Wannan gaskiya ne ko da hankalin shi yabar jikin shi. Wata irin mikewa yayi yana kama zanin gadon ya yaye shi daga kai, fita yayi daga dakin kamar sabon mahaukaci.
Bokitin daya fara cin karo da shi ya saka zanin fadon a ciki ya koma daki ya dauko omo, ya nufi bokitin da sukan tara ruwa ya bude ya diba, kallo daya zakayi mishi da yanda yake wanke zanin gadon kasan ba a cikin hayyacin shi yake ba, yayi mishi wanki yafi biyar kafin ya shanya. Ruwan ya kara diba ya shiga wanka, sai dai ya kai awa daya tsaye a cikin bandakin ko kayan shi bai cire ba, kalar wankan da zaiyi yake tunani, idan ya saka sabulu ya fito tabbas zai fito da daudar da yake ji har cikin ruhin shi.
Idan kuma yayi wankan da zai tsarkake daudar wajen shi baisan yanda zaiyi da ta ciki ba, kuma wankan zai tabbatar mishi da abinda yake so ko yayane tunanin shi ya karyata mishi. Bashi da wani zabi daya wuce yin wankan tsarki ya daura alwala ya fito zuwa daki, kaya ya sake yana fita da wanda ya cire kamar suna tare da wata dauda da ta girmi idanuwa ya saka su a bokiti, dakin dai ya sake komawa ya dauki darduma ya shimfida, har ya kabbara sallar azahar da yake tunanin ta wuce shi, saboda sanda ya fita yaga kamar yamma tayi sosai, komai bai kwance mishi ba sai da yayi sujjada, sai da ya dora goshin shi a kasa ya kara jin yanda bashida wata hijabi tsakanin shi da Ubangiji sannan sauran nutsuwar da yake tare da ita ta kwance.
Maimakon karatun sujjada sai
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Da yake fadi muryar shi can kasan makoshi yana maimaitawa ko Allah zai tausaya mishi ya sake mishi wata kaddara da zai iya dauka ba wannan da ta faru ba, tun yana yi muryar shi na fitowa harta daina ya koma yi a zuciya, tun kafafuwan shi na da sauran karfin durkuson sujjadar harya kife gabaki dayan shi, Ayya kance
"Ko rigimar yarinya bakayi ba Bilal, zan iya kirga lokuttan da naga hawaye a fuskar ka"
Amman yanzun kukane mai gunji ya kwace mishi, kuka yake daga zuciyar shi, rurin shi na fitowa da sauti kafin wasu irin hawaye masu zafi su zubo mishi, hade jikin shi yayi yana wani irin kuka yau da yake neman mai lallashin shi, saboda a labarai ma bai taba cin karo da kalar kaddarar su ba, bai taba jin labarin tashin hankali makamancin wannan da yake ciki ba, bayani yake nema yayiwa kan shi ya kasa, idan ya kasa gane abinda ya faru ko ya akayi ya faru taya zai ma wani bayani ya gane, wanne irin uzuri zai bayar
"Abbu..."
Ya kira sunan na fitowa da gunjin kuka, ta ina zai fara yiwa Abbu bayani, me zaice mishi, me zai cewa Abbu, ya dade yana jin bai cika mishi alkawarin daya rike ba, ya dade nauyin amana na bibiyar shi, amman yau yake jin duniyar shi ta tsaya cak, kuka yake na yanda lokaci daya kaddara ta bude mishi shafin da baisan ya zai karanta shi ba balle yayi tunanin wucewa, saboda an kashe fitilar da take haske da rayuwar shi, duhu ya baibaye ko ina. Yau kuka yake da dukkan zuciyar shi, kukan maraicin da bai taba shi ba shekarun da suka wuce sai yanzun.
Ji yake kamar wani abu na ruri banda zuciyar shi, kafin kwakwalwar shi ta sanar da shi wayace, wayar shi ce take ihu, dakyar ya iya daga jikin shi ya rarrafa inda wayar take kan tebir ya mika hannu ya dauka, zuciyar shi nayo tsalle zuwa cikin makoshin shi ganin
"Hamma"
Rubuce a jikin screen din wayar da ta subuce daga hannun shi tana faduwa kasa, baiko matsawa yayi kamar wayar na dauke da wani abu da zai iya cutar da shi, sam a lissafin da yakeyi na mutanen da zasu tuhume shi Rayyan ya bace mishi, komai ya bace mishi banda Abbu har wayar ta yanke bai iya motsawa ba, tana sake daukar ruri wasu hawayen na kara zubo mishi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Yake fadi yana maimaitawa, yanzun kam ya tabbatar da wannan shafin da kaddara ta bude mishi shine shafin karshe, babu yanda zai ayi yai tsahon ran ganin wucewar shi, zuciyar shi bata da karfin daukar wannan tashin hankalin
"Ka kula da Layla, ka kula mun da Layla kaji Bilal, zuciyata na mun wani iri"
Maganganun Rayyan suka dawo mishi, sake durkushewa yayi, da yawan mutane in suka shigo su kaga Bilal din zasuyi mamakin ganin namiji kamar shi yana kuka haka, abin zai zame musu baqo, saboda an san namiji da juriya, shi da kan shi in da wani yace zai kuka kamar dan shekara biyu zai karyata, saboda bai taba hango rayuwa zata bashi wannan dalilin ba, amman yau kuka yake
"Me zan ce musu?"
Ya furta a zuciyar shi, ashe akwai wani abu da ba zai fassaru ba, ashe akwai kalar kaddarar da babu kalaman da zasu misaltata, ya akayi Layla ta zo dakin su? Yaushe Layla ta shigo dakin su?
"Sai kayita bacci kamar ba namiji ba, ka dinga rufe daki idan ba kowa a gida..."
Rayyan kan ce mishi, saboda kar a shigo a illata shi yana bacci, amman bai taba bacci irin wannan ba, bai taba baccin da za'ace Layla ta shigo har tahau kan gadon shi bai sani ba, har wani abu ya shiga tsakanin su haka
"Ko mafarki nake? Ko da gaske mafarki ne?"
Ya furta yana tashi zaune, fuskar shi harta kumbura saboda kukan da yakeyi, wayar shi ce take ci gaba da ruri, dakyar ya iya mika hannu ya dauka
"Layla"
Ya gani, cikin sauri ya daga yana karawa a kunnen shi, watakila da gaske mafarki yake, muryar shi a dakushe yace
"Layla..."
Sai dai yanayin tata muryar ya tarwatsa wani abu a cikin tashi zuciyar da ba yajin zai taba komawa dai-dai
"Hamma ba mafarki bane ba, ba mafarki bane Hamma..."
Wayar ce ta sake subucewa daga hannun shi a karo na biyu, sosai yake kokawa da numfashin shi, sai dai wannan karin a juye ta fadi, yana ganin screen din, baisan iya mintinan da ya dauka ba kafin ya ga kiran Aisha ya shigo, dariya yayi wannan karin, saboda abin ya fara fin karfin shi, nata kiran na yankewa na Ayya ya shigo
"Ayya..."
Ya kira wata dariya da ta fito da sautin kuka na kwace mishi, da gaske karshen duniyar shine yazo, sosai yake tabbatar da hakan lokacin da idanuwan shi da suke wani irin radadi suke kafe akan screen din wayar da kararta ta daina zuwa kunnen shi, yana kallonta in wani kiran ya yanke sai wani ya sake shigowa, kiran mutanen da kamar sun san abinda ya faru, kamar suna jira ya daga ne su fara jeho mishi tambayoyin da yasan bashi da amsar su...!
*
Littafina na siyarwa ne akan naira #300
Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:07 PM - 111: Dec 12, 2020
19
Har ta sauka daga cikin napep din jinta take kamar a wata duniya ta daban. Tayi gaba yayi mata magana
"Hajiya kudin"
Jakarta ta bude, bata san nawa bace ta dauko ta miqa mishi, tayi juya ya sake cewa
"Ga canjin, ko kin barmun?"
Hannu tasa ta karba tana zuba su cikin jakar da ko zageta batayi ba. Ta sha jin kalmar tsiraici, ta dauka tasan ma'anar kalmar, a da ta dauka tsiraici shine ka rabu da tufafin jikin ka, sai yau ta fahimci akwai tsiraicin daya girmi rabuwa da tufafi. Akwai suttura da ba kaya bane kawai yake saka jinta a ranka, haduwa take da mutane a hanyar hostel din, musamman da ta shiga, sai ta tsinci kanta da jan mayafinta tana kara gyara shi, babu inda yake bude a jikinta, amman jinta take kamar bata saka komai ba, kamar kowa na ganin duk wani tsiraici da yake tare da ita.
A daddafe ta karasa dakin su, babu kowa sai Anisa da take zaune akan gadon Layla din, da yake nata saman na Layla ne, in ba lokacin baccinta yayi ba anan suke zaman su, wasu ranakun ma in tayi bacci Layla bata tashin ta. Yau ita batayi lakca ba sai karfe sha biyu na rana. Tana dawowa ruwa ta kara watsawa ta samu waje ta kame ta dauki waya tana dannawa, da yake taci abinci a restaurant, yayarta ta turo mata banner din Zahra Tabiu. Su kan siyi Donut dinta sosai, matar karshe ce, taje gidan Yayar tata ne ta samu Donut, duk a tunaninta na Zahra Tabiu ne, ko da ta fada mata ita tayi sam bata yarda ba, sai da ta kwana taga tayi a gabanta
"Inalillahi... Anty yaushe kika koya? Ina kika koya?"
Murmushi Antyn tayi
"Zahra Tabiu dince fa ta koya kwanaki, kin san nayi saving lambarta saboda siyen Donut, to shine naga tana talla zata koya yanda akeyi online, dubu biyar"
Ware idanuwa Anisa tayi, zatayi abubuwa da yawa da dubu biyar
"Kuma har kika iya haka?"
Tayi maganar cikin rashin yarda, dariya Antyn tayi mata
"Akwai videos haka, sosai ake ganewa, dan su Ammar sun fasa mun screen din waccen wayar dana nuna miki, kiyi joining in zata sakeyi"
Batayin ba ko da Anty ta turo mata, amman duk wani Donut da zata siya sai taji kamar bai kai na Zahra Tabiu ba, shine da safe da ta tashi taga Anty ta turo mata banner din, ta zabtare rabin kudin koyarwar daga dubu biyar zuwa dubu biyu da dari biyar. Gara dai ta koya ta huta, in ta koma gida ta dinga cin kudin Yayyenta, tana da kwalayen Donut Fairy data siya, in sun ce tayi musu order sai ta karbe kudin tayi a gida ta saka a kwalin, in sun cinye tabi ta kwashe. Lambar wayar take dubawa ko iri daya ce da wadda take da ita +234 806 515 6303. Ta gama dubawa kenan ta ga ita din dai ce, sai ga Layla ta shigo dakin kamar an korota. Kallo daya Anisa tayi mata tace
"Layla?"
Tana sauko da kafafuwanta daga kan gadon, tsaye Layla tayi bakin kofar, so take wani abu da zai nuna mata mafarki takeyi ya faru, kamar ace Anisa ta girgizata tana tashinta yanda ta saba da fadin
"Ke banza takwas saura"
A ranakun da suke komawa sallar asuba bayan sun makara. Amman kallon da Anisa takeyi mata ya tabbatar mata da cewa ba mafarki takeyi ba, idonta biyu. Ta dai kasa karasawa cikin dakin ne, kafafuwanta take ji sunyi wani irin sanyi. Ganin haka yasa Anisa ajiye wayar tana saukowa daga kan gadon tazo ta kamata
"Layla? Lafiya?"
Kai ta girgiza ma Anisa da ta kamata tana janta zuwa kan gadon, sai da ta zauna sannan jikinta ya fara bari
"Dan Allah menene? Me ya faru? Ko wani ne ya rasu?"
Anisa ta karasa muryarta na karyewa. Gabaki daya yanayin Layla ya gama daga mata hankali, ta san yanda mutuwa take, Yayanta ya taba rasuwa, ta kuma ga kalar hargitsin da kowa ya shiga, yanayin Layla ya nuna cewa tana cikin matsananci shock da ba labari bane me kyau yake haifarwa. Shisa gabaki daya hankalinta ya tashi
"Ki saka mun ruwa inyi wanka"
Layla ta fadi daga kasan makoshinta, watakila ruwa da sabulu su fitar mata da daudar da takeji, kila kuma idan ta saka ruwa a fuskarta zata farka. Babu musu Anisa ta tashi, sukan ajiye ruwan zafi a flask ko dan shan shayi, shi ta juye mata a bokiti tana sirkawa, da kanta ta kai mata komai bandaki ta dawo tana fadin
"Ki tashi ga ruwan can"
Mayafi kawai Layla ta cire, ko towel bata dauka ba ta fice daga dakin. Da yake sukan dibo ruwa da bokatan wankan nasu, da sun fito bandaki sukan saka omo su wanke shi har bayan. Shisa tasan ruwan ciki mai tsarkine, karkatawa tayi ta fara wanke hannayenta, a karo na farko da takejin sauqi irin na addinin musulunci, niyyarka a zuciya idan ka daurata tayi, ba saika fadeta a fili ba, bata da kwarin gwiwar motsa labbanta da daura niyyar wannan wankan da take tunanin ya zame mata dole. Tashin hankalinta bai fara ba sai da ta wanke fuskarta tana sake bude idanuwanta a cikin bandakin.
A daddafe ta karasa wankan, kayanta ta mayar tana fitowa, can ta baro bokitin, sai Anisa ce ta koma ta dauko, doguwar riga ta dauka