Showing 99001 words to 102000 words out of 150281 words

Chapter 34 - MARTABARMU HAUSA NOVELS LUBNA SUFYAN .txt

23 Nov 2025

3963

sha sai naga menene"

Dan murmushi Bilal yayi, shi me zai ma kaishi asibiti. Har yanzun duk yanda ake magana kan mental health bai shiga zuciyar shi ta yanda zai dauki kafafuwan shi yaje asibiti a kai ba.

"In shaa Allah. Lafiyata kalau da gaske, damuwa ce kuma kowa na tare da ita yanzun..."

Ya karasa da yar dariya dan ya saukaka musu yanayin daga shi har Rayyan din

"Zan zo karshen wata In shaa Allah... Zan zo in gan ka"

Kai Bilal yake girgizawa

"Kar ka baro hidimar ka nace maka lafiyata kalau Hamma"

Wayar Rayyan ya kashe a kunnen shi alamar ya rigada ya gama yanke hukuncin zuwa, babu kuma abinda zai sake hakan. Tun jiyan yake lissafa kwanakin da suka rage a cikin watan, yana ganin saura kwana tara, tabbas nauyin da kan shi yayi zai karu idan Rayyan da Abbu suka kasance waje daya yana ganin su a duk rana. Tunda yazo ya kasa bari idanuwan shi su shiga cikin na Abbu sam, ko hira mai tsayi ya kasa zama suyi, kullum cikin uzuri yake dan yabar dakin Abbu din. Ga Aisha yanzun da fada suke na rashin dalili, ko yau sai da sukayi kafin ya taho

"Damuwar ka na damuna duk da ban santa ba, amman baka mun adalci ka sani..."

Ta fadi tana tashi tabar shi a wajen, ya rasa yanda zai ya dinga bata hankalin shi kamar da, ko waya suke yakan shiga wani tunani sai taita magana bai san tanayi ba, haka idan suna chatting yakan manta ya ajiye wayar, wasu lokuttan sai ta kira sannan yake tunawa, banda hakuri babu abinda yake da shi da zai bata, amman yana bukatar duk wasu kalamai na hakuri da zai iya adanawa, saboda yanajin yanda shine kawai abinda ya rage a tsakanin shi da mutanen da suka fi kowa kusanci da shi.

*

Ganin karfe sha biyu saura yasa Mami sake tashi dan taje ta duba taga ko lafiyar Layla. Bataji motsin ta ba da asuba sai da ta tasheta, wajen tara na safe ma ta sake tashin ta dan ta karya. Tana tura dakin kuwa taga bacci takeyi, karasawa tayi tana dan bubbugata

"Layla..."

Mami ta kira a dan tsorace, dakyar Layla ta bude idanuwanta, da zazzabi ta kwana ga kasala, jikinta kamar ta aro takeji, da tana sallah da asuba sai takejin jiri na dibarta, raka'a ta biyu a zaune ta karasa ta dakyar

"Lafiyar ki kuwa?"

Mami ta tambaya tana taba jikin Layla da taji kamar wuta

"Subhanallah..."

Ta furta tana kama Layla ta dago ta

"Mami bani da lafiya"

Cewar Layla tana sake komawa ta kwanta saboda yanda take jinta, tana zazzabi kala-kala, amman wannan daban yake, tunda take a duniya bata taba jinta a irin yanayin da take jinta yanzun ba, ko dazun da Mami ta shigo ba bacci takeyi ba, maganar ce take mata wahala da ta fada mata bata da lafiya. Gabaki daya Mami ta gama rikicewa, tashi tayi tana wucewa ta dauko hijabi ta saka a jikinta tana dawowa dakin Layla da take jin wani sanyi na ratsa sassan jikinta, lokaci daya tunanin mutuwa na gifta mata, yana sakata jin ko dai ciwon ajali ne ya kamata

"Ko mutuwa zanyi Mami? Jikina baya mun dadi"

Zuciyarta Mami taji tayo wani tsalle tana dawowa makoshinta

"Wacce irin magana ce wannan? Jiba shirme"

Ta karasa tana daukar wayarta da take kan gadon Layla tana rasa waya kamata ta fara kira, Haris dai baya garin ma, sunje wani Seminar a Katsina. Idan ta kira Jabir da wahala yana kusa, lambar Bilal ta lalubo tana kiran shi, sai da tayi tunanin ba zai dauka ba sannan taji sallamar shi cikin kunnenta

"Dan Allah Bilal idan kana kusa kazo ka kaimu asibiti, Layla bata da lafiya..."

Da sauri ya amsa da

"Gani nan... Bari in shigo"

Sauke wayar tayi daga kunnenta tana mikewa, hijabi ta samo ta kama Layla ta dago ta tana saka mata, duk ta langabe a jikin Mami, ga amai da yake tukarta amman yaki fitowa, tunda asuba take jin shi. Gabaki daya sama-sama take ji, kamar rabinta a duniya rabinta a wani waje da bata san ina bane ba. Ko minti goma ba ayi ba sai ga Bilal din ya shigo bangaren Mami da sallamar shi, dan a kwance yake sanda kiran Mami ya shigo, da kamar ba zai daga ba, baisan me zaice mata ba, tunda ya dawo sau biyu ya ganta, yana duk kokarin shi wajen ganin basu hadu ba, sai dai Mami ba zata taba kiran shi babu wani dalili mai karfi ba.

Yana dagawa kuwa yaji dalilin ne mai karfi, motar su ta sami matsala tun shekaranjiya daya ajiyeta wajen gyara bai waiwayeta ba sam. Kuma yaji muryar Mami kamar hankalinta a tashe yake, shisa yana fitowa ya wuce dakin Ayya, a Kitchen ma ya sameta

"Bilal... Lafiya?"

Ayya ta tambaya, ganin yana balle maballan rigar shi kamar a hanya ya sakata

"Mukullin mota zaki bani Ayya, yanzun Mami ta kirani inzo in kaisu asibiti Layla bata da lafiya"

Wani irin kallo Ayya takeyi mishi, duk yaran Maryama din sai ta kira Bilal saboda gulma da neman dalili, Haris baya nan tasani tunda ko da safe sunyi waya. Amman Jabir aikin me yakeyi

"Ina Jabir? Sai kaine zaka kaisu asibiti? Ita ina motar hannun ta?"

Numfashi Bilal ya sauke

"Ayya dan Allah, tun da kikaga ta kirani watakila basa nan ne shisa"

Karamin tsaki Ayya taja

"Kinibibi ne dai da neman magana irin nata, sai kaje ka dauka yana kan drawer din gefen gado, in ka kaisu ka dawo mun da motata zan fita"

Wucewar yayi ya dauko, yanajin Ayya na fadin

"Kabi a hankali kaketa rawar jiki..."

Baiko juya ba harya fice ya na nufar dakin Mami. Aikam yanayin da ya ga Layla din ya daga mishi hankali

"Ki taso Mami"

Ya fadi, kama Layla tayi suna fitowa, sunzo harabar gidan dan ya dauki motar Ayya, sai ga Jabir ya shigo shima da motar Mami din da Ayya take magana a kai

"Bilal ga Jabir nan ma ya dawo, bari sai mu tafi kawai"

Kai ya jinjina mata

"Bari in maidawa Ayya mukullin dan zata fita sai in zo mu tafi"

Wannan karin kai Mami ta girgiza mishi, daman saboda tana tunanin idan ta tsaya jiran Jabir za'a bata lokaci shisa. Tasan halin Ayya, zata iya fadar maganganu idan Bilal din ya bisu asibiti, kwana biyu basuyi ba, bata neman tashin hankali

"Nasan muma ba jimawa zamuyi ba In shaa Allah...ka koma kawai dan Allah"

Dan juya zancen yayi, kafin ya jinjina kai

"In dai sun rike ku dan Allah a kirani"

Ya fadi yana rakasu har wajen motar, sai da yaga sun shiga har sun juya sannan ya koma ciki. Kai tsaye Aminu Kano Jabir ya nufa da su, in da ba'a bata lokaci ba, basu ma samu layi ba, Jabir ya sai musu kati, mutum daya aka gani sai su da suka shiga, Mami ta zaunar da Layla da take jin kamar zata shide akan kujera ita tana tsayawa, tambayoyi likitan ya fara yi kamar yanda sukan yi

"Tun yaushe kike zazzabin?"

Ya tambaya, dan jim Layla tayi, takan kwana da shi tun dawowar ta, amman baya damun ta, tun da sai ta farka ko fitsari taji shi, in ta samu ta koma bacci kuma da safe ya tafi, yaune kawai ya kwantar da ita haka, cikin rawar murya ta amsa shi

"Na kai sati, amman da dare ne kawai. Yaune har yanzun bai tafi ba"

Sosai yaci gaba da mata tambayoyi kala-kala, jin ance za ayi awon jini dana fitsari yasa Mami fadin

"Bata da aure fa"

Murmushi kawai likitan yayi

"Za'a duba komai ne Hajiya, babu wata matsala"

Haka kawai sai ta tsinci kanta da shiga damuwa, tare da Jabir sukaje aka dibi jini da su biyan kudi, zuwa duk wani abu da ake bukata suka dawo suka zauna suna jiran results din

"Ko zaki sha wani abu in siyo miki?"

Kai Layla ta jinjina

"Ka siyomun Sprite"

Da mamaki Jabir yake kallonta

"Yaushe kika fara shan sprite?"

A shagwabe ta kalli Mami

"Ka wuce ka siyo mata bata da lafiya karku sakani surutu"

Dan tasan halin Jabir baya gajiya da tsokanarta, kawai dan yaga tana mitarta da kai kara. Wucewar yayi, bai jima ba ya dawo. Mami yasan ba sha zatayi ba, ruwa ya siyo mata, shi ya siyowa kan shi coke. Suna zaune aka ce musu result din ya fito

"Mami kiji me zaice, jiri nakeji Allah"

Kai Mami ta daga mata, nan ta ajiye robar ruwan da ta fasa ta dan sha, sai Layla take jin ta dan samu, ba kamar sanda suka fito daga gida ba, har ranta ta dauka ciwon ajaline ya kamata. Zaune sukayi abinsu ita da Jabir yana mata hirar wani film da suke kalla su dukan su mai suna Blind spot

"Hamma banyi nisa ba, kabarni, bana son jin me zai faru..."

Dariya yayi, ya bude baki yayi magana ya hango Mami, yanayin ta na saka shi mayar da bakin shi ya rufe, saboda a hargitse take, a hargitse kuma ta karaso inda suke

"Ki bude bakin ki Layla, ki fadamun karyane, ki ce mun likitoci da kan su nayin kuskure, na'urar su na samun tangarda..."

Cike da rashin fahimta suke kallon Mami da take magana kamar ta sami tabin hankali

"Mami..."

Jabir ya fara magana Mamin ta katse shi ta hanyar daga mishi hannu, idanuwanta kafe suke cikin na Layla

"Ki tashi muje ki fada mishi ke din budurwa ce, ki kalli idanuwan shi ki fada mishi babu yanda za ayi ki samu ciki!"

Wannan karin har mutanen da suke wajen sai da hankulan su ya tattaru ya dawo kan su, robar lemon da take hannun Jabir tana subuce mishi

"Ciki? Mami ciki? Bashi da hankali? Wanne irin ciki kuma?"

Layla tun daga kalmar "ciki" komai ya daina karasawa kwakwalwar ta, in dai ciki likita ya gano mata tasan inda ta same shi, in dai da gaske akwai wani abu a cikin ta tasan ya akayi, ba karya yayi ba, na'urar su bata da matsalar komai, kwakwalwar ta ce ta samu tangarda, tunaninta ne ya yaudareta da alamomin duk da ta dinga gani amman ta kasa fahimta, ba infection bane ya dauke mata al'ada, shigar cikine.

"Layla..."

Mami tayi maganar tana girgizata cikin yanayin da ya sata daga ido ta kalli Mami din

"Ciki Mami... Ciki ne da ni"

Ta karasa cikin wata irin murya da yasa wani abu kullewa a cikin Jabir, yaune ya fara sanin tashin hankalin, Mami kuma da ta yanke jiki ta fadi tana kara mishi wani sabon tashin hankalin, ya sha ganin yanda duniya take birkicewa mutane a fina-finai. Yau a gaske yake ganin yanda duniyar ta karkata ta juya da shi a ciki, kamar film haka wani gefe na kwakwalwar shi yake daukar hoton komai, kafin ya tsugunna a kasa cikin lemon daya zubar yana kama Mami, magana yake amman sautin muryar shi baya fita saboda tashin hankali.

Cikin Nurses din wajen ne wasu suka rugo dan su taimaka mishi, har aka dauke Mami yana tsugunne a wajen, Layla na zaune ko motsi ta kasa, tun tasowar shi duk wata damuwa tashi kafin Mami ta sani Abbu ya sani, ya saba abu koya kai ko bai kai ba ya nemi Abbu, shine babban abokin da yake da shi saboda mutum ne shi da yarda da mutane takewa wahala, shisa yanzun ma wayar shi ya laluba yana kiran Abbu

"Abbu kazo Aminu Kano, Layla bata da lafiya"

Ya iya fadi saboda kirjin shi da yayi nauyi, bayason fadama Abbu cewar Mami ta yanke jiki ta fadi, baima ji me Abbu yake fadi ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana sakata a aljihun shi. Yana wani irin sauke numfashi yake kallon Layla

"Ciki gare ki Layla?"

Ya bukata yanajin maganar ta fito mishi kamar da wani irin yare, saboda kalamai ne da baisan yanda za ayi ace sun gifta tsakanin shi da kanwar shi ba, tsakanin shi da Layla, sai da ta dago kanta tana kallon idanuwan shi da suke rokonta da ta karyata maganar, ko da ta zamana da gaskene ta saukaka mishi tashin hankalin da yake ciki ta karyata. Amman bata san ta inda zata fara ba itama, ta dauka ta gama fahimtar menene shock, sai yau tasan da gaske komai zai iya tsaya maka cak, ciki harda emotions dinka

"Ciki ne da ni Hamma"

Ta karasa maganar da dariyar da batasan ta inda ta fito ba, duk da kuwa tana jin idanuwanta cike suke taf da hawaye

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Jabir ya furta yana zama a kasa, cikin asibiti, batare daya damu da cewa cikin lemar lemon daya zube bane, balle kuma ya damu da cewa fararen kayane a jikin shi. Tarin tashin hankalin daya kunno musu yake hasasowa, MARTABAR SU da ta samu gurbata ta fannonin da ba zasu misaltu ba ke mishi yawo, rayuwar kanwar shi da ta canza har mutuwarta yake dubawa.

*

Littafina na siyarwa ne akan naira #300

Account details
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank

Whatsapp Number: 08074545149 (Domin tura shaidar biya)
1/30/21, 8:09 PM - 111: Dec 26, 2020.

24

Can nesa Layla take jin duk wata magana da sukeyi, ba zata ce ga abinda ya dinga faruwa ba, daga asibiti, zuwan Abbu, dawowar su gida, banda sautin kukan Mami babu abinda take ji, dan yanzun haka da suke a tsakar gidan ta samu wajene ta zauna a kasa, gefen Mami da ta kasa shiga daki ta durkushe a wajen. Kuka takeyi kamar ranta zai fita, dan har yanzun ta rasa ta inda zata fara yiwa Abbu bayani, sanda yazo asibitin ta farfado, dan haka suka dawo gida, ita da shi a mota daya, sai Jabir daya kama hannun Layla yana sakata a motar da suka zo suka taho.

"Wai dan Allah wani a cikin ku ya bude baki yayi mun magana, tun dazun na tambaye ku abinda ya faru"

Abbu yake maganar da wani yanayi a muryar shi, hankalin shi a tashe ya same su asibiti, sai dai lokacin harma sun fito, tun daga can kuma Mami take kuka, sau daya ya tambayeta abinda ya faru, da bata amsa ba sai yayi shiru saboda bayason su fada mishi abinda zai saka shi kasa yin tuqin su iso gida.

"Layla me ya faru? Wani abin suka ce ya same ki?"

Ya karasa tambayar yana kallon Layla da ta dago idanuwanta tana saka su cikin na shi, bata san me zata ce mishi ba, saboda har yanzun wani irin shiru take ji cikin kanta. Kafin jikinta gabaki daya ya dauki bari, zuciyarta na soma dokawa, girman abinda yake faruwa da ita yana danneta, so take ta bude bakinta, ba ta dan ta bawa Abbu amsa ba, sai dan ta kira sunan Allah, ta furta kalmar

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Ko zata samu sauki, ko Allah zai kawo mata dauki abinda yake faruwa ya zama mafarki, amman ta kasa, Abbu kallon shi ya mayar kan Jabir da karo na farko a duniya yake son kasancewa ko ma ina ne da cikin gidan, banda fuskantar abin nan da yake faruwa da su

"Abbu karka tambayeni, dan Allah karka sa in fara fada maka"

Ya karasa maganar muryar shi na karyewa, zuciyar shi zafi takeyi, so yake yabar wajen, amman ya kasa, ba kukan Mami bane baya ci mishi rai, tunanin halin da Abbu zai shiga ne yake hautsina mishi lissafi.

"Ciki gare ta, cikine a jikin Layla... Ahmadi ciki"

Mami ta karasa tana jin kamar ana zare mata rai, ya kusan mintina biyu maganganunta na yawata mishi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su, so yake ya ga shin shi kadai ne yake ganin wani duhu-duhu ko kuma garin ne gabaki daya ranar da ake kwallawa ta lumshe, amman da ya bude wannan karin ma duhun ya sake gani, kamar a cikin duhun wani abu na jujjuya mishi. Ba dan Bilal daya fito daga bangaren Ayya da kofi a hannun shi ba, ya hango su ya fara karasowa in da yake ganin kamar Abbu na shirin faduwa, yanayin da ya saka shi yin jifa da kofin zobon da yake rike da shi ya karasa ya tallafe shi yana taimaka mishi ya tsaya kan kafafuwan shi, tabbas da zancen ya bambanta

"Subhanallah, Abbu..."

Bilal ya kira zuciyar shi na wani tsalle cike da tashin hankali, Abbu kuwa kafadar Bilal ya dafa yana samu ya tsugunna saboda kafafuwan shi da suke rawa, kokawa yake da numfashin shi saboda tashin hankali, baiga ta yanda Mami zata ce mishi Layla na dauke da ciki ba. Kirjin shi na zafi yake kallon Mami

"Maryama ki fadamun abinda zuciyata zata iya dauka... Dan girman Allah, rokon ki nakeyi"

Hannu ta saka tana share hawayen da suke sake zubo mata, ta bude bakinta yafi sau biyar tana rasa kalaman fadi, haka kawai Bilal ya tsinci kan shi da shiga tashin hankali, bai san me yake faruwa ba, amman zuciyar shi duk ta gama birkicewa, hannun shi yaji Abbu ya kamo

"Bilal kaji me tace? Wai Layla ce take dauke da ciki, yata Bilal, yarinyata, amana ta"

Runtsa idanuwan shi Bilal yayi, ya bude su a cikin na Layla da take kallon shi, duniyar na karasa hautsine musu a lokaci daya. Kai ta girgiza mishi a hankali tana neman hawayen da zasu sama mata sauki ko yayane. Amman ta rasa su, sunki fitowa. Tsaye Bilal yake a waje daya, amman duniyar duka juyawa takeyi da shi, kamar wanda aka dauka ana zagayen cikar shekara haka yake jin shi, so yake wani ya taba shi ko zai daina jujjuyawa haka, kamar an amsa rokon shi yaji hannuwan Ayya akan kafadar shi, hannun da yake da yakinin zai gane shi a cikin dubban hannaye.

Hannun daya kama nashi a lokacin daya rasa kowa, hannun daya taimaka mishi tun kafin ya budi bakin rokon hakan. Ayyar shi, juyawa yayi yana ganin damuwar da take kan fuskarta

"Ayya"

Ya kira da wani yanayi da ya sata fadin

"Menene? Me akayi maka? Me akace kayi?"

Saboda ta san yaranta, tasan Bilal ba zai hargitse haka ba idan ba wani laifin akace yayi ba, ganin yana kallonta kamar duniyar shi na shirin zuwa karshe ya sa Ayya kallon su Abbu sa suma a hargitsen suke, ba zatace ga abinda ya fito da ita ba, zuciyarta ce taki samun natsuwa sam. Ashe yaranta aka saka a gaba haka shisa hankalinta yaki kwanciya

"Me yayi muku?"

Ta watsa tambayar, tana saka Mami share hawaye kafin ta kalli Ayya

"Ba shi bane ba, Rayyan ne"

Ta amsa muryarta na fitowa a dakushe, yanayin da yasa Abbu fadin

"Maryama!"

Juyawa tayi ta kalle shi

"Karka ce mun baka san in har cikine a jikin Layla to na Rayyan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login